THREE BROTHERS Complete Hausa Novels By Bil-Fauzee U-Adyan.txt

Author :  Bil-Fauzee U-Adyan Category :  Hausa Novels 001

Chapter   1 / 48

1 to 3K   out of 142.8K words

Compil By Umar Dalha Funtua.

Copies By Bil-Fauzee.

[12/18/2021, 8:47 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑

*_TREE BROTHER'S_*

👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑

*Page one*


*To Alhamdulallah ala kalli halin ina mai ara yiwa Allah ubangiji godiya, mai kowa mai komai wanda cikin ikon sa ne da buwayarsa ya sake bani damar dawowa gareku, tare da wani sabon littafina mai taken suna TREE BROTHER'S ina mai addu'ar yanda na fara lafiya Allah ya bani damar kammala lafiya Allahumma Amin.*

*Sadaukarwa*

*Na sadaukar da wannan littafin wa kai ne, hakama wannan k'irkiranran labari ne dan haka ba zan iya yafe wa duk wanda yayi k'oqarin canjamin labari ba. Dan haka a kiyaye sannan kuma dan Allah in kinsan ba zaki yi comment ba to dan Allah karki karanta please na gode.*


✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/



*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.


*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*


Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.



Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.



*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*Saturday 18/12/2021*

*Time 01:55pm*

*Typing................*

*SHINFID'A*

Zaune take sai wani hargitse fuska take kallo d'aya tak zaka yi mata ka fahimci cewar ba qalau take ba. Bugun ƙofar da a kai ne yasa ta tashi ta nufi ƙofa dan ganin waye, tafiya take sannu a hankali tamkar wacce kwai ya fashewa a ciki, ta isa ga ƙofar tare da bud'ewa ta samu mai gidanta tsaye a ƙofa tayi murmushi sosai tare da furta masa kalmar sannu da zuwa, ya amsa yana wani lallausan murmushi ya janyota jikin sa sun shiga ciki sai wani kallonta yake kallo sosai, ya gama fahimtar cewa ba qlau take ba, nan kuwa ya shiga tambayar ta abin da yake faruwa da ita.

"Rabin raina qlau kike kuwa fad'a min mai yake damunki dan Allah.?" Tayi shiru kad'an sannan ta amsa shi, "ba komai Prof zaka iya yarda da ni." Ya girgiza ka tare dajan numfashi yana cewa, "Aisha shin baki shirya sanar dani gaskiyar ba ko a'a kawai kin za'bi da ki cutar da ni ta wannan hanyar fad'a min.?" Magana yake yayin da yake ri e da fuskar ta sai wani kallonta yake kallo sosai, ita ma haka kallonsa take kuma kallo sosai ta nisa tare dajan numfashi cikin tautasa murya tare da kwantar da ita take magana. "Ba komai Prof kawai ciki na ne yake yi mun ciwo amma ba wani sosai ba zan iya jure zafin to ba buqatar ka damu sosai ka ji ko."

Da sauri ya kai kallonsa ga cikin ta tare da d'ora hanunsa yana shafar cikin, ya qara da sunbata sannan ya mai da kallonsa gareta cikin rawar murya har yana sarkewa yake magana. "Aisha ya kamata mu tafi asibiti a duba ki sabo da ba zanso wannan yanayin naki ya cutar da yaronmu ba, ke kin san irin yanda nake matuqar masifar qaunar yarona to sam ba zan jure ganin wani abu ya cutar da shi ba to mu tafi." "Prof zafin fa kad'an ne zan iya jure wa to sam ba buqatar sai mun tafi asibiti dan Allah." "Aisha ni saidai kawai na baki hak'uri amma dole sai mun tafi asibiti yanzu." Sam bata da wani za'bi wanda wannan dalilin ne yasa ta amsa masa da to ta tashi sun fita zuwa asibiti.

