Author : Bil-Fauzee U-Adyan Category : Hausa Novels 001
duka soyayya ta, masoyina gaskiyar ita ce kai ne nan abin da nafi so fiye da komai dana mallaka a rayuwata. *Adnan* ni zan iya yin komai sabo da zanma iya baka rayuwata gaba d'aya, ina sanka sosai d'ana Allah ya ma albarka ya kuma sanya wa rayuwarku albarka data yaronku gaba." Ya amsa da Amin tare da k'ara shigewa jikin sa, sun jima sosai a nan sannan daga bisani Papa ya ja mota suka tafi. Sun isa gida zuwa wannan lokacin barci ya fara kama idon sa, Papa ya fito ya zaga ya bud'e masa k'ofa ya rik'o hanunsa ya fito, ya janyo sa jikin sa sun shiga ciki sun samu su Mamie zaune a parlour, ganin Papa ri e da shi ya tabbatar musu da cewar ba lafiya ba, yasa su *Afnan* tashi tsaye cikin hanzari har tana sarkewa Mamie take magana.
"Subhanalillah Innalillahi wa'inna'ilaihi raji'un mai yake faruwa da shi ne haka.?" Sun k'arasa ciki Papa ya shinfid'e sa a kan doguwar kujera, kafin Papa ya amsa ta *Adnan* ya amsa ta. "Mamie ina lafiya ki yarda da ni qlau nake to dan Allah karki yi k'unci kin ji ko please." "Rabin raina kawai kana san ka kwantar min da hankali ne, amma gaskiyar ita ce baka da lafiya kuma kana tare da k'unci sosai, wanda kuma hakan barazana ce ga lafiyar ka sosai ya kamata mu tafi asibiti yanzu." "A'a Mamie ni qlau nake ina lafiya sannan kuma." Lokaci ďaya kuma wani wawan barci yazo ya d'auke sa, Mamie ta mai da kallonta ga fuskar tare da fad'ar sunan sa. *"Abban Adnan* ka sanar da ni gaskiyar abin da yake faruwa da yarona? Mai ya saka shi k'unci sosai har haka sannan kuma mai ya saka kazo da shi nan a maimakon asibiti.?"
Shiru bai amsa ta ba yayin da k'unci da damuwa suka yi yawan gaske a tare da shi sosai. Yanayin sa ya k'ara tabbatar musu da cewar ba lafiya ba, cikin kasa-kasa da murya tare da kwantar da ita *Afnan* take magana. "Papa wai mai yake faruwa ne mai ya saka ku biyun kuke tare da k'unci sosai? Na tabbata wani abu ya faru daku to dan Allah ka sanar damu abin da yake faruwa.?" "Zan sanar daku komai bayan ya samu lafiya." Sun jinjina masa ka a lamar to ganin yanda yake ta kiran layin sa bai d'aga ba, yasa shi kiran layin *Afnan* domin ya ji ko lafiya, zaune suke yayin da suka saka *Adnan* da kallo wayar *Afnan* ta d'auki ruri, ganin mai kiran ta yasa ta d'aga kiran ba kuma tare data furta masa komai ba daga ciki ya anbaci sunan ta. *"Afnan* Aboki fa tin da jimawa nake kiran layin sa amma baya d'aga wa shin qlau yake kuwa.?"
Tayi shiru kad'an sannan ta shiga sanar da shi abin da yake faruwa, cike da firgicin abin data fad'a yake magana. *"Afnan* to mai ya saka baki sanar da ni ba? A k'alla zan duba shi sannan kuma na ba shi kulawa sosai gani nan tafe." Ta fara da ba shi hak'uri sannan suka yi sallama, ba jimawa sosai sai ga *Adyan* wanda kuma tare yake da *Alishart.* Ya fara gaisawa dasu Mamie sannan ya shiga duba shi, bayan ya k'arasa ya mai da kallonsa gasu Papa tare da fad'ar sunan *Afnan. "Afnan* shin yayi wani abin daya gajiyar da shi ne? Ko a'a wani ya b'ata ransa sosai wanda har ya saka shi k'unci sosai? *Afnan* ki sanar da ni gaskiyar abin da yake faruwa da Abokina waye wanda yake da alhakin cutar da shi sosai har haka.?"
"Ban sani ba Doctor sai dai kayi magana da Papa, sabo da shi ne wanda yake da sani a kan komai." Ya mai da kallonsa ga Papa tare da tambayar sa abin da ya faru da *Adnan,* ganin yanda yake tayi masa magiya yasa ya yanke shawaran sanar da shi. *"Adyan* yayi musayar baki ne da *Abban Adeel* ne." "Mine shi har ma ya isa ya cutar da shi sosai har haka, a'a ni ďin nan zan hukunta shi a bisa zunubin sa, sabo da ba zan tab'a gafarta wa duk mutumen daya cutar da Aboki na ba. Yanzu ka sanar da ni a wane asibiti Prof yake da akwai buqatar nayi magana da shi yanzu.?"
