MUGUWAR MACE COMPELET HAUSA NOVELS.txt

Author :  HAMIDA SANUSI AHMAD Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   1 / 17

1 to 3K   out of 48.3K words

MUGUWAR MACE.





NA : HAMIDAH SUNUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✨✍️



*Ƴar'uwa kema kin yi ta shan maganin slimming amma har yau ya ƙi karɓar ki? Matso na zo maki da haɗin da zaki sha ki sauke ƙiba da nauyin jiki cikin sauƙi,Shayi ne mai daɗi da ƙamshin da ba zai baki damar yin ƙiwa ba wajen amfani da shi. Bayan haka akwai slimming oil da zai rage maki kitse a duk gaɓar da kike da buƙata a jikinki;kamar tumbi,damtse,kitsen baya,da cinya.*

*Slimming Tea 6k.*
*Slimming oil 3500.*
*Body scrub 3500*
*Skin oil 2500*
*Location Kano.*
*Phone No 09031416423.*

03/21/2026.



PAGE 1.




Tsafi gaskiyar me shi in ji Malam Bahaushe. Mata da dama sun kauce hanya domin cikar burinsu,su na iya yin komai dan ganin sun mallaki abinda suke so;ta kowacce hanya. Kowacce mace na son a san da zamanta a waje,ta zamo mai muƙami da mulkin gidanta. Wannan dalilin ne ya sa matan ke bin hanyoyi mabanbanta wajen ganin burinsu ya cika;wato hanyar halal da haram. Labarin Aabidah da Aabid ya zo mana da sabon salon mulkin gidan aure wanda yake da tsananin ban al'ajabi,mamaki,burgewa kai har ma da takaici. Ku biyo ni dan jin yanda waɗannan ma'aurata suke gudanar da tasu rayuwar...

***************

Wani irin zafi ake yi a gari wanda mutane ke jin kamar su kama da wuta saboda yanda ya tsananta,gashi ruwan sama bai sauka da wuri ba ballantana a samu sassauci. A daidai wannan lokacin Mahreen ce kwance a madaidaicin gadonta tana tsiyayar da zufa sai kukan shagwaɓa take yi wa Yah Maheer ta rasa inda za ta saka ranta ta ji daɗi. A ɓangaren Yah Maheer kuwa ya dage sai firfita yake yi mata cike da kulawa tare da lallashinta kamar wata ƙaramar yarinya har yana jin hannuwansa na yi masa zogin azaba tsabar gajiyar da ya yi. Kallon Mahreen ya yi wadda bacci ya fara ɗaukanta ya shafi kuncinta ya na murmushi ya ce.

"Sarkin rikici kenan."

A hankali ya ajiye abun firfitar zai kwanta ta motsa tana ƙunƙuni kamar ba bacci take yi ba. Yah Maheer bai bi ta kanta ba ya yi kwanciyarsa domin ya huta,dan ba zai iya da rikicin Mahreen da baya ƙarewa ba. Kwanciyarsa ke da wuya aka fara buga gidan nasu da wani irin ƙarfin da ya yi sanadiyyar farkawar Mahreen daga baccin da ta fara yi wanda bai wani yi nisa ba. A firgice ta tashi ta zauna tana rarraba ido tsakanin bakin ƙofar ɗakinsu zuwa fuskar Yah Maheer dake ɗauke da tsananin mamaki. Ƙara buga gidan aka yi kamar za a ɓalle ƙofar,cikin sauri Mahreen ta matsa kusa da Yah Maheer jiki na rawa ta lalubo wayarta da ke gefensa ta kunna hasken fitilar domin samun ƙarin haske akan na ƴar ƙaramar rechargeble lamp ɗin dake kunne a ɗakin. Sauka Yah Maheer ya yi daga gadon nasu ya ɗauki rigarsa da dogon wando ya saka,sannan ya miƙa wa Mahreen babban hijabinta da zani domin ta saka a kan ƙananan kayan baccin dake jikinta. Da hannu ya yi mata alamar kada ta damu bari ya leƙa ya ga waye,tinda ba yau aka fara yi musu irin wannan zuwan ba zatan ba. Kai ta hau girgiza masa tana son ta yi kuka. Sauyawar zamani da rashin tsaron da ake fama da shi ne ya sake jefa ta a cikin tsoro da tunanin wanda yake buga musu gida a wannan tsohon daren. Ba tare da Yah Maheer ya biye mata ba ya buɗe ƙofar ɗakin ya fita zuwa madaidaicin Parlourn su mai ɗauke da abubuwan more rayuwa. Ya na shiga parlourn ana sake buga ƙofar gidan nasu cike da zaƙuwa,da sauri ya ƙarasa buɗe ƙofar parlourn ya fita farfajiyar gidan yana faɗin.

