THREE BROTHERS Complete Hausa Novels By Bil-Fauzee U-Adyan.txt

Author :  Bil-Fauzee U-Adyan Category :  Hausa Novels 001

Chapter   43 / 48

126K to 129K   out of 142.8K words

wane d'a zai so yayi nasaran samun uwa ta gari kamar ki, kin kasance kamar Mamie na da kuma Ammie dukanku iyaye na gari ne a garemu, kuma dukanmu muna alfahari da hakan sosai." Magana yake cikin wani irin yanayi wanda ban san ta yanda zan fad'ar sa ba, dukansu sai kallonsa suke yayin da suka gagara fahimtar abin da yake fad'a, cike da jin mamakin abin daya fad'a Mum take magana.

*"Adnan* dan Allah ka fad'a min ina yarana suke? Dan Allah ka fad'a min suna ina sabo da ina buqatar had'uwa dasu sosai to yanzu fad'a min suna ina dan Allah.?" *Adnan* ya mai da kallonsa ga *Adyan* lokaci d'aya suka yi ido biyu da juna, kasancewar shi ma kallonsa yake ya kuma jinjina masa ka a lamar ya sanar da ita, ya amsa shi da to ta hanyar jinjina masa ka ya mai da kallonsa ga Mum tare da fad'ar sunan ta. "Mum gaskiyar ita ce kin jima sosai tare da yaranki, kuma ko yaushe kina kulawa dasu sosai kamar dai yanda suma suke baki cikakkiyar kulawa sosai." *"Adnan* wai a kan me kake magana ni sam na gagara fahimtar ka.?" Yayi shiru na jim kad'an sannan ya amsa ta. "Eh Mum ina nufin kin jima sosai tare da yaran kuma zan iya cewa, duka yaran naki suna tare dake Mum ni da kuma Aboki mune yaran da kika rasa." Dukansu wani irin kallo suke yi masa mai cike da jin mamakin abin daya fad'a. *"Adnan* wai gaskiya kake fad'a kuwa.?" "Eh Kaka ni gaskiyar nake fad'a sabo da nayi binkice a game da wannan tin da jimawa." Nan ya shiga sanar dasu komai daya faru cike da jin mamakin abin daya fad'a take magana.

"Tin da jimawa kun san gaskiyar to amma mai ya saka ni baku tab'a tunanin sanar da ni ba.?" *Adyan* ne wanda ya amsa ta wanda kuma sai zuwa wannan lokacin ne yayi magana. "Mum bamu da wani zab'i ne sabo da ba zamu iya cutar da iyayenmu ba, ta hanyar sanin gaskiyar dukanku kun san irin soyayyar da iyayenmu suke yi mana, Mum ba zamu iya yafe wa kanmu ba idan har wani mummunan abu ya faru da ahalinmu ba, musamman iyayenmu shi yasa muka yi shiru bamu sanar da kowa gaskiyar ba. Yanzun ma muna masu rok'onku da karku sanar da kowa wannan gaskiyar, kawai mu bar wannan a tsakaninmu ina nufin ya zama sirri dan Allah please." Magana yake yayin da idanuwan sa suke zubar da kwalla, mai tsananin zafi da k'una sosai hakama *Adnan* abin da yake yi kenan, wani irin kallo take yi musu mai tare da so, yayin da take jin qaunar su tana zaga ko ina na jikin ta. Ta shiga share musu kwalla tare da sunbatarsu ta k'ara da yin hugging d'in su, cike da qauna da soyayya take magana dasu..............






*BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.*
[3/16, 11:47 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ‘‘

