Author : Zahra Surbajo Category : Romantic Hausa Novels
[5/14, 11:30 AM] Ummu Fadila v: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*ƊAN ƘARAMIN SAURO*
*KADA UWAR GIWA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
.*Zahra Surbajo*
*Da sunan Allah me rahama me jin ƙai*
*wannan littafi me suna asama labarine da yake ƙirƙirarre,ban yi shi dan cin zarafin kowa ba,seda nishaɗantarwa da faɗakarwa gamida ilimantarwa,abinda zanyi daidai Allah yabani lada wanda nayi kuskure Allah ya yafemin*
*shine ze maye gurbin littafin gimbiya sabrina,maana na sauya masa suna,kuma ba free bane, meso seya biya kan ya karanta,dan gujewa ɗaukar hakkin da ba nasa ba*
*07044600044 domin biya afara tuntuɓar wannan number ta whatsapp ngd*
*1*
"Jalila you have to be very smart akan mijin nan naki,na gama lura dashi ɗan ɗaukar ƙafane,wanda kuma be dace musa ido muna kallonshi ba"cewar Aunty Sakeena dake cika tana batsewa.
Wacce aka kira da Jalila gyara zamanta tayi ta ƙyaɓe fuska irin ta ƴaƴan hutu tace a shagwaɓe"Aunty sakeena,nayi iya yina,amma wallahi bilal baya gani,kullum faɗa banyo kaza ba ban iya kaza ba, toni bansan ya yakeso in masa ba wallahi"
"mtsuuu rubish, why can't you tell him that ke ba ƴar wahala bace?ko be san daga inda ya auroki bane, kinga nifa Bilal ɗin nan raga mishi nake dan kina sonshi amma har shi waye daze dinga sa miki dokoki na banza da wofi."
"Nide aunty sakeena ki taimaka min wallahi gaba ɗaya banida kwanciyar hankali dan jiya yasha alwashin ƙaro aure matuƙar ban gyara ba kuma wlh aunty in ya faɗi magana baya sauyawa,"
A fusace sakeena ta miƙe tsaye tana gyara tsayuwar mayafinta tace da kakkausar murya"shekarun mahaifiyarmu talatin agidan babanmu,ko budurwa daddy be taɓa gigin yiba,dan haka muma ba namijin daya isa yay mana kishiya wallahi ko ɗan gidan uban waye,dan haka ki kwantar da hankalinki"tana kaiwa nan ta sury handbag ɗinta ta kwashi key ɗin motarta tace.
"Da zaran ya dawo daga tafiyar ki sanar dani zanzo na sameshi har gida inji uban daya ɗaure masa gindi yake miki abinda yaga dama"
Bata jira amsawar jalilar ba tasa kai tai ficewarta cikin takun isa da jinkai da izza da ƙasaita ta masu faɗa aji.
Motarta ta faɗa tai mata key,ta fice daga harabar gidan na ƙanwarta,zuwa nata wanda tsabar haɗuwar gidan nata bazaka ɗauka aduniyar mutane yake ba.
Tana parking ta fito masu aykin gidan tuni suka iso kwasar gaisuwa, bata kula ko ɗaya acikinsu ba,ta wuce cikin gidan,ranta a ɓace.
*******
Jalila da Sakeena ya da ƙanwa ne uwarsu ɗaya ubansu ɗaya,ƴaƴane ga attajirin ɗan kasuwar nan,Alhaji Habu Ɗan iya,me kamfanin Ɗan iya investiment limited dake afaɗin ƙasar nan baki ɗaya,
Akwai shaƙuwa me ƙarfi atsakaninsu,da soyayya me girma,sakeena nason jalila fiye da tunani,shiyasa duk abinda ze dameta take iya bakin ƙoƙarinta wajen ganin ta kawar mata dashi, kome girma da tsananinsa.
Tun daga primary har jamia a ƙasar holland suka yi,kasancewar mahaifiyarsu can take zaune,dan kasuwancin mahaifinsu yafi ƙarfi aƙasar.
Jaleela sun haɗu da mijinta bilal a can ƙasar ta holland,suka fara soyayya wanda ƙarshe akai musu aure kasancewar shima ubansa ƙusane aƙasar tamu.
