THREE BROTHERS Complete Hausa Novels By Bil-Fauzee U-Adyan.txt

Author :  Bil-Fauzee U-Adyan Category :  Hausa Novels 001

Chapter   12 / 48

33K to 36K   out of 142.8K words

gwiwa a wajen rubutu mai yawa.



*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*Monday 03/01/2022*

*Time 12:07pm*

*Typing.............*

Sun isa asibiti cikin hanzari nurse suka shigar da su ciki, haka Ahmad ya dawo tamkar wani qaramin mahaukaci ko wanda ya zauce, to zamu iya cewa ya soma fita haiyacinsa sai aikin kai komo yake yayin da bakinsa yake anbatar kalmar Innalillahi wa'inna'ilaihi raji'un. Bayan wani lokaci nurse ya fito tare da ba shi wata takarda, "ka tafi ka kawo wannan." ya amsa da to ya juya ya fice da sauri har yana gudu bai d'auki wani lokaci ba ya dawo. Ya baiwa nurse ďin kayan da ya siyo ya kar'ba ya koma ciki, bayan wani tsayin lokaci sosai doctor suka fito cikin hanzari Ahmad ya isa garesu tare da tambayar su jikin ahalinsa. Dr Sam ne yake magana, "muna yin abin daya dace ne yaron yana samun sauki sosai, hakama Mummyn sa amma munyi rashin sa'a babyn da yake tare da ita bai rayu ba. Kayi hak'uri a kan hakan zata samu lafiya insha Allah to zaka iya yarda da ni please, hakama yanzu zaka iya shiga ciki domin ka duba dukansu.”

Wani irin kallo yake yi masa mai tare da firgici yayin da ya gagara furta komai, banda kalmar Innalillahi wa'inna'ilaihi raji'un ba abin da yake fad'a. Jiki a san yaye ya juya ya nufi d'akin da suke hakama su Dr Sam suma tafiya suka yi a bakin aikin, sannu a hankali yake tura k'ofar har ta bud'e ya shiga ciki, cikin mutuwar jiki yake tafiya har ya isa inda suke kwance sai wani kallonsu yake kallo sosai yayin da damuwa tayi yawan gaske a tare da shi. Kukan zuci yake yayin da idanuwan sa suke zubar da kwalla mai tsananin zafi da k'una sosai, ya sauke kallonsa ga cikin Ahlam ya shafi cikin har zuwa mara cike da k'unci tare da tarin damuwa yake magana. "Yarinya ta bai kamata ki tafi ba sam bai kamata hakan ta faru dake ba, nayi ta burin had'uwa dake hakama Ammie da kuma Yayanki dukanmu muna sanki sosai, 'yata dukanmu muna matuqar qaunar tare da san burin kasancewa a tare dake to amma mai ya saka lokaci d'aya kika tafi? Kin dakatar da duka burinmu da muke da shi a kanki hakan yana da zafi sannan kuma da matuqar k'una sosai. Ahlam taya zaki iya jure wannan zafin yana da matuqar cutar sosai, *Adyan* kai ma hakan zai yi matuqar cutar da kai sosai sabo da irin yanda ka damu da zancan qanwarka, a kullum cikin tambayar yaushe zata zo gareka kake ga shi kuma ita ta tafi, duka wannan laifi na ne dana kasa kareku gaba d'aya ban kula daku yanda ya kamata ba, shi yasa duka wannan ya faru ina fatan zaku yafemin dan Allah ku gafarce ni please."

Magana yake cikin wani irin yanayi mara dad'i yayin da damuwa tayi yawan gaske a tare da shi sosai, ba kuka yake ba amma kuma idanuwansa kwalla suke zubar wa mai tsananin zafi da k'una sosai, kuma zamu iya kiran abin da kukan zuci wanda yafi na zahiri ciwo. Misalin k'arfe 08:30pm *Adyan* ya farka daga suman da yayi ya kuma farka cikin firgici, kamar dai a yanda ya suma da sauri Ahmad ya isa inda yake ya rungumasa jikin sa yana rarrashin sa. *"Adyan* ya isa haka ina tare da kai ba abin da zai faru da ka ji ko." "Appa zomo ne yazo inda nake sai famin bina yake ni ina tsoron sa sosai." Magana yake yana kuka, "Ka dena tsoro sabo da Appa yana tare da kai to kukan ya isa haka yanzu fad'a min mai kake so.?" Ya girgiza tare da furta a'a ya qara shigewa jikin Ahmad yayi kwance, shi kuwa sai wani jijjigasa yake yana rarrashin sa bayan wani lokaci ya anbaci sunan Ahmad yana cewa. "Appa zanyi fitsari." Ya amsa shi da to ya tashi tare da d'aukan sa sun nufi toilet, bayan wani lokaci suka fito kai tsaye gurin Ahlam ya nufi da sauri har yana gudu yayin da yake fad'ar sunan ta.

