Author : Bil-Fauzee U-Adyan Category : Hausa Novels 001
"Eh yaronmu ne fad'a mana mai yake faruwa da shi.?" "Am kuyi hak'uri a na kan duba shi ne yanzu amma da akwai buqatar ku sanar damu sunan sa, sabo da zamu cike masa wasu takardu yanzu." Sunyi shiru dukanku sai nazari jin likitan ya maimaita tambayar sa wato sunan yaron ta amsa shi da *Adyan Ahmad Ali.* Ya amsa da ok ya juya ya koma ciki cike da unci Ahmad yake magana, "ke wai kin fita haiyacinki ne ta ya ma zaki yi ba shi sunana fad'a min mai ya saka kika yi hakan.?"
"Ahmad wai kai wane irin mutun ne mara tausayi? Shin kai baka ga a irin halin da yaron yake ba? Ni sam bani da wani za'bi wanda wannan dalilin ne yasa ni ba shi sunan ka, godiya ma ya kamata a ce kayi mun a maimakon wannan mummunan halin da kake nuna wa, ina fatan yaron ya samu lafiya cikin sauri sannan kuma shi ďin zai ci gaba da amsa sunan ka na har abada." Cike da jin mamakin abin data fad'a yake magana, "Ahlam mai kike nufi da fad'ar hakan.?" Tayi shiru kad'an sannan ta amsa shi, "Ahmad ban sani ba zaka yarda ko a'a amma dai ni ina da kwad'ayin a kan mu raini wannan yaron." Cikin rawar murya har yana sarkewa yake furta mata kalmar miye, "Eh Ahmad dan Allah." Ya girgiza ka yana cewa.
"Ahlam shin wai ke kin fita haiyacinki ne ta ya ma har zaki yi tinanin fad'ar hakan? Ta ya zamu d'auki rainon yaro bayan kuma ba aure muke ba? Ahlam ya kamata ki dena wannan shirmen kawai zamu kai wannan yaron gidan marayu ko office d'in an sanda, da zaran a ka gama duba shi wannan ne hukunci na ba kuma zan canja wannan ba." Wani irin kallo take yi masa mai cike dajin mamakin abin daya fad'a shi ma haka kallonta yake kallo sosai, wani irin kallo suke yiwa juna wanda ban san ta yanda zan iya sanar daku shi ba. "Ahmad wallahi tallahi ni ba zan ta'ba barin ka aikata hakan ba ko da kuwa mai zai faru, sabo da wannan yaron ďana ne shi ďin yaronmu ne kuma wallahi ba wani wanda ya isa ya canja wannan ko da ma kuwa kai ne, to kawai dai ka yarda ka kuma amince da hakan please."
Kallonta kawai yake yayin da ya gagara furta mata komai, suna haka sai ga doctor ya fito da sauri cikin hanzari Ahlam ta isa inda yake tana tambayar sa jikin yaron. "doctor ya jikin *Adyan* fatan yana samun sauki sosai.?" Ya girgiza ka tare da jinjina sa sannan ya amsa ta, "Madam a gaskiya yaronku bai ya cikin kyakkyawan yanayi, yayin yaronku yayi tsauri sosai amma zamu ci gaba da ba shi kulawa sosai, zai samu lafiya insha Allah to zaku iya yarda da ni." Cike da firgici take magana, "doctor dan Allah kuyi komai domin ku ceci rayuwar ďana ku fitar da shi daga hatsari." "Eh Madam abin da muke k'oqarin yi kenan kuma zamu nasara yaronku zai samu lafiya insha Allah to zaku iya yarda da ni." "Na gode doctor amma zamu iya ganin yaronmu kuwa.?" "Eh amma ku kula da shi sosai." "Eh zamu yi zamu kula da shi sosai nayi alkawari." "Ke uwa ta gari ce kina san yaronki sosai to Ubangiji zai taimaki yaronku insha Allah." Ta jinjina masa ka tana wani gajeran murmushi shi ma abin da yake yi kenan, da kuma haka suka rabu ya juya ya nufi office ita kuma ta nufi gurin yaron da ta sanya wa suna *Adyan. Ahmad* ya bita da kallo har ta shige ya nisa tare dajan numfashi ya juya ya nufi gunta, ya same ta zaune kusa da yaron sai wani kallonsa take kallo sosai.