"Waye?"

"Malam Maheer buɗe ni ne Aabid."

Cikin sauri Yah Maheer ya isa bakin gate ɗin gidan ya hau kiciniyar buɗewa ya na faɗin.

"Aabid you again,me ya faru this time?"

Wani irin gurnani ya ji Aabid na yi irin na marasa lafiya,cikin sauri ya ƙarasa buɗe ƙofar ya tari Aabid dake ta rawar jiki saboda tsananin sanyin da yake ji,ƙafarsa ya kalla ya ga yanda ta yi fururu da ita bata samu arziƙin a tsaya saka mata takalmi ba, hakan ya tabbatar masa da cewa da ƙafa ya tako tin daga gidansa. Yah Maheer na kai hannu jikin Aabid ya ji shi ya ɗauki zafi zauu kamar wuta. Cikin sauri ya kama shi suka shiga gidansa ya kulle sannan suka ƙarasa ciki. A parlour ya zaunar da Aabid sannan ya shiga ya sanar da Maheer abinda ke faruwa. Nan take tsoron da ya cika mata zuciya ya yi ƙaura,tausayi da jimami suka maye gurbinsu,kewa da shauƙi tare da ƙawa zuci suka mamaye zuciyarta. Sauka ta yi daga gadon da sauri ta bi bayan Maheer da ya koma parlour riƙe da abun rufa da matashin kai,dan ya san halin Aabid ba yarda zai yi ya kwanta a ɗaki ba. Yana zuwa ya miƙawa Aabid pillow dan ya saka a kansa,sannan ya yi amfani da abun rufa ya lulluɓe shi. Aabid kuwa jinsa yake yi kamar zai kama da wuta saboda damuwa,ga wani irin zazzaɓi da ya kama shi mai tsananin azaba. Cikin mayen ciwo yake faɗin.

"Kin yi min alƙawari kin kasa cikawa Baby, alƙawarin har abada kika yi min ba na shekaru ba. You promised me forever my love please don't leave me."

Tagumi Mahreen ta zabga ta na kallon Aabid hawaye na zubo mata daga idanuwanta na tsantsar tausayinsa. Tashi ta yi ta nufi kitchen ɗinsu ta dama masa custard ta zuba madara da sugar ta watsa gyaɗa a ciki kamar yanda yake so,sannan ta ɗakko ruwan pure water ta ɗora a ƙaramin faranti da paracetamol. Parlour ta dawo ta kama hannun Aabid ta na faɗin.

"Yah Aabid tashi ka sha magani don Allah ko zazzaɓin zai sauka ka ji?"

Muryar Mahreen ce ta sanya Aabid rushewa da wani irin kuka ya ƙanƙame hannunta ya na wata iriyar jijjiga. Cikin hanzari Yah Maheer ya isa gabansa ya dafa shi yana faɗin.

"Hasbunallahu wa ni'imal wakil..Lahaula wala ƙuwwata illa billah."

