Author : Bil-Fauzee U-Adyan Category : Hausa Novels 001
yayin da Prof Abbas yake ta aikin kai komo sam ya gagara samun natsuwa, sai fatan cikar burin sa yake na samun yaro ďaya tak kamar yanda Aisha tayi masa alkawari. Bayan wani tsayin lokaci da suka d'auka da ita sosai a d'akin tiyata sun fito, cikin hanzari tare da nuna kulawa Prof ya isa ga Dr Salim yana tambayarsa mai yake faruwa. "Sam ba buqatar ka damu sosai sabo da mun yi nasaran ciro mata baby boy, yaron kyakkyawa ne sosai kamar iyayen sa Mummyn sa da Dadyn sa to kuyi farin ciki sosai, yanzu zamu canja mata guri zuwa ďakin hutu sannan zaku had'u da babyn a can."
Cike da farin ciki da d'auki Prof yayi hugging d'in sa yana furta masa kalmar. "Ina godiya sosai Dr Salim ni sam ba zan iya biyanka wannan ba saidai kawai nace da kai na gode sosai." Sai kuma zuwa wannan lokacin ne ya sake sa daga rungumar da yayi masa, shi kuwa murmushi kawai yake yayin daya gagara furta masa komai, sai ma juya wa da yayi ya koma ciki su kuma sun nufi d'akin da za a kai ta. Zuwan su yayi daidai da zuwan su Dr Salim nurse sun shirya ta a kan gado tare da shinfid'e babyn daga gefen ta, bayan sun qarasa sun juya sun fice Dr Salim kuma ya buqaci ganin sa ya tashi sun fita. Bayan tafiyar su Umma ta isa gurin Aisha ta zauna a kujeran da take kusa da gado, sai wani kallon ta ƴarta take cike da jin tausayin ta sosai ta kai hannun ta ga babyn tare da d'aukan sa, sai wani kallonsa take kallo sosai cike da d'auki da soyayyar sa take magana.
"Jikana ina farin cikin had'uwa da kai sosai, na so kuma nayi burin a ce kai ka had'u da Kakan ka tabbas daka samu duka soyayyar sa, amma ni zan kula da wannan zanyi duk wani abin da na san zai saka shi farin ciki sosai wannan alkawari ne yarona, ina sanka sosai Allah ya baiwa Maman ka lafiya Amin." A can gurin su Dr Salim kuma suna fita kai tsaye office d'in sa ya nufa da shi sun shiga ciki ya fara rufe ofar sannan suka zauna. Prof sai wani kallonsa yake kallo sosai domin kuwa ya gama fahimtar cewar ba qlau yake ba cike da firgici da rud'ani yake magana. "Dr Salim fad'a min wani abu shin da akwai wata matsala ne gaskiyar zaka fad'a.?" Yayi shiru kad'an sannan ya jinjina masa ka a lamar eh cike da firgici rud'ani da kuma tashin hankali yake magana.
"Dr Salim miye matsalar kawai dai ka sanar da ni koma miye ka ji ko.?" Yayi shiru na jim kad'an sannan ya amsa shi, "Prof gaskiyar ita ce Madam yara uku ta aifa amma nayi kamar dai yanda nayi umurni, zuwa yanzu yaran guda biyu sun isa gidan marayun da ka ce a kai su kuma ba wani wanda zai san da wannan nayi alkawari." Prof ya jinjina ka yana cewa, "Dr Salim kawai dai ka tabbatar da hakan domin idan har wannan zancan ya futa to fa ni zan hukunta ka da kai na, lallai karka yarda ka bar wannan sirrin ya fita ko da mai zai faru ka ji ko." Ya jinjina masa ka yana furta masa kalmar, "Prof ba wanda zai san da wannan kai ka biya ni farashin da ba zan iya yi ma yankan baya ba to zaka iya yarda da ni ka ji ko." "Kawai dai ka tabbatar da hakan." Ya jinjina masa ka a lamar to shi kuma ya tashi yayi tafiyar sa wanda kuma kai tsaye d'akin da Aisha take ya nufa.
Ya shiga ciki ya samu Umma rungume da babyn cike da d'auki ya isa inda take tare da kar'ban babyn sai wani kallonsa yake kallo sosai, lokaci d'aya yaji soyayyar yaron da qaunar sa suna shigar sa ta ko ina jikinsa yayin da farin ciki yake ta shigarsa, sai wani kyakkyawan murmushi yake mai tare da ar dariya ya sunbace sa a ka da ma fuskarsa gaba d'aya. Umma kuwa sai wani kallonsa take tana murmushi ta gama fahimtar cewa yana farin cikin had'uwa da yaronsa sosai. "Yarona *Adeel* Dadyn ka yana matuqar masifar qaunarka fiye ma da yanda yake sanka, ina sanka *Adeel* soyayyar da ban ta'ba yiwa wani ba a duk fad'in duniyar nan, Allah ya raya ka ya kuma sanya wa rayuwarka albarka Allah ya baiwa Mummyn ka lafiya ta yanda zamu kasance tare da juna."
