Author : Zahra Surbajo Category : Romantic Hausa Novels
ya lura gab yake da mutuwa,
Magunguna suka shiga Ɗirka masa na gargajiya,yana ji yana gani be hanasu ba haka yasha,zuwa can de ya sauke ajiyar zuciya ya buɗe idanunsa yana faɗin "yunwa abinci a taimakeni"ayko haruna jikinshi har ɓari yake yaje ya kawo masa abincin ya dinga bashi a baki har ya ƙoshi abinda shi kanshi harunan mamaki yake yadda yake jin baƙon nasu aransa.
Cikin saukƙi amdaz ya samu karɓuwa agurin ƴan gidan gaba ɗaya har dashi kanshi harunan sede banda ƙanwar harunan Abeeha wacce itace ta taimakeshi amma ko kaɗan bata son zamanshi agidan.
Sosai suke bashi kulawa,koda suka tambayeshi labarinshi,amdaz gyara zama yayi yace cikin acent ɗin zamfarawa "acan zamfara nake, to gwamnati ta hanamu sukunin gudanar da kasuwancinmu wallahi baffa kwanana goma kenan ina gudunma jami'an tsaro,da ba ƙaramar ƙiba Ce dani ba amma dubi yadda na koma"yafaɗi cikin ɗacin rai
Cikin zaƙuwa haruna yace" wacce irin Sana'a kakeyi acan garin naku.?"
ɗan Sosa kai yayi sannan yace "don Allah Ku rufamin asiri,wallahi sana'ar ma ba iyawa nayi ba sani akayi muke yi nida abokaina, shine su aka kamasu aka kashe ni kuma na gudo"
A tsorace baffa bakinsa na rawa yace"kaima kidmashin ɗin kake yi?"
Cikin yanayin danasani amdaz yace"eh baffa amma wallahi so uku kawai nayi Dan Allah ka rufamin asiri karka haɗani da hukuma"
Wata dariya haruna gyauto yayi gamida fito yace"Aradu ka kai namiji,ay kawai kadena faɗawa baffa Dan baze ganeba,kullum rigimar da muke kenan dashi,be san arziƙi be samuwa da sauƙi ba."
Cikin yanayin rashin fahimta amdaz ya dubesa yace"Ban fahimceka ba kaimin Ƙarin bayani"
Baffa ne ya amshe zancan da cewa"kude ji tsoron Allah Dan hakkin jama'ar dake kanku baze barku kuji daɗin rayuwarku ba Dan haka kuji tsoron Allah wallahi akwai ranar ƙin dillaci"daga haka bece komai ba ya miƙe yabar gurin.
Haruna kamo hannun amdaz yayi yace"man she dashi do Allah taso muje zama guri ɗaya da baffa matsalane"
Muje zuwa
.Surbajo for life.
[5/14, 11:30 AM] Ummu Fadila v: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*DAN KARAMIN SAURO*
*KADA UWAR GIWA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*zahra surbajo*
*6*
Da gudu amdaz yayi kan mahaifin nasu haruna ya d'agoshi,sede ko kusa ba rai tare dashi wasu hawayene masu zafi suka biyo idanunshi.
Ihun su Abeeha dake kulle ad'akine ya ankarar dashi yaje ya bud'esu,da gudu sukayi kan mahaifinsu suna kuka suna kiran shi abun gwanin tausayi.
Y'an jarida tuni sun fara turo kai cikin gidan,da sauri amdaz ya dakatar dasu yace su jira tukuna.
Abeeha cikin tsananin bak'in ciki ta d'ago idanunta ta dubeshi tace afusace "me yayi saura mayaudari kasa bindigar muma ka harbemu mu huta,kazo jikinmu ne Ashe Dan ka kashe mana uba da D'an uwa Allah ya isa bamu yafe maka ba"ta k'arasa maganar tana kuka.
Amdaz kasa cewa komai yayi se hawayen tausayinsu dake biyo idanunsa,
Umarni shugabansu ya bada na su wuce mafakar tasu haruna amdaz ya nuna hanya zuwa cikin jejin.
