KARUWA MAI CAPACITY COMPLETE BY ZAHRA MUHAMMAD SURBAJO.doc

Author :  Zahra Surbajo Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   3 / 13

6K to 9K   out of 38.9K words

shiyasa abin ke masa ciwo.
mi?ewa tayi ta fice zuwa kitchen taje ta Wora abincin,tana gama dafawa,ta dawo ta kulle Sangarensu sannan taje ta bashi abincin tausayinshi na ?ara kamata.
*********
haka aresha taci gaba da bashi abinci so uku arana bata taSa fasawaba.dan bataga dalilin denawarba tunda ba hajiyar bace ke Waga mata shi ba.
Rana dubu ta Sarawo rana Waya ta me kaya,yau areesha ta mance bata rufe ?ofa ba garin saurin ba amreesh abinci sabida yau ta Wan makara tasan yana jin yunwa.
tayi nisa a bashi abincin hajiya ta shigo Wakin,sosai ta tsorata da ganin hajiyar,ta rakuSe can gefe tana ware ido jikinta na rawa.
"lalle yarinyarnan wiyanki ya isa yanka,har nice zance miki ga abinda nakeso kiyi ki?i bin umarnina,to bakomai,arhar abincin ne yasa har kike tsallake dokata.,tunda abun hakane na hanaki girkin a gidannan,kidinga saukowa kina amsa aguna."cewar hajiya cikin fushi,danma idanuwan amreesh Win dake zube akanta suna mata kwarjini dase tayiwa areesha mugun duka.
ficewa hajiyar tayi afusace taje ta kulle ?ofar store da kitchen Win ta tafi da Wan mukullin.
areesha komawa tayi ta zauna taci gaba da bashi abincin tana share hawayen dake biyo idanunta.
*****
haka hajiya ta maida amsar abincin agunta,da ranane kawai take bada na amreesh,ita kuma areesha ta bata so ukun duka ba a wadaceba.
Areesha intazo seta raba biyu taba amreesh rabi itama taci rabin da rana se kowa yaci nashi.
Cikin ?an?anin lokaci jikinsu ya nuna dan daga areeshar har amreesh Win sun rame dan abincin be isarsu.
areesha bata taSa yun?urin guduwabadan tausayin amreesh Win takeyi,shiyasa take ci gaba dakulawar dashi.

************
"Lami nazo wancan satin nace miki ki tashi nasiyar da gidannan amma kin?i tashi,to wlh masu gidan sunce zasu zo su yaye kwanon saman gidan,anjima,shawara ta rage naki"cewar bagobiri a fusace lokacin dayazo faWawa lamin batun saida gidanshi.
"Baban areesha,in kace infita anan to inane kakeso inkoma,tunda ay zamanka nakeyi kaine keda alhakin bani gurin zama nida ?a?ana"cewar lami cikin kuka.
"Lalle zama a birni yasa kin fara iya rashin kunya lami,to bari kiji wlh bazan baki gurin zamaba inde a birnine,amma inkika amince kika koma ?auye kije gidana ki share ki zauna na yarda,amma baze yiwu inbaki gun zama anan ba"cewar bagobiri cikin fushi
"Anya kuwa kana tunawa da akwai mutuwa?"cewar lami cikin kakkausar murya dan ya kaita bango yau.
Tsabar mamakin jin abinda lamin ta faWa masa,kunnuwansa basu gasgata masa dashi takeba,hakanne yasa yawaiga dan yaga koda wani take ba shiba.samun tabbacin dashi Win take ta bashi ta hanyar cigaba da cewa.
"Allah yana kallonka duk cutarwar da kake tunanin kanamin,wlh kanka kakewa,kuma bagobiri inaso kasani wlh ba zan fita agidannanba matu?ar akwai igiyar auranka akaina ba inda zani"ta faWi cikin yanayin gushewar tsoron komai.