Ya qara sunbatarsa tare da qara saka shi jikin sa farin cikin sa yana faruwa Umma dai sai kallonsa take tana murmushi, sannu a hankali yake tafiya har ya isa inda Aisha take ya zauna gefen ta sai wani kallonta yake kallo sosai ya shafi fuskarta tare da sunbatarta. "Rabin raina ina godiya sosai a gareki da kika cika min alkawarin ki yau kin bani abin da na jima ina fatan samu, yau gani rungume da yarona *Adeel* hakan yana matuqar saka ni farin ciki sosai, ina fatan ki samu lafiya cikin sauri ta yanda zamu kasance tare da yaronmu ina sanki sosai Allah ya baki lafiya Amin." Farin cikin Umma ya qaru sosai ganin irin yanda Prof yake nuna wa arta kulawa sosai tare da bata duka soyayyar sa.
"Abas a zahirin gaskiya ina farin ciki sosai da irin yanda kake nuna wa Aisha kulawa sosai, ni sam bani da wani abin da zan iya biyanka da shi saidai kawai nace na gode sosai Allah yayi albarka ya albarkaci rayuwar yaronku Allahumma Amin." Ya amsa da Amin yana murmushi ita ma abin da take yi kenan. Misalin arfe 06:00pm Aisha ta farka daga dogon barcin da tayi, sannu a hankali take bud'e idanuwanta har suka bud'e sai wani kallon d'akin take ta sauke kallonta ga fuskar Umma, wadda bama ta san cewar ta farka ba ta ganta rungume da babyn ta wanda bata da sani a kan macace ko namuji. Lokaci d'aya tsoro da firgici suka shigeta rashin ganin Prof ya qara d'aga hankalin ta sosai, lokaci d'aya ta fara zubar da kwalla mai tsananin zafi da una sosai bata ankara ba sai kuka, sautin kukan ta ne ya sanar da Umma cewar ta farka da sauri ta kai kallonta gareta cike da firgici ta isa inda take tana fad'ar sunanta. "Aisha mai yake faruwa da ke ne mai kuma yasa kike kuka.?" Ta girgiza mata ka tare da tambayar ta mai ta aifa.
"Aisha d'a namuji ne kika aifa Dadyn sa ya sanya masa suna *Adeel* fad'a min wani abu shin yanzu kina farin ciki.?" Ta jinjina mata ka tana mai furta kalmar, "Alhamdulallah Allah na gode ma daka bani ikon cika alkawarin da nayi wa Mujina, na tabbata Prof yana farin ciki sosai sabo da zuwa yanzu burin sa ya cika domin kuwa shi ya samu abin da yake so, hakan yayi kyau Alhamdulallah! Alhamdulallah!! Alhamdulallah!!!"
Umma dai kallonta kawai take tana murmushi mai had'e da ar dariya ba tare data furta mata komai ba, ba jimawa sosai Prof ya dawo yayi farin ciki sosai da yanda yaga Umma tana fira da Aisha, wanda hakan ne ya tabbatar masa da cewar tana samun sauki sosai taci gaba da samun kulawar doctor, ta samu mako d'aya sannan a ka bata sallama zuwa gida inda daga bisani suka shirya liyafar bikin suna. An yi komai na ba jinta da ban girma bikin yayi kyau sosai kuma ya qayatar da duk wanda ya halarta, sunci gaba da bawa yaronsu kulawa sosai dukansu suna cikin kyakkyawan yanayi tare da nuna wa yaronsu soyayya musamman Prof bayan wata shida. Zaune take ta buga wani irin uban tagumi ga wasu zafafan hawaye suna fita daga cikin idanuwan ta masu tsananin zafi da una sosai, kallo d'aya tak zaka yi mata ka fahimci cewar tana tare da damuwa mai girman gaske. Tana haka sai ga mai gidan ta ya shigo ya kuma same ta a cikin wannan mummunan yanayin, yayi tsaye jikin ofa sai wani kallonta yake kallo sosai ya nisa tare dajan numfashi yana mai sauke a jiyar zuciya tare da girgiza ka ya nufi inda take.
