Allah Gatan Bawa Complete Hausa Novel By Zahra Muhammad Surbajo.doc

Author :  Zahra Surbajo Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   9 / 12

24K to 27K   out of 33.5K words

adalciba sabida basu cancanci haka agurintaba to amna yataiya dansune bataso kuka tafashe dashi afili tanayiwa anwar Allah yaisa Dan dashi badansu mommy bane baabinda zeshiga tsakaninta dasu narashin kyautawa
kuka tayi me isarta sannan tamike tanufi daya daga cikin dakunan part dinta Wanda bata taba shigarshiba tsawon zamanta agidan koda shigarta dakin kamshin turaren anwar yakeyi jin kamshinne yasa zata juya da sauri idontane yasauka akan wani littafi akan side drower na gadon dasauri taje tadauki littafin haka kawai taji tanason karanta abinda keciki Dan ta Lura diary ne
fara karantawa tayi
abinda tagani a littafinne yarura tsananin kiyayyar da takewa anwar azuciyarta domin kuwa gaba daya labarin haduwarshi da itane a littafin harda irin azabar daya dunga ganamata hawayene yake zuba afuskarta jin first night dinta a toilet sukayishi bakincikine yaziyarci zuciyarta tabbas tayarda anwar ba masoyintabane duk da a diary din yafadi irin tsantsan kaunar dayake mata amma bata Lura dashiba kiyayyar daya bayyana yamata itace tafi tsayamata arai daukar littafin tayi ta tafi dashi dakinta yayinda taci gaba da kuka akan rashin kyautawar datayiwa su daddy
Daga karshe yanke shawara tayi akan gobe zata bar musu gida sabida zamanta da anwar yakare Ashe shidin bakin azzalumine haba no wonder taji tatsaneshi da yawa


maman yusuf
[3/13, 07:09] Ussaina: *ALLAH GATAN BAWA*('('('('('('('('('('


Zahra Muhammad mahmud




*page67-68*




Tun karfe takwas nasafe ilham tagama shiryawa tashirya su twins tadebi kayan sawarsu da duk wani Abu me amfani takira security yafitar mata dasu zuwa mota itama fitowa tayi rike dasu twins suna ganin tafito suka bude mata kofar baya tashige ita dasu twins Kai tsaye kaduna tanufa


Se sha biyu na rana suka isa kaduna
Sallama tayi tashiga falom gidan yayin excode dinta suka shigo mata da kayanta sallamarsu tayi suka juya Abuja

Mommy tunda tashigo take kallonta baki bude
Guri ilham tasamu tazauna sannan tagaida mommy
Bata amsa gaisuwarba tashiga jero mata tambaya
Ilham mekikeyi a nigeria bayan anwar bashida Lfy yana Egypt zaman mekikeyi baki bisu kuntafiba
Baki ta turo sannan tace ni ni ni bansan suntafiba ay
Salati mommy tayi tasanar da ubangiji
Sannan tace ilham Anya kinada imani kuwa dama Ashe baki janye wannan maganar tsakaninki da anwar innalillahi wainna ilaihir rajiuna ilham tafadi da karfi
sannan taci gaba wlh ilham kingama asara duniya da lahira yanzu irin wannan sakayyarce tadace da mahaifan yaronnan yau ko yau ko yankaki anwar yakeyi ki mutu ki dawo bedace da abinda kike masa ba

Wlh ko rantsuwa nayi bazan Yi kaffaraba ciwon anwar da hannunki aciki

Tunda baki da hankali duniya zata koyamiki
Kina da yara dashi Amman kike neman kashemusu mahaifi wlh insukayi wayo suka fahimci kece silar mutuwar mahaifinsu ko kallonki bazasuyiba
tunda haka kika zabawa kanki kije kiyi Allah yabaki saa
mommy nagama fadin haka tatashi taja hannun su twins suka shige daki suka bar ilham zaune afalo kamar mayya


Hawaye takeyi kamar fanfo tabbas jikinta yayi sanyi dajin kalaman mommy kuma tayarda tayi kuskure sosai su daddy basu can canci hakaba kuka takeyi kamar ranta ze fita