Bayan auransu da shekara guda suka yo ƙaura zuwa nigeria,dan ci gaba da faɗaɗa kasuwancinsu.wanda shima bilal dole tasa ya baro holland badan yaso ba sedan farincikin matarshi.
Sakeena,ko Shekararta biyar kenan da auranta inda take auran Ɗan Hamshaƙin ɗan kasuwar nan wanda duniya ma tasan da zamansa sabida shura da shaharar sa.wato,Alhaji Aliyu wanda aka fi sani da Abu turab me suna Amdaz Abu turab.
Tun Auransu da Amdaz take sha ƙwayoyin hanz haihuwa dan ɗawainiyar yara baya daga cikin burinta,bata son haihuwa ma ita kwatata.
Sakeena mace ce me tsananin kishi da ji da kanta,bata son ƙasƙanci koya yake,kuma bata ƙaunar ko ƙuda ne inde na mace ne ya gogi mijinta,tana masifar sonshi shima kuma haka yake tsananin ƙaunarta.
Suna zaune a garin Abuja su duka,harda jalila da nata mijin Bilal da iyayensu sede kowa unguwarsa da ban.
Muje zywa
Surbajo for life.
[5/14, 11:30 AM] Ummu Fadila v: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*ƊAN ƘARAMIN SAURO*
*KADA UWAR GIWA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
.*Zahra Surbajo*
*Da sunan Allah me rahama me jin ƙai*
*wannan littafi me suna asama labarine da yake ƙirƙirarre,ban yi shi dan cin zarafin kowa ba,seda nishaɗantarwa da faɗakarwa gamida ilimantarwa,abinda zanyi daidai Allah yabani lada wanda nayi kuskure Allah ya yafemin*
*shine ze maye gurbin littafin gimbiya sabrina,maana na sauya masa suna,kuma ba free bane, meso seya biya kan ya karanta,dan gujewa ɗaukar hakkin da ba nasa ba*
*07044600044 domin biya afara tuntuɓar wannan number ta whatsapp ngd*
*2*
"Wannan lamari ba abune na wasa ba, dole ka maida hankalinka yayin gudanar da wannan bincike,mutanene masu matuƙar hatsari dan haka kayi komai da kulawa"cewar commissioner ƴan sanda.
Gyara zama Amdaz yayi yace"insha Allahu kamar de sauran ayyukan da muka gudanar,cikin nasara shima wannan haka za'ayi shi"
"wannan aykin ba irin wancan bane kagane hakan,Ƙauyan kurkujawa da zakaje ka zauna kanshi tashin hankaline agareka damu baki ɗaya,look amdaz baka saba da yanayin ba dan haka ba abune me sauƙi agareka ba,duk yadda kake kallon hatsarin aykin yafi haka"cewar shugaban ƴansandan.
"ranka ya daɗe aykina ajinina yake badan kuɗi ko neman suna zani ba,komai na zaman duniya Allah yaba mahaifina,amma basa gaba na kishin ƙasata kawai shi nake yi araina,kuma insha Allahu zan gudanar da komai successfully"
Badan ya gamsu ba yabar amdaz yayi signing ɗin aykin da zasu turashin dan yasan mahaifin amdaz ɗin kanshi baze barshi yayi ba amma baride ya rakashi.
Amdaz bayan barinshi office kai tsaye gida ya nufa,dan kewar matarshi duk ta dameshi.
Koda ya shigo harabar gidan yaga motarta sosai farinciki ya kamashi,dan beso yazo be sameta ba,dan ɗazu sunyi waya ta shaida mishi tana gidan jalila,.
Cikin takunsa na ƙasaita ya shiga ɗakin matar tashi,wacce ke zaune kan sofa tana waya yayinda hannu ɗayan kuma tana mulka wata humura ajikinta,fitowarta wanka kenan ta zauna wannan aykin na shafe shafe.
Jin da wa take wayar ne yasa be yi magana ba,zuwa gefenta yayi ya zauna,kwantowa tayi jikinshi shi kuma ya rungumeta yana shinshinata,idanunsa a lumshe.
Ita ko cigaba tayi da cewa"Mom jalila bata da hankali na faɗa mata ta tashi tsaye ta nuna masa ita ba house girl bace,amma taƙi dole se mun tashi haiƙan akan bilal momy"
Har ta gama wayar shide bece komai ba waigowa tayi gareshi tana murmushi tace"my d sannu da zuwa ya office?"
