Author : Bil-Fauzee U-Adyan Category : Hausa Novels 001
a zabtar da su sosai kafin na yanka su shashasha kauce min a nan."
Magana yake cikin fushi sosai T. K ya shiga basa hakuri sannan ya koma daga gefe, zuciyarsa cike da tausayin yaran sosai a tare da shi waɗanda kuma har zuwa wannan lokacin kuka sosai suke. Rabi'u ya kai kallonsa ga Babawo tare da fad'ar sunansa, "Babawo ka kula da yaran sannan kuma kasa suyi shiru saboda wannan kukan nasu ya fara damuna sosai." Yayi wani murmushi irin na mugunta tare da furta, "an gama Oga yanzun nan zasu yi ko kuma dai suyi barci na har abada." Cike da firgici T. K ya kai kallonsa ga Babawo yana san yayi magana amma ba shi da wannan damar, sabo da ba zai so a cutar da yaran ta hanyar yanka su ba, yasan halin Rabi'u tsab zai iya yanka su kamar dai yanda ya fad'a. Wanda wannan dalilin ne yasa dole yayi shiru Babawo ya kar'bi yaran daga hannun T. K yana ƙoƙarin tafiya Rabi'u ya dakatar da shi. "Babawo ka kula da yaran sosai sabo da jarinmu ne su dole cikin biyu ďaya zai faru, ko iyayensu su biya kud'in fansa ko mu raine su sannan kuma mu bautar da su."
"Gaskiyar ka ne Oga dan haka zan kula da su sosai." Rabi'u ya jinjina masa ka alamar to yana murmushi shima abin da yake yi kenan, T. K kuwa sai wani kallonsu yake yayin da tausayin yaran yayi yawan gaske a tare da shi sosai bayan kwana biyu. Zaune take yayin da ta saka photon twin's a gaba da ma kayan su tana kallo yayin da take fad'ar sunan su tana kuka kuma kuka sosai, Anas ya fito daga wanka yayi tsaye sai kallonta yake kallo mai cike dajin tausayin ta sosai, cike da unci bak'in ciki tare da tarin damuwa yake tafiya har ya isa inda take, ya zauna tare da rungumata jikinsa ya qara da sunbatarta cikin mutuwar jiki da sanyin murya yake magana. "Kiyi hak'uri dan Allah ki dena cutar da kanki haka kar wani mummunan abu ya faru da ke please." Magana yake cikin wani irin yanayi mara dad'i yayin da damuwa tayi yawan gaske a tare da shi sosai.
"Abban twin's ni kawai na damu ne a kan yaran to ya idan kuma suka cutar dasu fa? Zuwa yanzu ni uwa ce kuma na damu sosai a kan yarana sabo da ina qaunar su sosai, Abban twin's mai ya saka basu harbeni ba a maimakon raba ni da twin's sun raba ni da farin ciki na gaba d'aya. Sunsa ina jin cewa kamar ni ban ta'ba kasancewa a cikin farin ciki ba, duka wannan laifi na ne sabo da sam bai kamata a ce nazo nan ba tare da twin's ba. Ni wace irin uwa ce sam na kasa taimakon yarana ni sam ba uwa ta gari bace ga twin's amma." Ta kuma yi shiru tare da sauke kallonta ga fuskar Anas sai wani kallonsa take kallo sosai, da sauri ta fita daga jikinsa har tana turesa cike da firgici da rud'ani yake fad'ar sunanta zai yi magana tayi saurin dakatar da shi.
"Karka fad'i komai sabo da ni sam ban shirya sauraran ka ba, Yaya Anas duka wannan laifin ka ne eh kai ne kake d'auke da alhakin duka wannan, Yaya Anas kai wane irin muji ne kuma wane irin uba ne ga twin's? Ya kamata a ce kai ka kula da komai amma kai ba ma ka iya kare yaranka ba haka ka sanyo ni mota muka zo nan ba tare da kayi tinani a kan yaranmu ba. Kabar yaranmu a hanun wad'an nan mugayen mutanan zuwa yanzu ban san komai a game dasu ba, amma na san cewar su zasu yi kewata sosai sannan kuma zasu buqaci a shayar dasu kuma Maman su ce kawai zata iya yin hakan kuma ni ce wannan. Amma kuma bani zaune a nan na kasa taimakon su da komai tamkar wata mata anfani, kai ma kana zaune haka baka yi komai ba ka fad'a min kai wane irin uba ne sam ka kasa kare yaranmu daga cutarwa? Ni nayi kewar twin's sosai ina san na runguma su a jiki na sannan nayi musu wasa suna yawan saka ni murmushi sosai, musamman idan na sunbace su amma kuma duk da haka ni na kasa karesu amma." Bata qarasa fad'ar abin da yake ranta ba sai kawai gani yayi ta dukurshe ta fad'i kwance a qasa da sauri ya isa inda take yana fad'ar sunanta amma bata amsa ba, cike da firgici rud'ani tare da tashin hankali ya d'auke ta ya nufi asibiti da ita yayin da damuwa tayi yawan gaske a tare da shi sosai.
