KARUWA MAI CAPACITY COMPLETE BY ZAHRA MUHAMMAD SURBAJO.doc

Author :  Zahra Surbajo Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   2 / 13

3K to 6K   out of 38.9K words

sannan kiyi masa wanka kamin sauyin in kin gama zanzo in duba"cewar hajiyar gamida juyawa ta koma inda suka fito.
Areesha a tsorace ta nufi Wakin se kalle kallen falon take hartazo bakin ?ofar,a hankali ta murWa murfin Wakin ta shiga.
Wani mahaukacin warine ya bugi hancinta da sauri ta toshe hanci,takai dubanta cikin Wakin.
ga mamakinta, wani matashine,kyakkyawa ajin farko,kwance akan gado yana kallon ?ofar shigowar,idanunsa na zubar da ?wallah
ga ?udaje se binsa sukeyi gwanin tausayi,a hankali areesha ta taka ta isa kusa dashi,zuciyarta a karye,ita da zatonta yarone ?arami seda ta shigone taga ashe saurayine maji ?arfi kwance cikin kashi da fitsari.
ajiye jakarta tayi agefen gadon,ta tsaya tunanin ta inda zata fara,shiko kallonta kawai yakeyi,dan ko wiyansa baya iya juyawa.
"sunana Areesha nice sabuwar me aykinka,ina maka fatan samun lafiya dauwamammiya"ta faWi hawaye na biyo idonta dan ita Allah yayita da saurin kuka,da tausayawa.
lumshe ido yayi alamun amsawa,
Toilet ta fara shiga,taje gurin karambanita har tasamu ta iya kunna fanfunan bayin,ta surko ruwa me zafi,ta dawo Wakin.
Areesha zuciyarta Waya,ta karSi aykin,dan tasan ko ba komai zata samu lada,shiyasa ta fara da yaye bargon jikinshi,da sauri ta kauda kai dan babu komai ajikinshi tsirara yake kwance duk yayi kashi da futsari,dubanta takai fuskarshi,se taga ya lumshe idanunsa,wasu siraran hawaye na biyo gefen idanunsa
tausayinsane ya ?ara kamata,ta cire kunyar da taji,tasawa zuciyarta ?arfi ta hanyar yarda zata iya.
juyashi tayi,a hankali,ta zaro zanin gadon tasa,gefen zanin a Wan rarrage na jikinshi,takai zanin gadon bayi wanda kashin jiki har tsutsa yakeyi,alamun ba yin yanzu bane.
kujerar wankan guragu data gani agefen gadon ta janyo,da ?yar da taimakon Allah ta Worashi akai,ya jingina,sannan,ta turashi zuwa cikin Sayin,tai masa wankan tass ta rabashi da duk wata ?azanta.sannan ta baroshi a bayin ta dawo Wakin tasa soso da sabulu da izal ta fara wanke katifar wacce ta kasance rover formce me Suli Suli ajiki,bata ri?e ruwa,haka ta wanke ta tsane sannan ta buWe waldrope Win ta nemo zanin gado tazo ta shimfiWa ta gyara Wakin fess ta fesa turarukan kan mudubin Wakin,ta Wauko masa jallabiya da pampers na manya ta fito dashi tashiryashi fess kamar ba shiba.
Gefe ta koma tana haki,dan da ?yar ta gudanar da komai danma tana da ?arfin hali da kuma girman jiki,amma a shekarunta goma sha biyar ba lalle ta iya ba.
Kallonshi tayi cike da tausayawa,kyau iya kyau,namiji har namiji sede shida babu banbancinsa kaWanne,jakar kayanta ta Wauka ta shige toilet ta fara wanke kayan daya Sata,fess ta wankesu,sannan,itama tayi wanka,ta sauya kaya,sannan ta fito da kayan,data wanke Win ta sauka ?asa,inda tasamu hajiyar zaune tana waya.
"me ya sauko dake bakiji abinda nace miki bane?"cewar hajiyar cikin haWe fuska.
Wan rusunawa tayi tace"wankine zan je in shanya"ta faWi a tausashe.
"muje sama in nuna miki injin da ake busar da kayan,insun bushe ki goge,bana bu?atar ki kuma sakkowa koda shekara zakiyi,in wani abune akwai waya acikin Wakin ki kira numbobin dake ajiye agurin."