Waga hannu yayi da nufin ?waWa mata mari,carab ta ri?e masa hannun sannan tace cikin fushi."shekararmu sha bakwai da aure,amma har yanzu bakajin nauyin duka ko marina duk da tarin zuiaar dake tsakaninmu,wallahi yau idan hannunka ya sake ya taSani sena yi sanadin rayuwarka"cewar lami cikin matsanancin fushin dake tabbatar da abinda take faWi na zuwane daga zuciyarta.
tsabar razani bagobiri seda yayi baya itako ?ara matsoshi tayi cikin ?araji tace tana cakumo kwalarshi"ka taSani ka gani nace!!!!!!"ta faWi tana jijjigashi kamar zata hau iska.
da?yar ya ?wace ru?on da tai masa,a tsorace yabi hanyar ficewa dagagidan yana waigenta,tsoronshi karta Wauko wu?a tabiyoshi.
Tun daga,layin ?osai katagum road inda gidan lami yake seda bagobiri yaje sambisa road can jikin titin jirgin ?asa dake hayin rigasa a ?afa ba tare daya tuna a ?afar yake tafiyaba.tsabar tsoratashi da lamin tayi
haka ya shiga gidan mari se tsiyayar gumi yake.
be jira tabarma ba ya zube a ?asa ya zauna yayi tagumi hannu bibbiyu.
"Abban marainiya lafiya kuwa kake,ina takardun gidan?"cewar mari jiki a sanyaye lokacin data ?araso gunsa Wauke da tabarma .
da hannun rigarsa ya goge gumin dake fuskarsa sannan ya fara magana.
"mari batun gidannan kawai abarshi,dan wallahi yau lami yun?urin kasheni tayi,dan har ta faWamin da bakinta zatayi sanadin rayuwata"
"Tace zata kashekanne shine ni ka tahomin nan baka wuce wajan ?an sanda kakai ?araba,to wlh baze saSu ba bazan jure rashinka ba dan haka ni zani in sanar da jamian tsaro suyi muku takadda"cewar lamin cikin fushi na jin haushin lalacewar shirinta na mallakar takaddum gidn na bagobiri.
"mari mubar maganar nan don Allah ni wlh baa daidai nakeba,ta tsoratani"
mi?ewa tayi tace "wlh matu?ar ina mazaunin matarka sena kai ?ara dan bazan yarda akasheka a cuceniba,dan haka kaga tafiyata"tana kaiwa nan ta Wauki hijabinta a igiya ta fice gidan ranta,ba daWi.
direct police sation na unguwarsu ta nufa,cikin tashin hankali,tana kuka,koda ta isa gun ?an sanda ce musu tayi "kishiyartace ta biyo mijinta da wu?a zata kasheshi,su taimaka kar ta ida nufinta azuwa gaba hukuma ta Wauki mataki.

Lami ta cika da mamaki lokacin da taga jamian tsaro sunzo kamata,batai ?asa a guiwaba dan taji me ake ?ararta akai.
koda taje Win ganin mari da bagobiri be wani bata mamakiba,ta nemi guri ta zauna.
Dop ne ya zo ya Wauki statement Winsu duka,bayan ya gamane ya kaisu gaban DPO dan ya saurari case Win.
lokacin da dpo yaji bayanin compliners Win ya cika da mamaki amma beyi ?asa aguiwaba yaba lami damar faWin nata Sangaren
"Ranka ya daWe,mijinane shi da muka haifi ?a?a takwas dashi,amma besan kowanne hakki namuba,kullum sede yazo ya zaneni inna fita neman taimako,wai zan tona masa asiri,ya kwashemin ?a?a biyar biyu mata uku maza bansan inda sukeba ko zaa kasheni,sannan yanzu gidan da nake zaune wai ya siyar nace ya bani gun zama se in tashi wai in koma ?auyenmu, shine dan nace yaji tsoron Allah akan cutarwar da yakemin ya Waga hannu ze dokeni dalilin dayasa kenan nace masa inya dakeni senayi sanadin rayuwarshi,wlh jikina gukshatin dukansane nagajine,nima ?ar adamce,kuma in ya musa inada shedun gani da ido na irin azabar da yake ganamim"ta ?arasa maganar cikin matsanancin kuka.
dpo dubansa yakai gurin su mari dake ta faman zare ido,Yace"duk abinda ta faWi gaskiyane?"ya faWi yana kallon bagobiri.
"eh to ranka ya daWe anyi,haka baa yiba,sabida koma menene rashin jintane yaja mata"cewar bagobiri yana zare ido.
