THREE BROTHERS Complete Hausa Novels By Bil-Fauzee U-Adyan.txt

Author :  Bil-Fauzee U-Adyan Category :  Hausa Novels 001

Chapter   29 / 48

84K to 87K   out of 142.8K words

sauke ni a k'aramin hotel." Ya amsa da to sun tafi ya sauka a hotel wanda ya d'auke sa, na tsayin kwana ki yana aikin nai man Mummyn sa inda daga k'arshe yayi nasara.

Bayan tsayin kwana kin daya d'auka a hotel yayi nasaran gane gidan da matuqar Mummyn sa take, hakan tasa ya bar hotel ya nufi gidan da Mummyn sa take wani yammaci. Zaune suke a nan cikin harabar gate sai gasu Farha sun isa inda take, kamar dai kullum sun shiga tsokanar ta da teady abin da take gani a matsayin ďan ta. Sun tashi sun gudu suna dariyar ta ita ma tashi tayi ta bisu a baya tana fad'a musu cewar, "ku bani d'ana yana kuka sosai dan Allah ku bani yarona." Magana take yayin da take kuka kuma kuka sosai yayin dasu kuma suke dariyar ta, Maman ta sai binta take tana fad'ar sunan ta tana cikin tafiya lokaci d'aya taji ta fad'a cikin ruwa, ihun ta ya k'aru sosai su Farha kuwa sai dariyar ta suke sosai. Lokacin yayi daidai da shigowar *Adeel* cike da firgici ya cillar da jakar sa, ya nufi gurin ta da gudu ya fad'a ruwa tare da kamata ya d'ago fuskar ta sama, yaci gaba da tafiya har ya isa bakin gab'a ya fito da ita sannan ya fito.

Wanda zuwa wannan lokacin ta suma *Adeel* ya shiga danna cikin ta ruwa na fita, yayin da yake fad'ar sunan ta amma bata farka ba ya shiga buga fuskarta, yana murza k'afafun ta amsa bata yi wani yunk'urin farkawa ba. Cike da fishin zuciya ya tashi ya nufi gurin su Farha inda ya rufe su da duka, duka yake musu sosai duk da kasancewar su yara sai da Umma ta kwace su hanun sa. Ya juya da sauri har yana gudu ya koma gurin Aisha wacce take kwance, ya wani rungumata jikin sa yana fad'ar sunan ta yayin da yake kuka kuma kuka sosai. Umma sai wani kallonsa take kallo mai cike da jin mamakin sa cikin tautasa murya take magana. "Yaro waye kai mai yasa kake kiran 'yata da Mummy? Na gode ma daka taimaki 'yata amma banso kayi duka wasu Farha ba, sabo da hakan zai yi matuqar cutar damu sosai ban kuma san ya zanyi ba." Magana take cikin wani irin mummunan yanayi yayin da idanuwan ta suke zubar da kwalla, mai tsananin zafi da k'una sosai wanda zamu iya kiran abin da kukan zuci wanda yafi na zahiri ciwo, cike da k'unci bak'in ciki b'acin rai tare da tarin damuwa yake magana. "Kaka *Adeel* ne ya dawo gareku sannan kuma sam bana nadamar abin dana aikata wa yaran, sabo da sun cancanci fiye da haka daga gareni nayi tunanin cewa wannan kawai a mafarki ne, amma yau gaskiyar ta bai yana cewa hakan yana yawan faruwa da ita. Kaka sam bai kamata a ce hakan ta faru da ita ba yanzu fad'a min ina zai kai ta, sabo da ya kamata ta bar nan gurin yana da sanyi sosai to zai iya cutar da ita."

*"Adeel* kai ne bayan shekaru ashirin yau ka dawo garemu? Gaskiya ina farin ciki sosai zo nan ďana." Cike da d'auki ta wani rungumasa jikin ta sai wani shafar sa take tana sunbatarsa, lokaci d'aya kuma ta saki kuka shi ma abin da yake yi kenan, bayan wani lokaci ya d'auki Mummyn sa suka nufi ciki ya shinfid'eta, a kan wata shamamar katifa mai kama da tabarma ya mai da kallonsa ga Umma tare da fad'ar sunan ta. "Kaka shin zaki iya sanar da ni komai a game da Mummy na dan Allah.?" Tayi shiru na jim kad'an sannan ta shiga sanar da shi abin daya buqata, *"Adeel* Mummyn ka tin bayan data aife ka take fama da wannan rashin lafiyar, wanda kuma Dadyn ka ne yake da alhakin duka wannan ya kuma taka muhimmiyar rawa sosai, a game da wannan rashin lafiyar ni ina jin kamar ba zan iya yafe masa ba. *Adeel* a daidai gab'ar daya kamata ya taimake ta ne ya tsinke duk wata halak'a da take tsakanin su, haka ya kalli tsabar cikin idanuwana sannan ya fad'a min cewar ya sake ta, a lokacin da nake rok'onsa a kan ya kai ta asibiti sai fad'a min yayi cewar 'yata mahaukaciya ce bata da wani anfani. Sannan kuma ya d'auke ka daga gareta hakan ya k'ara wa ciwan ta girma sosai, *Adeel* sai da a ka kai fagen ba zan iya biyan kud'in haya ba ga kuma siyan maganin ta."