Gawarwakin su haruna aka kwashe aka bar ta baffa yashe ak'asa,inda amdaz yazo gunsu Abeeha yace a raunace"baffa kwanansa ne ya k'are Abeeha,ko ba'a kuskure harbinshi ba yau Allah ya zab'i kiranshi,bari muje mu dawo ay masa sutura kuyi hak'uri"
Ko kallo be isheta ba bare yasa ran zata kulashi.innarsu ce ta d'ago ta dubeshi tana kuka tace"yaro baka mana laifin komai ba k'addarar muce tazo ahaka,kai aykinka ka gudanar bada zummar cutar damu ba kaje kawai mun yafe maka"ta karasa maganar tana kuka.
Dak'yar yake daga k'afarshi suka fice zuwa cikin jejin.
Bayan fitarsu jama'ar gari suka shigo suka taimaka musu aka yiwa baffa sutura,sede ana dawowa daga mak'abarta matasan gari suka cinnawa gidan wuta kan bazasu zauna musu agariba,su cucesu kuka da magiya ba wacce basuyiba haka suka fito dak'yar ko kayansu nasawa basu d'auka ba.
Haka sukai ta jifansu har suka fito dasu daga garin sannan suka koma,innarsu ce ma me dauriya aciki,ta kamasu ta rungume suna kuka duk anji musu ciwo Abeeha tace"ya cucemu inna ki duba kiga sanadinshi yadda rayuwa ta koma mana"ta sake rushewa da kuka.
Hannunsu inna taja suka nausa cikin jejin suka fara tafiya Dan aganinta in suka bi cikin gari komai ze iya faruwa dasu.
Amdaz sun jima suna bata kashi da sauran yaran haruna kamin suyi nasara akansu,suka kub'utar da wa'inda ke tsare a hannunsu.
Basu de kammala komai ba se gefin magriba,sannan suka baro gurin,koda suka zo gidan nasu haruna amdaz ya kad'u dajin abinda ya faru,sosai yake tausayinsu.
Haka suka bi hanya shida sadeeq d'anlasan suna nemansu sede ko kusa basu gansu ba,haka ya hak'ura suka wuce headquarter.
Muje zuwa
Surbajo for life.
[5/14, 11:30 AM] Ummu Fadila v: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*DAN KARAMIN SAURO*
*KADA UWAR GIWA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*zahra surbajo*
*7*
*Bayan shekara d'aya*
Amdaz yayi wannan shekarar ne cikin tsananin bakinciki duk sati seyaje garin nasu yaga ko ze gansu ko ya samu labarinsu,amma shuru,gidan ma an rusheshi se fili.
Ya rasa abinda ke damunsa,Wanda sakeena tayi rarrashin duniya amma yaki sanar da ita,,abun cinshi yake arai yarasa ya zeyi kullum cikin tunàni.
Zaune yake a falonshi yayi nisa cikin tunani,sakeena ta turo kofar ta shigo,ido kawai yasa yana kallonta ba tare daya ce komai ba.
Kusa dashi taje ta zauna asanyaye,ta kamo hannunshi tace hawaye. Na biyo idonta tace"wallahi in baka fadamin damuwarka ba kashe kaina zanyi"
A gigice ya rungumeta ajikinshi da karfi kamar wani ze kwace masa ita..
"No baby karki kuma cewa haka nima mutuwar zanyi rayuwa babu ke ina amfaninta kiyi shuru zan fadamiki".
Daga haka ya kwashe komai daya faru ya sanar da ita.
Sauke ajiyar zuciya yayi yace"hakkin su nakeso in biyasu,wato diyyar ran mahaifinsu,gashi ban gansuba bansan a ina zan gansu ba,ina gudun hakkinsu ya tambayeni baby"
Shigewa jikinshi tayi tana shafa kirjinshi tace"wannan ba abin tada hankali bane my d,tunda Allah yasani bada niyya hakan ta faru ba, Dan haka wannan kudi ka bude musu hannun jari dasu,a kamfanin dad dinku, kaga riba zasu dinga samu,kai kuma ka tsananta bincike,lungu da sako na Nigeria har Allah yasa adace agansu ka basu Dan Allah kadena daga hankalinka"ta fadi tana kwantar da kanta a kurjinshi..
Rungumeta yayi ajikinshi yana jin sonta da kaunarta na sake ratsa zuciyarshi,Dan se yanzu ya samu mafita.
"Shiyasa nake sonki babyna kanki naja koda yaushe kina bani mafita,in hanya ta rifemin"ya fadi yana sunbatarta.
Yinin ranar cikin farinciki sukayita amdaz ya cire komai aransa,se wani Abu dake can kasan zuciyarshi Wanda yaki barinsa yayi tasiri....
