Allah Gatan Bawa Complete Hausa Novel By Zahra Muhammad Surbajo.doc

Author :  Zahra Surbajo Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   3 / 12

6K to 9K   out of 33.5K words

yayi yace ka kyauta Anwar you Will pay for it kansa yagirgiza yashige daki momyce tashiga yimasa nasiha sosai seda taga yasauko sannan tace yaje yahuta itama tabi megidanta daki



love you all maman yusuf
[3/13, 07:08] Ussaina: *ALLAH GATAN BAWA*('('('('('('('('('('

_writting by Zahra Muhammad mahmud_


*this page is dedicated to Zahra Muhammad hausa novels group thanks you all am really appreciated*


*page 30*



Tunda daga wannan rana Anwar yafita harkar kowa agidan kamar yadda kowa yafita harkarshi ko momy tadena bi takanshi sabida dady yamata bayanin abinda yake aykatawa a mascow.
Kuma dady yashaida mata wlh seya dauki mummunan mataki game da abinda ya aykata


Yau lahadi Wanda yay dede da sati daya kenan da zuwan ilham abuja. tun karfe goma dady yashirya yafice agida tare da excord dinshi bazame ko inaba se gidan dayasa akai masa ilham gidan akwai tsaro sosai kai tsaye yashiga falon gidan tare da excord din daya ba alhakin kulawa da ilham wata dattijuwa suka samu zaune afalon wacce shekarunta basu wuce hamsinba matar kallon farko zaka mata kagane tanada kirki matar mesuna inna ladi jiki nabari tasauka akujera tana mikawa dadi gaisuwa Cikin mutunci yaamsa gaisuwarta sannan yasami guri yazauna bayan yazaunane yabada umarnin akawomishi ilham
Domin yaganta inna ladice tashiga daki tafito rike da hannun ilham wacce ko dawasa akacemaka itace bazaka yardaba sabida tin lokacin daaka Daukota ake aykin gyarata asatin datayi a abuja har wata kiba tayi ga haskenta daya fito Wanda ada datti yaboyeshi gashin kanta har kusa da duwawunta yasha gyara bakamar da daya dankareba sanye take da Riga da siket na kanti Wanda suka kara bayyanar da kyanta sede harzuwa lokacin miyau nanan kamarda da sauran lalurorinta
koda aka fito da ita dady yayi matukar mamakin ganinta ahaka sabida betaba kawowa ransa akwai wani mahaluki afadin Nigeria daze gwadawa Anwar kyauba segashi yagani atattare da ilham baiwar Allah azuciyarsa yafara magana yana fadin inbanda iskanci irinna Anwar wannan ay baabar dariya bace sabida duk kyan dayake takama dashi wannan tafishi matsala dayace kawai lalurarta yanacikin wannan tunaninne aka zaunar da ilham agabansa dagowa yayi yakalleta cike da tausayawa itako se dariya take mishi hadi da gwarancinta Wanda ko baa fadamasaba gaisheshi takeyi yayin datake magana shikuma miyau yashiga ambaliya ko afuskar dadi babu alamar kyamatarta illa tausayamata dayayi juyawa yayi game kula daita wato inna ladi dan tayimai karin bayani kara rusunawa tayi sannan tafara magana ranka yadade a iya zamana da yarinyarna nafahinci ba mahaukaciya bace kawai dolancine da ita domin har biro da takarda take rubutu bide bansan metake rubutawaba amma nasan duk dan makaranta yaga rubutun zeiya karantawa jeki kawo min rubutun inji dady mikewa tayi taje tadauko takardu wainda yawansu yakai goma daya bayan daya dadi yashiga dubasu abu dayane arubuce duka ajikin takaddun wato
*ilham shetima bukar*dady yayi matukar mamaki kobaaceba yasan sunanta kenan amma daya gwada seyace ilham bukar shetima dasauri tadaga hannu alamar itace kamar yadda takeyi amakaranta dariya duka sukayi anan suka gane sunanta amanarta yakara dankawa inna ladi sannan ya umarceta data share wa ilham miyan bakinta zedauki hotonta haka kuwa akayi inna ladi harda sake shafamata hoda tasamata jambaki wayyo Allah naso ace kuna gurin kuga yarda ilham tahadu ko kusa bame ganinta yayi zaton badaga indiya takeba dasauri dady yamata hoto kala biyu daya tasoma dariya wacce tabayyana hushiryarta me matukar kyau yayin da beauty point dinta shima yafito intakaicemuku ilham tayi kyau matuka
bayan yagama daukar hotontane yamike yamusu sallama yawuce.