Gashi yanzu su daddy sunyi fushi da ita uwa uba ga hakkin mijinta har ga Allah yanzu tausayin anwar yakamata tuno irin wulakancin data dunga yimasa yana hakuri tayi wani sabon kukanne yasake kamata lalle tayarda in anwar yamutu itace takasheshi Allah kagafartamin tafadi afili
Babu abinda inta tunoshi yakemata ciwo ayanzu irin yadda mommy taganta Tana rawa alokacin da anwar yafadi ya ilahi cigaba tayi da kukanta harsu mommy da daddyn Adnan suka shigo falon batasaniba seda daddy yayi gyaran murya sannan tadago dasauri
Tana ganinnshi dagudu taje tarungumeshi Tana kuka Tana cewa daddy karkace komai wlh nagane kuskurena kugafarceni wlh bazan Kara ba natuba kakira daddyn anwar kace suyafemin wlh bazan kumaba nayi nadama kukan datakeyine yasa jikin daddy yin sanyi rungumeta shima yayi sannan yace to yaisa haka naji share hawayenki kuma naji dadi dakika gane kuskurenki dawuri sede fatan Allah yasa agurin mijinnaki baki makaraba Dan iyayensa nasansu zasu yafemiki kitayin addua

haka suka sata agaba sunatayimata nasiha Wanda bakaramin shigarta tayiba

Koda tazo bacci kasayitayi tunanin anwar kawai takeyi da irin cin kashin da tamasa
takosa tasashi a idonta kozata samu sassauci azuciyarta danjitakeyi kamar zuciyarta zata fashe haka takwana Tana kuka




*EGYPT*

Tunda suka isa likitoci sunfi goma akan anwar Wanda yake asume suna kokarin ganin numfashinshi yadedeta allurai akayimasa sannan suka daura masa drip daga karshe suka turashi cikin wani machine Dan yataimaka Wajansashi yafarfado dansu sami damar gudanar da aykinsu

gidan dasuka sauka su daddy suka koma sabida baa zama a asibitin

tunda suka shiga gida ihsan da mommy suke kuka dakyar daddy yashawo kansu sukayi shuru wanda koshi kanshi dabasa gurin kukan zeyi Dan dauriya kawai yakeyi


hirar rashin hallaccin ilham sukeyi mommy tace wlh alhaji bantaba tsammanin ilham ko wuta mukace tashiga zata musamanaba amma wai kirikiri tanuna bata kaunar gudan jininmu tabbas ilham tacika tsintacciyar mage kuma tabani mamaki

daddy ne yakatseta dacewa ku kwantar da hankalinku ilham baita tadorawa anwar ciwoba kuma baitace zata yayemasa ba se Allahn daya dora masa Dan haka banaso kuna damun kanku kawai muyiwa anwar addua shine mafita


koda dare yayi basu rintsaba sallah sukai tayi tanafila dannemawa anwar sauki agurin Allah.



koda gari yawaye suka nufi asibitin
babban likitanne yataresu
bayan sungaisane yake shaidamusu anwar yafarka

murna ce takamasu gabadaya suka rungume juna
likitan yaci gaba dacewa tun karfe uku nadare yatashi amma tunda yafarka yanata kiran sunan ilham har zuwa wayewar garinnan duk da maganarshi bata fita sosai asakamakon paralyse din daya samu
pls wacece ilham dinnan

kallonkallon suka shiga yiwa juna cande daddy yace matarsace
good inji likitan sannan yadora dacewa to magana tagaskiya danku yana matukar kaunar wannan ilham din kuma rashinta akusa dashi ze iya jawowa arasa Ransa
agigice suka Kalli juna
likita yaci gaba
azahirin gaskiya inda hali kukawomasa ita kusadashi

sabida semun samu natsuwar zuciyarsa sannan mudorashi akan magani zuciyarsa ta kumbura sosai dole da ita zamu fara sannan muzo kan paralyse din dayayi

mommy ce tace zamu iya ganinsa
eh xaku iyamana amma banda yin abinda zebatamasa rai