Sun isa asibiti kai tsaye office d'in Dr Mas'ud ya nufa, yayi nasaran samunsa amma kuma yana duba wani sun jira na wani lokaci sannan suka shiga ciki. Bayan sun gaisa Prof Abas ya sanar da shi abin da yake tafe dasu Dr Mas'ud ya mai da kallonsa ga Aisha yana cewa, "tin yaushe hakan yake faruwa dake.?" "Kwana biyu." "watan nin cikin ki nawa.?" "Wata shida ne." Ya jinjina ka yana nazari daga bisani yaci gaba yana cewa, "ok yanzu zan baki Scan ya kamata na san lafiyar Babyn sannan sai nasan wane magani zan iya baki." Ta jinjina masa ka a lamar to nan ya basu takardar Scan sun tashi sun fice, wanda kuma kai tsaye gurin Scan suka nufa ba wani d'aukan lokaci suka gama, sun koma gurin Dr Mas'ud sun kai masa ya duba yayi murmushi sosai yana cewa.

"Prof da akwai yuwar madam ta aifa maka twin's insha Allah." Yayi wani gajeran murmushi kad'an sannan ya amsa shi, "Dr Mas'ud kenan to ai Allah ne kawai ya san karatun karma Allah dai ya sauketa lafiya." Ya amsa da Amin yana murmushi cikin harshen turanci suke magana wanda wannan dalilin ne yasa Aisha bata iya fahimtar duk abin da suke fad'a ba, kasancewar ita bata yi makaranta ba sam bata jin turanci. Ya rubuta mata magani ya baiwa Prof takardar ya kar'ba tare dayi masa godiya sannan suka tashi suka fice zuwa gida, ya fara siya mata magani sannan suka isa gida sun shiga ciki ya zaunar da ita shi kuma ya tafi ya d'auko ruwa ya shiga bata magani. Bayan ta sha magani tayi masa godiya ya amsa da ba komai yaci gaba yana cewa.

"Aisha ina fatan baki manta duk wani alkawarin da yake atsakaninmu ba? Ina nufin ni na fad'a maki cewar d'a d'aya kawai nake so mu aifa, sannan kuma ke kin yi man alkawarin cewar d'a ďaya kawai zaki bani to ina fatan baki manta wannan ba.?" Tayi shiru kad'an sannan ta amsa shi, "eh Prof ni ban manta alkawarin da nayi maka ba kuma zan cika alkawari na insha Allah to zaka iya yarda da ni ka ji ko." Yayi murmushi sosai mai tare da ar dariya ya shafi fuskarta tare da sunbatarta yana cewa, "na gode sosai da kika amince da buqata na ina godiya sosai." Ta girgiza masa ka tare da furta masa kalmar, "sam ba buqatar ka gode min sabo ni nayi abin daya dace ne, amma Prof to idan kuma Allah ya bamu tagwaye fa shin ka shirya amsar yaran kuwa.?"

Wani irin kallo yake yi mata wanda ya gagara furta mata komai yayi shiru na wani lokaci sosai sannan ya amsa ta, "Aisha ni d'a d'aya kawai nake buqata daga gareki kuma na muji ba mace ba, dan haka karki yarda kiyi kuskuran aifa min yara biyu ko da kuwa sun kasance dukansu maza ne, ni kawai yaro ďaya nake buqata daga gareki kuma shi zaki bani to karki ta'ba mantawa da wannan kinji ko." Magana yake cikin fishi sosai yana kai arshen maganar sa ya tashi yayi tafiyarsa bedroom, Aisha ta bisa da kallo har ya shige yayin da mamakin sa da tsoron sa suka yi yawan gaske a tare da ita sosai. "Na shiga uku na ni Aisha wane irin muji na aura ne haka? Shi kawai d'a d'aya yake buqatar na aifa sannan kuma na muji yake so ba mace ba, ga shi kuma a can gurin awo an fad'a min cewar da akwai yuwar na iya aifan tagwaye, to ya zanyi kenan mai zai faru dani ko yarana idan na aifi tagwaye ni ba zan iya d'aukar hukuncin sa ba sabo da zai iya raba ni da d'ayan yarona ko yarinyata. A'a ni sam ba zan iya jure wannan ba lallai ya kamata nayi wani abu a game da wannan to mai zanyi kenan? Ya Allah ka taimaken ka aiko man da mafuta Allahumma Amin."