Ya zauna kusa da ita kusa sosai wanda kuma har zuwa wannan lokacin kallonta yake kallo mai cike dajin tausayin ta sosai, ya d'ago fuskarta wadda ta had'a da guiwa tana kuka sai wani kallonta yake kallo sosai ya shiga share mata kwalla, tare da sunbatarta yayi hugging d'in ta yana rarrashin ta tamkar wata qaramar yarinya. "Kiyi hak'uri dan Allah ki yafemin na san cewar ni sam ba muji na gari bane a gareki sabo da na gaza baki abin da kike buqata daga gareni, amma kuma Abida hakan yana matuqar cutar da ni sosai ta yanda ba ma zan iya kallon kai na na kuma kira kai da namuji ba. Shekarun mu uku da aure amma na kasa baki d'a ni na gaza amma duk da haka ni ba zanso kici gaba da cutar da kanki haka ba, Abida wallahi wannan yanayin naki yana matuqar cutar da ni sosai fiye ma da a salin cutar da take tare damu. Abida wani sati ne tafiyar mu jigawa to ya kamata mu fara shirin mu ki sanar da ni duk abin da kike so ni kuma zanyi nayi alkawari."
Shiru bata yi magana ba wanda kuma har zuwa wannan lokacin kuka take jin shirun yayi yawa yasa ya anbaci sunanta amma bata amsa ba, ya sake ta daga hugging d'in da yayi mata ya shiga share mata kwalla yana rarrashin ta. "Abida shin ba zaki dena cutar da ni ta wannan hanyar ba? Dan Allah ki dena a zabtar da ni haka please." Magana yake cikin wani irin yanayi mara dad'i yayin da damuwa tayi yawan gaske a tare da shi sosai, ba kuka yake ba amma kuma idanuwansa kwalla suke zubar wa mai tsananin zafi da una sosai, kuma zamu iya kiran abin da kukan zuci wanda yafi na zahiri ciwo cike da unci take magana yayin da take kuka.
"Yaya Anas ni sam bana ganin gazawar ka a game da wannan sabo da kai kayi duk abin da zaka iya, abin farin cikin shi ne daya kasance cewar dukanmu qlau muke kawai dai lokaci bai yi ba, amma kuma ni duk da haka na damu sosai idan ka yarda to ina san mu d'auki rainon mace ko namuji, ni sam bani da za'bi kawai dai burina na kasance uwa kuma uwa ta gari ga yarona ko yarinyata wannan ne kawai abin da nake so." Yayi shiru yana nazari daga bisani kuma ya jinjina mata ka yana cewa. "Shikenan na aminta da hakan yaushe zamu tafi.?" Cike da d'auki take furta masa kalmar mu tafi yanzu ya girgiza ka yana cewa. "Zamu tafi ne kawai idan ke d'in nan kin yarda kinci abinci." "Eh zanci." "Wai da gaske zaki ci.?" Ta jinjina masa ka tare da furta eh yayi murmushi sosai mai tare da ar dariya, ya shafi fuskarta tare da sunbatarta sannan ya tashi tare da tashin ta sun nufi tebur domin suci abinci.
Sun isa ga tebur yaja mata kujera ta zauna ya fara zuba abincin sannan ya zauna, sunci gaba da cin abinci cikin kyakkyawan yanayi bayan sun qarasa suka shirya tsab suka nufi gidan marayu domin d'aukar raino. Sun isa gidan sun kuma samu yin magana da shugaban gurin tare da sanar da shi buqatar su, yayi matuqar farin ciki sosai da hakan nan kuwa a ka tafi dasu gurin da yara suke, sai wani kallon yaran suke kallo mai cike dajin tausayin su sosai Abida ta sauke kallonta ga wasu yara su biyun wad'an da ga a lama twin's ne, sai kuka suke kuma kuka sosai cike da tausayin su tare da nuna kulawa ta isa ga yaran tare da d'aukan su ta rungumasu jikinta tana rarrashin su, Anas sai wani kallonta yake kallo sosai mai cike dajin tausayin ta hakama mutanan da suke tare dasu ya isa inda take tare da dafata yana fad'ar sunanta.
"Qlau kike.?" Ta jinjina masa ka tare da furta eh yaci gaba yana cewa. "Hakan yayi kyau to yanzu fad'a min mace zamu d'auka ko namuji.?" Tayi murmushi sosai mai tare da ar dariya sannan ta amsa shi cike da d'auki take magana. "Mujina ni na riga dana za'bi wad'an nan yaran da suke kwance a kan kafad'ata sune za'bina." "Rabin raina amma zaki iya hidimar yara biyu a lokaci d'aya kuwa.?" Ta jinjina masa ka tare da furta masa, "eh Abban twin's zan iya kuma zan kasance uwa ta gari ga yarona tare da taimakon ka to zaka iya yarda da ni." "Shikenan ina farin ciki sosai Maman twin's." Ya fad'a tare da sunbatarta a ka dama yaran da suke rungume jikinta ya kuma qara da yin hugging d'in su dukansu yana murmushi ita ma abin da take yi kenan.