"Ammie ki tashi ina jin yunwa sosai zanci abinci Ammie ki tashi." Magana yake yana kuka Ahmad yana ta k'oqarin ganin ya dakatar da shi amma sai da yayi nasaran tashin ta. Cikin barci ta riqa jiyo sautin kukan sa nan kuwa abin daya faru ya riga dawo mata, lokaci d'aya ta bud'e idanuwan ta yayin da bakinta yake anbatar sunan yaronta wato *Adyan,* ya amsa ta tare da saban ta kukan sa ya fita daga jikin Ahmad ya nufi gunta, da sauri har yana gudu yayin da bakin sa yake fad'ar sunan ta ita ma haka sunansa take fad'a, yana isa inda take ta wani rungumasa jikin ta tana shafar kansa zuwa bayan tare da sunbatarsa fuska zuwa wuya dama jikin sa gaba d'aya. "Ina qaunarka yarona ina fatan ba abin daya faru da kai fad'a min qlau kake mai ya saka kake kuka.?" "Ammie ni ina jin tsoron zomo sosai sannan kuma ina jin yunwa sosai." "Ka dena kuka yarona ni zansa a d'auke zomon daga gidan, zancan abinci kuma yanzu ka fad'i wa Appa duk abin da kake so zai tafi ya kawo ma ka ji ko." "Ammie ni zanci abinci tare da qanwata to ki fad'a mata tazo muci abinci, ina san na ganta sosai sabo da ina qaunar ta sosai." *"Adyan* qanwarka ma tana qaunarka sosai sannan kuma zaku abinci a tare amma ba yanzu ba, sabo da a yanzu bata nan amma tana kusa damu to yanzu fad'a min mai kake san kaci.?"

"Ammie ni zansha madara kawai." "Shikenan masoyi yanzu Appa zai tafi ya kawo ka ji ko." Ya d'aga mata ka a lamar to ta shafi fuskarsa tare da sunbatarsa tana murmushi, ta mai da kallonta ga fuskar Ahmad wanda banda kallonsu ba abin da yake. Lokaci d'aya suka yi ido biyu da juna tayi masa murmushi sosai shi kuwa kallonta kawai yake, ba kuma tare daya furta mata komai ba sun samu shiru na jim kad'an sannan ya fara magana. "Ahlam to ya jikin naki fatan kina samun sauki sosai.?" Ta jinjina masa ka tare da furta eh taci gaba da magana. "Eh Yaya Ahmad ina samun sauki sosai to sam ba buqatar ka damu sosai ka ji ko, yanzu yaronmu yana jin yunwa to ka tafi ka kawo masa madara ya sha tin kafin yunwar ta cutar da shi sosai." "Eh zanyi hakan to ke kuma fa mai zaki ci.?" "nima zansha madara kamar yarona." "Shikenan ku jira kad'an yanzu zan dawo insha Allah." Ta jinjina masa ka tana murmushi shi ma haka wani gajeran murmushi yake. Ya juya ya fita ya d'an jima sannan ya dawo ya basu abin da suka buqata daga garesa wanda shi ma madarar ya sha, bayan sun qarasa ba da jimawa *Adyan* yayi barci Ahmad ya d'auke sa ya tafi ya shinfid'e sa, ya dawo gurin Ahlam yayi zaune daga gefen ta sai wani kallonta yake kallo sosai. "Yaya Ahmad shin qlau kike kuwa sam baka cikin kyakkyawan yanayi fad'a min mai yake faruwa kuma gaskiyar zaka fad'a dan Allah.?"

Kallonta kawai yake daga bisani ya kai hanayensa ga nata ya d'an matse kad'an ta yanda ba zata ji zafi ba, ya qara da sunbatar hanayenta duka biyun cikin mutuwar jiki da sanyin murya yake furta mata kalmar ki yafemin. "Yaya Ahmad wai a kan me kake magana mai yasa kake nai man yafiya a gareni.?" Yayi shiru kad'an sannan ya amsa ta "Ahlam 'yarmu ta mutu kuma wannan duka laifi na ne, ni sam na kasa baku kulawa yanda ya kamata sannan kuma na kasa kareku, sabo da kuskure na d'aya tak ga shi mun rasa 'yarmu dan Allah ki yafemin." Wani irin kallo take yi masa mai cike da jin mamakin sa sosai cike da damuwa take magana. "Yaya Ahmad a zahirin gaskiya hakan yana da zafi sosai sannan kuma da matuqar k'una, na damu sosai musamman sabo da *Adyan* shi yana da buri sosai a kan qanwarsa. Ko yaushe cikin zancan ta yake shi yayi matuqar damu sosai a kanta sam bana jin cewar zai iya jure wannan, Yaya Ahmad idan *Adyan* ya san da wannan to hakan zai yi matuqar cutar da shi sosai, ni kuma ba zan iya jure ganin yarona a cikin mummunan yanayi ba ban kuma san ya zanyi ba."