Sun isa asibiti an shiga da ita ciki shi kuwa sai safa da marwa yake, bayan wani lokaci doctor ya fito tare da ba shi wata ar takarda yana furta masa, "ka tafi ka kawo wannan yanzu." Ya kar'bi takardar cikin hanzari ya fice ba jimawa sosai ya dawo ya shiga ciki ya ba likitan. Ya kar'ba tare da yi masa izinin ya fito ya amsa da to yayin da idanuwan sa suke a kan matar sa jiki a san yaye ya juya ya fita su kuma sunci gaba da abin da suke, bayan wani tsayin lokaci da suka d'auka a ciki tare da ita sun fito cikin hanzari tare da nuna kulawa Anas yake tambayar su jikin matar sa. "Matar ka tana samun sauki amma kuma ita d'in sam bata cikin kyakkyawan yanayi, amma zamu kula da ita sosai ba jimawa zata samu lafiya insha Allah to zaka iya yarda da ni." Ya jinjina masa ka a lamar to tare dayi masa godiya sunyi sallama doctor ya nufi office shi kuma ya nufi gurin Abida.
Sannu a hankali yake tura ofar har ta bud'e ya shiga ciki ya same ta kwance, wanda kuma har zuwa wannan lokacin bata farka daga dogon suman da tayi ba ya isa inda take ya zauna kusa da ita kusa sosai, ya shafi fuskarta tare da sunbatarta cike dajin tausayin ta yake magana. "Ki yafemin eh gaskiyar ki ne duka wannan laifi na ne, ni sam ban kasance uba na gari ga yaranmu sabo da na kasa karesu, amma kuma nima hakan yana matuqar cutar da ni sosai. Abida ban sani ba zaki yarda da ni ko a'a amma gaskiyar ita ce ni ina matuqar qaunar twin's sosai wallahi ina qaunar su sosai, amma ban san ta yanda zansa ki yarda da ni ba ina fatan karki jima a cikin wannan mummunan yanayin Allah ya baki lafiya Allahumma Amin." Misalin k'arfe 08:30pm Abida ta farka daga dogon suman da tayi sannu a hankali take bud'e idanuwanta har suka bud'e, yayin da bakinta yake anbatar sunan twin's tayi tozali da fuskar Anas cike da nuna kulawa yake anbatar sunanta, kallonsa kawai tayi ba tare data amsa ba ya tashi ya fita ba jimawa ya dawo tare da doctor, Dr Shahid ya duba ta kuma Alhamdulallah yaga tana samun sauki ya sanar da Anas sannan ya juya ya fita. Bayan tafiyar Dr Shahid Anas ya mai da kallonsa ga Abida tare da fad'ar sunanta amma dai bata amsa ba yaci gaba da magana.
"Gaskiyar ki ne ni sam ba muji na gari bane a gareki, hakama ban kasance uba na gari ga twin's ba ni ban san ma da wane suna zan iya kiran kai na ba, amma kuma duk da haka ni ba zan fasa nai man afuwar ki da gafarar ki tare da yafiyar ki ba dan Allah ki yafemin. Abida ni sam ba zan iya jure wannan hukuncin naki ba sabo da yayi min tsauri sosai ba zan iya d'auka ba, domin yana da zafi sannan kuma da una sosai ni ba zan iya jure wannan ba sabo da ni ba jarumi bane idan har a kan hukuncin ki ne to ina fatan zaki yafemin dan Allah.?" Magana yake cikin wani irin yanayi mara dad'i yayin da damuwa tayi yawan gaske a tare da shi, ba kuka yake ba amma kuma idanuwansa kwalla suke zubar wa mai tsananin zafi da una sosai, kuma zamu iya kiran abin da kukan zuci wanda yafi na zahiri ciwo har zuwa wannan lokacin kallonsa take ba kuma tare data furta masa komai ba sun samu shiru na wani lokaci sannan daga bisani ta amsa shi.