"to hajiya ngd kuma zan kiyaye."cewar Areesha a ladabce.
Hajiyar gaba tayi areesha ta bita a baya har zuwa loundry site na saman inda ta nuna mata komai dan har wankin anan zatayi,ta busar ta kuma goge,ga sabulai detergent kalakala da turarukan wanki,abun se wanda ya gani.
Tana gama nuna mata ne,ta le?a Wakin na mara lafiyan,tayi mamakin ganinshi fess se ?amshi yake yi,a zaune kan keken guragu,yana kallonta.
"hmmm Amreesh don't worry ,slowly but surely, one day one day"ta faWi gamida sakin wani murmushi ta gefen bakinta,lumshe idonshi yayi,ita kuma ta juya ta fice daga Sangaren nasu baki Waya.
Areesha ?arasawa tayi kusa dashi,jikinta asanyaye,duk da batasan me hajiyar ke cewa ba,amma ta fahimci kamar maganar batai masa daWiba,duba da yadda hawaye ke biyo idanunsa.
hannu tasa tana share mishi hawayen,ido yasa yana kallonta,wanda ta fahimci kallon Wauke yake da sa?wanni masu yawa sede bazata iya karantosuba.
ficewa tayi ta nufi kitchen ta haWo masa ruwan tea sabida hajiya ta nuna mata yadda zatayi amfani da gas Win,girki ko dama ta iya.
indomie ta dafa masa da ?wai,sannan ta haWo da ruwan tea Win ta dawo Wakin nasa.
abun cin abinci ta sa masa a wiyansa dan kar ya Sata kayansa.
turashi tayi kusa da gadon,ta fara bashi abincin duk da baya iya sarrafa bakinshi amma yana tsotsa,sun jima kamin yacinye abincin tass,tayi mamakin yawan abincin daya ci,dan bata taSa kawowa zeci kamar hakanba.
sosai ya bata tausayi dan ta fahimci ya jima rabonshi da abinci.
goge masa baki tayi ta cire abin wiyan,ta kwashe kayan takai kitchen Win sannan ta zauna acan taci nata abincin xuciyarta cike da tausayin ?an uwanta da mahaifiyarta.
wanke wanke tayi,sannan ta gyara komai ta fito a kitchen Win.
Wakin ta koma inda tasameshi yayi bacci akan kujerar,zuwa tayi,ta kwance belt Win data ri?eshi dashi sannan,ta rungumeshi da dukkan ?arfinta ta sashi akan gadon,sannan ta dawo ta Waga wajan Wuwawunshi da ?afafunsa suma tasa agadon.se haki take ga wata zufa dake karyo mota.
koda ta gama gyara shin,dubanta takai gurinshi,ga mamakinta kallonta yakeyi,tsintar kanta tayi da yimasa murmushi,tace"Allahn daya Wora maka wannan lalura ya yaye maka,domin alfarmar annabi,"takai mgnr hawaye na biyo idonta dan ita akwai raunin zuciya.
Lumshe mata idanunshi yayi alamun ya amsa,sannan ya maida su ya kulle.
Tsuru tayi agurin tana kallonshi,tana hasashen dalilin dayasa yake a hakan.
*********
Areesha an zama ?an gida inda ta zage take aykinta tu?uru,dan ta Waukeshi ba sanaa take yiba,Waukarshi take a matsayin sada?atul jariya da takesa ran Allah ze bata lada.
inda duk wata ake aykawa da bagobiri dubu Wari kuWin aykinta,shikuma ya Wauki dubu biyu yakaiwa lami,ladan ganin ido,sauran suyi wanda?arsu,da mari da?arta.
nafeesa ma gidan aykinta ana biya amma bekai na areesha,ba dan ita wanke wanke da wanki da sharane takeyi.
su waleed suma sun tsufa a dambua,sun zama almajirai ka'in da na'in.
**********
cikin watanni uku da fara aykin areesha,sega marar lafiyan,ya ?ara wani kyau namusamman kuma yayi ?iba,dan ko kaWan bata barinshi da ?azanta,kuma tana kunna mishi tv,a kwancen da yake,yana kallon tashar sports,yana Webe masa kewa.
tare suke kwana a Wakin sede shi yana kan gado ita kuma kan kujera take kwanciyarta.