koda isarsa gida hutawa yayi bayan yayi sallah yasa momy takiramishi Anwar da ihsan bayan sunzo dady ne yafara magana dacewa abinda yasa nataraku bakomaibane illa akan Anwar gaban anwarne yafadi azuciyarsa yace shikenan tafaru takare muryar dady ce tadawo dashi daga tunanin da ya fada inda dady yadora dafadin Allah yasani tun ashekarun baya nake umarta Anwar daya kawo matar dayakeso domin yayi aure amma yaki to hakanne yasa nidakaina nazabo masa wacce nake ganin tadace dashi ba Anwar ba hatta momy seda tafirgita dajin batun itako ihsan fadi take aranta Allah yakara dasauri yadago yana duban dady amma yakasa magana sabida zafin da zuciyarsa kemasa dady ne yaci gaba nasamomaka matar aure diyar mutunci sede yarinyace karama dan shekarunta basu wuce 14ba what inji momy takatse dady tahanyar cewa haba alhaji me yar 14 years zatayi agidan aure dan Allah kabar wannan maganar shide Anwar nashi ido dan yasan dady baya magana biyu amma azuciyarsa jiyake dama shi aljanine kawai yatashi yabace dady yaci gaba kuma nan da sati biyu zaa daura auren ba wani shagali zaayiba kawai daurin aure zaayi shagalin zaa dagashi zuwa lokaci namusamman. hawayene suka fara ambaliya a kan kyakkyawar fuskar Anwar. dan bakinciki yazaayi yana mazaunin dan shugaban kasa Wanda ahalin yanzu ankai sunanshi majalisar tarayya ta sanatoci da ta wakilai akan su tantanceshi zaa bashi mikamin ministan man petur na kasa amma ace bikinshi bashagali sekace wani mara gata kuka yaci gaba dayi dady ko kallonshi beyiba ita ko momy tundaga kallon fuskar megidan tasan bayason wargi dady ne yadauko wayarshi yanuno hoton ilham yamikama momy yana murmushi yace ga hoton surukartaki dasauri momy taamshi wayar tafara kallon hoton aybatasan sanda tarungume dady ba tanamishi godiya fadi take gaskiya kaiya zabe karfa kasa jamaarka sufarayi dakai tahanyar cewa se kyawawa kuke aure murmushi dady yakarayi yace wato naiya zabe ko ihsance taamshi wayar ahannun momy wani ihu tasaki gamida rungume yayannata Wanda tamanta fada sukeyi fadi take bross dady yagama yimaka komai tunda ze aurama wannan hurulinin dan Allah kalli hoton kagani da kamar baze kallaba amma se yadaure yakalla danyaga wanne kyaune wannan dahar yafi nashi da na momynshi kallon hotonyayi dasauri yamike yana fadin subuhanallah wani matsanancin farinciki ne ya ziyarceshi dagudu yakarasa jikin dady yarungumeshi yana masa godiya intakaicemuku Anwar harda yar kwallarsa ta farinciki godiya ko dady yashata tafi kwando dubu Anwar ne yafara magana dady yarinyar waye ita kuma yasunanta ilham bukar shetima sunanta wow gaba daya suka hada baki harda momy dady yaci gaba sanin yar gidan waye kuma wannan betasoba domin mahaifinta amininane dan haka aure nanda sati biyu sekaje kafara shiri rungume dady yakarayi sannan yanemi dady daya bashi contact dinta don su gaisa dady yabashi amsa da bata Nigeria se anyi auran zata taho kuma ba waya ahannunta Anwar beso hakaba amma kobakomai yasami hotonta dan wayar dady yadauka yatura hotunan atashi wayar tun agurin yadora daya akan dp dinshi yayi status da my wife to be shide dady kallonsu kawai yake yana dariya azuciyarsa dady ne yace kuma son kasaurareni dakyau duk ranar daka saki yarinyarna kobayan rainane banyafemaka ba dasauri suka kalleshi sannan Anwar yace haba dady karan haukane yacijeni dazan saki my Princess ay dady mutu karaba murmushi dady yayi sannan yace Allah yasa ameen dukansu suka amsa dady yaci gaba kuma in andaura auran anan zaku zauna zuwa wani lokaci kallon kallo suka fara Eh junansu momy ce kamarya alhaji banganeba hannu yadagamata sannan yace zaki gane senan gaba mikewa yayi yashige dakinsa yayin da momy tabishi jiki asanyaye
Anwar ko ko ajikinshi domin ji yake ko atiti aka ce yazauna da princess dinshi zama zeyi matukar yana tare da ita dasauri yayi wanka yashirya yafita tare da excord dinshi bezame koinaba segidansu wani abokinshi dane ga megirma ministan yada labarai wato bala usman kaita
Naseer bala usman kaita shine babban abokin Anwar tun secondry school har zuwa jamia suna tare tun ahanya yamishi waya akan yana tafe dan haka koda isarsu suntarar yana jiransu awaje Anwar nasauka amota suka rungume juna Jan hannunshi masser yayi zuwa part dinsa ayko ruwa beshaba yafara ba naseer labarin auransa sannan yanuna masa hoton matar bakaramin murna naseer yataya abokinshiva har yana cewa abokina Allah yabaka duniya kayi kokari kasamu kiyama daganan suka shiga shirya yadda bikin zekasance.