"Ahlam shi yasa sam bai kamata a ce shi ya san a salin gaskiyar ba ba zai ta'ba sanin wannan ba. Ni zan kula da komai to fatan zaki yafemin a kan kuskure na dan Allah.?" "Yaya Ahmad wannan ba laifin ka bane to ka dena cutar da kanka haka dan Allah." Magana take yayin da take share masa kwalla lokaci d'aya kuma suka yi hugging juna. Sun jima sosai suna jimamin rashin yarinyar su sannan daga bisani suka yi barci bayan kwana biyu, Dr Sam yake sanar da Ahmad cewa Ahlam ta samu matsala wacce ba zai yu ta iya aihuwa ba. A zahirin gaskiya hankalin Ahmad yayi matuqar tashi sosai da jin wannan mummunan labarin, amma kuma duk yanda ya kai mak'ura to ba zai iya canja kaddarar ta ba, wanda wannan dalilin ne yasa ya sanya wa zuciyar sa salama ya d'auki dangana. Sai dai kuma sam ya gagara iya sanar da Ahlam abin da yake faruwa da ita ya 'boye mata gaskiyar, sabo da sam ba zai iya jure ganin irin k'uncin da zata shiga ba wanda wannan dalilin ne yasa ya 'boye mata gaskiyar.

Ahlam ta samu tsayin mako d'aya asibiti sannan ta samu sallama zuwa gida hakama *Adyan* ya samu lafiya sosai, haka suka ci gaba da zama cikin kyakkyawan yanayi ba tare da Ahmad ya sanar da ita komai a game da ita ba, wani yammaci zaune take tana yiwa yaronta karatu wayar ta ta d'auki ruri *Adyan* ne wanda ya tafi ya d'auko mata wayar ya bata, ta kar'ba tana murmushi ta sunbacesa tare da furta masa kalmar Allah yayi albarka ya amsa da Amin yana dariya ita kuwa murmushi take, ganin sunan Ahmad a kan wayar yasa murmushin ta ya qaru ta d'aga kiran tare da fad'ar sunansa. "Yaya Ahmad yau kayi dogon zango ka tafi ka barmu da kewarka sosai fad'a min kana ina.?" "Kina magana da Dr Sam ne ba Ahmad ba, mujin ki ya samu hatsari yana asibiti." Cike da firgici rud'ani tare da tashin hankalin abin daya fad'a take magana. "Dr Sam to ya jikin nasa fatan yana samun sauki sosai.?" Yayi shiru na jim kad'an sannan ya amsa ta, "ni ba zan iya sanar dake komai a game da shi ba a yanzu kiyi hak'uri please."

"Shikenan gani nan tafe yanzu." Da kuma haka suka yi sallama ta tashi ta shiga ciki ba jimawa ta fito tare da tashin *Adyan* sun fita zuwa asibiti, sun isa asibiti kai tsaye office d'in Dr Sam ta nufa sai dai tayi rashin sa'a bai ya ciki ta shiga tambayar sa an fad'a mata cewar yana aiki, bayan wani lokaci ta samu had'uwa da shi cikin hanzari tare da nuna kulawa take tambayar sa jikin mujin ta. "Doctor ya jikin Yaya Ahmad ka fad'a min mai yake damunsa please.?" Yayi shiru kad'an sannan ya amsa ta, "Madam gaskiyar ita ce mujin ki bai ya cikin kyakkyawan yanayi yanzu haka da akwai buqatar a yi masa aiki cikin gaugawa sosai, to muna buqatar da a cike mana takarda sannan kuma a yi duk wani abin daya dace." "Doctor ni zanyi mu tafi to amma ka sani ya zama dole Mujina ya samu lafiya, lallai ina matuqar buqatar Mujina a tare da ni hakama yaronmu yana buqatar mahaifin sa a tare da shi sosai. To yanzu ina san ka kalli cikin ido na sannan kayi man alkawarin cewar Mujina zai samu lafiya."

Magana take yayin da take kuka hakama *Adyan* kuka yake ganin tana kuka, Dr Sam ya jinjina mata ka a lamar eh ta fara kiran layin Abbu ta sanar da shi abin da yake faruwa sannan suka tafi, tayi duk wani abin daya buqata daga gareta bayan wani lokaci a ka shiga da shi d'akin tiyata. Lokaci zuwa lokaci su Abba suke kiran ta suna tambayar ta abin da yake faruwa, haka-haka dai har zuwa lokacin da a ka fito da shi daga d'akin tiyata Dr Sam ya sanar da ita cewar yana samun sauki. Tayi matuqar yin farin ciki da hakan sosai bayan kwana biyu kwance yake yana barci, Dr Sam ya shigo domin ya duba jikin sa bayan ya qarasa ya sauke kallonsa ga Ahlam yana cewa.

