THREE BROTHERS Complete Hausa Novels By Bil-Fauzee U-Adyan.txt

Author :  Bil-Fauzee U-Adyan Category :  Hausa Novels 001

Chapter   9 / 48

24K to 27K   out of 142.8K words

πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ‘‘

*Page 10*

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

*wΜΆΜΆΡ” Ξ±rΜΆΜΆΡ” Π²Ρ”Ξ±rΜΆΜΆΡ”rΜΆΜΆ'sΜΆΜΆ ΟƒfΜΆΜΆ sΜΆΜΆΟƒ gΜΆΜΆΟƒlΜΆΜΆdΜΆΜΆΡ”nΜΆΜΆ pΜΆΜΆΡ”nΜΆΜΆ*
*wΜΆΜΆΡ” wΜΆΜΆrΜΆΜΆΓ­tΜΆΜΆΡ” Ξ±sΜΆΜΆsΜΆΜΆΓ­dΜΆΜΆΓ­ΟƒuΜΆΜΆsΜΆΜΆlΜΆΜΆΡ‡ pΜΆΜΆΡ”rΜΆΜΆcΜΆΜΆΡ”Γ­vΜΆΜΆΡ” nΜΆΜΆΟƒ pΜΆΜΆΞ±Γ­nΜΆΜΆ,*
*sΜΆΜΆΟƒ mΜΆΜΆΞ±gΜΆΜΆΓ­cΜΆΜΆΞ±lΜΆΜΆ ΟƒuΜΆΜΆrΜΆΜΆ cΜΆΜΆrΜΆΜΆΡ”Ξ±tΜΆΜΆΓ­vΜΆΜΆΡ” gΜΆΜΆΟƒlΜΆΜΆdΜΆΜΆΡ”nΜΆΜΆ pΜΆΜΆΡ”nΜΆΜΆ* ✍ *,Π²Ρ”hΜΆΜΆΟƒlΜΆΜΆdΜΆΜΆ ΟƒuΜΆΜΆrΜΆΜΆ wΜΆΜΆΟƒrΜΆΜΆdΜΆΜΆsΜΆΜΆ.Ξ± pΜΆΜΆrΜΆΜΆΟƒdΜΆΜΆuΜΆΜΆcΜΆΜΆtΜΆΜΆ ΟƒfΜΆΜΆ ΟƒuΜΆΜΆrΜΆΜΆ pΜΆΜΆΡ”nΜΆ*ΜΆ *,sΜΆΜΆΞ±vΜΆΜΆΟƒuΜΆΜΆrΜΆΜΆ ΟƒuΜΆΜΆrΜΆΜΆ wΜΆΜΆΟƒrΜΆΜΆdΜΆΜΆsΜΆΜΆ, fΜΆΜΆΟƒrΜΆΜΆ Γ­tΜΆΜΆ wΜΆΜΆΓ­lΜΆΜΆlΜΆΜΆ* *cΜΆΜΆΞ±uΜΆΜΆsΜΆΜΆΡ” Ρ‡ΟƒuΜΆΜΆ nΜΆΜΆΟƒ pΜΆΜΆΞ±Γ­nΜΆΜΆ.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.


*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*


Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buΖ™ata namu daga farko.



Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana Ζ™ara mana Ζ™arfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.