"Kayi hak'uri da duk abin dana fad'a wanda ba zan iya tinawa ba, Yaya Anas ni kawai na damu ne sosai a kan twin's ina san yaran sosai sannan kuma ni sam na kasa jure rashin su nayi kewarsu sosai." Kukan da take yaci k'arfin ta wanda wannan dalilin ne yasa ta yin shiru taci gaba da kuka, cike da jin tausayin yake rarrashinta yana bata magana cikin hikima tare da nuna kulawa wanda daga bisani ta iya fahimtar sa. Haka taci gaba da samun kulawar doctor ta samu kwana biyar asibiti sannan ta samu sallama zuwa gida.
"Babawo ka kula da wannan yaron a nan T. K kai zaka tafi ka d'auko kayan abinci kayi girki, ni dasu Falalu zamu shiga daji yin aiki sabo da muna buqatar kud'i sosai J. B ka d'auko d'ayan yaron mu tafi da shi." Dukansu sun amsa da to sun nufi gurin aiki ba jimawa sosai T. K ya dawo domin ya d'ora girki kamar yanda Rabi'u ya umurcesa, ya samu Babawo yana ta yiwa yaron ihu tare da tsawa shi kuwa sai kuka yake kuka sosai da sauri ya a jiye kayan dake hanun sa ya isa inda yake, da sauri ya fizge yaron daga hanun sa ya shiga jijjigasa yana rarrashin sa cike da 'bacin rai Babawo yake magana. "Kai T. K wai mai ka aikata ne haka shin ka manta da abin da oga ya fad'a ma a game da wad'an nan yaran? Shikenan tin da kana buqatar tabbaci to ka sani ni da kai na zan yanka wannan yaron a yanzu."
"Wallahi tallahi idan har kayi yunk'urin cutar da wannan yaron to ni da hanu na zan kashe ka, ba kuma tare da ji nadamar hakan ba to ka kiyaye ka ji ko." "T. K karka yi kamar kana bani umurni sabo da ni sam ba zan saurari komai daga gareka ba, kuma ni zan cika umurnin oga ka tsaya kaga yanda zan yanka wannan yaron a ga ban idanuwan ka kuma ba abin da zaka iya." "Shikenan to kawai ka aikata kila ka qosa gurin ganin ka bar duniya ne, dan haka ni sam ba zan dakatar da kai ba." "Shikenan to mu gwada domin ganin wanda zai yi nasara." T. K ya a jiye yaron daga gefe sun kama kokawa fad'a suke sosai, tamkar da basu san juna ba suna haka T. K ya hangi wani sadaukin maciji yana zuwa kusa da yaron. Cike da firgici rud'ani tare da tashin hankali yayi saurin sake Babawo ya nufi gurin yaron har yana gudu, kad'an ya isa garesa Babawo ya riqo wuyan sa ta baya tare da shage wuyan sosai, "a tinanin ka ni zan barka ka ceci wannan yaron a'a to kayi kuskure sabo da ni ba zan ta'ba barin wannan yaron ya rayu ba. Kawai dai ka tsaya kaga yanda zai mutu a ga ban idanuwan ka ba kuma tare da kayi komai ba."
Ganin yanda macijin yake qara kusa sosai da yaron yasa T. K ya tattara duka k'arfin sa tare da jajircewa ya samu, cikin hikima da dabara ya kife Babawo a qasa ya tashi da sauri har yana gudu ya isa inda yaron tare da d'aukan sa. ya kauce daga gurin da sauri Babawo ya nufi gun da yake yana cikin tafiya ba ankara ba sai jin saran maciji yayi a qafarta kuma duka biyun, ya fad'i kwance tare da sakin wani uban ihu yana kururuwa amma a haka ya fito da bindiga daga jikinsa ya daddallawa macijin harbi har ya mutu, ya mai da kallonsa ga T. K wanda yake daga gefe rungume da yaron yayi wani gajeran murmushi yana cewa.
"T. K karka yi farin ciki da yawa sabo da ba zai yu na mutu ni kad'ai ba, ni kai da kuma wannan yaron da yake rungume jikin ka to zamu mutu a tare wannan alkawari ne kuma zan cika yanzun nan." Ganin yana k'oqarin harbin sa yasa T. K ya tashi ya kama gudu Babawo yayi wani ihu tare da sakar masa harbi, inda shi kuma yace ga garin ku nan rai yayi halinsa ya mutu, waiyo T. K na cikin tafiya ya ji harbi lokaci d'aya ya kife a qasa wanda bai ma san lokacin da hanun sa ya saki yaron da yake kwance jikin sa ba. Haka yaron yaci gaba da gangara har zuwa wani guri daban wanda zuwa wannan lokacin ya suma................