"Office ba daɗi baby,nayi missing soft skin ɗinnan naki"
Shigewa ta ƙarayi jikinsa tana ƙoƙarin lalubo bakinsa tace tana hawa kan cinyarsa,"am always yours my d kayi yadda kakeso"tana kaiwa nan ta haɗe bakinsu guri guda ta shiga kissing ɗinshi yana biye mata
sannu a hankali ya ɗora hannunshi kan boobs ɗinta ya fara pressing a hankali,ayko sakeena ƙara sakar masa jiki tayi tana wani sakin sauti dake ƙara kashe masa jiki,tana ɗan kukan shagwaɓa.
Tana sake kamoshi,miƙewa yayi tsam ɗauke da ita suka ƙarasa kan gado dan yadda yake jinta ba abinda ze iya inba jinta yayi ba,kasancewarsa mutum mabuƙaci.
Tuni sukayi fatali da duk wata sutura ta jikinsu suka manne da juna,bakin amdaz nakan boobs ɗinta yana surcking,yayin da hannunta ke kan hajiya kande tana wasa da ita,kowa cikinsu da ƙyar yake fitar da numfashi,sabida kullum basa gajiya da juna.
A haka suka raya wannan dare cikin so da ƙaunar junansu,koda gari ya waye manne suke da juna kamar sabbin ango da amarya,
Wrek end ne shiyasa har sha ɗaya na safe yana gida suna zuba soyayya shida abar ƙaunarsa,wacce yake jin yafi kowa son matarshi Dan so tari in yana kallon sakeena har mamakin mazan dake ajiye mace sama da ɗaya yakeyi.
Zaune suke akan dinning,asabe me aykin dafa abinci ta shigo da warmers na breakfast ta shirya musu sannan ita ta zuba musu komai sannan tabar gurin dan sakeena cokali bata ɗaukewa da sunan ayki.kuma amdaz hakan be damunsa dan acewarsa aurota yayi tazo ta huta batazo tayi ayki ba,yana da kuɗin daze mata komai dan su zauna lafiya.
Suna kammalawa falo suka dawo zamansu ba jimawa hanifa ƙawar sakeena ta kirata awaya ayko tana ɗagawa suka fara wasa tsakaninsu inda hanifa tace"agidan amdaz"
Sakeena tace"ni kaɗaice"
Haneefa tasake cewa"keda kishiya"
"se bayan na mutu"cewar sakeena tana dariya shima amdaz dake jin duk abinda suke cewar dariyar yakeyi.
"in yace zeyi miki kishiya"cewar haneefa.
"shi ze mutu"ta bada amsa tana kwantawa ajikin amdaz ɗin shima yana sake riƙeta suna dariya.dan daga shi har ita suna da tabbaci da yaƙinin da ga kanta ya gama ƙara aure.
Sun jima suna hirar su ta manyan mata kamin ta kashe wayar.
Fuskarta amdaz ya shafa yace atausashe"baby bakison kishiya ni kuma duk abinda bakiso nima bani sonshi,kishiya kota kwana ɗaya ce ni amdaz bazan miki ba,ke ni ko a aljannah inde yadda nakeso zaay min ke kaɗai acan ma kin wadaceni"
Rungimeshi tayi tana jin sonshi na ƙara shiga zuciyarta tace"zan dawwama ni kuma ina yiwa soyayyarka hidima"
Haka suka yini farantawa juna rai,se da gari ya waye amdaz ya sanar da ita aykin sirrin da aka turashi ƙauyan kurkujawa,kamo wani hatsabibin ɗan kidnapping daya addabi alumma,wanda suka samu masaniyar yayi mafaka a ƙauyen.
Wanda amdaz ya aminta zashi amatsayinsa na ɗan sandan farin kaya,wanda kuma ya kasance jamiin sirrine shi.
Mahaifinsa yayi iya yinsa yaga ya rabashi da wannan ayki amma sam yaƙi bari acewarshi tsaftace ƙasarshi na cikin abinda ke sashi nishaɗi kuma burinsa kenan.
Sakeena bata so tafiyar ba amma kasancewar abinda yakeso itama tana so se tayi masa fatan alkhairi gamida samun nasara akan aykin.