*THREE BROTHER'S*

πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ‘‘

*Page 51*

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

*wΜΆΜΆΡ” Ξ±rΜΆΜΆΡ” Π²Ρ”Ξ±rΜΆΜΆΡ”rΜΆΜΆ'sΜΆΜΆ ΟƒfΜΆΜΆ sΜΆΜΆΟƒ gΜΆΜΆΟƒlΜΆΜΆdΜΆΜΆΡ”nΜΆΜΆ pΜΆΜΆΡ”nΜΆΜΆ*
*wΜΆΜΆΡ” wΜΆΜΆrΜΆΜΆΓ­tΜΆΜΆΡ” Ξ±sΜΆΜΆsΜΆΜΆΓ­dΜΆΜΆΓ­ΟƒuΜΆΜΆsΜΆΜΆlΜΆΜΆΡ‡ pΜΆΜΆΡ”rΜΆΜΆcΜΆΜΆΡ”Γ­vΜΆΜΆΡ” nΜΆΜΆΟƒ pΜΆΜΆΞ±Γ­nΜΆΜΆ,*
*sΜΆΜΆΟƒ mΜΆΜΆΞ±gΜΆΜΆΓ­cΜΆΜΆΞ±lΜΆΜΆ ΟƒuΜΆΜΆrΜΆΜΆ cΜΆΜΆrΜΆΜΆΡ”Ξ±tΜΆΜΆΓ­vΜΆΜΆΡ” gΜΆΜΆΟƒlΜΆΜΆdΜΆΜΆΡ”nΜΆΜΆ pΜΆΜΆΡ”nΜΆΜΆ* ✍ *,Π²Ρ”hΜΆΜΆΟƒlΜΆΜΆdΜΆΜΆ ΟƒuΜΆΜΆrΜΆΜΆ wΜΆΜΆΟƒrΜΆΜΆdΜΆΜΆsΜΆΜΆ.Ξ± pΜΆΜΆrΜΆΜΆΟƒdΜΆΜΆuΜΆΜΆcΜΆΜΆtΜΆΜΆ ΟƒfΜΆΜΆ ΟƒuΜΆΜΆrΜΆΜΆ pΜΆΜΆΡ”nΜΆ*ΜΆ *,sΜΆΜΆΞ±vΜΆΜΆΟƒuΜΆΜΆrΜΆΜΆ ΟƒuΜΆΜΆrΜΆΜΆ wΜΆΜΆΟƒrΜΆΜΆdΜΆΜΆsΜΆΜΆ, fΜΆΜΆΟƒrΜΆΜΆ Γ­tΜΆΜΆ wΜΆΜΆΓ­lΜΆΜΆlΜΆΜΆ* *cΜΆΜΆΞ±uΜΆΜΆsΜΆΜΆΡ” Ρ‡ΟƒuΜΆΜΆ nΜΆΜΆΟƒ pΜΆΜΆΞ±Γ­nΜΆΜΆ.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.


*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*


Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buΖ™ata namu daga farko.



Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana Ζ™ara mana Ζ™arfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.



*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*Monday 14/03/2022*

*Time 12:14am*

*Typing................*

*"Adyan* ni na fahimce ku amma duk da haka ya kamata nima na san gaskiyar, a gaskiya nayi matuqar farin ciki sosai da Ubangiji ya bani ku a matsayin yarana. Ban tab'a tunanin cewar ni ina da sa'a ba har haka gaskiya Ubangiji yana sona da yawa, tin da nake a duniya ban tab'a ganin wasu mutane masu kirki ba fiye da iyayenku. Su suna da matuqar kirki sosai sunyi abin da ba wani wanda zai iya yi, tabbas sun cancanci duka soyayyar ku, hakama sam bai kamata su san a salin gaskiyar ba, sabo da bai kamata mu cutar dasu ta wannan hanyar ba. To ina mai yi muku alkawarin cewa ba wanda zai ji wannan ko da kuwa a ce Prof ne, gaskiya nayi matuqar farin ciki sosai da kuka fad'a masa cewar yaran sun mutu, ta yanda tunanin sa ba zai tab'a kai wa gareku ba. *Adnan Adyan* dan Allah kuyi hak'uri ku yafe min dani na kasa kasancewa uwa ta gari a gareku, sam na kasa kareku balantana na iya baku kulawar data dace, ni kai na kulawa a ke da ni to kuma ta ya ni zan iya baku cikakkiyar kulawa sosai.?"

"K'ila kaddara ta fahimci hakan shi yasa ta had'aku da iyaye kamar, Papa Mamie Appa da kuma Ammie dama duka ahalin naku gaba ďaya. K'ila da kun rayu da ni to da ba zaku samu kyakkyawar rayuwa kamar haka ba, sabo da bamu da kud'i abinci ma wahala yake mana, to kuma ta ya Umma zata taimakeku kuyi karatu, k'ila da burina ba zai tab'a cika ba na aifa likita da lauya. Amma yanzu Alhamdulallah duka burina ya cika, dukanku ukun kuna raye sannan kuma kun kasance kamar yanda nake fata. Ina qaunarku dukanku Allah yayi muku albarka ya kuma albarkaci rayuwarku, data yaranku baki ďaya Allahumma Amin ya hayyu ya kayyum. *Adyan* ta ya a kai yanzu mu biyun muke magana da juna.?" "Mum idan har wannan na'urar tana kunanki to mu biyun zamu iya yin magana da juna." Cike da d'auki ta k'ara yin hugging d'in su tana sunbatarsu, ta mai da kallonta ga fuskar *Adeel* tare da yin kiran sa, cikin hanzari ya nufi inda take ya zauna ta had'asu duka ukun tayi hugging d'in su, tana sunbatarsu su kuwa sunyi kwance jikin ta har da wani rufe ido, Umma sai wani kallonsu take tana murmushi yayin da farin ciki yake ta shigarta sosai.