*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*Thursday 30/12/2021*

*Time 12:03pm*

*Typing...............*

Sun isa asibiti cikin hanzari nurse suka kar'bi yaron suka shiga da shi d'akin gaugawa domin a duba shi. Bayan tafiyar su Ahmad sai wani kai kawo yake ya sauke kallonsa ga Ahlam wacce gaba d'aya ta kusa ta fita hayyacinta, cikin hanzari ya isa inda take cike da k'unci bak'in ciki tare da tarin damuwa yake magana. "Ahlam yanzu mai kika aikata kenan? Duk sabo da ke ne hakan ta faru ina ta k'oqarin ganin na dakatar da shi amma kuma ke, sam baki sauraran ba sam kin gagara yarda da ni dama duk abin da nake fad'a, yanzu sabo da taurin kanki yaronmu yana cikin mummunan yanayi Ahlam mai yasa kika kasa saurara na ko da sau ďaya ne shin kin san abin da yafi so zafi? Ahlam ganin abin da kafi so cikin mummunan yanayi yafi komai zafi, Ahlam hakan yana da matuqar zafi sannan kuma da k'una sosai. Ahlam ke d'in nan kin aikata babban zunubi wanda yake da matuqar girma sosai sannan kuma. Tayi saurin dakatar da shi ta hanyar da bai ta'ba tinani ba, kamar a mafarki ya ji saukar wani wawan mari a fuskar sa, da sauri ya zaro ido yana kallonta kallo sosai mai cike da jin mamakin ta sosai, cike da k'unci bak'in ciki tare da tarin damuwa take magana yayin da take kuka kuma kuka sosai.

"Mai ya saka kake hukunta ni da zunubin ta? Kai ne a salin mai laifin amma kuma ni ce wacce kake hukunta wa, Yaya Ahmad tin da jimawa nake tambayar ka abu ďaya a game da *Adyan* amma ko sau ďaya baka ta'ba tinanin amsa ni ba. Sai faman 'boye min gaskiyar kake wanda da a ce ni na san a salin gaskiyar to da duka wannan bai faru ba, a kan me kai zaka 'boye min cewar yarona ba shi da lafiya? Ni Maman shi ne to akwai buqatar dana san komai a game da ta yanda ni zan iya karesa, shin baka ta'ba tinanin cewar wannan cutar wa ba ce gareni amma kuma shi ne duk da haka kake d'ora laifin a kai na? Wannan rashin adalci ne sabo da kai ne nan wanda yake da alhakin duka wannan, sabo da kai ne *Adyan* yake cikin wannan mummunan yanayin amma ba ni ba, to ka sani wallahi tallahi ba zan ta'ba gafarta maka ba idan har wani mummunan abu ya faru da yarona ka tina da wannan." Magana take cikin wani irin yanayi mara dad'i yayin da damuwa tayi yawan gaske a tare da ita. Shi kuwa sai wani kallonta yake kallo sosai ya gama fahimtar cewa sam bata cikin kyakkyawan yanayi, wanda wannan dalilin ne yasa bai iya amsa ta ba wanda shi ma zamu iya cewa yana cikin yanayi irin nata.

Sun samu shiru na tsayin wani lokaci ba mai magana a cikin su, sai jiran fitowar doctor suke domin ya jikin yaronsu, bayan wani tsayin lokaci da suka d'auka a ciki tare da shi sosai sun fito da sauri dukansu suka isa ga Dr Sam suna tambayar sa jikin *Adyan.* Yayi shiru na jim kad'an sannan ya amsa su dasu same sa a office, ya juya yayi tafiyarsa suma binsa su kai a baya sun isa office tare sun shiga ciki bayan sun zauna Dr Sam yaci gaba yana cewa. "Shin kun san cewa yaronku yana da rami a zuciya ko mu kira abin da rauni.?" Ahmad ya amsa shi da eh Dr Sam yaci gaba da magana, "to amma mai ya saka baku ba shi cikakkiyar kulawa sosai yanda ya kamata.?" Ko a wannan lokacin Ahmad ne wanda ya amsa shi yayin da Ahlam ta rufe su da ido ta gagara furta komai. "Doctor muna kulawa da yaronmu sosai yanzun ma wani tsautsayi ne ya faru da shi, to zaka iya yarda damu yanzu fad'a mana mai yake faruwa da yaronmu.?" Ya jinjina masa ka sannan ya amsa shi.