Haka Yah Maheer yayi ta maimaita addu'o'in nan kafin daga baya Aabid ya kama yi shima. Da ƙyar ya samu zuciyarsa ta samu nutsuwa har ya karɓi custard ɗin ya sha kaɗan ya kora da paracetamol ya koma ya kwanta. Sun jima zaune jigum-jigum kafin su fara jin saukar numfashin Aabid a hankali,cikin baccinsa kuma yana furta kalmar.

"You promised me forever baby, please don't leave me."
(Alƙawarin ƙarshen rayuwa kika yi min baby don Allah kada ki barni.)

Ɗaki suka koma Mahreen na share hawayen tausayin babban Yayan nata da rayuwarsa ta koma abar tausayi. Shi ne majinginarsu daga ita har mahaifiyarsu,sai dai rashin sa'ar mace ta gari ya jawo wa rayuwarsa rushewa ta koma kamar ta ƙaramin yaron da a koda yaushe yake neman kulawar iyayensa saboda kada ya faɗa wani mummunan halin ko ma ya rasa rayuwarsa gaba ɗaya.
Cikin kuka Mahreen ta kalli Yah Maheer ɗinta ta ce.

"In Sha Allahu Aabida ba za ta samu damar tuba akan laifukan da ta aikata ba za ta koma ga mahaliccinta. Zan yi matuƙar baƙinciki ace masu halayya irin tata su samu Rahamar Allah ko da da ƙiftawar ido ce."

"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un! Haba Mahreen wannan wanne irin mugun fata kike yi wa ƴar'uwarki mace haka? Kada fa ki manta gaba ɗayan mu Rahamar Allah muke nema a duniya har zuwa ƙiyama,akan me ke za ki dinga yi mata fatan ta mutu da irin waɗannan manyan zunuban da ta kwasar wa akanta? Ban taɓa zaton haka daga gare ki ba,kin bani mamaki da kunya Mahreen."

Hawaye Mahreen ta share tana kallon mijin nata da take matuƙar so da ƙauna ta ce.

"Idan har addu'ar da na yi wa wannan MUGUWAR MACEn ne zai sa na baka kunya da mamaki,na amince ka yi ta jin kunya ta har ƙarshen rayuwarmu,ko ka manta wacece Aabida ne in tuna maka? Aabida ita ce sanadiyyar rushewar ahalinmu,Aabida ita ce sanadiyyar da mahaifiyarmu ke kwance tana jinya har yau,na kuma tabbata da wannan jinyar za ta koma ga mahaliccinta,Aabida ita ce silar raba ni da ɗan'uwana na tsawon shekaru masu yawa,Aabida ita ce ta...."

Da sauri Yah Maheer ya rungume Mahreen ya na bubbuga bayanta ya ce.

"Ya Isa haka,ki yi haƙuri idan maganata ta ɓata maki rai,mu je mu ma mu kwanta saboda mu samu sallar asuba akan lokaci."

Ba tare da ta ce masa komai ba ta bashi dama ya kamata suka nufi hanyar ɗakinsu, suna tafe tana waiwayen Yayan nata da ta ɗauki tsawon lokaci bata zauna da shi a waje ɗaya ba har ta dena hango shi. A saman gadonsu Yah Maheer ya kwantar da ita tare da kashe fitilar tasu dan su yi saving cajin da ya yi musu saura zuwa asuba. Tinda ba wuta suke samu ba sai da rana,gashi mai ya ƙare a gen ɗin su Yah Maheer bai sani ba sai da ya je tada wa sannan ya gani,shi kuma a gajiye yake ya na jin ƙiwar sake fita siyo fetur. Kwanciyarsu ke da wuya suka ji ƙarar buɗe ƙofar parlour tare da kullewa da ƙarfi,cikin sauri Maheer ya miƙe zai fita Mahreen ta riƙe shi tana zubar da hawaye ta ce.

"Rabu da shi,ka san idan bai koma ba haukace mana zai yi anan,mu bi shi da addu'a kawai Allah Ya mayar da shi gida lafiya."