Magana take cikin wani irin yanayi mara dad'i yayin da unci da damuwa suka yi yawan gaske a tare da ita sosai. Bata ankara ba ta fara zubar da kwalla mai tsananin zafi da una sosai, to zamu iya kiran abin da kukan zuci wanda yafi na zahiri ciwo sosai. Ta tashi jiki a san yaye ta nufi bedroom d'in Abas ta shiga ciki tare da kyakkyawar sallama ya amsa ba tare daya kalleta ba, wanda hakan ne ya tabbatar mata da cewar yana fishi da ita kuma fishi sosai. Ta nisa sosai tare dajan numfashi sannu a hankali take tafiya har ta isa inda yake ya zauna kusa da shi kusa sosai, sai wani kallonsa take kallo sosai ta kai hanunta ga nasa ta shafi hanun tana murzawa cikin kasa-kasa da murya tare da kwantar da ita take magana.

"Kayi hak'uri ka yafemin dan Allah karka yi fishi da ni sabo da hakan zai yi matuqar cutar da ni sosai, mujina ni kawai tambayar ka nayi bawai dan na cutar da kai ba, ka sani ni kawai zanyi duk abin da kake so ne kamar dai yanda nayi alkawari to zaka iya yarda da ni dan Allah." Magana take cikin wani irin yanayi tamkar da zata yi masa kuka ya d'ago fuskarsa wanda kuma sai zuwa wannan lokacin ne ya iya kallonta sai wani kallonta yake kallo sosai, lokaci d'aya kuma ya shiga share mata kwalla yana girgiza mata ka a lamar a'a, "ki dena wannan kukan bana so sannan kuma sam bana san ki koma tambaya na irin haka kawai dai kiyi k'oqarin cika alkawarin ki kinji ko."

Ta jinjina masa ka a lamar to tana wani gajeran murmushi shi ma abin da yake yi kenan, ya shafi fuskarta tare da sunbatarta ya qara da furta mata kalmar ina sanki ta amsa shi da ina qaunarka. Ya d'ora kansa a kan cinyarta yana wani shafar cikin ta ya qara da sunbata yana furta kalmar, "I LUV U my Child I Love you so much." Ya fad'a tare da qara sunbatarta a ciki ta nisa sosai tare dajan numfashi tana mai sauke a jiyar zuciya yayin da take magana da zuciyarta. "Ya Ubangiji bani da wani za'bi a kan abin da mujina yake so, ban sani ba ko zan iya ba shi abin da yake so ko a'a duk da cewar ni nayi masa alkawari. Ya Allah ka bani ikon cika masa alkawarin da ni nayi masa na aifa masa d'a d'aya kamar yanda yake fata da kuma buri, ya Ubangiji idan ka bani d'a biyu ina nufin tagwaye ko kuma yarinya mace to ban san ya zanyi ba ya Ubangiji ba zan iya jure ganin mujina yana cutar da d'ayan yarona ba ko kuma yarinya ta, ya Allah karka yi man jarabawar da ba zan iya d'auka ba Allah ka aiko man da mafuta Allahumma Amin."

Maganar zuci take yayin da idanuwanta suke zubar da kwalla mai tsananin zafi da una sosai, kuma zamu iya kiran abin da kukan zuci wanda yafi na zahiri ciwo. Hawayen fuskarta sun zuba a kan fuskar sa da take kwance a kan cinyarta da sauri ya d'ago fuskarsa yana kallonta, kallo sosai mai cike dajin mamakin ta cikin rawar murya har yana sarkewa yake tambayar ta abin da yake faruwa da ita. "Aisha mai yake faruwa dake ne fad'a min wani abu mai ya saka kike kuka kuma gaskiyar zaki fad'a min dan Allah.?" Tayi shiru kad'an sannan ta amsa shi, "ba komai Prof ni kawai na tina da Abbana ne shi yasa nake zubar da kwalla, Prof ni ina matuqar qaunar Abba na sosai amma kuma hakan bai hana shi mutuwa ba ni nayi kewarsa sosai." Ya tashi zaune cikin dajin tausayin ta ya shiga share mata kwalla yana rarrashin ta tare da bata magana, bayan wani lokaci suka tashi suka nufi tebur domin suci abinci sunci abinci cikin kyakkyawan yanayi, bayan sun qarasa ya d'auke ta zuwa gidan Ummarta domin ya kwantar mata da hankali wanda ya d'auke ta har dare sannan ta koma gida.