********
*Gidan jaleela da Bilal*
"Ba jimawa zanyi ba na fada miki, jibi zan dawo"cewar bilal yana daura agogon hannunsa.
Jaleela dake biye dashi rai a bace tace"amma ay yakamata kafadamin batun tafiyar tun Daren jiya base yanzu kawai kacemin zaka Adamawa ba" ta fadi tana kumburo bakin gaba.
Gyara tsayuwar hular kansa yayi sannan ya kare mata kallo up to down sannan yace a wulakance"macen dake tattali da Adana miji ita ake fadawa zaayi tafiya kamin ranar tafiyar,Dan haka daurin aure dad dina yasani in wakilceshi kinga ko yazama dole inje"
"Wai bilal meyasa bakason mu zauna lafiya ne nida kai,narasa gane kan inda ka dosa kode kadena sonane?"cewar jalila kamar zatai kuka.
"Da ban sonki da tuni na sakeki, Nide zama da kazanta ne de bazan iyaba,Dan haka dole in kara aure kwana kusa wallahi"
"Kajima baka karo auranba,bilal ko Dan kaga ina raga maka, wallahi wallahi sena shayar dakai mamaki kaje kayi auran"tana kaiwa nan ta buga tsaki tabar gurin .
Inda sabo ya saba Dan haka kada kansa yayi yay tafiyarsa
Airport ya nufa yana zuwa yasayi ticket, yahau jirgin zuwa Adamawa.
Daurin auran a can wani kauyene,kamin ka isa mambila,Dan haka motocin da abokinsa Khalid ya danadar masa ne suka kaisu garin shida Khalid din cikin shiga ta alfarma.
Garin fulanin ne Dan haka ko ina yawanci bukkokine se tawagar yan daurin aure dasuka cika garin kasancewar auran na wani kusa ne agomnati.
An kammala daurin aure lafiya,inda dangin amarya suka shiga fito da abinci ga yan daurin aure,.
Bilal da Khalid mota suka koma,inda wata kyakkyawar bafulatana ta kawo musu nasu abincin motar,tun tahowarta bilal ya kasa sarrafa kansa gaba daya ta gama rikita kwakwalwarsa kyanta yakai kyau,duk inda akeso mace takai yarinyar takai.
Sallamarta ce ta sake jefashi cikin yanayi sabida zakin muryarta.
Khalid ne ya amsa sallamar sannan ta ajiye musu furar ta juya zata bar gurin bilal yace"mungode kanwata,ko zan iya sanin sunanki"yayi maganar kamar Wanda aka tsikaro.
Murmushi tayi ta sadda kanta kasa tace"sunana Ummu Abeeha"
Murmushi yayi shima yaji ya kara mutuwa akanta,yace"sunana bilal,nayi murna da ganinki,gaki da suna me dadi"be gama fadin abinda yakeso fadi ba kunya ta Fulani tasa ta bar gurin tana murmushi ta shige gidansu.
.muje zuwa
Surbajo for life.
[5/14, 11:30 AM] Ummu Fadila v: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*ƊAN ƘARAMIN SAURO*
*KADA UWAR GIWA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
.*Zahra Surbajo*
*Da sunan Allah me rahama me jin ƙai*
*wannan littafi me suna asama labarine da yake ƙirƙirarre,ban yi shi dan cin zarafin kowa ba,seda nishaɗantarwa da faɗakarwa gamida ilimantarwa,abinda zanyi daidai Allah yabani lada wanda nayi kuskure Allah ya yafemin*
*shine ze maye gurbin littafin gimbiya sabrina,maana na sauya masa suna,kuma ba free bane, meso seya biya kan ya karanta,dan gujewa ɗaukar hakkin da ba nasa ba*
*07044600044 domin biya afara tuntuɓar wannan number ta whatsapp ngd*
*9*
Misalin ƙarfe takwas na dare bilal yadawo gida ransa fess dan tabbas mafarkinshi na gab da cika na samun irin macen da yakeso,
Yana jin son Abeeha akowanne sashi na jikinsa dan haka baze yarda yayi sanya akanta ba.
Jalila ko ta kanshi bata bi ba,dan aunty sakeena ta shaida mata taba banza ajiyarsa ta haka zasu zauna lafiya.