Lokaci d'aya ta ji wata soyayyar yaron tana dad'a shigarta, yayin da tausayin sa kuma ya cika zuciyarta sosai ta shafi fuskarsa tare da sunbatarsa tana furta sunan sa. Ahmad dai kallonta kawai yake cike dajin mamakin ta sosai a tare da shi, sannu a hankali yake tafiya har ya isa inda take ya zauna daga gefe wanda kuma har zuwa wannan lokacin kallonta yake, kallo sosai ya anbaci sunan ta kafin ya furta komai tayi saurin rufe masa baki tana wani girgiza masa ka, ta koma gefen sa ta zauna wanda kuma har zuwa wannan lokacin hanun ta yana kan bakin sa, ta kai bakin ta daidai kunnansa cikin sannu a hankali take rad'a masa kalmar. "Dan Allah ko zaka iya yin shiru sabo da yaronmu yana buqatar hutu sosai please.?"
Ta janye bakin ta daga kunnan sa sai kuma zuwa wannan lokacin ne ta janye hanun ta daga kan bakin sa, ta mai da kallonta ga fuskar yaron sai wani kallonsa take kallo sosai, hakama Ahmad abin da yake yi kenan wanda kuma lokaci d'aya ya ji tausayin yaron yana shigarsa, ta ko wane lungu da sak'o na sassan jikin sa haka ya rik'a jin soyayyar yaron tana ratsa ko wane sak'o na jikin sa. Ya kai hanun sa ya shafi fuskarsa ya qara da sunbatarsa tare da furta Allah ya baka lafiya, lokaci d'aya Ahlam ta kai kallonta garesa tayi murmushi sosai tare da rik'o hanun Ahmad sun fice daga d'akin, sun fito waje sun samu guri sun zauna kusa da d'akin ta yanda zasu iya kulawa da yaron.
"Ahmad fad'a min wani abu shin yanzu kai ka aminta da mu raini yaron.?" Shiru bai yi magana ba jin shirun yayi yawa yasa taci gaba tana cewa. "Ahmad ni na san cewar mu biyun bama wani shiri da juna, ko yaushe cikin fad'a da musayan baki muke sam ba ma yiwa juna fatan alkhairi amma kuma duk da haka mu d'in ahali ne, Ahmad ko da mai zai faru mu biyun nan ba zamu iya canja gaskiyar ba kai Yayana ne ni qanwarka ce. Ahmad dukanmu mun san cewar hakan yana matuqar yiwa iyayenmu zafi sosai hakan kuma yana cutar da duka ahalin gaba d'aya, Ahmad na ro e ka da mu kawo k'arshen wannan dan Allah ka ji please."
Har zuwa wannan lokacin kallonta kawai yake kallo mai cike dajin mamakin ta sosai, wanda kuma wannan dalilin ne ya hana masa iya fad'ar komai. "Ahmad dan Allah ka amsa ni shin kai baka san duka wannan ya wuce.?" Ya nisa tare da jan numfashi wanda kuma sai zuwa wannan lokacin ne yayi magana. "Ahlam nima ina san duka wannan ya wuce ya yanda ahalinmu gaba d'aya zasu yi farin ciki sosai, to amma ai ba daga ni bane ke ce nan wadda take da matsala damuwar a kanki take, sam kin kasa bani damar da zan kasance Yaya na gari a gareki kinsa ko yaushe cikin nuna maki tsana da tsangwama nake. Ahlam wani abin da baki sani ba shi ne wallahi hakan yana cutar da ni sosai, amma kuma ni sam bana da wani za'bi a kan rayuwar da ke kika za'ba mana shi yasa ni nake duka wannan, amma zuwa yanzu duka duhun ya gushe haske ya bai yana a garemu gaskiya ina farin ciki da hakan sosai. Yanzu fad'a min wani abu ya zamu yi da wannan yaron sabo da bana san hakan ya saka mu a matsala.?"
"Shin zan iya kiran ka da Yaya Ahmad.?" "Amma ai kinyi alkawari a gaban kowa na cewar ke ba zaki ta'ba kira na da Yayan ki ba, shin kin manta da wannan ne.?" Tayi shiru kad'an sannan ta amsa shi, "eh ban manta ba tabbas ni na fad'i hakan a gaban duka ahalin, amma kuma na anbaci kalmar insha Allah a k'arshen magana ta Ahmad ni ina san mu daidai ta komai sabo da yaronmu. Ni ba zanso *Adyan* ya fahimci cewar mu biyun ba ma jituwa da juna sabo da hakan zai saka shi unci sosai ni kuma sam ba zanso hakan ba, ba zan bar wani abu ya cutar da yarona ba zan iya jure komai da ko wane irin qalubale domin sa. Ni kawai ina san mu kasance iyaye na gari ga yaronmu wanda shi yasa ni nake yin duka wannan, to dan Allah karka dakatar da faruwar hakan ni zan iya jure duk wani unci kawai dai alfarma d'aya zan nai ma a gurin ka, Yaya Ahmad dan Allah da girman Allah ka yarda ka kasance uba na gari a gurin *Adyan.* Wannan kawai alfarma ce idan ka amince zanyi matuqar farin ciki sosai kuma zanyi alfahari da kai, idan kuma kak'i ka amince da wannan to zan kasance ina fishi da kai na har abada kuma hakan ba zai canja ba. To yanzu fad'a min shin ka shirya amince min gurin rainon *Adyan* ko a'a.?"
*BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.*
[12/24/2021, 8:25 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑
*THREE BROTHER'S*
👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑
*Page Five*
*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*
*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*
Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.
*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*
*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*
Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.
Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.
*Bismillahir Rahmanir Raheem*
*Wednesday 22/12/2021*
*Time 10:25pm*
*Typing...............*
Wani irin kallo yake yi mata mai cike dajin mamakin ta sosai, wanda kuma wannan dalilin ne yasa yayi mata shiru jin shirun yayi yawa yasa ta fad'ar sunan sa. "Yaya Ahmad dan Allah ka amsa ni shin ka shirya amince min gurin rainon *Adyan* please.?" Magana take cikin wani irin yanayi na ban tausayi yayin da idanuwan ta suke zubar da kwalla, mai tsananin zafi da una sosai kuma zamu iya kiran abin da kukan zuci wanda yafi na zahiri ciwo. Ya nisa sosai tare da jan cikin kwantar da murya yake magana, "Ahlam to ya kuma hakan zata kasance har yanzu mu yara ne, Ahlam yanzu haka muna shirin koma wa school ne sannan kuma ba a nan muke karatu ba, Ahlam ya kamata ki fahimci abin da nake nufi yana da kyau wannan yaron ya koma hanun a salin iyayen sa."
Da sauri ta dakatar da shi ta hanyar furta masa kalmar a'a, "a'a Yaya Ahmad ni sam ba zan yi hakan ba sabo da zuwa yanzu *Adyan* ďana ne, mu biyun nan mune a salin iyayen sa ba abin da zai canja wannan." Magana take cikin fishi sosai ta tashi domin tafiya yayi saurin dakatar da ita, ta hanyar ri e hanun ta yana girgiza mata ka a lamar a'a ya zaunar da ita tare da fad'ar sunan ta. "Ahlam yanzu fad'a min ta ya ni zan iya taimaka maki gurin rainon *Adyan* ni kuma zanyi nayi alkawari.?" "Da gaske zaka yi komai na fad'a.?" Ya jinjina mata ka a lamar eh, "kayi alkawari.?" Ya jinjina mata ka a lamar eh tayi gajeran murmushi sannan taci gaba da magana. "Yaya Ahmad ina san mu biyun muyi aure ta yanda zamu raini *Adyan* a matsayin ďan mu, Yaya Ahmad ina san mu baiwa yaron kyakkyawar rayuwa wadda zai yi farin ciki sosai. Yaya Ahmad gaskiyar ita ce ni ina matuqar qaunar *Adyan* sosai sannan kuma sam bana san kowa ya san a salin waye shi."
"Yaya Ahmad kai kad'ai ne wanda zai iya taimako na a kan wannan, Yaya Ahmad dan Allah karka ce a'a eh na san cewar mu biyun ba ma wani jituwa da juna, bamu ta'ba kasancewa matsayin abokai ba balantana kuma masoya, amma kuma zamu yi aure sabo da yaronmu nayi alkawari ni ba zan ta'ba shiga rayuwar ka. Zama ka iya auran duk wadda kake a duk lokacin da buqatar hakan tazo ma ni ba zan ta'ba dakatar da kai ba, Yaya Ahmad ni kawai alfarma ďaya nake nai ma a gurin ka shi ne ka kasance uba a gurin *Adyan.* Ba kawai uba ba a'a so nake ka kasance uba na gari a garesa to fad'a min shin zaka yarda da hakan kuwa.?" Yayi shiru na jim kad'an yana nazari sannan daga bisani ya amsa ta, "Ahlam amma ta ya hakan zata kasance *Adyan* ba zai 'boyu ba musamman a gurin iyayen mu, sannan kuma ni sam bana jin cewar zasu yarda da hakan cikin sauk'i, Ahlam ni sam bana jin cewar hakan zai yu ya kamata kiyi tinani a kan wannan sosai." "Yaya Ahmad idan har kai ka amince da aure na to zan tabbatar da abin dana fad'a a yanzu." "Shikenan na amince to kawai ki tabbatar." Lokaci d'aya ta saki wani kyakkyawan murmushi tana yi masa godiya, kallonta kawai yake ba tare daya furta mata komai ba ta ciro wayar ta daga jaka ta shiga kiran layin Abbu.