*"Adeel* nayi aiki gidaje da dama sabo da na samu na kula da 'yata musamman abinci da magani, kuma babu wani wanda ya taimaka min sabo Kakan ka ya mutu na aurar da Aisha ga Dadyn ka, duk da cewar tana da k'ananan shekaru a tunani na shi zai kula da ita sosai, kamar dai yanda yayi min alkawari amma ina kawai yaudarar mu yayi, ya kuma yi anfani da takaicin mu a kanmu ba tare daya tausaya ba. *Adeel* da k'yar na iya samun aiki a gidan nan ina musu wanke-wanke da shara, suna bamu abinci bayan ko wane wasa suna bani dubu biyar dasu ne nake samu ina siya mata magani, yanayin ta ya tsananta ne sabo da maganin ya k'are kuma ba a yi min biya ba. To yanzu kuma ban san mai zai faru ba da kai ka daki yaran ina jin tsoro karsu ce mu bar nan, duk da cewar ko yaushe suna tsokanar ta amma sam ba zanso mu bar nan ba, sabo da bamu da wani gurin da zamu tafi *Adeel* shin ko zamu iya tafiya mu bawa yaran hak'uri dan Allah.?"

"Hak'iqa Dady mugun mutum ne sosai shi yayi matuqar cutar da Mummy na da kuma ke, nima haka yayi ta cutar da ni ta hanyar saka min tsanar Mummy a raina dama zuciyata, nayi zurfi sosai gurin k'yayyar Mummy na amma Allah cikin ikon sa sai ya had'a ni da aboki na gari, *Adnan* shi ne wanda ya sanar da ni a salin gaskiyar wacece mahaifiya. Da kuma yanda zan san addini na domin samun kyakkyawar rayuwa, daga bisani kuma na had'u da *Amna* ita ta taimaka sosai a game da rayuwata. Yayin da Dady yake ta fama da Campany da kuma kasuwancin sa, ya b'oye min gaba d'aya gaskiya a game da Mummy na domin ya fad'a min cewar ta mutu, ko photon ta bai ta'ba nuna min ba amma kuma daga k'arshe na gano a salin gaskiyar. Kaka kiyi hak'uri da ban taimake ki a kan komai ba amma yanzu ni ne wanda zai ci gaba, Kaka ni zan d'auki d'awainiyar kuma zamu bar duk da cewar bani da ishashshan kud'i sosai, amma kuma hakan ba zai dakatar da ni ba zanyi iya abin da zan iya. Daga k'arshe kuma Mummy na zata samu cikakkiyar lafiya sosai insha Allah yanzu ki bani takardar maganin ta."

*"Adeel* hakan zai yi matuqar cutar da lafiyar ka sosai to kawai ka barni naci gaba ka ji ko." "Kaka ni qlau nake to dan Allah karki dakatar da ni please ki bani takardar na tafi." Ta jinjina masa ka tare da yin hugging d'in sa tana sunbatarsa ta k'ara da furta masa Allah ya ma albarka. Ya amsa da Amin yayin da idanuwan sa suke zubar da kwalla mai tsananin zafi da k'una sosai, ita ma Kaka abin da take yi kenan sun shiga share wa juna kwalla, Umma ta tashi ta d'auko takardar maganin ta ba shi ya tashi ya fita ya d'an jima sannan ya dawo, inda ya samu mai gidan yana ta yiwa Umma ihu a ka sabo da dukan da a kayi wa yaransa. Inda kuma daga k'arshe ya furta mata cewar su bar masa gida cike da k'unci yake magana.