"Sargent"dpo ya kira wani dan sanda ya shigo da sauri ya kame gamida sarawa,sannan ya tsaya jiran umarni.
"Kaje da wannan mutumin kasashi a cell,ya WanWana rayuwar rashin ?enci yaji ko ya take,"cewar dpo rai aSace..
"don Allah ayi ha?uri kar akulleni wallahi bazan ?ara dukanta ba, na tuba,lami kiyi ha?uri"cewar bagobiri a ruWe lokacin da sargent Win ya dam?eshi.
ba wanda ya kulashi,haka aka tafi dashi aka kulleshi yanata magiya.
bayan an wuce da bagobirinne dpo ya kalli mari yace"kibar su su zauna lafiya,idan ya fito,sabida ta fiki tabbas agurinsa tunda uwar ?a?anshice,sabida shi be kawo ?arar matarsaba sekece mazaunin kishiyarta kika kawo,to kiji tsoron Allah,rayuwar ba iya nan bace akwai gaba".
shuru mari tayi jikinta na Sari tsoronrta kar itama ace akulleta.
"tashi kije"dpo ya bata dama,ayko arce ta fice tana godiya.
Dubansa yakai gun lami yace"kici gaba ha?uri watarana ze zamo labari,kibarwa Allah ze taimakeki,kuma ro?o ba abune me kyauba kidena zuwa kinayi,tunda beso,zan baki dubu hamsin kije ki kama sanaa Allah ya shiga lamarin"
lami fashewa tayi da kukan daWi ta zube agun tana masa godiya.
?ara kwantar mata da hankali yayi sannan ya bata kuWin ya sallameta.
********
"dawa kanaji ko zaa kawo motar asibitin yau dazata Waukeshi zuwa general hospital dan ay masa wasu vaccine before akaishi airport,don Allah ku maida hankali wajan gudanar da aykin nan,ka tabbatar da ka fasa masa kai da bindiga,kamar yadda akayi na mahaifiyarsa,wlh matu?ar kai nasarar raba amreesh da rayuwarsa,nayi maka al?awarin naira biliya Waya"Cewar hajiya saratu awaya lokacin da ta kira Wan taadan daze kashe mata amreesh adaren yau kamar yadda ta tsara.
Areesha dake tsaye bakin ?ofar falon na hajiya saratu tazo karSar abincinsu,babu abinda bata jiba.jikinta karkarwa yake,fitsari ya kubce mata agurin ba tare da tasan tayi ba,tsabar tsoro da firgicin da take ciki.
da ike hajiya tasan ita kaWaice a falonta hakanne yasa tasa wayar a handsfree,ta ajiye akusa da ita suke wayar da dawa Win,tana gyara farcenta.
daga can Sangaren dawa yace"karki damu hajiya yau zamu tabbatar da amreesh yabi uwarsa,tunda akwai kwashe awajanki wallahi yau seya ba?unci lahira,ya shedule Win nasu yake?"
"Kamar yadda baban ya faWamin yace,da laasar zaa kaishi asibitin,jirginsa na sha biyun darene,?arfe goma na dare ze isa airport,seku shirya"cewar hajiya cikin farincikin yau zata rabu da amreesh.
Areesha hannu tasa ta toshe bakinta sakamakon jkukan dakeson kubce mata,da baya da baya ta fice agurin zuwa Wakinsu,?irjinta na mata zafi,ta tura ?ofar Wakin nasu ta shige da gudu ta maida ?ofar ta rufe tana haki,
amreesh kallonta yake,yana son yimata magana amma ba hali,da gudu ta ?arasa gurinshi,ta kama hannaensa tana kuka tace"wallahi rai da rayuwata fansane agareka ya amreesh,ban sankaba amma ?addara ta haWamu,bazan iya bari ka mutu a hannun azzalumar matar nan ba,wlh koda zan mutu sena taimakeka"ta faWi cikin matsanancin kuka.
shima kukan yake sede baze iya maganaba,sede kallo,haka suka zauna zugum zugum ranar ko abincin bata koma amsowarba.
ga mamakinta hajiyar da kanta ta haWo abincin me rai da lafiya ta kawo musu Waki,bayan areesha ta karSane hajiyar tace tana murmushi.