Zaune take kusa dashi tana Wan matsa masa ?afafuwa dan yaji daWin rashin takata,wayar gefen gadonce tayi ?ara alamun ana kira.
hannu ta mi?a ta Wauki wayar,muryar hajiya taji tana faWa mata"ki sauko ?asa inason ganinki"
"to hajiya gani nan zuwa "tana ajiye wayar ta mi?e da sauri ta nufi gun kiran.
samunta tayi zaune a falon ta Wora ?afa Waya kan Waya.rusunawa tayi agabanta tace"hajiya gani"
"na ganki ay"hajiyar ta bata amsa tana haWe fuska.
shuru areesha tayi ta du?ar da kanta ?asa.dan batason ko kallon fuskar hajiyar tanayi.
"na kirakine zan saki wani aykin akan wanda kikeyi,kuma banaso asamu matsala,dan in aka samu matsalar sakamakon baze miki kyauba"cewar hajiyar cikin kakkausar murya.
AruWe areesha ta Wago tana kallonta bakinta na rawa tace"don Allah hajiya tunda har kinsan aykin akwai matsala karki bani aykin"
"ay tunda na ambata ya zame miki dole kiyi,shine zamanki lafiya,"cewar hajiyar tana doka mata harara.
Shuru areesha tayi tana son yin mgn amma tsoro ya hanata.
"Mahaifin Amreesh,ze dawo ?asar nan gobe in Allah ya kaimu,ina sone ko ya tambayeki matsayinki agidan nan kice ke maaikajiyar jinyace dake kula da lafiyar Wansa,kuma inaso ki suffantu dasu Win aduk lokacin da yake agunsa"cewar hajiyar tana kallon areesha wacce keta sauke ajiyar zuciya.
"Hajiya to ay bazan iya suffantuwa dasuba tunda banida kayansu,sannan ko turanci banaji,daga yes se no na iya"cewar areesha a Wan tsorace.
"wannan ba damuwa bane,,ga kayan na tanada,turanci kuma inkinso kice yess inkinso kice no,bade naso ne error ya bayyana"
"to hajiya zan kiyaye"cewar areesha.
Labcort ta bata,da sauran tarkacen kayan asibitin sannan ta sallameta bayan ta kwatanta mata yadda zatai amfani dasu.
Wakinsu takai kayan tana ta wasiwasi aranta akan dalilin hajiyar na sata tayi wannan aykin akan Wanta.
haka de ta kauda batun aranta taci gaba da bashi kulawar,abun askinshi ta gani acikin kayansa,tako Waukoshi,ta gyara masa fuska,da sajenshi,ta Wan rage masa gashin kansa,sama sama,sosai yayi kyau,farinshi ya ?ara fitowa.
shi kanshi yaji daWin askin dan anjima ba ai masa ba se yau.
***********
Washe gari, areesha tayi mamakin ganin jamian tsaro ta koina agidan nasu lokacin data le?a ta window,bata san meke faruwaba shiyasa ta shashance a gurin window tana kallon abinda ke faruwar,tunda ta gama shirya,Amreesh cikin shiga ta alfarma dan har taklmi da hula tasa mishi ta fesheshi da turaruka kala kala.
Tana nan tsaye taga jerin gwanon wasu motoci na alfarma sun shigo gidan,sojoji ri?e da manyan bindigu,sunyiwa wata mota ?awanya.dan bada kariya ga wanda ke cikin motar.
tana nande tsaye na cikin motar ya fito sanye da kakin sojoji. fuskarsa tabi da kallo baki buWe ta waigo ta kalli fuskar Amreesh,taga tsantsar kama da na wajan wanda ko baa faWa mata ba tasan mahaifinshine.
baro jikin window tayi tazo ta zauna kan kujera,bayan tayi shigar likitocin da hajiya tasata.
bata jima da zama ba taji ana tunkaro Wakin nasu,?ara gyarawa tayi,tana kallon ?ofar,ayko turo ?ofar akayi ga mamakinta,hajiyace,fuskarta Wauke da faraa,se mahaifinsa dake biye da ita a baya.
"my son yau de ga Abba ya dawo,"cewar hajiya tana dafo kafaWun amreesh Win.tsabar mamaki seda areesha ta kusa faWuwa ganin hajiya a Wakin nasu,harda dafa Amreesh,wanda tunda tazo gidan so Waya ta taSa shigowa Wakin.