*Yawan comment yawan typing insha Allah.*
*BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.*
[12/22/2021, 9:04 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑
*THREE BROTHER'S*
👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑
*Page Four*
✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
.
*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*
*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*
Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.
*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*
*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*
Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.
Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.
*Bismillahir Rahmanir Raheem*
*Monday 20/12/2021*
*Time 10:38pm*
*Typing.............*
Tafiya suke a kan hanya sai jiran wanda zasu tare suke, sun jima a nan ba wani labari kamar saukar aradu suka ji sautin jiniyar motar ƴan sanda, ai kuwa nan suka ce mai zasu yi in ba gudu ba sun fad'a daji da gudu sun nufi ma'buyarsu. Ganin kamar yaron da yake d'auke da shi zai zame masa matsala yasa ya ajiye sa a gefen hanya yayi tafiyar sa, ya bar shi nan yana ta tsala ihu amma duk a cikin su ba wani d'aya wanda ya iya dawowa garesa. Haka suka yi tafiyar su suka bar shi cikin rashin tausayi tafiya kawai suke amma ba mai magana a cikin su tamkar masu gaba, ya koma gefen hanya yayi parking ya fito ita ma fitowa tayi tana mai furta masa kalmar. "Malam miye haka zaka kama kayi parking a nan? Bayan kuma ka san cewar hanyar nan bata da kyau wannan ganganci ne to ya kamata mu tafi."
Ko kallon kusa da inda take bai yi ba ballantana kuma ya iya amsa mata, ya buɗe both ya ɗauko ruwa ya juya yayi tafiyar sa, ta bishi da wani wawan kallo mai kama da harara. Ta qara da jan tsaki tana wani juya baki ba jimawa sosai ya dawo ya hangeta ta nufi wani guri sai tafiya take, yayi tsaye sai kallonta yake yayin da takaicin ta ya cika zuciyar sa sosai, ganin sai tafiya take tana shiga daji yasa ya nufi inda take yana fad'ar sunanta. "Wannan yarinyar ta fiye shashancin da yawa ina kuma zata tafi haka? Kawai tana naiman ta 'bata min lokaci a banza lallai ya kamata na hukunta ta."
Ya fad'a tare da jan tsaki ya juya ya nufi gunta, tafiya take tana jin kukan yaron yana qara kusa da ita can ta hangesa kwance yana kuka, da sauri cikin hanzari ta nufi gurin sa har tana gudu ta d'auke sa tare da rungumarsa a cikin jikinta tana jijjigasa. Cike da tsoro tare da firgicin ruɗani tare da tashin hankali ta juya domin tafiya, lokaci d'aya tayi ido biyu da fuskar Ahmad wani irin kallo yake yi mata kallo sosai. Sun juya sun nufi mota sun shiga ciki wanda kuma har zuwa wannan lokacin kallonta yake kallo sosai, ita kuma yaron da yake kwance jikinta take kallo wanda numfashin sa yake ƙoƙarin ɗauke wa, da sauri ta kai kallonta ga Ahmad lokaci d'aya suka yi ido biyu da juna kasancewar har zuwa wannan lokacin kallonta yake. "Ahmad wai mai kake kallo ne haka shin kai baka ga halin da yaron yake ciki ba? Ya kamata mu kai shi asibiti to ka tuqa motar mu tafi yana buqatar kulawa sosai." Sam bai iya amsa mata ba saidai ya ja mota suka tafi a nan funtuwa suka kai yaron asibiti, an shiga da yaron ciki a na duba shi Ahmad ya maida kallonsa ga Ahlam wacce take ta safa da marwa, tare da fatan yaron ya samu lafiya ya isa inda take ya janyo hannun ta sun koma gefe kafin ya furta komai tayi masa rigagi. "Malam lafiya zaka wani janyo ni nan mai kake buqata daga gare ni.?"
"Ke wai mai kika yi ne haka waye wannan yaron kuma mai ya saka kika d'auko sa zuwa nan.?" "Ban sani ba ko an fad'a maka izinin ka nake jira kafin aikata wani abu.?" "Ba buqatar ki nai mi izinin aikata wani abu amma ki sani." Kafin ya furta komai suka ji doctor yana yi musu magana, "am shin ko kune iyayen wannan yaron da a ke duba wa a ciki.?" Ahmad na k'oqarin yin magana tayi saurin yi masa rigagi ta hanyar amsa doctor.