Tin daga lokacin da Aisha ta fahimci yanda mujin ta ya tsani ta aifa masa tagwaye ko mace hankalin ta ya tashi sosai, domin kuwa Allah ne kawai ya san kwanan makaho cikin ne kawai a tare da ita amma bata da sani a kan abin da zata aifa. Tinanin hakan ne yasa duk ta fita haiyacinta yayin da tinani da damuwa suka yi yawan gaske a tare da ita sosai, Prof sai aikin tambayar ta yake mai yake damunta hakama Ummarta amma amsa ďaya take basu ita ce ba komai. Haka dai Prof yaci gaba da tarairayarta yana wani lalla'bata tare da bata cikakkiyar kulawa sosai har zuwa lokacin da cikin ta ya shiga watan aihuwa, duk da cewar qlau take amma kuma Prof ya buqaci da a yi mata C. S.

Ya tafi wata kyakkyawar asibiti ta kud'i ya biya anyi shirin komai tare da saka musu ranar kwana biyu, Aisha dai biye kawai take da shi ba tare da ta san a salin gaskiyar abin da yake faruwa ba, har a kayi komai a ka gama sai ma bayan sun dawo gida ne take tambayar sa. "Prof wai mai yake faruwa da ni fad'a min wani abu shin ina da wata matsala ne dan Allah ka sanar da ni ka ji.?" Yayi murmushi sosai mai tare da ar dariya cikin kyakkyawan yanayi yake magana. "Karki wani damu rabin raina kina lafiya sam ba wata damuwa ko matsala a tare dake, Aisha ni kawai ina nai ma maki sauki ne ta yanda ke da kuma yarona ba zaku wahala ko cutuwa ba, shi yasa ni nake duka wannan Aisha zuwa jibi za a yi maki C. S a ciro yaronmu to kiyi farin ciki sabo da yaronmu ya kusa zuwa garemu insha Allah." Wani irin kallo take yi masa mai cike dajin mamakin sa sosai cike da firgici da rud'ani take magana.

"Prof wai mai kake fad'a ne haka mai ya saka za a yi man C. S bayan kuma zan iya aihuwa da kai na? Gaskiya ni bana san C. S sabo da ina jin tsoro sosai to dan Allah karka tilassa man na ro e ka. Nayi alkawari zan baka abin da ka buqata daga gareni kuma zan cika alkawari na insha Allah to zaka iya yarda da." Magana take cikin wani irin yanayi wanda ban san ta yanda zan iya sanar daku shi ba yayin da damuwa tayi yawan gaske a tare da ita sosai. Ba kuka take ba amma kuma idanuwanta kwalla suke zubar wa mai tsananin zafi da una sosai, hakama zamu iya kiran abin da kukan zuci wanda yafi na zahiri ciwo, shi kuwa sai wani kallonta yake kallo sosai cikin tautasa murya tare da kwantar da ita yake magana.

"Aisha ni bani da niyar cutar da ke to balantana kuma yarona eh na sani na kuma yarda da cewar ke zaki cika alkawarin ki, zaki bani d'a d'aya kamar dai yanda na buqata daga gareki to amma ina san ke da kuma yarona ku kasance cikin k'oshin lafiya sosai, wanda wannan dalilin ne yasa na buqaci da a yi maki C. S to ya kamata ki fahimce ni sannan kuma ki yarda da ni please." Shiru bata amsa ba haka ya shiga rarrashinta yana lalla'bata tare da bata magana, cikin hikima da nuna kulawa yake yi mata magana tare da nuna soyayyar sa a gareta. A zahirin gaskiya tana matuqar qaunar mujin ta sosai wannan yasa take yin duk abin da yake so, sam bata da wani za'bi wanda wannan dalilin ne yasa ta amince da buqatar sa ta a yi mata C. S yayi matuqar farin ciki sosai da hakan sai godiya yake yi mata ya qara da yin hugging d'in ta yana sunbatarta, yayin da bakinsa yake ta furta mata lafuzza masu tsananin dad'in sauraro hakan ya saka ta farin ciki sosai bayan kwana biyu.................




*BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.*
[12/19/2021, 8:32 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑

*TREE BROTHER'S*

👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑

*Page two*

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.


*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*


Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.



Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.



*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*Sunday 19/12/2021*

*Time 01:06pm*

*Typing..............*

Misalin ƙarfe 10:00am a ka shiga da Aisha d'akin tiyata Umma na daga gefe zaune zaman jiran tsammani,

1 / 48