Mahaifinshi baya gari dan haka mahaifiyarshi kawai ya sanarwa sannan ya kama hanyar ta kurkujawa,bayan ya gama seta duk abinda ze seta na baɗda bami,be bar kowacce alama dake nuna shi ɗin jamiin sirri bane.
Muje zuwa
Surbajo for life.
[5/14, 11:30 AM] Ummu Fadila v: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*ƊAN ƘARAMIN SAURO*
*KADA UWAR GIWA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
.*Zahra Surbajo*
*Da sunan Allah me rahama me jin ƙai*
*wannan littafi me suna asama labarine da yake ƙirƙirarre,ban yi shi dan cin zarafin kowa ba,seda nishaɗantarwa da faɗakarwa gamida ilimantarwa,abinda zanyi daidai Allah yabani lada wanda nayi kuskure Allah ya yafemin*
*shine ze maye gurbin littafin gimbiya sabrina,maana na sauya masa suna,kuma ba free bane, meso seya biya kan ya karanta,dan gujewa ɗaukar hakkin da ba nasa ba*
*07044600044 domin biya afara tuntuɓar wannan number ta whatsapp ngd*
*3*
*ƙauyen Kurkujawa*
Sosai ya wahala akan mashin ɗin daya hau dan ya ƙarasa dashi ƙauyen garin,dan motarsa can cikin gari ya barota.
Kayan dake jikinshi ko kusa ko alama bazasu nunama shi ɗin wani bane.
Da la'asar ya isa ƙauyen garin na kurkujawar yayi mamaki sosai ganin garin kowa harkar gabanshi yakeyi,kamar basu da damuwar komai.
Masallaci ya nema yaje yayi sallolin da ake binshi,bayan ya idar ne ya zauna cikin masallacin yana nazartar masu shigowa da ficewa ciki,
Wani bafulatanine ya shigo masallacin fuskarsa ɓoye cikin rawani,gefe guda ya koma ya zauna acikin masallacin sannan ya duba ko ina da ina yaga bame shirin shigowa,sannan ya Ciro waya a aljihunsa ya kira wata number,da fillanci yake maganar shiyasa amdaz be fahimci komai ba,yana gama wayar ya yunƙura ze tashi,inda rigarshi ta yaye amdaz ya hangi hancin bindiga a jikinsa maƙale.
Ko kaɗan be nuna yama san da zaman ɗan filanin ba shiyasa ɗanfilanin be lura dashi ba,yayi ficewarsa.
Da sauri amdaz ya Mara masa baya shima ya fice daga masallacin.
Cikin salon da mutumin baze fahimci shi yake bi ba ya dinga bin bayansa har suka isa ƙofar gidan daya zo sannan amdaz ya raɓe shi kuma ya shige cikin gidan ya turo ƙofa.
Amdaz rasa abun yi yayi Dan haka juyawa yayi ya koma masallacin, fura da nono ya siya gurin wasu Fulani da kyar ya iya shan fura sabida tsantsani da kyar de ya samu ta zauna.
Wasa wasa kwanan amdaz uku amasallacin nan yana bincike sannu a hankali ya samu tabbacin Wanda yake nema shine ke shigowa masallacin nan yin waya. Wato Haruna Gyauto.
Sede ya fahimci haruna gyauton a ankare yake da motsin kowa shiyasa ya ɓoye fuskarsa gareshi gudun ya zargi wani Abu.
A binciken na amdaz ya fahimci haruna tare yake da iyayensa da ƙannansa a wannan gida,Dan haka dole se ya samu alaƙantuwa da ƴan gidan sannan ne ze samu nasara kan abinda ya kawoshi.
Cikin gari yake zuwa yayi waya da matarsa sannan ya sayi abinda yake so yayi amfani dashi,ko kaɗan be zama kullum a masallacin gudun agane shi baƙone.wani lokacin makarantar primary yake zuwa ya kwana,a ɗan wannan lokaci gaba ɗaya amdaz yayi baƙi ya rame sabida rashin sabo da yanayin.
So yake ya fahimci waye ubangidan harunan da yake waya dashi kullum,Dan haka dole seya bibiyeshi zesan ko waye.
Yau da wuri ya baro cikin gari yazo inda ze hangi duk me fitowa daga gidan nasu haruna.