Shiko mahaifin nashi da sauri ya ?arasa gurin Wanshi ya rungumeshi,yana bubbuga bayansa,yana sumbatarshi,hawaye ke zubowa a idanun Amreesh,ga ranar da yake dakon zuwanta,dan ya rungumi mahaifinsa,amma ba hali,sede shi ya rungumeshi.
sun jima rungume da juna,kamin mahaifin nashi ya sakeshi,ya dur?usa agabansa ya kamo hannayensa yana kallonshi,sosai yaji daWin ganin sauyawar Wan nashi alamun yana samun kulawa.
"Amreesh se yaushene zaka dawo zakin nan dana sani?ina mazantakar ka take,my son banason ganinka a haka,zuciyata zafi takeyi "cewar mahaifin nashi hawaye na biyo idanunshi.
Areesha dake gefe tuni ita tayi nisa cikin nata kukan,na tausayinsu harda sheshshe?a.
jiyo sautin kukan natane yasa babanshi da hajiya waigawa inda take,cike da mamaki ganin yadda tai zaman dirshan cikin fararen kayan likitoci ga abun gwaji rataye a wiya amma kuka take kashirSan.
"wacece ita me takeyi anan?"cewar mahaifinshi yana yiwa hajiya kallon tuhuma.
Murmushi hajiya tayi sannan ta Wan sosa kai,sannan tace."ay itace likitar dake kulawa dashi"ta faWi tana hararar areesha a sace da mata nunin tami?e tsaye.ita ko ina bata ma san hajiyar nayiba,koya takai dubanta gun Amreesh wani sabon kukanne ke sake kubce mata,ssbida tausayin da yake bata.
"likitansa fa kikace saratu,kinsan dawa kike magana kuwa?,da zaki dubeni kicemin itace likitanshi,a asibitin wainne mahaukatan take ayki da zata zamo likita,tana wannan shirmen."ya faWi dede lokacin da areesha tasa gefen rigirta ta likitocin ta face majina data tarun mata a hanci.
hajiya zagayawa tayi ta kusa da areeshn tana murmushi tace"doctor Areesha ay haka take,amma wlh tana ba amreesh kulawa fiye da zatonka,kuma ay shi kanshi yana jinmu,ka gwada tambayarsa"
Dubansa yakai gurin amreesh da tun Wazu yake fatan su haWa ido da mahaifin nasa,"wai hakane zaki?"cewar Abban.
Lumshe mishi ido yayi alamun hakanne,ajiyar zuciya Abban ya sauke,sannan ya mi?e tsaye yace"bari inje inyi wanka my lion,indawo musamu lokaci tare,"ya faWi yana sumbatar goshin shi.
se alokacin areesha ta farga basu gaisa da Abbanba,zumburr ta mi?e,tana goge hawayenta,ta Wan du?a tana gaisheshi.
murmushi yayi,dan ya fahimci akwai ?uruciya kuma da raunin zuciya tattare da ita,"brk doctor,"ya faWi yana murushi ya fice daga Wakin.
Da sauri hajiya ta kamo kunnenta ta murWe tai ?asa da murya tace"se k??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????inci kutumar ubanki,ze tafine"ta faWi gamida zuba mata wani ran?washi,sannan tabi bayan Abban da sauri.
Areesha ri?e gun tayi tana mulmulawa,dan ran?washin ya shigeta.
********
Wanka Abba yayi ya kimtsa sannan ya zauna yaci abinci,yana kammalawa,ya nufi Wakin Amreesh,
Hajiya saratu na ganin fitarshi ta zaro wayarta ta kira aminiyarta hajiya jummai.
bayan sun gaisa ne,tace"jummai kinsan ko abban amreesh ya dawo,?"
"bari kedai ?awata yanzu nake gani a nta news ya dawo,ina fatan de be gano shirinmu ba?"
"hmmmm Allah de ya kiyayene amma ?ar bura uban me aykin tawa takusa sawa kwaSata tayi ruwa na tufke"daga haka ta kwashe yadda akayi ta faWa mata.
"ah zan zo gidan muci bura ubanta,tare sabida ko dan gaba karta kira mana ruwa,tunda ta iya ayki bazamu koretaba ita amma dole muja mata kunne"
"Hakane ?awata,bari de inbishi abaya ya tafi Wakin nasu kar inje ta ji?amin ayki ganin bana gurin"cewar hajiya saratu.