"Shikenan tinda ka fad'i haka amma dai ku sani yaronku sam bai kamata yayi duk wani abin da zai saukar masa da gajiya ba, sabo da yana buqatar hutu da kulawa sosai hakama yana da kyau yayi farin ciki sosai. Idan kuma irin hakan taci gaba da faruwa da shi to fa zai shiga mummunan yanayi, wanda zaku iya rasa yaronku gaba d'aya dan haka ya zame dole ku ba shi kulawa sosai." "Shikenan doctor zamu kula insha Allah muna godiya sosai." Cike da firgici rud'ani tare da tashin hankalin abin data ji suna fad'a ta anbaci sunan doctor tana cewa. "Doctor ta ya yarona zai samu lafiya ya rabu da wannan cutar gaba d'aya.?" Magana take yayin da take kuka Dr Sam ya amsa ta, "shin ke kin rabu da wannan cutar ne? Karki fad'a min cewar ke bakya tare da wannan cutar ko dai an yi maki aiki ne.?" Wani irin kallo take yi masa mai cike da jin mamakin abin da yake faruwa, yayin data gagara fahimtar komai daga cikin abin daya fad'a kafin ta furta komai Ahmad yayi mata rigagi. "Eh doctor ita ma har yanzu tana tare da cutar muna dai ta shirin yi mata aiki ne insha Allah." "Shikenan ka kula da dukansu yanzu zaku iya tafiya." Ya amsa da to ya tashi tare da tashin Ahlam sun fita suna fitowa tayi saurin cire hanun sa daga jikin ta tare da fad'ar sunan sa.

"Yaya Ahmad wai mai kake fad'a masa ne a kai na wane aiki kake magana a kansa.?" Ha!!! Ya nisa sosai tare da jan numfashi yana mai sauke a jiyar zuciya, "Ahlam ni bani da wani za'bi ne dole sai na sanar da shi haka, idan kuma ba haka to fa shi zai zargemu dalilin da yasa na fad'i hakan kenan." Nan ya shiga sanar da ita gaskiyar komai a game da rashin lafiyar, "Ahlam." Tayi saurin dakatar da shi ta hanyar d'aga masa hanu tare da girgiza masa ka tana furta kalmar a'a. Ta juya tayi tafiyarta ta nufi d'akin da *Adyan* yake domin ganin yanayin jikin sa, hakama Ahmad binta yayi a baya sun isa d'akin ta shiga ciki yana k'oqarin shiga tayi saurin dakatar da shi. "A'a kai sam baka da damar da zaka ga d'ana, a yau ďin nan kai kayi matuqar cutar da ni da kuma yarona dan haka ya zama dole ka kar'bi hukunci daga gareni, hukuncin ka shi ne ba zaka ga d'ana ba to kawai ka tafi sabo da bana buqatar ka a nan to jeka man kawai ka tafi." Magana take cikin fishi sosai yayin da take kuka kuma kuka sosai.

"A'a Ahlam ni ba zan tafi ba sabo da ina buqatar na kasance tare da yarona sabo da shi ma yana buqata na sosai a tare da shi. Ahlam ni na riga dana sanar da ke duka gaskiyar a yanzu da kuma dalilin da yasa ni na 'boye maki gaskiyar to mai yasa ba zaki yafemin ba? Ahlam ni kawai bana san na cutar da ke ta hanyar sanar dake rashin lafiyar sa sabo da na san cewar jin hakan zai yi matuqar cutar dake sosai, sannan kuma ni ina kulawa da yaronmu sosai Ahlam ni na yarda da cewa nayi maki laifi, sannan kuma na baki hak'uri idan ba zaki yafemin ba to ki hukunta ni amma bata hanyar nisanta ni da *Adyan* ba. Sabo da ni ba zan iya jure wannan ba Ahlam ni zan iya kama qafafun ki na baki hak'uri idan kina so, to dan Allah ka da ni dakatar da ni daga ganin yarona please." Magana yake cikin wani irin yanayi wanda ban san ta yanda zan iya sanar daku shi ba sai dai ku misalta. Shiru bata amsa ba sai ma k'oqarin rufe k'ofa da take ganin hakan ne yasa shi dukursawa qasa ya kai hanun sa zai kama qafafun ta, da sauri taja da baya tare da furta a'a tayi saurin rufe k'ofar yayin da take kuka ta nufi gurin, *Adyan* wanda kuma har zuwa wannan lokacin bai farfad'o daga dogon suman da yayi ba.