Shima bata ko isheshi kallo ba,yayi wucewarshi ɗakinshi,yashiga wanka ya fito,yayi kwanciyarsa agado bayan ya ɗauko hollandia milk yasha, dan ko abinci baze nema ba.
Wayarshi ya zaro ya kira number Abeeha daya bata ɗazu A Yola.
Ta jima tana ringing kamin ta ɗaga,sallama tayi cikin siririyar muryarta,wani abu yaji ya taso masa tun daga tafin ƙafa,zuwa kansa,daƙyar ya amsa sallamar tata sabida shauƙin daya shiga.
"Abeeha ya kike"yafaɗi murya can ƙasa.
Itama akunyace tace"Hamma ina lafiya,ya kukaje gida?"
Sosai bilal yaji daɗin sabon sunan data raɗa masa cikin zaƙuwa yace"lafiya lau adda abeeha,ya kewata ko bakiyi ba?"
Ɓoye fuskarta tayi kamar yana gurin tace akunyace"nayi mana hamma"
"yess,"ya faɗi gamida ɗaga hannu sama,sannan ya ƙara da cewa"Kin hanani sukuni abeeha da tunaninki na iso gida,zuciyata cike da fargabar karkice bakya sona"
Batace komai ba se murmushi da tayi me ƙayatarwa
"kibani amsa don Allah abeeha shin na chanchanta da in zama abokin rayuwarki koko ban kai ba?"ya jefa mata tambayar a marairaice.
.
A hankali tace"ka cancanta hamma harma kayi yawa"
"kina nufin kin amince da soyayyata?"yasake jefo tambayar a ƙagauce
"hakane hamma"ta faɗi akunyace.
Irin daɗin da bilal yaji baze misaltuba,rasa inda zesa kansa yayi dan farin ciki,lalle rayiwarsa na gab da sauyawa shigowar abeeha cikinta.
Sun jima awaya yana jaddada mata soyayyarsa gareta,wani ta biye mishi wani kuma sede tayi shuru kode murmushi.a ƙarshe ne yace mata.
"Abeeha ina da mata fa,zaki iya zama da me mata?"
.
Ko ɗar bata jiba dan zuciyarta ɗaya take sonshi dan haka amsa ta bashi tana murmushi"ay kai nakeso,dan haka ko da wata lalurace ba mat ba zanci gaba da sonka da ita"
Daɗi kan daɗi bilal wata ƴar dariya ya saki tajin daɗi yace"duniya de ni bilal na dace ta,Allah ka bani ƙiyama"
"Ameen hamma"ta faɗi tana murmushi.
"faɗa mini so nawa kika faɗawa wani kalmomin nan kafin ni"
Murmushi tayi me sauti tace
"ban taɓa ba hamma sabida bana yarda da kowa"
"meyasa bakya yarda da kowa ni kuma kika yarda dani"
"zuciyata ce tace in aminta dakai kai alherine agareni shine kawai"
Ji yayi kamar ƙafafunshi bazasu iya ɗaukarshi ba sabida sanyin da jikinshi yayi,jin girman yardar da Abeeha tai masa.
A hankali yace"Allah ya bani ikon sauke hakkin ki ummu Abeeha,kina da matsayi me girma araina"
..Sun jima a waya kamin suyi sallama ya kashe
..Yana kashewa,ya lumshe idonsa yana ƙara jin sonta aransa.
Buɗesu yayi ahankali karaf ya saukesu akan jalila dake tsaye tun ɗazu acikin ɗakin tana jin duk abinda yake wakana,kallonshi take da rinannun idanunta,wadda tsabar masifar daya hango acikinsu seda cikinsa yayi ƙugi.
Muje zuwa
Surbajo for life.
[5/14, 11:30 AM] Ummu Fadila v: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*ƊAN ƘARAMIN SAURO*
*KADA UWAR GIWA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
.*Zahra Surbajo*
*Da sunan Allah me rahama me jin ƙai*
*wannan littafi me suna asama labarine da yake ƙirƙirarre,ban yi shi dan cin zarafin kowa ba,seda nishaɗantarwa da faɗakarwa gamida ilimantarwa,abinda zanyi daidai Allah yabani lada wanda nayi kuskure Allah ya yafemin*
*shine ze maye gurbin littafin gimbiya sabrina,maana na sauya masa suna,kuma ba free bane, meso seya biya kan ya karanta,dan gujewa ɗaukar hakkin da ba nasa ba*
*07044600044 domin biya afara tuntuɓar wannan number ta whatsapp ngd*
*8*
"Bilal ban ganeba fa anyi yamma da kare"cewar khalid yana murmushi.