"to ga abincinan duka kuci na ?arshe,ke areesha zaki rakasu asibiti anjima dan ?arasa aykinki,dan yau zaa wuce da amreesh uk zaa masa ayki yasamu lafiya,kaikuma amreesh inkaci wannan bazaka sake cin wani abincinba sede acan,ina maka fatan sauka lafiya,inka isa ka gaida mana da idon sani"
"hajiya sekace wanda ze mutu,da zakice yaci na ?arshe,bayan kina mazaunin mahaifiyarshi"cewar areesha tana bin hajiyar da kallon tuhuma
"Ah ke ba mutuwaba nake nufi,to inbanda ma abunki areesha ay kowa maze mutu,dan haka amreesh koyana so ko beso dole seya mutu,cewar Allahce ay"cewar hajiya tana ?an kame kame.
"ba iya amreesh Allah yace ze mutu ko baya soba,azzaluman da suke shirya makirci ma hajiya Allah yay musu gargaWi da mutuwa ba tare da sun shirya mata ba,dan haka mutuwa na kan kowa ciki harda ke dani,ba wanda yasan gawar fari"Cewar areesha muryarta na rawa.
hajiya ta kasa gane inda zancan na areesha ya nufa,hakanne yasa ta juya ta fice a Wakin bavtare da damuwar komaiba aranta.
Areesha komawa tayi kusa da amreesh, ta mi?a masa abincin da nufin yaci sede akaro na farko daya datse bakinshi alamun be son cin abincin.dole ta ?yaleshi itama bata ci ba ta ajiye agefe.
ta mi?e ta Wauro alwala tazo ta du?ufa sallah tana ro?on Allah ya bata ikon ceto rayuwar amreesh daga kaidin hajiya.
gab da laasar motar asibitin ta zo Waukarshi,hankalin areesha sosai ya tashi,amma bata da yadda zatayi,tanaji tana gani akasashi a motar,sannan hajiya ta bata umarnin itama ta shiga ta rakasu,inyaso in zaa tafi dashi airport ta dawo ta kwana anan in gari ya waye ta wuce garinsu.
haka akaja motar suka tafi hajiya se dariya take musu wanda areesha tasan manufar dariyar amma Allah ze maida dariyar kuka.
sun isa asibitin lafiya,duk wani gwaji da zaay masa an masa,inda aka barshi a wani Waki keSantacce daze fi sakewa shida me jinyarsa,kamin akaishi airport.
Areesha ta kasa zama se kaiwa da komawa take,a Wakin,ta rasa abinda ke mata daWi,,tabbas intabari aka kashe amreesh bata kyautaba,kuma bazata yafewa kantaba,dolene tayi me yiwuwa wajan ganin ta tseratar dashi.
fara bincike Wakin dasuke tayi,bata ga komai daze iya taimaka mata ba.
buWe ?ofar tayi ta fita,Wakin dake kallonsu,ta le?a ga mamakinta ba kowa aciki,se tarin kayan datti,wanda alamu suka gwada ba wankesu zaayiba sabida wasuma duk jinin jiki ya bushe, duk a fatattake suke,motsi taji abayanta da sauri ta waiga wani dattijone sanye da kayan ?an sharar asibitin Wauke da wasu kayan yazo zubawa.
gaisheshi tayi,cikin girmamawa sannan tace"Baba nan Wakin menene naga ba kowa aciki?"
murmushi yayi yace "?ata Wakin ajiyar kayan wanda sukayi mummunan hatsarine suka mutu,to in ankaisu mutuware nan ake kawo kayan jikinsu,wainnan ma da kike gani anjima zamuzo mu kwashesu muje mu zubar a inda aka tanada domin hakan,shiyasa ma suke a?u??ule"
shuru areesha tayi bata ce komaiba har tsohon ya shiga yaje ya ajiye kayan yazo ya wuceta,ay tana ganin fitarsa ta koma da gudu,cikin nasu Wakin,gadon da amreesh yake kai taje ta turo da gudu dan saura minti talatin akaishi airport Win.