Papa ya girgiza masa ka tare da furta, "A'a ďana ba buqatar sai ka tafi can sabo da Abokin ka yana matuqar buqatar ka a yanzu, to ya kamata ka kasance a nan tare da shi ina ga hakan zai fi." Ya jinjina masa ka a lamar to tare da ciro wayar sa, ya shiga dannawa ba jimawa ya kara a kunne ba jimawa ya fara magana. *"Adeel* na san cewar kana tare da Prof to ka saka ni a amsa kuwa zanyi magana da shi." Ya amsa shi da to yayi kamar yanda ya fad'a, shi kuma yaci gaba da magana. "Prof a gaskiya yau ďin nan ka aikata min mummunan zunubi, ta hanyar cutar da Abokina da kayi to kayi fatan kar ya jima sosai cikin wannan yanayin, ta yanda zan sauk'ak'a maka hukunci ko kuma dai na cutar da kai sosai." Yana kai k'arshen maganar sa ya kashe wayar sa, ba ma tare daya jira ya ji abin da za shi fad'a ba......................
*BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.*
[3/12, 7:55 AM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑
*THREE BROTHER'S*
👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑
*Page 49*
✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*
*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*
Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.
*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*
*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*
Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.
Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.
*Bismillahir Rahmanir Raheem*
*Thursday 10'03/2022*
*Time 03:24pm*
*Typing..............*
Duk kan su sun gama fahimtar cewa yana cikin fushi sosai, sun riga da sun san waye *Adnan* a garesa shi yasa sam basa mamakin sa. Parlour yayi shiru na jim kad'an Papa ne ya kau da shirun parlour ta hanyar fad'ar sunan *Adyan. "Adyan* dan Allah karka yi fushi sosai sabo da hakan zai iya cutar da kai sosai, na san cewar ka damu sosai a kan abokinka, to zai kasance lafiya insha Allah, na tabbata duka wannan zai wuce komai zai zama daidai, ni da kai na zan gyara komai to zaka iya yarda da ni." "Papa wannan a game da abokina ne to zan iya aikata komai ga mutumin, da yayi yunk'urin cutar da shi koma waye Papa na rantse." Da sauri Papa ya rufe masa baki tare da furta masa a'a. "A'a ďana dan Allah karka fad'i komai, kawai ka barni zan daidaita komai nayi ma alkawari insha Allah." *Adyan* dai kallonsa kawai yake yayin da yake magana da zuciyarsa.
"Na rantse idan wannan yanayin ya cutar da d'an uwa na, to sai na tabbatar da cewa Prof ya shiga k'unci wanda har sai ya gwammaci mutuwa fiye da rayuwa. Ya aikata abubuwa da dama a rayuwarsa amma wannan shi ne, babban zunubin da zai aikata a gareni wanda kuma zai karb'i hukunci daidai da zunubin sa. Kayi hak'uri Papa sabo da ba zan iya amincewa da tayin ka ba dole na cutar da Prof, wannan alkawari ne kuma zan tabbatar cewa na cika alkawari na insha Allah." Bayan wani tsayin lokaci daya d'auka a kwance ya farka, sannu a hankali yake bud'e idanuwansa har suka bud'e, sai wani kallon mutanan da suke tare da shi yake suma haka kallonsa suke. Lokaci ďaya kuma suka shiga furta masa kalmar sannu, kamar ba zai amsa ba sai daga bisani ya amsa su, zamu iya cewa har zuwa wannan lokacin baya cikin kyakkyawan yanayi, jiki a san yaye ya tashi ya nufi d'akin sa Papa zai bisa, *Adyan* ya dakatar da shi tare da tashi ya bisa a baya. Ya shiga ciki ya same sa sai safa da marwa yake, *Adyan* kuwa sai kallonsa yake daga bisani kuma ya ja hanun sa suka tafi suka zauna. Sun samu shiru na muntuna biyu zuwa uku sannan *Adyan* ya fara magana.