love you all =?? maman yusuf
[3/13, 07:08] Ussaina: *ALLAH GATAN BAWA*('('('('('('('('('('



_Written by Zahra Muhammad mahmud_


*page 31*



Lokacin bikin Anwar se karatowa yake yi yau saura kwana uku
Gaba daya Anwar yazama busy sabida zirgazirga yakosa adaura auren yayi tozali da kyakkyawar amaryarsa

Shima dady beda lokaci duba da yanayin aykinshi wani lokacinma baya kwana agida. Momy ce ke cigaba da hidimar komai duk da itama akwai nata aykin but bakamar dady ba

Kayan lefe kuwa tuni anhadoshi daga dubai baabunda babu fadin abinda ke cikin lefen ze cinye data baa gamaba
Bangaran dazasu zaunama tuni komai ansaka inkukaga daular daakasa abangaren da ilham zata zauna zaku dauka bazaa mutuba kayane na nunama saa yayinda shikuma megayya me ayki wato ango tuni yabada hotunan ilham akayimasa enlargemet dinsu manyan size yasaka agidan wasu kuma akayi editen danashi aka hada bame cewa batare suka daukaba abokanshi kuwa kowa yaga hoton amaryarsa murna suke tayashi insuka bukaci yakaisu sugaisa da ita sede yace bata gari wani lokacin har mamakin Anwar sukeyi sabida Anwar miskiline nabugawa ajarida amma yanzu yazama suda sabida auran ilham dazeyi
Ko invitation card na bikin abin kallone sewanda yagani


***********
Abangaren ilham kuwa har yanzu bawani sauyi dangane da lalurarta batamasan wainar daake toyawa akantaba
Inna ladi tsohuwar arziki itace tashiga gyara ilham tunda taji labarin aure zaamata duk da tana tausayinta agame da lalurarta haka taci gaba da durawa ilham magani na gyara mace dan ita gani take wata kila wani yakusanci ilham kafin zuwanta abuja.
Ilham ko takara wani fresh tayi kiba yayinda hips dinta suka fito masu kyan tsari cikinta ashafe yake maana bata da tumbi ilham mace ce har mace sede lalurarta ita zata hana ganin hakan


momy ce zaune ita da dady suna tattaunawa gameda bikin tace alhaji har yanzu baka fadamana ranar kai lefennanba gashi yau saura kwana uku biki nifa banganewa wannan auranba kaki kabudemin komai insanshi meke faruwane.murmushi dady yayi sannan yace sweet heart matukar baa daura aurannanba ankawo amarya ba bazaki gane komaiba dan haka kisa ranki a inuwa. Lefe shi kuma abangaranta zaku ajiye intazo tayi amfani dashi kallon mamaki momy take binshi dashi zatayi magana yadakatar da ita tahanyar fadin enough hajiya rai abace yatashi yabata guri baki asake.


Anwar yakosa yaga Princess dinshi dan yanzu har mafarkinta yakeyi. ahalin yanzu tunda dady ya sa ranar auranshi yadena shaawar kowacce mace bayan Princess itace burin ranshi yanzu duk da haka amma yana ganin yanzu tayi kankanta da daukar lalurarsa duk da yalura tanada girman jiki but zebi komai ahankali shiko romance da ita yakeyi yawadatar
Shiyasa gaba daya yagaza sukuni yakosa ashafa fatiha

gidansu yafara cika da danginsu kama daga na uwa harna uba sabida bikin Anwar duk inda yabi andunga ango ango kaga na ilham ay in ana masa wannan kirarin har kyautar kudi yakeyi Wanda shi kanshi besan yawansuba har security na gidan yimasa sukeyi dan su Samu nasu rabon
media kuwa bainda labarin auren Anwar bekaiba in tv ka kunna labarin ake in radio ne itama haka social media kuwa baa magana dan hotunansu daaka hada ake ta yadawa koina kowa yagansu yasan sundace dajuna yan mata masu son Anwar kamar zasuyi hauka dan bakinciki dan sunyi imani me mace kamar ilham baze kara kallon wata y'a maceba dasunan soyayya itako nafeesat yar gidan gomnan kano ganin hoton seda tayanke jiki tafadi agigice akayi asibiti taita Dakyar akasamu tafarfado kuji wahala darai shida besan tanayiba amma shine harda suma =?D?