"Ba zan maka ihu ba sabo da gidan ka amma ka sani wannan ba qanwarka bace, a k'alla zata kai sa an nin mahaifiyar ka amma kuma kana yi mata ihu, kawai sabo da tana a k'arkashin ka to ko da baka fad'a ba yau zasu bar gidan ka. A game da yaranka kuma suna buqatar kyakkyawar tarbiya ta yanda zasu iya sanin, girman na gaba dasu ko kuma dai duniya ta yi musu horo mai tsananin sosai. Kuma daga k'arshe kai ne wanda zai yi kuka hakama kai ne wanda jama'a zasu ga gazawarka, sannan kuma su zageka to kawai dai kayi abin daya dace." Yana kai k'arshen maganar sa ya runguma Umma sun shiga ciki ya samu Mummyn sa ta farka daga suman data yi, da sauri ya k'arasa inda take har yana gudu yayin da yake fad'ar sunan ta, yayi hugging d'in ta yana sunbatarta cike da d'auki yake magana. "My Mum na ji dad'i kin farka bayan wasu tsayin shekaru, yau mun sake kasancewa a tare ina farin ciki sosai to ya kamata ki sha magani yanzu."

Sai kuma zuwa wannan lokacin ne ya sake ta daga hugging d'in da yayi mata, sai wani kallonta yake ita ma kallonsa take ya tashi ya d'auko maganin Umma ta ba shi ruwa. Nan ya shiga bata magani bayan ya qarasa ya kwantar da ita tare da d'ora kanta a kan cinyarsa, sai wani shafar kanta yake zuwa bayan ta tare da sunbatarta duk da cewar basa cikin kyakkyawan yanayi, amma ya samu kansa da jin farin cikin kasancewa tare da Mummyn sa sosai. Bayan wani lokaci ya sauke ka ga fuskar Umma tare da fad'ar sunan ta. "Kaka ya kamata mu tafi tare nake da mai mota na riga dana samu gurin da zamu zauna, a hotel ne zamu zauna na kwana biyu kafin na samu gidan da zamu zauna to dan Allah karki ce a'a kin ji please." Ta jinjina masa ka a lamar to nan kuwa ta shiga had'a kaya *Adeel* ya ta ya ta bayan sun qarasa, Umma ta tafi tayi sallama da matar gidan sannan suka tafi. Hakan kuwa ta kasance sun samu tsayin kwana biyar a hotel sannan ya samu gida, ba shi da wani kud'i shi yasa ya siyar da wayar sa da laptop d'in sa ya biya hayar wata uku, sannan ya siya musu kayan abinci ya siyar da duk wani abin sa mai tsada yaci gaba da kulawa da Mummyn sa dama Kaka.

Ya mai da ta asibiti amma sam ba wani abin da suka yi mata, sai dai kawai suka ba shi shawaran a kan ya fita da ita k'asar England domin a yi mata aiki. Ganin ba shi da komai yasa ya shiga damuwa sosai haka ya shiga nai man aiki amma bai samu ba, nan ya fara aiki gurin wasu masu gyaran babura da d'an abin da yake samu suke cin abinci, sannan yake siya wa Mummyn magani dama shi kansa wani yammaci yana cikin aikin sa, Kabir yazo yana anbatar sunan sa ya amsa Kabir yaci gaba yana cewa. *"Adeel* wani yana san zai yi magana da kai yana baya cikin mota." "To waye shi mai yasa ya tsaya ta baya.?" *"Adeel* dan Allah ka tafi sabo da ba zai cutar da kai ba." Ya jinjina masa ka ya tashi ya tafi shi kuma yaci gaba da aikin, *Adeel* ya isa gurin da Kabir ya sanar da shi yayi tsaye sai wani kallon motar yake, cike da k'unci bak'in ciki tare da tarin damuwa ya juya domin tafiya da sauri ya fito mota yana fad'ar sunan sa.

*"Adeel* ďana dan Allah kazo gareni ka dena wannan fishin da ni haka, sabo da rashin ka ya cutar da ni sosai rabin raina ji yanda ka koma kamar ba kai ba, *Adeel* kasa mutane sai zagina suke suna ganin kamar ni na kasa kulawa da kai yanda ya kamata. *Adeel* har yanzu kai yaro ne sam bai kamata a ce ka fuskanci irin wannan mummunan qalubalen ba, ďana ta ya zaka rayu a haka ba abinci mai kyau ko abin sha babu sutura sannan babu kyakkyawan muhalli, *Adeel* ni nayi matuqar damuwa sosai a kanka ko waya baka da shi *Adeel* naro e ka daka dena cutar da ni haka. Yanzu kawai kazo mu tafi mu koma gida dan Allah." "A'a Dady ni qlau nake ina lafiya sannan kuma Mummy na tana matuqar buqata na sosai, to ba zan tafi na barta ba Kaka tayi iya abin da zata to ni zan k'arasa zanyi aiki tuk'uru sabo dasu, abinci mai kyau ko abin sha da sutura zuwa muhalli basu suke nuna mutum zai rayu ko zai mutu ba, sabo da har yanzu Mummy na da kuma Kaka ta suna raye."