"Aboki mai ka aikata ne haka a wane dalilin ne yasa zaka yi musayar baki da Prof? Aboki hakan bai dace ba sannan kuma ka sab'a wa yarjejeniyar mu, sabo da muna shirya komai ne a tare amma kayi wannan ba tare daka sanar da ni ba mai yasa? A k'alla ya kamata ka sanar da ni ko ba komai zan iya kareka daga cutarwar sa. Kai ba kawai Abokina bane a'a kai ďin d'an uwa na ne kuma abin da nafi so fiye da komai, Aboki bayan Appa da Ammie to kai ne abin da nafi so shi yasa nake matuqar baka kulawa sosai. Aboki nayi matuqar damuwa sosai dana kira layin ka baka d'aga ba, nayi matuqar shiga firgici da rud'ani tare da tashin hankali sosai, a lokacin da *Afnan* ta sanar da ni halin da kake ciki, sam na kasa jure ganin wannan yanayin naka, Aboki da a ce wani abu ya faru da kai fiye da haka to da ba zan tab'a yafewa kai na ba na har abada. Sabo da na kasa kare ďan uwa na wannan abin kunya ne da bak'in ciki a gareni, Aboki wallahi tallahi ba zan tab'a yafe maka ba idan har ka k'ara aikata haka, sannan kuma zanyi matuqar yin fishi da kai sosai to yanzu kayi min, alkawarin cewa ba zaka k'ara yin komai ba tare da sani na ba dan Allah." Yayi shiru kad'an tare da jan numfashi yana mai sauke a jiyar zuciya, cikin mutuwar jiki da sanyin murya yake magana tamkar da zai saki kuka.
"Kayi hak'uri Aboki bawai dan karan kai na, na had'u da Prof ba a'a wannan buqatar Mum ne, sabo da tana da buqatar had'uwa da *Adeel."* Na ya shiga sanar da shi komai cike da jin mamakin abin daya fad'a *Adyan* yake magana. "Aboki wai mai kake fad'a ne haka ta ya Papa da Prof suka kasance 'yan uwa.?" "Ban sani ba Aboki amma dai da jimawa na san cewa Papa yana da Yaya, wanda bai san inda yake ba amma ban tab'a tunanin cewar Yayansa zai kasance a matsayin Prof ba. Papa yana da matuqar kirki sosai banso a ce Prof ya kasance Yayansa ba, amma kuma sam bani da wani zab'i sabo da ba zan iya hana faruwar hakan ba, amma kuma duk da haka ina farin ciki ta wani gefen, abin shi ne har yanzu Papa ahalina ne wannan shi ne abin da nafi komai dad'i. Aboki yanzu ka fad'a min mai zanyi musamman ga Papa sabo da Prof yana barazanar cutar da Papa na." "Aboki mafua ďaya muke da shi a yanzu, kawai mu tafi muyi magana da Papa ya sanar damu komai a game da Prof, ina daga nan ne zamu iya sanin abin da zamu yi." Ya jinjina masa ka tare da furta to sun tashi sun fita, sun kuwa samu su Mamie zaune a parlour bayan sun zauna, *Adnan* ya sauke kallonsa ga fuskar Papa tare da fad'ar sunan sa. "Papa shin ko zaka iya sanar damu wani abu a game da Prof dan Allah.?" Yayi shiru kad'an sannan ya amsa shi.
"Masoyi abin shi ne tin muna yara ni ko da na tashi ban samu Baba na a raye ba. Bayan haka kuma mu talakawa ne sosai wanda abinci ma wahala yake mana sosai, wani lokacin abincin kad'an ne hakan ke sawa Mama take bani ta hana Yayana, abin da bata sani ba shi ne hakan yana matuqar saka Yayana k'unci sosai. Ganin yanayin yana dad'a tsananta sosai yasa Mama ta yanke shawaran kai Yayana makaranta almajiranci, ta had'a masa d'an abin da take da shi ta kai shi makaranta, duk da kasancewa ta yaro sosai d'an shekaru biyar amma nayi kuka sosai, sabo da na saba da Yayana sosai hakama bayan tafiyar sa, a kullum a ko yaushe cikin zancan a kai ne garesa nake bayan wasu watanni, Mama ta shirya tare da duk wani abin buqata muka nufi gurin Yayana domin ziyartar sa. Sun isa makarantar cike da d'aukin had'uwa da shi, inda kuma a nan ne malamin su yake sanar da Mama cewa, tin washe garin ranar da a ka kawo shi makaranta ya gudu ba wanda ya san inda yake."