Ahmad kuwa yayi zaune a kan kujeran da take gefen ďakin yayin da k'unci da 'bacin rai yayi yawan gaske a tare da shi sosai, sai tinani yake iri daban-daban yana haka ya jiyo wayar sa na ruri ya ciro wayar daga aljihu ya duba mai kiran sa ganin sunan Umma yasa shi saurin d'aga kiran. "Umma na naji dad'i sosai da kika kira." Cike da firgici da rud'ani take magana, "Ahmad mai yake faruwa da kai ne shin komai qlau kuwa.?" "A'a Umma sabo da Ahlam tana matuqar yin fishi da ni kuma fishi sosai gaba d'aya tak'i saurara na, Umma ita ta hana ni kasancewa tare da yarona duk da cewar ni ina da buqata da hakan sosai. Umma hakan yana da matuqar zafi sannan kuma da matuqar k'una Umma muna asibiti da *Adyan* ba shi da lafiya sosai, Umma ina san na runguma yarona a jiki na sannan na sunbacesa na kuma fad'a masa cewar ina qaunar sa, amma kuma Ahlam duk ta dakatar da ni daga yin hakan Umma hakan yana yi mun zafi sosai ban kuma san ya zanyi ba. To dan Allah ki fad'a min ya zanyi ta ya zansa Ahlam ta bud'e min k'ofa na shiga na ga yarona.?" Magana yake cikin wani irin yanayi mara dad'i yayin da damuwa tayi yawan gaske a tare da shi sosai, sai wasu zafafan hawaye yake zubar wa masu tsananin zafi da k'una sosai, kuma zamu iya kiran abin da kukan zuci wanda yafi na zahiri ciwo.

Cike da firgici da rud'ani take magana, "Ahmad mai yake faruwa da jikana? Yaron ba shi da lafiya sosai amma kuma duk da haka ku biyun kuna fad'a? Ahmad dan Allah ku dena wannan shirmen banzan ku kula da yaran sosai, jikana yana buqatar kulawar dukanku to ya kamata ku kula da shi sosai, sannan kuma kayi hak'uri da yanayin Ahlam to amma mai ya saka ita ta dakatar da kai daga ganin *Adyan.?"* "Umma ita tana fishi ne sabo da na 'boye mata gaskiyar cewa yaronmu ba shi da lafiya, bayan ta gano duka gaskiyar shi ne take fishi da ni kuma tana hukunta ni da rashin ďana. Umma hakan yana da matuqar zafi sannan kuma da k'una sosai dan Allah ki fad'a min ya zanyi please.?" Tayi shiru na jim kad'an sannan ta amsa shi, "Ahmad dole Ahlam ta hukunta ka sabo da ba wani dalilin da zai sa ka 'boye mata gaskiyar to amma mai ya saka kai kayi hakan.?" "Umma ni kawai na damu da ita ne sosai sam bana san ta fuskanci k'unci sosai, Umma ni na damu sosai a kanta shi yasa na 'boye gaskiyar a gareta amma ita sam ta kasa fahimtar hakan ban kuma san ta yanda zansa ta fahimce ni ba."