Ita tashi tayi ta k'arasa gurin su cike da farin ciki tayi hugging d'in dukansu, tare da sunbatarsu cikin kyakkyawan yanayi take magana. "Bayan tsayin wani lokaci yau ahalinmu ya k'ara cika, a gaskiya ina matuqar farin ciki sosai wanda har ba zan iya fad'ar sa ba. Sai dai kawai na ce ina farin ciki sosai Allah yayi muku albarka, ya kuma albarkaci rayuwarku data yaran da zaku aifa Allahumma Amin." Sun amsa ta da Amin tare da k'ara shigewa jikin ta, bayan wani lokaci suka sake juna Mum taci gaba da magana.

"Umma kamar dai yanda yaran suka fad'a ba wanda zai san a salin gaskiyar, ba zamu sanar da kowa wannan sirrin ba musamman ma Prof. Ba zai tab'a sanin wannan gaskiyar ba na har abada, wannan shi ne sakamakon zunubin daya aikata mana, tabbas ya cancanci fiye ma da hakan daga garemu, idan ma da akwai abin da yafi wannan to ni zan iya aikata wa a garesa. Sabo da ina buqatar ganin sa cikin k'unci fiye da wannan da yake tare da shi, auran sa da nayi shi ne babban kuskurena a rayuwa. Ba zan tab'a yafe masa ba na har abada kayi hak'uri *Adeel,* sabo da na san irin yanda kake qaunar Dadyn ka sosai. To ina fatan zaka fahimce ni ba kuma hakan ba zai saka ka cikin k'unci ba.?"

"Mum zuwa yanzu ni na san duka a shi d'in ya cutar daku sosai, abin takaicin shi ne har da yaransa ya saka a ciki, ya cutar da yaran da basu san komai ba. Ya kasa baki damar da zaki kasance uwa a garemu, ya hana ki damar da zaki rungumi yaranki ki kuma shayar dasu, ni kawai sabo da wani buri basa Mum ni narasa wace irin zuciya ce a jikin Dady, ta ya uba zai iya cutar da yaransa tin a ranar da a ka aife su? Bama tare daya ga ko fuskarsu ba sannan kuma ya iya manta hakan, yayi k'oqarin cutar dasu amma Ubangiji ya karesu, dukansu sun samu kyakkyawar rayuwa wadda kowa zai so ya rayu a cikin ta. Godiya sosai a gurin iyayen da suka fi kowa kirki a cikin wannan duniyar, Papa Mamie Appa da kuma Ammie dama duka ahalinsu gaba d'aya. Sai yanzu ne na san dalilin da yasa Doctor da Barrister suke tare da tsanar Dady, shi ďin ya cancanci hakan daga garesu, amma duk da haka ina fatan wata rana rayuwa ta sake bawa Dady na dama, ta hanyar sawa ya zama mutumen kirki wanda zanyi alfahari da shi, k'ila a wannan lokacin ku iya yafe masa ina fatan hakan ta faru nan kusa kuma kusa sosai."

Magana yake cikin wani irin yanayi wanda shi ba k'unci ba shi kuma ba farin ciki sosai ba, a zahirin gaskiya yana matuqar qaunar Dadyn sa sosai, amma kuma hakan ba ya nufin zai goyi da bayan sa. Ya zama dole ya nuna masa kuskuran sa domin yayi k'oqarin gyara wa, *Adyan* ya shafi fuskarsa tare da fad'ar sunan sa. *"Adeel* na fahimci irin yanayin da kake ciki, amma duk da haka ya kamata kayi farin ciki sabo da har yanzu mu ukun muna tare, to ina ga sam bai kamata kayi k'unci ba musamman a kan Prof. *Adeel* abin farin cikin shi ne Mummy na nan sannan kuma yanzu tana farin ciki sosai, duka ahalin muna farin ciki to kai ma ya kamata kayi farin ciki, yanzu abin da yafi muhimmanci shi ne mu fara shirin auran ka da *Amna.* K'ila hakan zai sa ka rage yawan tunani da kuma yawan damuwa a kan Prof, to muyi hakan cikin sauri mako ďaya zuwa kwana goma to ya ka ji wannan shawaran tawa.?"