Sallama sukayi ta ajiye wayar sannan ta ruga zuwa Wakin nasu areesha.
Shiko Abba lokacin daya shiga Wakin samun Areesha yayi tana ba amreesh abinci abaki akan gado,se haki take tayi gumi tai kashirSan,
cike da kulawa ya zauna akusa dasu yana kallon yadda duk hankalinta ya koma kan Wanshi,tana lura da bashi abincin.
"Likita waye ya maida amreesh kan gadon?"cewar Abba yana matsa hannun amreesh Win.
murmushi tayi tace"nice na maidashi dan ya jima a zaune yagaji"ta faWi a tausashe.
shuru yayi yana nazarin maganar,kamin ya nisa yace"wanka kuma fa waye yake masa?"
Shigowar hajiya saratuce ta katse ta daga bashi amsa,ita hajiyar ta amshi zancan da cewa.
"Waye ko zeyiwa amreesh Wina wanka daya wuce ni mahaifiyarsa?"ta faWi tana murmushi gamida jefawa areesha wani kallo na gargaWi.
"ok to duka Allah ya baku lada ku duka,amma de duk da haka zaa siyo mishi naurar da zata dinga Wagashi aduklokacin da bu?atar hakan ta taso"cewar Abba yana shafa kan Wan nashi.
"in banda kai ma abban amreesh ay base ka siyoba tunda zaman nasa anan Win ay waadinsa ya kusa ?arewa,"ta faWi tana murmushin muguntar abinda take ?ullawa akan amreesh Win.
"Duk da haka de gwara a siya masa,tunda yanzufa saura kusan watanni uku kamin ayi tafiyar,tunda likitan dazeyi aykin be dawo uk ba,kuma shi kaWaine babban likita na fannin lalurar tashi,shiyasa nafiso shi ya masa da kansa"cewar abba yana kallon hajiya.
"kamin zuwan lokacin na aykashi lahira,sede ay masa aykin akabarinsa"cewar hajiya a zuciyarta.a fili ko murmushi tayi tace"Allah ara mana rana."

"Doctor yanzu ba wani magani daze iya sha daze taimaka masa koda da ya samu ya fara mgn ne?"abba yayi tambayar yana kallon areesha,wacce tunda yazo yake ganinta ma?ale da abun gwajin bugun zuciya,ta ma?ala akunnenta kamar eirpiece,
Areesha ganin yana kallon sashinta ne yasa itama ta juya tana kallon ?ofar shigowa Wakin,dan zatonta doctor Winne ya shigo,tunda dama ?ofar abuWe take,shap ta mance sunanta doctor,
"Doctor ina magana kin juya"cewar abban a Wan fusace.
"doctor ana maganafa"cewar areesha gamida le?awa wajen ?ofar Wakin dan zatonta doctor Win na waje ne shi abban ya ganoshi.
hajiya tsabar takaici ji tayi kamar ta rufeta da duka amma ba hali.
zuwa tayi ta taSo areeshar tace"bakyajinsa yana miki mgn ne,wai meyasa tunda kika fara kulawa da amreesh tausayinsa ya fara sawa kina so kamar zaki zare,infa baki ajiye tausayinsa agefe ba,bazaki iya ci gaba da kulawa dashiba"cewar hajiya saratu cikin faWa.
"wacce irin maganace wannan hajiya kikeyi,zakice ta ajiye tausayinsa agefe,to so kike ta cutar min dashi,Wan nawa ?waya Waya dana mallaka a duniya."cewar abba cikin fushi.
"Aa ranka ya daWe nifa ba nufina kenanba,gani nayi tana so ta susuce sabida shi shine yasa kaji na jawo hankalinta data dawo hayyacinta,in banda abunka meson Wanmu da tausayinsa har kyautama ay zan masa."cewar hajiya tana karya wuya damurya.
murmushi abban yayi yace"to Allah ya bashi lafiya "
nan de suka jima tare dashi kamin hajiya ta hilaci abban su fice a Wakin zuwa nasu dan su samu damar raya wannan dare.