*RANA BATAKARYA*.............





Love you all maman yusuf
[3/13, 07:09] Ussaina: *ALLAH GATAN BAWA*('('('('('('('('('('

_written by Zahra Muhammad mahmud_


*page 32*



*RANAR ASABAR*

ayaune dubban jamaa suka shaida daurin auran Anwar tare da amaryarsa ilham shetima bukar daurin auran dayasamu halattar shugabannin wasu kasashen, gwamnoni, sanotoci, yan majalisu, yankasuwa damanya manya atajirai dasauran talakawa masoya mulkin dady amatsayin shugabansu.
Andaura aure abisa sadaki naira dubu dari biyar inda aka bada dukiyar aure 50 millions ? babban masallaci na kasa wato central mosque dake abuja taro yayi taro kota ina security ne dan tabbatar da tsaro Ango baki yaki rufuwa se gaisawa yake da jamaa ana mishi fatan alkhairi
Daga gurin daurin aure walima suka wuce wacce megirma shugaban kasa yahada anci ansha anyi danasha maroka ranar kakarsu tayanke saka


Abangaren matama momy kanta har zafi yadauka sabida taro matan gwamnoni da sanatoci abikin baa magana se tambayar momi suke wai yar gidan waye Anwar ya aura sede tace musu childhood friend na dady dahaka take kashemusu baki Wanda dayawansu haushi sukeji dan be auri yayansuba
Itama momy walima kawai tayi indatace sabida amarya Bata kusane dazaayi event kalakala suko sukace bakomai ayi da suna in amarya tahaihu


Bangaren amarya ilham ko inna ladi takira masu gyara amare dayimusu make off anyimata tsayawa fadinkyan datayi surmen? domin bame cewa itace gashi anmata Jan lalle Wanda yakara haskata intakaicemuku inna ladi kwalin tissue taajiye akusa da ita dazaran miyau yataho zebata kwalliyar tagogemata kwalliya akama ilham sosai dan harda gwaggwaro aka nadamata yayin da gashinta aka zubo mata dashi ta kafarda ta hannun dama hotuna masu kwalliyar suka mata awayar da dady yaba inna ladi akan in anshiryata adauketa hoto zeturo a anshi wayar karkuso kuga hotunan domin iya kyau tayi kyau sukansu masu kwalliyar basuyi zaton itace sirikar mister pr?sident ba duk da sunga hotunan a social media amma basu kawo ita bace har suka gama suka fice bayan fitarsu bajimawa dady ya ayko abashi wayar inna ladi tamikawa dan sakon yajuya.

koda aka kaiwa dady wayar beyi mamakin kyan datayiba dukda kyannata nayau namusammanne danyasan itadin mekyauce
Da har zekira Anwar yaga kawai gwanda yatura masa ta WhatsApp hakanko yayi shigar hotunan badadewa Anwar yabude ihu yasa acikin abokansa yana my Princess my Princess dakyar naseer yanatsar dashi tahanyar anshe wayar ahannunsa ba naseer ba har sauran abokansa Sun girgiza daganin ilham dayawansu sunjinjina ma Anwar shiko yayi wa hotunan Kiss yafi akirga baa Bata lokaciba gurin yadasu ? media


haka taro yaci gaba da wakana har zuwa dare kowa yawatse se dangi nakusa
Sebayan isha dady yasamu kansa yashigo gida momy ce tarufa masa baya bayan yazauna nane yasha ruwan data kawo mishi sannan tace alhaji yabatun zuwa daukar amarya ne naga har yanzu shiru gefen fuskarta yashafa yana murmushi sannan yace senanda sati biyu zaa kawota kallonshi kawai takeyi dan ita yanzu bata yarda da dadynba tasan dole akwai abinda yake boyemata amma yazatayi intayi wari zatajine afili kuwa cewa tayi Allah yanuna mana ameen yabata amsa


Anwar sanda labarin amarya se bayan sati biyu zata tare yasameshi jiyayi kamar zeyi hauka dan bakin cikin amma bayadda zeyi da dady shi yagode ma Allah ma da hukuncin dadyn yazomasa da sauki =??