"Karka damu ďana komai zai yi daidai jikana zai samu lafiya insha Allah to kawai ka jure ka ji ko." Haka taci gaba da rarrashin sa tana ba shi magana, sun jima sosai a kallayi sannan daga bisani suka yi sallama. Bayan ta a jiye wayar Abba ya shiga tambayar mai yake faruwa ta sanar da shi komai ya girgiza ka yana cewa. "Shin su ba zasu iya kulawa da yaronsu ba sabo da sakacin su jikana yana kwance a asibiti su biyun sun cika shashanci zanyi magana da dukansu." Ta jinjina masa ka a lamar to zaune yake a kan kujera sai wani rawar sanyi yake, ya rufe idanuwan sa sai tinani yake iri daban-daban tsaye take a window sai wani kallonsa take kallo sosai, lokaci d'aya taji wani tsayin sa yana shigarta ta ko ina lungu da sak'o na jikin ta. Ta nufi gado ta d'auki zanin gado ta fita ta nufi gurin Ahmad, ta bud'e k'ofar ta fito ta isa inda yake tayi tsaye sai wani kallonsa take kallo sosai yayin da take jin yana birgeta sosai. Nan ta shiga rufe masa jikin sa da bargo sannu a hankali yake bud'e idanuwansa har suka bud'e, lokaci d'aya suka yi ido biyu da juna kasancewar ita ma kallonsa take, wani irin kallo suke yiwa juna wanda suka gagara sanin mai suke nufi da shi.

Sun jima sosai a haka sannan daga bisani ta kau da idanuwan ta daga garesa, ta tashi domin tafiya yayi saurin dakatar da ita ta hanyar ri e hanun ta tare da fad'ar sunan ta. "Shin ke kina jin tsoron kar sanyin gurin nan ya cutar da ni? Ahlam amma kuma a nan kin yi matuqar cutar da ni sosai." Ya nuna zuciyar sa ya kuma ci gaba da magana, "Ahlam raunin yana da matuqar zafi sosai sannan kuma yana da matuqar zurfi sosai hakan yasa k'unar take da zafi sosai. Ahlam naro e ki dan Allah ki barni na tafi ga yarona, ina matuqar san na had'u da shi ina buqatar na rungumasa jikina sannan kuma na sunbacesa na kuma fad'a masa cewar ina qaunar. Ahlam dan Allah." Da sauri ta dakatar da shi ta hanyar rufe masa baki tana girgiza masa ka a lamar a'a. Ta tashi tare da riqa hanun sa sun shiga ciki tare cike da d'auki ya nufi gurin *Adyan,* cike da d'auki yayi hugging d'in sa sai wani lalla'basa yake yayin da yake furta masa kalmar ina qaunarka sosai d'ana.

Ita kuwa sai wani kallonsa take ba kuma tare data furta masa komai, bayan ya sake sa daga rungumar da yayi masa ya gyara masa kwanciya sannan ya mai da kallonsa ga Ahlam. Wacce har zuwa wannan lokacin kallonsa take ya tashi ya nufi inda take cikin kasa-kasa da murya tare da kwantar da ita yake magana. "Na gode sosai Allah ya saka da alkhairi fad'a min wani abu har yanzu kina fishi dani.?" Har zuwa wannan lokacin kallonsa take ba kuma tare data furta masa komai ba shi ma haka kallonta yake kuma kallo sosai. Sun jima sosai a haka ba kuma tare da sun furta wa juna komai ba jin shirun yayi yawa yasa yaci gaba da magana. "Shikenan ni ba zan tilassa ki a kan kiyi min magana ba, amma zanyi farin ciki sosai idan kika fad'a min cewar kin yafe min." Har zuwa wannan lokacin kallonsa kawai take ba kuma tare data amsa shi ba, jin tayi shiru na tsayin wani lokaci bata amsa shi ba yasa yayi tinanin cewar tana fishi da shi kuma fishi sosai.