Shugaba dama jama'ar sa sai wani kallonsu suke suna murmushi bayan sun sake juna shugaba ya sanar dasu duk wasu dokoki a game da raino sunyi duk abin da a ka buqata, sannan kuma daga bisani suka d'auki twin's suka nufi gida dasu yayin da farin ciki yayi yawan gaske a tare dasu sosai musamman ma Abida. Kafin su isa gida sun fara zuwa sunyi wa yaran siyayya ta komai da komai na buqata sannan suka isa gida. Ai kuwa tin daga wannan ranar duhun da yake tare dasu ya gushe suka fara sabuwar rayuwa cikin farin ciki da jin dad'i sosai, yayin da suka d'ora duk wata kulawar su a kan yaran su wad'an da suke jira da Hassan da Hussaini, sun kuma ci gaba da shirin tafiya jigawa kasance cewar a can ne a ka mai da Anas aiki sunyi shirin su bayan kwana biyu suka kama hanyar jigawa.
Suna cikin tafiya sai gani su kai an sha gaban su da mota an fashi ne zasu kai su goma koma fiye da haka, lokaci d'aya suka shiga anbatar kalmar Innalillahi wa'inna'ilaihi raji'un sun shiga tambayar su kud'i sun basu duk abin da suke da shi. Amma hakan bai sa sun barsu sun tafi ba inda suka rufe su da duka, duka suke yi musu irin na rashin tausayi wanda har sai da suka suma. Hakan bai isa ba sun d'auki yaran sunyi tafiyar su yayin da suke ta tsala ihu kuka suke sosai, wanda zamu iya cewa kukan yunwa ne suke amma ko rarrashi basu iya samu daga garesu ba. Sai ma fad'a da tsawa da suke yi musu Allah sarki yara abin tausayi, bayan wani lokaci Anas ya farka daga suman da yayi ya nufi gurin Abida yana anbatar sunanta tare da d'an buga fuskarta.
Ta tashi wani a firgici cike da firgici sun tashi sun fad'a mota wanda kuma a nan ne suka fahimci cewar twin's basa nan, cike da firgici rud'ani tare da tashin hankali sun fito mota yayin da suke anbatar sunayen su, sun duba ko ina na gurin amma basu yi nasaran ganin su ba. A zahirin gaskiya hankalin su yayi matuqar tashi sosai musamman ma Abida sai wani irin kuka take kuma kuka sosai, duk ta kid'ime ta fita haiyacinta yayin da bakinta yake ta anbatar sunan twin's, Anas ya shiga rarrashinta yana bata magana sai wani lalla'bata yake wanda shi ma kuka yake, amma kuma shi kukan zuci yake yayin da idanuwan sa suke zubar da kwalla mai tsananin zafi da una sosai. Ya tashi tare da tashin ta sun nufi mota ya bud'e ofa tare da saka ta ciki shi ya shiga sun fice zukatan su cike da uncin rashin twin's....................
*BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.*
[12/20/2021, 9:23 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑
*THREE BROTHERS*
👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑
*Page three*
*Sister Ferdy wannan page d'in naki ne.*
✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*
*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*
Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.
*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*
*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*
Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.
Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.
*Bismillahir Rahmanir Raheem*
*Monday 20/12/2021*
*Time 10:00am*
*Typing............*
"Oga ya zamu yi da waɗannan yaran sai kuka suke da alama yunwa suke ji to ya zamu yi kenan.?" "Ka rufe musu baki ko kuma ku basu abin da muke da shi a nan." "Oga su ďin fa yara ne to ta ya kuma zasu ci irin abincin da muke ci wanda gaba d'aya ba shi da ɗanɗano." Rabi'u ya dakatar da shi cikin tsawa, "T. K ya isa kayi shiru haka, su ďin wasu ahalinka ne da zaka wani damu a kansu? Yaushe zuciyarka ta zama mai tausayi shin ba yanzu nan ka gama dukan iyayen su ba? Amma shi ne kake ƙoƙarin nuna min cewar kai mai tausayi ne, to bara ka ji wallahi tallahi idan har ka qara yi man maganar yaran nan cikin nuna jin tausayi to sai na yanka su, kuma cikin nuna rashin tausayi sabo da sai na fara