Ba jimawa ya d'aga cikin hanzari yake anbatar sunan ta tare da tambayar ta suna ina. "Ahlam kuna ina haka shirun ya fara yawa fatan kuna cikin k'oshin lafiya.?" Tayi shiru na jim kad'an sannan ta amsa shi, "Abbu gaskiya ba lafiya muna matuqar buqatar taimakon ku sosai kai da Kawu, yanzu zan turo maka adres na inda muka kazo tare da Kawu sannan kuma karka sanar da kowa bayan Kawu dan Allah." "Shikenan ba wanda zai ji nayi alkawari sai mun qaraso." Ta amsa da to da kuma haka suka yi sallama ba jimawa ta tura masa text na inda suke, Ahmad dai kallonta kawai yake yayin da ya gagara furta mata komai ita ma haka kallonsa take tayi murmushi kad'an tare da fad'ar sunan sa. "Yaya Ahmad zuwa yanzu ya kamata mu koma ga yaronmu sabo da zai iya buqatar mu a kusa da shi to mu tafi. Har zuwa wannan lokacin kallonta kawai yake yayin da mamakin ta yayi yawan gaske a tare da shi sosai, wanda kuma wannan dalilin ne yasa ya gagara furta mata komai ta tashi tare da tashin sa sun nufi d'akin da yaron yake.
Sun shiga ciki tare da isa inda yake sun zauna daga gefen sa sai wani kallonsa suke kallo sosai. Yayin da suke jin yana birgesu sosai bayan wani lokaci Ahmad ya sauke kallonsa ga fuskar Ahlam tare da fad'ar sunan ta, "Ahlam zuwa yanzu ya kamata kici abinci to fad'a min mai zaki ci.?" Ta girgiza masa ka tare da furta masa kalmar, "a'a ni sam bana jin yunwa sannan kuma ina lafiya to zaka iya yarda da ni." "Ahlam ki fad'a min mai zaki ci.?" "Shikenan shawarma kawai ta isa." Ya jinjina mata ka sannan ya tashi ya fita bai wani jima ba sosai ya dawo, ya bata ledar dake hanun sa ta kar'ba tare dayi masa godiya ya amsa da ba komai. Nan ta fara cin shawarma wanda shi kuma samosa yake ci bayan wani lokaci sai gasu Abbu, sun shiga kiran layin Ahlam ba jimawa Ahmad ya fita sun dawo tare, cike da d'auki Ahlam ta isa inda Abbu sunyi hugging juna bayan sun sake juna, ta ja hanun sa sun qarasa inda babyn yake wato *Adyan* sunan da suka ba shi cike da firgici da rud'ani su Abbu suka tambayar su waye shi har suna had'a baki. "Ahmad waye wannan yaron mai yasa yake tare daku.?" Kafin ya furta komai Ahlam tayi masa rigagi ta hanyar amsa Abbu lokaci d'aya ta sanar dasu komai da ma duk wani plan da suke a game da shi.
Abbu sai wani kallonsu yake kallo sosai hakama Abba shi ma kallonsu yake yayin da mamakin su yayi yawan gaske a tare dasu sosai, "Abbu Abba dan Allah karku dakatar damu sabo da muna san yaronmu sosai, sannan kuma mu sam ba zamu jure rashin sa ba to ina fatan zaku aminta da wannan burin dan Allah.?" "Amma Ahlam." "A'a Abbu kawai dai ku amince dan Allah." Abbu ya kai kallonsa ga Abba lokaci d'aya suka yi ido biyu da juna ya anbaci sunan sa yana cewa. "Yaya to mai ya kamata muyi a kan wannan.?" Yayi shiru na wani lokaci sannan daga bisani ya amsa shi, "eh Al'ameen muyi hakan ina nufin abin da suka buqata daga garemu shin dama ba wannan bane burinmu ba? To ya kamata muyi hakan tabbas za a yi auran kuma nan kusa insha Allah." Cike da farin ciki Ahlam tayi hugging d'in Abba tana cewa.
"Na gode Abba daka amince da wannan ina godiya sosai, amma Abba sam bana san kowa ya san da wannan zancan a game da *Adyan* ko da kuwa Umma da Ummi ne dan Allah, sannan kuma za a shirya wa *Adyan* visa sabo da mu samu damar da zamu tafi tare da yaronmu dan Allah." Abba yayi murmushi sosai yana cewa, "eh Ahlam zamu yi hakan to kawai kiyi farin ciki kinji ko sannan kuma ba wanda zai ji komai a game da jikana ko da kuwa Umma da Ummi wannan alkawari ne." Magana yake cikin kyakkyawan yanayi yayin da fuskar sa take fitar da wani lallausan murmushi abin birgewa, ya sunbaceta a ka tare da furta mata kalmar Allah yayi maki albarka ta amsa da Amin tana murmushi mai tare da ar dariya, Abbu da Ahmad sa wani kallonsu suke suna murmushi Abba