Jagora yamusu zuwa dakin da anwar yake
idonshi biyu
sunashiga yana kallonsu dasauri mommy taje tarungumeshi kuka yake abin tausayi yanacewa mommy ilham bata sona tace bazata taba sonaba har abada yafadi cikin muryarsa irin tamasu paralyse
Kara rikeshi mommy tayi Tana shafa kansa tace kayi hakuri my son ilham zata soka amma sekayi hkr kakwantar da hankalinka
rokonsu yashigayi akan Dan Allah sucema ilham tayafe mishi koda ta Allah takasance agareshi
maganarshi tafadarmusu da gaba danhaka dasauri daddy yakira daddyn Adnan awaya yake shaidamishi halin daake ciki hankalinshi atashe
shima daddn Adnan hankalinshi ne yatashi kwantarma da daddy hankali yashigayi inda yamasa alkawarin insha allahu duk yadda zeyi yasamarma ilham visa itadasu twins yau zeyi zuwa gobe insha Allahu zata iso sallama sukayi yanata masa godiya
doctor ne yashigo yace sufito haka daga dakin hakanan badan ransu yasoba suka tafi gida kowa zuciyarshi namasa zafi

Koda labarin zuwa gurin anwar yasamu ilham ranar kasa bacci tayi dan tun yamma tahada musu kayansu dan takosa gari yawaye taje tanemi gafarar mijinta. Duk da tasan batasonshi amma Tana tausayinshi yanzu kuma tayi alkawarin zama dashi abatasonshidin

*washe gari*

damisalin karfe goma nasafe jirgin su ilham yadaga zuwa kasar Egypt

anan semuce fata nagari anwar da ilham


maman yusuf
[3/13, 07:09] Ussaina: *ALLAH GATAN BAWA*('('('('('('('('('('

zahra Muhammad mahmud



*page 69-70*


Ilham ta isa kasar Egypt Lfy kuma su mommy sunyi murna dazuwannata danbasu taba tsammanin zatazoba rungume mommy ilham tayi tana kuka Tana fadin tagafarceta Don Allah wlh tatuba bazata sakeba kuka take iya karfinta tana nemam gafarar mommy

Wani sanyine yaratsa zuciyar mommy kuma dama ita mommy harga Allah tanason ilham dagota tayi Tana sharemata hawaye tace ya isa haka ilham nayafemiki Allah ya yafemana gabadaya

Kafar daddy taje tarike tana wani sabon kukan tace daddy baku cancanci haka agurinaba nayi kuskure megirma amma Don Allah kugafarceni sharrin shaidanne abinda nayimuku natuba tafada taname tsananta kukanta kanta yadafa yace Allah yamiki albarka ilham mommy ma tayafemiki bare ni nayafemiki duniya da Lahira yafadi yana murmushi

Kara durkusawa tayi tanamusu Godiya
Daganan tamike tanufi ihsan wacce secika take Tana batsewa Dan ita bataso suka yafewa ilham ba Dan laifinta babbane
rungume ihsan ilham tayi Tana neman yafiyarta itama tureta ihsan tayi gamida Jan tsaki tabar gurin tofa ilham binta tayi da kallo yayinda wasu siraran hawaye sukacigaba da zubowa afuskarta jitayi andafata dasauri tadago dantaga waye ihsance rungume Junasukayi suna kuka dakyar su mommy suka rarrashesu

doctor ne yafito yace ilham tabiyoshi bamusu tabishi suka shiga dakin da anwar yake
Suna shiga lokacin idonshi biyu kallon ilham yakeyi yayinda wasu hawaye ke fita a idonsa
Dasauri takarasa inda yake itama Tana kuka zama tayi agefen gadon dayake tadago kanshi tadora akan cinyarta tana wasa da gashin kanshi
Cikin kuka take cewa anwar kagafarceni natuba wlh bazan sakeba kayimin afuwa nacutar dakai dayawa Wanda baka cancanci hakaba kayafemin

anwar Wanda farinciki tuni yagama lullubeshi kanshi yadaga mata alamar yayafeta nuni yamata datadena kuka

Karar bude kofane yasa su waigawa sutwins ne tare da doctor dagudu suka karasa jikin anwar suna daddy daddy yayinda suka haye jikinshi sunata tsalle tsallensu namurnar ganinsa Dan sundade basu ganshiba

Farincikin da anwar yake ciki bashida iyaka koda doctor ya aunashi bakaramin mamaki yayiba ganin cikin kashi Dari kashi hamsin da biyar na kumburin zuciyar anwar yaragu yayi murna sosai sudaddy ma dasuka sami l??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????br sunyi murna se sama ilham albarka sukeyi tare da rokonta akan takula da anwar Don Allah