Wakin ta tura gadon da ?yar ta iya mirgina wani ?ullin kayan ga mamakinta zip ne ajikin abinda aka ?ulle kayan,zugewa tayi ta tona tsakiya,sabida babban ?ulline,matso da gadon nashi tayi sannan ta mi?e ba tare da tunanin komai ba ta tuSe doguwar rigar jikinta ta abaya,ta tsaya daga ita se pant nonuwanta duk awaje,
cirewa amreesh jallabiyar jikinshi tayi tasa mishi rigsrta sannan tasa tashi rigar ajikinta duk yana kallnta.
mirginashi tayi cikin kayan dattin,sannan tace masa hawaye na biyo idonta,"ina maka adduar samun tsira da lafiya,inna tsallakewa mutuwarka da zan amsar maka, amreesh ina fatan Allah ya ?ara haWani dakai"tana kaiwa nan ta tuttura kayan kanshi a maida ta rufe zip Win sannan ta tura gadon zuwa Wakin da aka kaisu,
da sauri ta haye gadon ta kwanta, tasa facemask Win fuskar amreesh Win data cire mishi tun kawoshi Wakin,sannan taja hular jikin jallabiyar akanta,ta kwanta kamar yadda amreesh Win yakeyi.
ta kwanta ba jimawa,taji anzo an fara kwashe kayan dattin datasa amreesh aciki ana ficewa dasu,seda taji shuru alamun angamane hankalinta ya kwanta,hawayen farin ciki na ganin amreesh ya fita a asibitin,sede adduarta itace Allah yakai masa agaji da gaggawa a buWeshi acikin kayn da wuri .
turo ?ofar Wakin da take ciki akayi,da sauri ta runtse idonta tana karanto duk adduar da tazo bakinta,dan tsoronta kar su gane bashi bane.
suko maaikatan basuma fahimci komaiba dan wanda suka kawosu Wakin basu bane sukazo Waukarshi,dan anyi changing dutie.
Waukarta sukayi agadon marasa lafiya,suka gungurata zuwa motar da zata kaita airport Win,akasata aciki,driver yaja suka fice daga asibitin.
wanda hakan ya faru,akan idon yaran dawa daya turosu suzo suga tashin motar.
awaya suka kirashi suka shaida masa motar ta fito daga asibitin yazama cikin shiri.
motar data kwashe kayan dattin asibitn bata zame ko ina ba seda taje kogi state,domin a ruwan lakwaja ake zubar da kayan,gudun kar a?ona ya gurSata yanayi.
suna zuwa,bakin ruwan suka juye dattin aciki bayan sun buWe kowanne zip dan kayan sufi sauri ruSewa acikin ruwan.in suna a wawware.
juyawa sukayi suka bar gurin bayan sun juye kayan.
Wayyo amreesh,da areesha tasan aruwa zaa sashi da bata sashi acikiba,dan gashi yanzu yana ji yana gani yana nutsewa acikin ruwa bashi da damar taimakawa kansa.wanda ko baa faWaba yasan dole ne yau seya mutu kamar yadda hajiya saratu ta bu?ata.
ita ko areesha suna tafe a hanya ?irjinta kamar ze tsage zuciyarta ta fito sabida tasan tana kan hanyar mutuwarta,tunda tasan akan hanyar zaa harbi kan amreesh wanda take zaune amazauninsa.

sunyi nisa da tafiya kamin su isa airport Win dawa ya hango motar tasu,dan har hotonta anturo masa,?ara seta bindigarshi yayi,ya Wana kunamarta yana jiran dama me kyau daze saki kunamar.
tsaye yake kan wani dutse ya Wora bindigar tashi kan wani dutsen,yana kallon motar.