Abangaran dady kuwa yayi hakanne dan zuwa lokacin duk yanbiki Sun tafi sabida yayi imani Inde aka kawo ilham akan idonsu to labari mutumin dake china ma seyaji kamar agabansa akayi kunji dattijon arziki.



love you all=??maman yusuf
[3/13, 07:09] Ussaina: *ALLAH GATAN BAWA*('('('('('('('('('('

_written by Zahra Muhammad mahmud_

*salam sis kuyi hakuri da mistake din danayi narashin fadin Wanda yayiwa ilham waliyyi aranar daurin auranta.wani amintaccen malamin dadyne ya tsaya amatsayin waliyyin amarya.i hope that my apology is accepted*=?O?

*page 33*



Anwar ne kwance akan hadadden gadonsa yana baccinsa mecike da kwanciyar hankali.abaccinnasane yayi mafarki da ilham gurguwa dayakewa dariya wai gasunan awani lambu me kyau yayi matashin kai da cinyarta yana fadamata kalaman kauna yayinda itakuma take wasa da gashin kansa tana murmushi miyau nazuba abakinta zuwa fuskarsa amma bedamuba sema kokarin hada bakinshi danata yakeyi azuwan zema Kiss bakinsu nagab da haduwane yafarka abaccin agigice zufa tawanke mishi jiki rawa jikinshi yafara kamar meshin sanyi yayinda cikinshi yafara juyawa kafin wani dan lokaci zuciyarshi tafara tashi dagudu yashiga toilet yafara kwara amai kamar ze amayar da kayan cikinshi ko aman yatsaya hannunsa yake kara sawa abaki wani yataho domin gani yake kamar da gaske ne abin yafaru tube kayan jikinshi yafada shower dirzar jikinshi yake kamar ze sauya fata yana gama wankan yafara brushing din bakinsa seda yaga yana kokarin jima kanshi ciwo sannan yadena. Tun abayin zazzabi yarufeshi me zafin gaske kuma har yanzu zuciyarshi tashi take dakyar yafito daga bayin akan kafet yakwanta domin gadon kyamarshi yake ga zazzabi yanaji amma ko bargo yaki dauka yarufa kuma baze iya dauko waniba dakyar yamika hannu yadauko rumote din ac yakashe ahaka yakwanta agurin yana rawar sanyi yayinda idonshi ke zubar da hawayen bakincikin mafarkin dayayi yayi danasanin ganin gurguwarnan afili da zuciyarsa haka har wani wahalallen bacci yayi nasarar awon gaba dashi

Koda gari waye lokacin yin breakfast yayi kowa yahallara amma banda Anwar ganin shuru befitoba dady yace ihsan taduboshi ko lafiya

Dakinshi tanufa kai tsaye sabida ko kofa baa kullewa agidan sabida security din gidamma sunwadatar turawa tayi tashiga gami da sallama amma baya falo danhaka dakunan baccinshi guda hudu tafara dubawa daya bayan daya se ana hudun tasameshi kwance akasa idonshi yajuye ba baki se fari kawai ga wani kumfa da ya fito abakinsa ihu takwala Wanda yajawo hankalin su dady da security din dake kofar dakin dagudu duka suka shigo dakin abin dasuka gani bakaramin daga musu hankali yayi ba momy kuka kawai takeyi yayinda ihsan ketayata suna jijjigashi suna Kiran sunanshi
Dady ne kawai me karfin halin Kiran family doctor din gidan baayi minti gomaba yakaraso dasauri yasa aka dauki Anwar akamaidashi kan gado gwajegwaje yafara inda yagano suma yayi allura yayi masa sannan yadaura masa drip suka koma gefe suna jiran farkowarsa domin doctor yabada tabbacin ze farka akowanne lokaci
dukansu tambayar junansu suke meyasameshi Bayanjiya lafiya suka rabu dashi abinda basu saniba shine bayan mafarkinshi nafarko yadawo kasa yakwanta wani mafarkin yayi Wanda yafi nafarko domin nabiyunne suke excanging na miyau shida ita yayin da gefe guda kuma yana making love da ita har yanamata kuka dan dadin dayakeji. Tofa koda yafarka yaso shiga bayi amma yanayin zazzafan zazzabin daya rufeshi yahanashi samun damar hakan shine dalilin sumannashi
suna nan zaune har azahar sannan yafarka koda farkawarsa da amai yatashi Wanda yashiga kwarashi bakadanba hankalinsune yakara tashi koda yagama aman bayi yanufa yafara brush hmmm intakaicemuku Anwar harda wankan tsarki=?H?

bayan yafitone dady yakamashi ze zaunar dashi akan gadon dasauri yakwace jikinshi yayi hanyar kofar fita daga dakin dasauri ska biyoshi dady yarikeshi dan har lokacin jiri yake

3 / 12