A karo na farko kenan daya ganta ta fito daga gidan.
ƴar matashiyar budurwa wacce bata wuce shekaru sha biyar ba aduniya,kyakkyawace ajin farko,Dan karo na farko kenan da idonsa ya ga macen data fi sakeenar sa kyau.yayi mamakin faruwar hakan matuƙa.
Ɗauke take da ƙwaryar nono akanta alamun tallah zata tafi,sanye take da hijabi da takalminta silifas,se zanin atamfa da rigarta t-shirts.
Ko kwalliya bata yiba,tafe take tana rangaji Wanda jama'a ke ɗauka tana sane take tafiyar.
Ta gabanshi tazo ta wuce,bata lura dashi ba,ayko zama yayi agurin be tashi ba,har taje ta dawo lokacin duhun dare ya kawo kai Dan haka,tana zuwa zata wuce ya riƙe cikinshi ya fara yunƙurin amai yana faɗin "ataimakamin zan mutu wayyo Allah na"
A tsorace ta waigo inda yake,da sauri tayo baya tana faɗin "bawan Allah lafiya me ya sameka"ta faɗi cikin muryarta ta ƴanfulani.
Da ƙyar yace"yunwa.... yunwa ....yunwa nakeji kutaimakamin"yafaɗi gami da yanke jiki ya faɗi.
Ayko agigice ta ruga cikin gidansu tana faɗin "hande ɗun boni baffa kazo wani mutumi ze mashe a ƙofar gida"agigice take maganar hakanne yasa haruna dake ɗaki fitowa da sauri yace mata"yana Ina?"
Waje ta nuna masa Dan haka shida baffan suka ɗunguma zuwa wajen zuwa lokacin gishirin Andrew ɗin da amdaz ya sha kan ta kirawo sun ya fara turoshi,ta bakinsa.
Muje zuwa
Surbajo for life
[5/14, 11:30 AM] Ummu Fadila v: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*ƊAN ƘARAMIN SAURO*
*KADA UWAR GIWA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
.*Zahra Surbajo*
*Da sunan Allah me rahama me jin ƙai*
*wannan littafi me suna asama labarine da yake ƙirƙirarre,ban yi shi dan cin zarafin kowa ba,seda nishaɗantarwa da faɗakarwa gamida ilimantarwa,abinda zanyi daidai Allah yabani lada wanda nayi kuskure Allah ya yafemin*
*shine ze maye gurbin littafin gimbiya sabrina,maana na sauya masa suna,kuma ba free bane, meso seya biya kan ya karanta,dan gujewa ɗaukar hakkin da ba nasa ba*
*07044600044 domin biya afara tuntuɓar wannan number ta whatsapp ngd*
*5*
Ɗakinshi ya kaishi,inda ya shiga nuna masa bindigunsa,da kuɗaɗensa,daga haka kuma ya bayyana masa kansa amatsayin wanda gomnati ke nema ruwa a jallo.sannan ya ƙara da cewa.
"in har zaka saki jiki damu kayi ayki damu zaka samu arziƙi,aykinmu sirri yakeso dan haka ka kula zamyi ayki dakai kafaɗa da kafaɗa"
amdaz cikin tsananin farinciki ya rungume harunan yana fadin"nagodewa Allah haɗuwata da kai wallahi nasan hutuna yazo zan samu arziki"
Haka de haruna yasaki jiki da amdaz yana ta buɗe masa sirrinsa,ƙarshe ma daji ya kaishi ya dinga koya masa harbi da bindiga.
Zaman amdaz da haruna ya fahimci akwai sauran sirrinsa dabe gama sanar masa ba,shiyasa yaci gaba da kwantan ɓauna Dan ya naɗi bayanin da yakeso ya Naɗa.
Wasa wasa yau kimanin watanni uku kenan da zaman amdaz da haruna, a wannan lokacin har inda ya ɓoye mutanen da suke garkuwar dasu yajashi ya kaishi,sosai tausayinsu ya kama amdaz amma ko kusa be nuna ba.