?arasowarsu tayi dede da zamewar ?afarshi,ya saki kunamar bindigar,kai tsaye harsashin ya tafi kan direban motar dake Wauke da areesha fus ya fasa masa kai,ayko motarce ta fara juyawa atiti,areesha ta ri?e kujera da kyau,tana salati,kwatsam motar ta bugi poll Win gefen hanyar ta kama da wuta dede lokacin areesha ta dire ta windon motar, da mahaukacin gudu,

da gudu su dawa sukayo kan motar ganin ta kama da wuta dansu ?ara buWewa motar wuta,ganin fitar ta mace da gudu daga motar be wani basu mamakiba,dan sun san cewa dama tare dame aykinsa ya baro gida,
wutar dake ci aciki da wajen motarne ya basu tabbacin amreesh ya amsa kiran Allah,.da gudu suka bi bayan areesha da nufin itama su kasheta ayko gudu take tamkar zata tashi sama,ko gabanta bata kallo,
su dawa dake biye da ita hango motocin sojojin dake nufar airport Winne alamun zasu raka wani babban sojan, yasa su Soyewa da sauri,itako batai auneba se ji tayi anyi sama da ita an makata da bishiyar gefen hanyar ta faWo ?asa jini na zuba ta hanci ta baki.
Da sauri motocin suka taka burki,sannan sojojin suka nufeta da gudu ciki harda Conel Maleek Abba ?anbatta,wanda shine zaa raka airport zashi meduguri.shine motar gabansu ta buge areesha.
ya riga sauran sojojin ?arasawa gurin da sauri ya Wagota ganin yadda jini ke zuba ajikintane yasa be tsaya Sata lokaciba ya nufi mota da mahaukacin gudu da ita,driver yaja da gudu suka juya,zuwa asibiti.
su dawa basu damu ba suka bar gurin dan dama fuskokinsu a rufe suke bare suyi zaton ta ganesu,kuma dama ay ba ita aka basu kwangilar kashewa ba,amreesh ne,kuma sunyi hakan.

Kai tsaye aka nufi asibiti da ita inda aka karSeta hannu bibbiyu,aka shiga ceto rayuwarta,
conel maleek be bar asibitinba yana jiran yaga farfaWowar yarinyar.
soke tafiyarshi yayi,aranar ya kira number mahaifiyarshi,bayan ta Waga sun gaisane yake sanar da ita abunda ya faru inda hajiya sosai ta tausayawa yarinyar.
"Inanso zan baro asibitin hajiya,ki sa driver ya kawo sabuwar me aykin nan taki tazo ta zauna da ita a asibitin kamin asan inda ?an uwanta suke."cewar maleek cikin tattausan lafazi.
"To maleek yanzu zaa kawota,Allah de yay maka albarka "cewar hajiya cikin jin daWin kyawawan Wabiun Wan nata maleek.
bayan sun gama wayar zama yayi yana yana ?are mata kallo tabbas wannan yarinya akwai kyau koma daga ina take ta haWa jinsi,da fulani.
yana nan yana wasafata aranshi,har ?ar aykin hajiyar ta ?araso asibitin.
har ?asa ta du?a ta gaisheshi ya amsa mata sannan ya dubeta yace"ki zauna tare da ita ki bata kulawar data dace da ita, mun bigeta a motane bamusan ?an uwantaba tukunna"cewar maleek a tausashe.
Amsawa tayi gamida mi?ewa ta matsa kusa da ita agigice ta waigo tana kallonshi tace"yayatace areesha ya mleek,wallahi ?aruwata ce"cewar nafeesa cikin matsanancin kuka.
cike da mamaki yake kallon nafeesar wacce se yanzu yaga kamanninta da marar lafiyar,duk da ita marar lafiyar tafi nafeesa kyau nesa ba kusa ba amma jini Waya yasa suna kama.
"to ya akayi tazo abuja,me takeyi a airport road?"cewar maleek yana kallon nafeesar.
"Itama aykatau Win muka zo yi,bansan me taje yi a airport Winba"cewar nafeesa tana kuka ri?e da hannun areeshar.
"to Allah ya bata lafiya zamu san abunyi akan matsalar data fito daku daga gaban iyayen naku"cewar maleek cikin kyakkyawan lafazi.
Nafeesa gefen areesha ta zauna se kuka take,dan gani take areeshar mutuwa zatayi.
Ficewa maleek yayi daga Wakin suka wuce gida shida masu tsaron lafiyarshi.
Bayan maleek ya isa gida sanar da hajiya abinda ya faru yayi,sosai itama ta jimama,ta ?ara da cewa."na rasa meke damun mutanenmu na arewa,su dinga maida rayukan ?a?ansu ba

3 / 13