*BAYAN WATA UKU*

zuwa yanzu anwar yasamu sauki sosai tuni zuciyarshi tawarke komai ilham take masa batason ganinshi cikin damuwa ko kadan Dan Adan zaman datayi dashi wani zazzafan sonshi yakamata bata daburin dayawuce tafarantamasa

yanzu abinda yay saura kawai shine tafiyar anwar ta dedeta kuma shima kullum ilham seta rike hannunshi sunfita waje Tana koyamasa

Tuni su daddy suka koma Nigerian suda su twins tunda sukaga yafara samun sauki

daddyn Adnan ma shida iyalinshi harda ameera sunzo duba anwar

Manyan yan siyasa tare da yan kasuwa yawancinsu sunzo dubashi sabida anwar mutumne na mutane uwa uba daddynsa mutumin kirkine
Nafeesat ma diyar gwamnan kano so uku Tana zuwa dubashi Wanda hakan bakaramin bakanta ran ilham yakeyiba yayinda shikuma anwar yakejin dadin hakan



yanzu sede muce anwar Allah yakyauta gaba Dan ahalin yanzu babu me kallonshi yace yatabayin paralyse Dan Gama yawarke sumul tafiyarma tadedeta har wata kiba yayi sabida kulawar dayake samu daga ilham Wanda shi har mamaki take bashi yadda itace kemasa wanka shiryashi bashi abinci abaki dadukkanin wani Abu daya bukata har ga Allah yanajin dadin hakan



*Nigeria*


yaune ilham da anwar suka dawo gida kasa nigeria

dubban jamaane suka cika airport domin tarbarsu aciki harda mahaifinshi da mommy da ihsan dakuma su daddyn Adnan


koda suka fito daga jirgi ilham kusan tsorata tayi daganin mutanen dake gurin harkusan faduwa tayi anwar yatarota dasauri itakuma taratayo hannuwanta akan wuyansa suna kallon juna (tamkar arnav da khushi)

masu hotuna aykinyine yasamesu Dan daukar hotunansu sukashigayi kamar bagobe

suko sunyi nisa basu sanma abinda kefaruwaba dasauri ihsan takarasa gurinsu danta Lura shirin yiwa juna kiss sukeyi gudun abin kunya yasa taje garesu rungumesu tayi gaba daya dasauri suka dawo tunaninsu
gabadaya gurin akasa tafi Raf Raf Raf

suko su daddy kasancewarsu yan Boko hakanma burgesu yayi kuma sunyarda yanzu ilham ta gyaru

Karasowa sukayi gurinsu daddy ay su twins naganin iyayensu dagudu suka kwace daga hannun mommy suka nufesu suma suna ganinsu sukaduka suka daukesu suka rungume

dakyar securities suka janyesu zuwa mota Dan gama yan jaridane kamar zasu cinyesu da tambayoyi


Kai tsaye gida suka nufa
inda daddy yahada wata walima sabida farincikin samun saukin anwar
anci ansha anyi bishasha malamai sunyi adduoi sosai sannan akawatse taron

kowa yagaji gashi dama har anyi sallar ishai danhaka kowa part dinshi yanufa

ilham nashiga dakinta komai nanan pes wanka tayi tayi alwala tayi sallah sannan tazauna gaban madubi ta tsantsara kwalliya Dan yau sotake tafara faranta ran soulmate dinta Sunan databa anwar kenan
wata fitinanniyar rigar bacci tasa =?H?base namuku bayaniba atakaicede tahadu
turaruka tashiga fesawa jikinta
sannan tazauna zaman jiran anwar yafito
Dan su twins suna part din mommy

tananan zaune har karfegoma amma anwar befitoba danhaka tanufi dakinshi taga ko lfy

tura kofar tayi taji akulle danhaka tashiga nucking daga ciki yaamsa mata da wai wayene yake damuna=?3?
jiki asanyaye tace nice yace kewa dankari kirjinta tadafe sabida wani mugun bugawa da zuciyarta tayi nufinshi begane muryartaba daurewa tayi tace ilham

banza yayi da ita takai awa guda atsaye abakin kofar tanajiran koze budemata kofa amma shuru