"Dady shi mutum kawai yana buqatar gwarin guiwa ne sannan juriya da kuma jajircewa, domin cimma nasara na kuma koyi hakan daga gurin Kaka. To yanzu kawai ka tafi sannan kuma karka koma dawowa dan Allah to ka tafi please." "Amma *Adeel."* "A'a kawai ka tafi dan Allah." Yana k'arshen maganar sa ya juya yayi tafiyarsa yayin da idanuwan sa suke zubar da kwalla, Prof ma abin da yake yi kenan cike da k'unci ya shiga mota yayi tafiyarsa, bayan tafiyar sa ne *Adeel* shi ma ya nufi gida bayan kwana biyu yau ya jima sosai wajen aiki, misalin k'arfe 08:00pm ya dawo gida cike da nuna kulawa Umma ta shiga yi masa sannu da zuwa.

Ya amsa yana murmushi ya nufi gurin Mummyn sa yayi hugging d'in ta tare da sunbatarta, sannan ya zauna ya gaisa da Umma sannan yaci gaba da magana. "Kaka yau nayi aiki sosai hakan yasa na tara kud'i sosai, to ni na siyo wa kowa abin da yafi so Mummy na tana da kayan shayi, musamman madara abin da tafi so sosai ke kuma kina da kaza ni kuma ina da samosa, zan had'a madara sai na sha tare da samosa had'in yana da dad'i sosai." "Kayi hak'uri *Adeel* na san cewar kai sam baka saba da irin wannan rayuwar ba amma kuma yanzu." Da sauri ya rufe mata baki yana girgiza mata ka, "Kaka shin ko zaki dena fad'ar min haka? Sabo da ina jin dad'in yanda nake rayuwa a nan ke da kuma Mummy na kune gwarin guiwa ta, eh a baya ina da kud'i sosai amma kuma bana farin ciki sosai, ko yaushe ina k'unci amma yanzu ina farin ciki sosai sannan kuma na koyi yanda zan tsaya da k'afafu na, sannan kuma na kula da wad'an da suke tare da ni musamman Mummy na. Hakan yana matuqar saka ni farin ciki sosai to ki dena fad'a min haka kin ji dan Allah." Ta jinjina masa ka a lamar to tare da rungumasa jikin sa bayan sun sake juna, Umma ta fara yiwa kaza aiki ta hanyar cin naman *Adeel* kuwa tashi yayi ya had'a madara ya fara cin abincin sa bayan wata uku...............






*BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.*
[2/3, 11:10 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑

*THREE BROTHER'S*

👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑

*Page 35*

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/


*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.


*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*


Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.



Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.



*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*Tuesday 01/02/2022*

*Time 05:39pm*

*Typing..............*


Zaune yake ya wani rabka wani uban tagumi sai tunani yake, kwana biyu jikin sa ba kuzari sosai shi yasa ya dena fita aiki, ga maganin sa dama na Mummyn sa duka ya k'are kuma dukansu da akwai buqatar su sha magani musamman Mummy. Yana cikin wannan k'uncin ya ji a na buga musu k'ofa tare da fad'ar sunan sa, ha!!! Ya nisa sosai tare da jan numfashi ya tashi ya nufi k'ofa Umma ta bisa da kallo tana girgiza ka. Ya fito ya samu Malan Nura tsaye a k'ofa ya ba shi hanu sun gaisa, bayan sun gaisa Malan Nura yaci gaba da magana. *"Adeel* lokaci sai tafiya yake amma sam baka ce dani komai ba, na baka duk wata dama amma kuma har yanzu banji daga gareka ba. To zuwa yanzu sai dai na baka hak'uri sabo da lokaci yayi da zaku tashi a gidan nan, *Adeel* na baku kwana biyu kawai sabo da ina san zan sanya wasu mutane a gidan, to dan Allah karku b'ata min lokaci kawai ku fita ka ji ko sai an jima." Ya juya yayi tafiyarsa ba tare daya jira ya ji mai za shi fad'a ba, cike da k'unci bak'in ciki tare da tarin damuwa ya juya ya koma ciki, yanayin sa yayi matuqar tsorata Umma sosai ta shiga tambayar sa mai yake faruwa da shi. Ya girgiza mata ka a lamar ba komai ya sauke kallonsa ga Mummyn sa wacce take rungume da pillow, a matsayin ďan ta sai wani jijjigasa take tana yi masa wasa cike da k'unci ya juya zai fita, yayin da idanuwan sa suke zubar da kwalla mai tsananin zafi da k'una sosai, da sauri Umma ta ri e hanun sa ya juyo yana kallonta ta zaunar

29 / 48