Dariya bilal yayi yace"naga iri khalid wallahi sone daga kallon farko,ina son yarinyar can"
Ajiyar zuciya khalid ya sauke sannan yace"amma kasan da matsala ko?"
"Wacce iri kenanfa?"bilal ya buƙata
"matarka da danginta bazasu taɓa barin faruwar haka ba,musamman sakinar nan,so inaga kawai ka mance"
"lalle khalid kana da abin mamaki,wallahi yarinyar nan in kaga ban aureta ba kawai va rabona bace,amma wlh dangin matata basu isa su hanani ba"ya fadi cikin nuna tabbacin abinda yake faɗi.
Dariya khalid yayi yace"Allah ya shiga lamarin ya yafa masa ruwan sanyi,amma ka ɗebota da zafi mutumina"
Bilal be kulashi ba sema ficewa da yayi daga motar ya taka zuwa ƙofar gidan nasu ummu abeeha.
Yana zuwa ko yayi saa wata matashiyar na shirin fitowa daga gidan suna kama da ummu abeehar sede wannan bata kai girman wancan ba.
Rusunawa tayi ta gaisheshi,sosai abin yayiwa bilal daɗi dan ya fahimci gidane na tarbiyya.
"yayarki fa?"cewar bilal yana murmushi.
"Adda Abeeha na cikin gida,yanzu ta shiga"cewar yarinyar.
"ke ya sunanki ?"
"Zainabu"ta faɗi tana murmushi.
"suna me daɗi,"cewar bilal yana murmushi.
Murmushi tayi ta sunkuyar da kai ƙasa
"kimin sallama da baffanku mana in ba damuwa"cewar bilal.
Batace komai ba ta juya cikin gidan,bata jima ba ta fito tace"gashi nan zuwa"tana idawa tayi gaba abinta.
Dattijo ne fari me yawan faraa ya fito daga gidan hannunsa riƙe da tabarma.
Hannu ya miƙawa bilal sede bilal ɗin be riƙe ba ya durƙusa suka gaisa.
Tabarma ya shimfiɗa musu sannan yayiwa bilal iso zuwa kan tabarmar.
Bayan sun zaunane,bilal yasake rusunawa yace akunyace"baffa mu baƙine daga abuja ɗaurin aure mukazo nan"
"masha Allah auren Arera ba,nagane sannunku da zuwa"cewar baffan cikin sakin fuska.
"baffa lokaci na ƙurewa zamu tafi shiyasa na zaɓi inyi magana dakai kai tsaye,acikin ƙawayen amarya akwai wata mesuna ummu abeeha,kuma naga nan gidan ta shiga,inde ƴarkace baffa kuma baay mata mijiba ni ina nemawa kaina auranta inka amince zan turo iyayena wani satin"cewar bilal batare da tsoron komai ba.
Murmushi baffa yayi me ƙayatarwa yace"Abeeha ɗiyar ƙanina ce kuma Allah yay masa rasuwa,amma inada cikakken iko akanta,na baka damar zuwa ka nemi soyayyarta,tunda zamani muke da yara yanzu sukeso abasu damar zaɓan mijin aure,inhar ta gamsu tana sonka mu muna murna"
Sosai bilal yaji daɗin dattakon baffan,dan haka sake rusunawa yayi yace"nagode baffa Allah ya ƙara girma nagode sosai"
Daga haka baffa ya miƙe ya shiga gida,baa jimaba Ta fito tana ɓoye fuska acikin mayafi ta rakuɓe can gefe tana wasa da hannunta.
Kusa da ita bilal ya matsa yana murmushi,yace"ran gimbiyata ya daɗe cikin aminci"
Sake cukuikuye fuskar tayi cikin mayafi tana murmushi,sosai kunyarta tai masa kuma tana ƙara masa sonta.
"Adda Abeeha,ga bilal agabanki da ƙoƙon bara,tun ganin farko zuciyata ta aminta dake,gashi ni baƙone,banida isasshen lokaci,sede ina roƙonki da kema kimin hukunci kamar yadda nima nayi,ki sanar dani ko kema kina sona"
Durƙushewa tayi ta ɓoye fuskarta a tsakanin ƙafafunta sabida girman zancan agurinta.