dakinta takoma tahaye gado Tana kukan takaici meyasa anwar zemata Hakan kode dama be huce bane amma inde yace haka zemata gaskiya ze kwareta sabida yanzu sonshi takeyi kamar ranta
kwalliyar datayi ta goge sannan tacire rigar baccin tasa wata tahaye gado Tana ta kukan tausayin kanta



maman yusuf
[3/13, 07:09] Ussaina: *ALLAH GATAN BAWA*('('('('('('('('('('



zahra Muhammad mahmud




*Page 71-72*



Ranar ilham batayi bacciba kwana tayi kuka

Shiko abangaren anwar daurewa kawai yayi yawa ilham wulakanci beso ba to amma bashida zabi dole ne yakare martabar sunanshi na anwar a idon duniya



Duk yadda ilham taso su shirya da anwar batasamuba sabida baya bata fuska tayi kuka tayi magiya akan yafada mata abinda tayimasa amsa dayace bakiyimin komai daraja da martabar Sunana na anwar nake karewa a idon duniya
Duk sanda yabata wannan amsar rasa ina zata sa kanta takeyi sabida kwatakwata takasa gane meyake nufi

Dayake dakanta take girki ko abinci tashirya masa bayaci yadda taajiye haka zata dauki kayanta

Damuwar datake cikine yasa gabadaya tayi duhu tarame ko abinci bata iya ci kuma bazata iya tunkarar kowa da matsalartaba tabarwa cikinta


Tuni takammala karatunta inda kuma tasamu results me kyau
Daddy yashiryamata walima haka aka gama taron ba anwar abin bakaramin ciwo yamataba amma ta danne


Mommy ce takirata take tambayarta shinko akwai abinda kedamuntane dayasa tarame haka
Babu komai taba mommy amsa
Kintabvatar inji mommy
Kai Kawai tadagawa mommy
Mommy de takyaletane tunda batason fadamata Amman tabbas tasan akwai abinda kedamunta


Shiko anwar anashi bangaren yanzu soyayya yakeyi da nafeesat yar gidan gwamnan Kano sabida yanzu yayarda da kalmar hausawa dasukace kaso mesonka
nafeesat kuwa jitakeyi Kamar tafi kowacce mace saa aduniya tunda anwar yadawo dasoyayyarsa gareta
Kusan duk Friday yana Kano yaje gurinta soyayya sukeyi kamar zasu cinye junansu
Mahaifinta bakaramin farinciki yayi da hakanba

Anwar yaune yayanke shawarar sanarwa da daddy aje nemamasa auran nafeesa Dan so yake ahada bikin dana su ihsan Wanda yanzu saura wata biyu ayishi
Dan tuni ameera takammala karatun


A Falom daddy yasamesu shida mommy gaishesu yayi sannan yasanar da daddy bukatarshi tason auran nafeesa
Jikin mommy da daddy ne yayi sanyi dajin batun
to amma basuda ikon hanashi abinda yakeso kuma dama Sunsha alwashin bazasu sake tilastamasa yin abinda bayasoba

daddy ne yafara mgn dacewa aurefa kace anwar Anya kuna zaune Lfy da matarka kuwa

Amsawa yayi dacewa Lfy lau muke zaune kawai de ina raayin aurenne kuma inason nafeesan kuma ko na aureta banan gidan zan ajiyetaba gidana Dana Gama ginawa a asokoroad can zan kaita kunga bamasa guri daya bare har suyi rigima
daddy ne yakatseshi dacewa wannanne baze yiwuba sede kahadasu guri daya konan gidan kocan gidannaka
alfarma yanema akan to subari yafara tarewa da amaryarsa inyaso daga baya ilham takoma
kin amincewa daddy yayi inda daga karshe yabashi umarni akan ana saura sati daya Bikin yadauki ilham yamaidata gidan tafara zabar inda takeso sabida itace babba amma inyace amaryace zata fara shiga gidan yajawa uwar yayansa raini
amincewa yayi da batun daddyn

mommy cewa tayi to my son Allah yatabvatar da alkhairi sede inason kasani Dan zakayi aure baka isa kawulakanta ilham ba muddin kasan bazakayi adalciba karkasoma inbanda rigima irin taka nawa Kake dahar zakayi mata biyu nide kaji tsoron Allah kawai shine fatana kuma kaje kasanar da matarka
Hakade sukaitamasa nasiha akan yaji tsoron Allah yayi adalci
Sallama yamusu yawuce part dinsu
afalo yasamu ilham ita dasu twins tana koyamusu homework
dakinshi yashige bayan yama su twins wasa