Kafin ya furta komai *Adnan* yayi masa rigagi yana cewa. "Eh *Adeel* domin kuwa *Amna* ma tana matuqar buqatar hakan, to kawai ka amince da abin da Aboki ya fad'a please." Yayi shiru kad'an sannan ya amsa su. *Adnan Adyan* nima zanso hakan sosai amma kuma hakan ba zata faru ba." "Mai zai dakatar da faruwar hakan.?" "Barrister kai kariga da ka san komai a game dasu, har kullum har ko yaushe suna tare da k'uncin rashin twin's, tare da tunanin ina zasu gansu ko labarin su. Barrister abin a baiyane yake basu k'ara farin ciki ba tin bayan b'acewar twin's, duk da cewar sun aifi *Amna* amma har yanzu suna cikin k'unci sosai, gaskiyar ita ce suna matuqar qaunar yaransu sosai shi yasa har yanzu suka gagara manta dasu. To wannan yanayin nasu ne yasa sam bana jin cewar aure na da *Amna* zai kasance kamar yanda kuke fad'a." Dukansu sunyi shiru suna nazari a kan abin daya fad'a, daga bisani kuma *Adnan* yaci gaba da magana.

*"Adeel* sabo da wannan dalilin ne yasa zaku yi aure yanzu, sannan kuma za a yi auran naku tare da twin's sabo da ahalinsu zai k'ara cika, nan kusa kuma kusa sosai insha Allah, to kawai ka fara shirin zama Ango ka ji ko." Cike da jin mamakin abin daya fad'a yake magana. "Barrister shin kai ka san inda twin's suke ne.?" Ya jinjina masa ka tare da sanar da shi cewar shi da *Adyan* ne yaran da suke nai ma, nan kuwa ya shiga sanar dasu komai a game dasu da kuma rayuwarsu. *"Adeel* na tabbata su Mama zasu yi farin ciki sosai da ganin mu, zamu tafi garesu sannan kuma zamu sanar dasu duka gaskiyar, sun kasance iyaye na gari a garemu to zasu amince da duk wani burinmu. Wanda wannan dalilin ne yasa zamu sanar dasu duka gaskiyar, to kawai ka fara shirin auran ka da qanwata, sannan kuma ka fara shirin kiran mu da Yaya sabo da zaka yi aure da qanwarmu." Magana yake cikin kyakkyawan yanayi yana dariya haka suma abin da suke yi kenan.

"Na ji mamaki sosai daya kasance cewar ku biyun kune twin's, sabo da irin soyayya da qauna dasu Abba suke nunawa a gareku, to ba wani wanda zai ci basu ne a salin iyayenku ba. Gaskiya ku kuna da matuqar sa'a sosai a rayuwa, sa'ar da kuke da ita ne yasa baku rayu tare da Dady ba, sai Ubangiji ya yanke hukuncin kai ku wani guri daban inda zaku samu ingantatciyar rayuwa. Ni kuma ni ne mara sa'ar cikin ku ina farin ciki sosai da samun ku brother's." "Karka fad'i haka bro dukanmu abu ďaya ne kuma 'yan uwan juna mun kasance *THREE BROTHER'S.* To ba wanda yafi wani a cikin mu wannan ce gaskiyar kuma ba zata canja ba, to kawai muyi farin ciki sannan kuma mu rungumi juna." Sun amsa shi da to suna dariya lokaci ďaya kuma suka yi hugging juna, suna haka wayar *Adyan* ta d'auki ruri sun fara sake juna sannan ya d'aga kiran.

"Masoyi ina ka shiga haka? Dare yayi sosai yanzu k'arfe 10:30pm amma har yanzu baka dawo gida ba fad'a min qlau kake.?" "Eh Appa ina lafiya kayi hak'uri da ban sanar da kai cewar na fita tare da Aboki ba, nasa ka damu ba dalili amma yanzu zan dawo gida insha Allah, ina Ammie na *Adlishart* da kuma baby na dama duka gidan fatan kana kulawa dasu yanda ya kamata.?" "Eh rabin raina abin da nake yi a ko yaushe kenan, amma ya kamata ka dawo yanzu sabo da dukanmu muna tare da kewarka sosai ďana, Appa yana san ya rungumaka jikin sa ya kuma sunbaceka, hakama Ammie abin da take buqata kenan dama su Abbu to ka dawo gida yanzu dan Allah." "Eh Appa zanyi ka fara duba agogo mintuna goma zuwa sha biyar zan k'araso insha Allah, ina sanka Appa ka kula dasu Ammie sosai sai na k'araso." "Eh masoyi zanyi to ka kula da kanka sosai ina qaunarka ďana."