"Hankalin Mama yayi matuqar tashi sosai da jin wannan mummunan labarin, wanda har sai da yayi sanadin haifar mata da ciwon zuciya, wanda yayi sanadin mutuwar ta na shiga k'unci sosai a wannan lokacin, wani mak'ocin mu Kawu Bala shi ne wanda yaci gaba da kulawa da ni kamar d'an ta, duk da cewar ba shi da mata sannan kuma bai tab'a aihuwa ba. Haka nayi ta fad'i tashi ina nai man kud'i daga bisani na saka kai na a makaranta wato boko, ina S. S. Two Kawu Bala ya rasu na shiga k'unci sosai sabo da shi ďin uba na gari ne a gareni. Haka dai naci gaba da rayuwa da dad'i da ba dad'i tare da bawa karatuna muhimmanci sosai, nayi nasaran kammala karatuna na secondry har ma na shiga babbar makaranta, inda nake karantar fannin shari'a kuma a can ne na had'u da mahaifiyar ka, mun fara ne da k'awance daga bisani kuma ya zama soyayya, duk da cewar na sanar da ita komai a game da ni da kuma rayuwata amma bata gujeni ba, ta bani duka soyayyar ta sannan kuma ta soni da duka zuciyarta. Ita d'in ta musamman ce a gareni hakama iyayen ta sun amince da ni a matsayin siriki, bayan mun kammala karatu muka yi aure."
"Mun aifeka cikin qauna da soyayya bayan wasu shekaru muka aifi qanwarka, amma kuma har zuwa wannan lokacin ban manta Yayana ba. babu wata rana da zata riskeni ba tare dana tuna da Yayana ba, ďana ni na rayu da burin sake kasancewa tare da Yayana amma kuma shi ni matacce ne a gurin sa dama Maman mu, masoyi shi Yayana ko Maman mu bai iya tambaya na ba balantana lafiyar ta. Rabin raina sam na kasa fahimtar abin da yake faruwa da Yayana, ina tunanin da akwai wata cutar da take damunsa ya kamata nayi magana da likitan sa a yi masa a won kwakwalwa, domin gano a salin abin da yake faruwa da shi." Magana yake cikin wani irin yanayi mara dad'i, yayin da damuwa tayi yawan gaske a tare da shi sosai, dukansu sun cika da jin mamakin abin daya fad'a, cike da k'unci bak'in ciki tare da tarin damuwa yake magana yayin da yake kuka.
"Papa sam bai kamata ka damu da mutum irin Prof ba, hakama sam ba buqatar ka saka a yi masa a won kwakwalwa sabo da qlau yake, tsabar rashin mutunci ne kawai a tare da shi, sannan kuma d'abi'ar sa ce cutar da duk mutanan da suke tare da shi. Ya fara ne da Kaka ta da kuma kai Mum da kuma *Adeel* dama wasu da dama, yin hakan halaiyarsa ce to ba wanda ya iya ya canja shi, to ya kamata ka barsa sannan kuma ka dena nuna kulawar ka a kansa. Sabo da sam ba zan jure ganin irin yanda yake cin zarafin ka ba, sabo da ba zanyi k'asa a guiwa ba gurin cutar da shi ba, abin farin cikin shi ne ka kasance d'a na gari a gurin Kaka da Kawu Bala, sannan kuma ka kasance k'ani na gari a gurin Prof duk da k'ok'arin sa na cutar da kai. Sannan kuma muji na gari a gurin Mamie, kuma uba na gari a gareni da qanwata da kuma Besty."
"To wannan kawai ya isa dan Allah kawai ka huta, sannan kuma zanso ka bani damar da zanyi magana da shi dan Allah." Yana cikin magana kuka yaci k'arfin sa yayi shiru ya kamata aikin kuka, da sauri dukansu biyun suka isa garesa lokaci d'aya suka yi hugging d'in sa, sun shiga rarrashin sa sai wani lalla'basa suke suna ba shi magana. *Adyan* ma yana cikin yanayi irin nasa wanda shi ma kwalla yake zubarwa, mai tsananin zafi da k'una sosai zamu iya kiran abin da kukan zuci wanda yafi na zahiri ciwo. Shi ma sun shiga rarrashin sa bayan wani lokaci *Adyan* ya tafi wanda kuma tare da *Alishar* ya tafi, bayan kwana biyu da yamma lis suka nufi gidan Mum domin su duba ta.
Sun isa gidan tare da shiga ciki sun same su suna shirin fita, sun koma sun zauna sun gaisa bayan sun gaisa, *Adnan* ya shiga tambayar su inda zasu tafi Mum ta amsa shi. "Am zamu tafi gurin *Adeel* ne domin mu kai masa abinci, sannan kuma mu duba shi ko yaushe yana asibiti shi yasa muke tare da kewarsa sosai." "Shikenan muma zamu tafi tare daku." "Shikenan ďana zamu iya tafiya yanzu." Ya jinjina mata ka tare da mai da kallonsa ga *Adyan* tare da furta masa kalmar mu tafi, ya amsa shi da to sun tashi sun fice sun isa asibiti kai tsaye d'akin da Prof