Ilham ko Kokallo bata isheshiba


*bayan wata guda*


zuwa yanzu anje antambayarwa anwar auran nafeesat kuma antsaida ranar daya datasu ihsan
danhaka nafeesat tamatsamaa akan suje suyi free wedding pictures
ayko haka akayi sunyisu Kala Kala sewanda yagani tuni harsun bazasu a social media kowa se fatan alkhairi akemusu bama kamar nafeesa daake ganin tagama saa

ilham baiwar Allah batasan wainar daake toyawaba
Tana zaune adakinta da daddare anwar yayi sallama yashigo dakin
mamakine sosai akan fuskar ilham naganinsa inda daga karshe farinciki yakamata naganin Allah yaamshi adduarta anwar yazo gareta
tsugunawa tayi tagaisheshi kallonta yayi yaga tarame gawani baki datayi kamar ba ilham ba tausayintane yakamashi dakamar yafasa aywatar da abin da yakawoshi dakin wata zuciyarce tacedama kayi abinda yakawoka kafita Dan ilham bakanwar lasabace in tatashi yimaka Nata kalar iskancin rami take kokarin turaka

ya gamsu da shawarar zuciyartashi danhaka Kai tsaye
yamikawa ilham invitations card din auransa Wanda yake acikin wata envelop
amsa tayi Tana jujjuyawa dago ido tayi Tana kallonsa danyayimata Karin bayani
cewa yayi bawani abubane aciki Illa katin bikina zan Kara aure Nanda wata guda mezuwa
jiri ilham tafara gani yayinda takwalla wata Kara tazube kasa sumammiya
hankalin anwar ne yatashi agigice yadagota yana kiran sunanta shuru bata amsaba firish yanufa yadauko ruwa ya yayyafamata
ajiyar zuciya tayi daga karshe tarushe da matsanancin kuka har yanzu Tana rungume ajikin anwar din dagowa tayi Tana kallonshi ido cikin ido yayinda nata idon ke zubar da hawaye
[3/13, 07:09] Ussaina: *ALLAH GATAN BAWA*('('('('('('('('('('



Zahra Muhammad mahmud


*DEDICATED TO ALLAH GATAN BAWA FANS, MORE ESPECIALLY, RUMAYSA, TA YAKASAI, MRS SHAMSUR, MMN ILLOUA,MAMAN BATULA,HASSANA AHMAD,UMMU TWINS,HAFSAT IDRIS,DASAURAN WAINDA BANKIRA SUNANSUBA THANKS YOU ALL*


*page 73-74*

Kallonshi ilham takeyi idonta nazubar dahawaye bakinta na rawa tace abban twins Allah yasanya alkhairi yasa abokiyar zamanka ce yabaku zuria dayyiba. Tana gama fadin haka tasake rushewa da kuka

Jikin anwarne yayi sanyi dajin adduar ilham tabbas yasan abinda yayimata da ciwo to amma yana ganin shine mafita

Cigaba tayi da kukanta Wanda anwar har zuciyarsa yakejinsa dasauri yatashi yafice daga dakin
Kifewa ilham tayi agurin Tana cigaba da kukanta



Biki se matsowa yakeyi dan yau saura sati guda kuma yaune ilham tatare asabon gidan anwar
Fadin kyau da haduwar gidan seya cinye data 1gb =??bangama

Gidan samane danhaka ilham tazabi saman tana ganin zefiye mata duk da kasan yafi girma
Bangaren anwar ma asaman yake Wanda shi so yayi amaryarsa ta zauna asaman Amman bashida yadda zeyi ilham tazaba


Harda ameera da Mommyn Adnan suka rakota gidan dasu ihsan

Sata agaba mommy da ameera sukayi sunamata fada akan takwantar da hankalinta kishiya baakanta akafaraba kuma baakanta zaakareba
Sosai sukayimata fada gami da bata shawarwari
Daganan sukamata sallama suka tafi sabida gobe ne zaafara event na bukukuwan


Tunda

9 / 12