Ya amsa shi da ok da kuma haka suka yi sallama, ya mai da kallonsa ga *Adnan* tare da furta masa su tafi. Sun mai da kallonsu ga Mum kafin su furta komai tayi musu rigagi. "Na samu lafiya sosai to nima ya kamata na tafi gida." Lokaci ďaya suka saki murmushi dukansu mai tare da dariya sun tashi sun fita domin tafiya. sai da suka raka su Mum har gida sannan suka fice, *Adnan* ne wanda ya sauke *Adyan* gida sannan ya nufi nasu gida. bayan kwana biyu suka shirya tafiya Jigawa gurin su Mama, *Adyan* ya sanar dasu Appa cewar zai raka *Adeel* gurin budurwar sa, hakama *Adnan* abin daya sanar dasu Mamie kenan, sun shirya tsab dukansu sun kama hanyar Jigawa.

Sannu a hankali yake bud'e idanuwansa har suka bud'e yayi tozali da fuskar Papa, cike da nuna kulawa Papa ya shiga yi masa sannu da tashi tare da ya jiki, yayi shiru na wani lokaci sannan daga bisani ya anbaci sunan sa yana cewa. "Adam mai kuma kake yi a nan.?" "Yaya nazo ne domin na duba jikin ka sannan kuma na kula da kai." "A'a bana buqatar wata kulawa daga gareka ďana zai iya kulawa da ni sosai to zaka iya tafiya yanzu." "Yaya abin shi ne *Adeel* ya tafi Jigawa domin had'uwa da sirikarmu, ya kuma tafi tare da Mummyn sa Umma *Adnan* da kuma *Adyan.* To yanzu k'anin ka ne kawai zai kula da kai kuma ni ne wannan, dan haka kawai ka amince da hakan please." "Adam d'an dakata wai har kai ne wanda zai fad'a mani tafiyar ďana? Irin abin daka aikata min na shiga tsakanina da Mama shi ďanka yake yiwa yarona, wai har kai ne wanda zai fad'a min tafiyar ďana a maimakon shi ya sanar da ni? Adam ka fita daga rayuwa ta sannan kuma ka fad'a wa yaronka ya fita daga rayuwar d'ana dan Allah."

"Yaya dan Allah karka hukunta ni da ďana a kan zunubin da kai ka aikata, kai ne wanda ya barmu bamu bane wad'an da suka barka ba. Ita Mama makaranta kawai ta kai ka amma kuma kai sai ka zab'i, daka gudu zuwa wani guri daban ba tare da kayi tunani a kai na da kuma Mama ba. Haka Mama tayi ta fama da k'uncin rashin ka, daga k'arshe ta kamu da ciwon zuciya wanda yayi sanadin mutuwar ta. Nayi k'unci sosai duk da cewar ina tare da Kawu Bala, kuma shi ma yazo ya mutu haka naci gaba da rayuwa cikin matsatsi da k'unci sosai, amma kuma hakan bai hana ni sanka ba tare da fatan sake had'uwa da kai. Amma kuma har yanzu kana fishi damu duk da cewar kai ne wanda ya cutar damu, haba Yaya kai kuwa wace irin zuciya ce da kai haka? Mai kuma yasa kake da san kanka da yawa har haka.?"

"Adam garama ka dena wannan wasan banzan na fad'a min cewar Mama ta mutu, Adam sam na kasa manta abin da kai da Mama kun ka aikata min, Adam mai kayi a lokacin da Mama take baka abinci ta hana ni? Sannan kuma wace irin gudunmuwa ka ba da a lokacin data shirya kai ni almajiranci? To ka sani tin daga wannan ranar nasa a zuciyata cewar ni kad'ai nake bani da kowa, na rayu cikin k'unci sosai nayi fad'i tashi sosai domin na gina kai na. Kuma nayi nasaran zama kamar yanda nake fata amma sabo da yaronka yanzu narasa

43 / 48