Duk yadda bilal yaso tai masa magana taƙi sede murmushi,ganin taki ne yasa ya ciro waya a aljihunsa yaɗanyi danne danns aciki ya miƙa mata yace"ki riƙe wannan zamuyi magana in na koma abuja anjima da dare kinji ko"
Yasha magiya da roƙo kan ta amince ta amshi wayar.
Hannu tasa ta karɓa,tana murmushi,sannan tace akunyace"Allah ya kiyaye hanya"bata jira me zece ba ta shige gida abinta.
shima haka ya baro gurin cike da kewa yazo ya faɗa mota khalid yaja suka bar gurin yana ta masa dariya,danshi kunya ma bilal ɗin yabasa daya tsaya da ƙaramar yarinya kamar Abeehan.
Muje zuwa
Surbajo for life.
[5/14, 11:30 AM] Ummu Fadila v: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*ƊAN ƘARAMIN SAURO*
*KADA UWAR GIWA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
.*Zahra Surbajo*
*Da sunan Allah me rahama me jin ƙai*
*wannan littafi me suna asama labarine da yake ƙirƙirarre,ban yi shi dan cin zarafin kowa ba,seda nishaɗantarwa da faɗakarwa gamida ilimantarwa,abinda zanyi daidai Allah yabani lada wanda nayi kuskure Allah ya yafemin*
*shine ze maye gurbin littafin gimbiya sabrina,maana na sauya masa suna,kuma ba free bane, meso seya biya kan ya karanta,dan gujewa ɗaukar hakkin da ba nasa ba*
*07044600044 domin biya afara tuntuɓar wannan number ta whatsapp ngd*
*10*
............Ta maza iyi ya tattaro dukkanin ƙarfin halinsa ya miƙe yayi kamar be ganta ba ze fice daga ɗakin.
Ay kamar jira take tako sha gabanshi tace tana nunashi da yatsa"waye kai bilal?,to wallahi in barci kake ka farka, kai har ka isa kaimin wannan wulaƙanci,to wallahi tun wuri kanemo hankalinka inda ka direshi,ni jalila na girmi ka rainamin wayau"
A fusace ya dubeta yace cikin fushi"ki iya bakinki dan wallahi in sakeki ni ba komai bane,in kika nemi ɗaga min hankali aure ne nace se nayi ba wanda ya isa ya hanani dan kiji dakyau"ya faɗi yana nunata da yatsa.
"wallahi baka isa kaimun kishiya a gidan nan ba koda kuwa mutuwa zamuyi duka,wlh kasha ƙarya,kuma duk ranar dana kuma kamaka kana min waya agida wallahi sena wulaƙanta ka"
"tunda gidan a kayan gara aka haɗoki dashi ay dole kice haka,"
"ba'a haɗoni dashi ba amma ay kasan na girmewa arziƙin wannan gidan tun tuni,amma in kana shakka ka kuma zuwa cikin gidan kayi wayar wallahi sekasha mamaki"tana kaiwa nan ta fice daga ɗakin ranta na mata zafi.
Ajiyar zuciya ya sauke,ganin ta tafi,dan har ga Allah yaji tsoron ganinta,kawai de mazewace yayi ya fuske....
Itako jalila tana ficewa ɗakinta ta nufa ranta na suya taja waya ta kira sakeena,waccs ke can kwance aƙirjin mijinta suna soyewa ko ringing ɗin bata jiba har ta gaji ta dena kiran ta kife akan gado tasa kuka na baƙin ciki
Abeeha ranar kasa bacci tayi sabida ita sabon shigacs a soyayyar ji take kamar karsu rabu a wayar.
muje zuwa
Surbajo for life.
[5/14, 11:30 AM] Ummu Fadila v: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*DAN KARAMIN SAURO*
*KADA UWAR GIWA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*zahra surbajo*
*12*
"Bilal Kaine tafe kenan?"cewar dady lokacin da yake kokarin zama kusa dashi.
Murmushi bilal yayi sannan ya durkusa gaban daddy yace"nine dad ay na shigo nauwara tace kuna ciki shine yasa nazauna ka fito"
"Good, to ya iyalin naka take?"daddy yayi tambayar cike da kulawa irin ta da da mahaifi.
Dan bata rai bilal yayi sannan yace"daddy