"Mrs Ahmad ga a lama ke da kuma mujin ki irin kaddaran ku d'aya, hakan yayi kyau sosai sabo da a yanzu ba wani wanda zai cutar da ďaya a cikin ku. Mrs Ahmad gaskiyar ita ce mujin ki ba zai iya aihuwa ba kamar dai ke, abin farin cikin shi ne kuna da wani ďa hakan yayi kyau sosai ina muku fatan alkhairi kyakkyawar rayuwa sai an jima." Ya tashi ya fita ya bar Ahlam cikin wani irin mummunan yanayi mara kyau yayin da take kuka kuma kuka sosai. Cikin barci ya rika jiyo sautin kukan ta sannu a hankali yake bud'e idanuwansa har suka bud'e cike da firgici yake yi mata magana. "Ahlam mai yake faruwa dake mai ya saka kike kuka fad'a min wani abu ina *Adyan* karki fad'a min cewar wani abu ya faru da shi.?"

Ta sanar da shi cewar *Adyan* yana school ta kuma qara da sanar da shi abin da Dr Sam ya sanar da ita a game dasu. Ya nisa tare da jan numfashi nan ya shiga rarrashin ta yana bata magana cikin qauna da soyayya har ta iya fahimtar sa, sam basu da wani za'bi a game da kaddaran su wannan yasa suka amince da gaskiyar tare da d'ora duka kulawar su a kan *Adyan.* Bayan mako d'aya su Umma suka shigo musamman sabo da su duba jikin Ahmad hakan yayi matuqar yiwa su Ahlam dad'i sosai, Ahmad yaci da samun kulawar doctor har zuwa lokacin da jikin sa ya warware, ya samu tsayin mako biyar asibiti sannan ya samu sallama zuwa gida hakama har zuwa wannan lokacin su Ummi suna nan. Sun samu wata biyu a nan tare dasu sannan suka tafi wanda zuwa wannan lokacin Ahmad ya samu lafiya sosai bayan wasu shekaru...............




*BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.*
[1/6, 11:50 AM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑

*THREE BROTHER'S*

👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑

*Page 14*

*Sister 'yar gata ya k'arin hak'uri Allah ya gafarta mata ya mata rahma, Allah ya yafe mata Ubangiji ya bata gidan al'janna Amin Allah ya jikan iyayenmu baki ďaya Amin ya hayyu ya kayyum.*
✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/


*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.


*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*


Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.



Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.



*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*Tuesday 04/01/2022*

*Time 01:25pm*

*Typing..............*

Zuwa wannan lokacin *Adyan* yana da shekaru takwas, hakama zuwa wannan lokacin su Ahlam sun kammala karatu inda suke matsayin doctor, har sun fara aiki wanda hakan ne ya hana su komawa gida Nigeria. Bayan wani lokaci *Adyan* ya samu hutun makaranta hakama su Ahmad suna hutun k'arshen shekara, ganin hakan ne yasa Ahmad ya had'a musu visa domin kai wasu Abba ziyara. Da fari Ahlam sam bata yarda da hakan ba sai daga bisani sannan ta aminta da hakan, sunyi shirin su tsab na tafiya bayan mako d'aya jirginsu ya tashi zuwa qasar Nigerian.

*Nigerian.*

Tsaye yake a gefen hanya banda kuka ba abin da yake yana haka sai ga Prof, da sauri ya fito mota ya isa inda yake yana fad'ar sunan sa amma bai amsa ba. ya riqo hanun sa sun shiga mota ya shiga tambayar sa mai yake faruwa da shi cikin muryar kuka yake magana. "Dady gobe da akwai taron Mother day ina kuka ne sabo da ni bani da Mama, ita Mama na ta tafi ta barni sam bai kamata a ce ta mutu a wannan lokacin ba sabo da ina matuqar buqatar ta sosai. Amma ita sam bata wani damu da ni ba hakan yana saka ni k'unci sosai, Dady mai yasa Mama ta mutu mai yasa ta tafi ta barni? Dan Allah kace ta dawo garemu please." Magana yake yayin da yake kuka kuma kuka sosai cike da jin tausayin tare da qaunar sa yake magana. "Ka dena kuka *Adeel* sabo da Dady yana tare da kai, sannan kuma yana nan domin ka *Adeel* ni zan kasance da kai iya rayuwa ta, ba zan ta'ba barin ka ba to kayi farin ciki sannan kuma ka dena k'unci, sabo da hakan barazana ne ga lafiyar ka ni kuma sam ba zan jure hakan ba. Ina sanka yarona ina matuqar qaunar ka sosai zo nan."

Ya janyo sa jikin sa yana rarrashin sa yana wani lalla'basa da haka har suka

12 / 48