*********
To haka zaman ya kasance tsakanin areesha da hajiya,wacce da asuba zatazo tasa areesha ta yiwa amreesh wanka ta kimtsashi ba tare data taimaka mata ba,ta gyare Wakin fess,se ta dedeci fitowar abban nashi seta fito su haWu a hanya,inyace daga ina take,tace dama ay haka takeyi kullum da asuba take zuwa ta kimtsashi.
hakan sosai ta ?ara daraja a idonshi dan yana son duk wani wanda keson Wan nasa guda Waya da Allah ya bashi.
tsawon wata guda abba ya kwashe kamim ya Wage zuwa Somalia dan gudanar da wani bincike.bayn ya siyawa Wan nashi injinn daze taimaka wajan Washi a Wora akan kujerar guragun.
Ranar da ya tafi,hajiya jummai tazo gurin aminiyar tata hajiya saratu dan su san ta inda zasu Sullowa lamarin.
hajiya tayi murna da zuwanta nanko ta jata suka ?ule Waki.
"to wai saratu yanzu nufinki bari za muyi amreesh yasamu sau?i,asirin mu ya tonu,karfa ki manta amreesh yasan mune muka shirya hatsarin da mahaifiyarshi ta mutu,shi kuma dabe mutuba ya koma haka,Kowanne numfashi na amreesh barazace ga rayuwarmu,dan haka dole muyi gaggawar kaudashi."cewar hajiya jummai tana kallon saratu.
"Karki damu hajiya,na riga dana gama tsara komai amreesh baze kai labariba,da badan tsanani da zafin ubansaba da tuni na shayar da shege guba yasha ya bi uwar tashi,"cewar saratun tana cizon baki.
"To gwarade ki shirya,dan wlh in baki shirya ba,haka zaki zo a banza ki koma a alakoro,kina uwargida amma ace amaryarkice kawai keda babban kaso aduk dukiyar nan da mijinki ya tara,wlh gara kiyi maza ki aykashi kamin shima uban mu aykashi daga baya,dan in kika bar shi araye wata ze sake auro miki inda tsautsayi ta haifo Wa namiji,gara tun wuri ki ?ara masa gudu"cewar jummai.
"kisan uban me sau?ine akan Wan,bari mu fara kaudashi tukunna,dan in mukayi saa ba?in cikin mutuwar Wan ta sa zuciyar uban ta buga ya mutu kowa ya huta."
sun jima suna ?ullah makircinsu kamin jummai ta baro gidan bayan sun kira areesha sun ja mata kunne kan abinda ta aykata a zuwan Abban..
********
"areesha abincin da kikeba amreesh yana yawa ko ke baki ganine,dubi yadda yake ?iba ay ciwo zata zame masa nan gaba"cewar hajiya lokacin data lura da ?ibar da amreesh Win keyi kamar ba me jinyaba.
"hajiya bana cika mashi so uku kawai nake bashi,kuma bame yawaba,inaga de sau?ine ya fara samu shine yasa yake ?ibar"cewar areesha a tausashe.
"To daga yau so Waya zaki dinga bashi abinci shima na rana kawai na baki damar bashi."cewar hajiya a fusace.
a razane areesha ta Wago tace bakinta na rawa"hajiya so Wayafa kikace?"
"kina tantamane?"cewar hajiyar tana watsa mata harara.
"Aa hajiya gani nayi bashi da lfy cin abincin ze taimaka masa saSanin ace besamun wadatacce"
"to ko ?anin uwarkine,yadda nakeso haka zakiyi,inkuma bakijiba to wlh barinki gidannan yazo."cewar hajiyar kamar zata rufe ta da duka.
Shuru areesha tayi tana wassafa ta yadda zata fara yiwa amreesh horon yunwa,bawan dabe tarewa kowa komai ba.
Haka ta mi?e tabar gurin zuwa Wakin nasu jikinta a sanyaye dan batasan ta inda zata fara gudanar da wannan zalinci ba,tasan zafi da raWaWin yunwa to ko ma?iyinta bataso ajarabceshi da yunwa.
tunda ta shiga Wakin take kallonshi tausayinshi na kamata,shima kallonta yake,kawai seta fashe da kuka,ta zauna gefenshi,hannunsa ta kamo tace cikin kuka"mun kusa rabuwa amreesh,zan tafi in barka,dan bazan iya yiwa umarnin hajiyarka biyayyaba,ko kusa bazan iya yimaka horon yunwa ba,"ta faWi hawaye na ci gaba da zubo mata.
shima hawayen yake,sede beda bakin magana

2 / 13