Wannan yasa ya juya zai fita har ya kai k'ofa ya juya ya koma gurin *Adyan.* Ya shafi fuskar sa zuwa kansa tare da furta Allah ya baka lafiya Amin, sannan ya juya ya fita Ahlam ta bisa da kallo har ya fice daga d'akin, ya fito yayi zaune a kan kujera ya ciro wayar sa ya kama aikin chart. Ita ma fitowa tayi ta same sa zaune yana aikin chart tayi zaune gefen sa sai wani kallonsa take kallo sosai yayin da take magana da zuciyarta. "Yaya Ahmad kana matuqar birge ni sosai amma kuma kai ga a lama bana gaban ka, sabo da wannan yarinyar da kake kulawa wacce kake kira da Hayatee. Lallai ya zame dole da nayi koma miye domin na tabbatar da cewar ka zama nawa na har abada, wannan shi ne abin daya kamata nayi kuma tabbas zanyi hakan insha Allah." Ganin yanda ya mai da hankalin sa gaba d'aya ya karkata a kan waya yayi uwa bai ganta ba yasa ta kai hanun ta domin amsar wayar, yayi saurin janye wayar tare da kai kallonsa gareta kafin ya furta komai tayi masa rigagi................



*BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.*
[1/1, 8:51 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ‘‘

*THREE BROTHER'S*

πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ‘‘

*Page 11*

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/


*wΜΆΜΆΡ” Ξ±rΜΆΜΆΡ” Π²Ρ”Ξ±rΜΆΜΆΡ”rΜΆΜΆ'sΜΆΜΆ ΟƒfΜΆΜΆ sΜΆΜΆΟƒ gΜΆΜΆΟƒlΜΆΜΆdΜΆΜΆΡ”nΜΆΜΆ pΜΆΜΆΡ”nΜΆΜΆ*
*wΜΆΜΆΡ” wΜΆΜΆrΜΆΜΆΓ­tΜΆΜΆΡ” Ξ±sΜΆΜΆsΜΆΜΆΓ­dΜΆΜΆΓ­ΟƒuΜΆΜΆsΜΆΜΆlΜΆΜΆΡ‡ pΜΆΜΆΡ”rΜΆΜΆcΜΆΜΆΡ”Γ­vΜΆΜΆΡ” nΜΆΜΆΟƒ pΜΆΜΆΞ±Γ­nΜΆΜΆ,*
*sΜΆΜΆΟƒ mΜΆΜΆΞ±gΜΆΜΆΓ­cΜΆΜΆΞ±lΜΆΜΆ ΟƒuΜΆΜΆrΜΆΜΆ cΜΆΜΆrΜΆΜΆΡ”Ξ±tΜΆΜΆΓ­vΜΆΜΆΡ” gΜΆΜΆΟƒlΜΆΜΆdΜΆΜΆΡ”nΜΆΜΆ pΜΆΜΆΡ”nΜΆΜΆ* ✍ *,Π²Ρ”hΜΆΜΆΟƒlΜΆΜΆdΜΆΜΆ ΟƒuΜΆΜΆrΜΆΜΆ wΜΆΜΆΟƒrΜΆΜΆdΜΆΜΆsΜΆΜΆ.Ξ± pΜΆΜΆrΜΆΜΆΟƒdΜΆΜΆuΜΆΜΆcΜΆΜΆtΜΆΜΆ ΟƒfΜΆΜΆ ΟƒuΜΆΜΆrΜΆΜΆ pΜΆΜΆΡ”nΜΆ*ΜΆ *,sΜΆΜΆΞ±vΜΆΜΆΟƒuΜΆΜΆrΜΆΜΆ ΟƒuΜΆΜΆrΜΆΜΆ wΜΆΜΆΟƒrΜΆΜΆdΜΆΜΆsΜΆΜΆ, fΜΆΜΆΟƒrΜΆΜΆ Γ­tΜΆΜΆ wΜΆΜΆΓ­lΜΆΜΆlΜΆΜΆ* *cΜΆΜΆΞ±uΜΆΜΆsΜΆΜΆΡ” Ρ‡ΟƒuΜΆΜΆ nΜΆΜΆΟƒ pΜΆΜΆΞ±Γ­nΜΆΜΆ.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.


*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*


Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin

9 / 48