Ƙanwar haruna wato Abeeha ko kadan bata Ƙaunar ganin amdaz Dan ta tsani duk wani Ɗan kidnapping bata de da yadda zatayine dasu, amma har ranta bata Ƙi hukuma ta kamesu su duka ba
Haruna a cikin yaransa yasamu labarin an turo Ɗan leƘen asiri garin zaa kamashi Dan haka hankali tashe yaje gida,ya samesu zaune baffa na Ƙara yi ma amdaz nasiha kan su dena abinda sukeyi.
"Baffa Ku haɗo kayanku aradun Allah an yo min shune daga habuja,Dan haka kuzo mu bar nan yau ɗinnan dan in sun San wata basu San wata ba"cewar haruna cikin fushi.
Amdaz sosai yaji daɗin samun labarin da harunan yayi Dan yasan cikin sauƙi ze kamashi.
Baffa ko cewa yayi "ba inda zani haruna kaje koma inane amma banda ni, nagaji da mugun halinka"cewar baffa yana kwallah.
"Hikenan baffa mu to zamu fice yau ɗinnan nida amdazu"
Haruna bindigunsa ya shiga haɗawa inda shikuma amdaz yace bari yaje ya kwaso nashi kayan shima yana shigewa ɗakin harunan ya tura saƙon "attack" ga sauran jami'an da suka biyoshi amma suna cikin gari.
Cikin ƙanƙanin lokaci suka shigo garin cikin shirin yaƙi dauke da manyan bindigu
Hankali tashe haruna da yaransa guda biyu dasuka biyoshi ɗibar kaya,suka fara ƙoƙarin direwa ta Katanga.
"You're under arrest"cewar amdaz lokacin daya Ɗana kunamar bindigarsa akan haruna.
Cikin tsananin mamaki haruna ya dubi amdaz yace"hai meye haka kakeyi?"
"Jamiin farin kaya,Daga nigerian army,atisaye ƙarƙashin hukumar ƴansandan farin kaya ta nigeria amdaz abuturab daga abuja nazone Dan kamaka."cewar amdaz gami da sake cewa "kar ka motsa"
Ayko ɗaya acikin yaran na haruna ne ya zaro bindiga ya fara harbi ayko jin Harbin da jami'an waje sukayi ne yasa suka buɗewa gidan wuta dan basu ma san gidan da iyayensa ba .
Abeeha da baffa da inna da sauran ƙannan haruna su biyu indo da zainabu,sun cika da mamakin kasancewar amdaz jamiin tsaro
Nanfa aka shiga bata kashi,baffa haɗe sauran yayan yayi guri guda da matarsa ya kulle sannan yayo kan su amdaz dake bata kashi da haruna da nufin ya ruƙo harunan ta baya ya damƙawa amdaz ɗin,
Inspector sadeeq ɗanlasan ne ya hangi tahowar baffa a zatonshi temakawa su harunan zeyi beyi ƙasa aguiwa ba ya ɗaukeshi da bindiga inda yasameshi aka,
.faɗuwar baffa akan idoñ su Abeeha Wanda shi kanshi harunan ya girgiza da mutuwar mahaifin nasa
Shima buɗe wutar yayi sede amdaz ankare yake dashi be bashi damar hakan ba ya daukeshi da bindiga.
Ba karamin musayar wuta akayiba acikin gidan kasancewar basu da makwabta abin yazo da sauƙi duka seda aka kashesu kan asamu tsayawar wutar.
Muje zuwa
Surbajo for life
[5/14, 11:30 AM] Ummu Fadila v: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*ƊAN ƘARAMIN SAURO*
*KADA UWAR GIWA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
.*Zahra Surbajo*
*Da sunan Allah me rahama me jin ƙai*
*wannan littafi me suna asama labarine da yake ƙirƙirarre,ban yi shi dan cin zarafin kowa ba,seda nishaɗantarwa da faɗakarwa gamida ilimantarwa,abinda zanyi daidai Allah yabani lada wanda nayi kuskure Allah ya yafemin*
*shine ze maye gurbin littafin gimbiya sabrina,maana na sauya masa suna,kuma ba free bane, meso seya biya kan ya karanta,dan gujewa ɗaukar hakkin da ba nasa ba*
*07044600044 domin biya afara tuntuɓar wannan number ta whatsapp ngd*
*4*
A gigice suka Ɗagoshi ganin kumfa na futa abakinshi,haruna ya sureshi zuwa cikin gidan da sauri Dan