"Na sani ni dama ba dakatar da shi zan yi ba,zuwa zan yi na kai shi gida da kai na,dan da gani da ƙafa ya zo nan ɗin duba da ƙurar da ƙafarsa ta yi, kuma ko arziƙin talkalmi ma bai tsaya saka mata ba."

Murmushi ta yi mai ciwo ta koma ta kwantar da kanta tana tsiyayar da hawayen tausayin ɗan'uwan nata. A gaggauce Yah Maheer ya ɗauki makullin motarsa ya bi bayan Aabid dake tafiya da ƙafa babu ko takalmi daga shi sai jakar hannunsa da ya je gidan da ita. Da ƙyar Yah Maheer ya samu damar lallaɓa Aabid ya shiga mota suka wuce Sallari inda gidansa yake. Suna zuwa Yah Maheer ya tsayar da mota Aabid ya buɗe ya fita riƙe da jakarsa a hammata ya buɗe babban gate ɗin gidan nasa da makulli ya shige,tsaye ya tarar da mai gadi yana zare ido da gorarsa a hannunsa,ganin Aabid ne da kansa sai ya sanya shi saurin mayar da sandar bayansa ya ɓoye ta ya hau yi masa sannu da dawowa,ko kula shi Aabid bai yi ba ya sa kai ya shige cikin gidan. Sai da Yah Maheer ya ji ƙarar kulle gidan sannan ya kalli agogon dake jikin motarsa ya ga ƙarfe uku da kwata na dare har ta gota. Tada motarsa ya yi ya wuce gidansa bakinsa na bin karatun ƙur'anin da ya kunna a cikin motarsa.

*Aabid.*

Ya na shiga cikin gidan ya tarar da ko ina cikin duhu kamar babu kowa a gidan,banda ƙarar AC da fridge babu abinda ke tashi,sai hasken ƙananan fitulun abubuwan wuta dake kunne,kai tsaye sama ya hau ya nufi ɗakinta riƙe da jakarsa da ya kasa ajiyewa har a wannan lokacin. Yana shiga ya ganta kwance a gado ta yi ruf da ciki tana latsa wayarta cike da nishaɗi tana chatting hankalinta kwance. Zubewa Aabid ya yi a saman guiwowinsa ya na tsiyayar da hawaye kamar wani ƙaramin yaro ya ce.

"Don Allah Baby ki yi haƙuri,na amince zan yi miki duk abinda kike so,amma kar ki rabu da ni,idan kika rabu da ni mutuwa zan yi."

Ya ƙarasa maganarsa tare da rushewa da matsanancin kuka. Ta jima sosai tana latsa wayarta cike da nishaɗi kafin ta kunna dim light sannan ta ajiye wayarta a kife. A hankali fara kuma kyakkyawar matar da ba za ta wuce shekaru talatin da ɗaya ba a duniya ta sauka daga saman gadonta ta na wani ɓaɓɓata rai. Kallon Aabid da ke gurfane a gabanta yana rusa kuka ta yi a wulaƙance sannan ta ce.

"Har ka shanye yajin da ka daka kenan Aabii. Ai na ɗauka za ka iya kwana a wani wajen saboda kawai na roƙi abinda bai taka kara ya karya ba a wajenka. Ashe dama alƙawarin da ka yi min duk ƙarya ne? Ashe ba za ka iya ba ka fara? To ina son a cikin daren nan ka rubuta min takardar sakina na koma gida na ci gaba da rayuwar da na saba da ita tun kafin na sanka. Hakan zai fiye min kwanciyar hankali sama da na rayu da mutumin da yake ƙaryar so na."

Da rarrafe Aabid ya ƙarasa wajen Aabida ya kama ƙafafuwanta yana goga fuskarsa a jiki yana kuka kamar zai shiɗe. Da ƙyar ya iya ɗaga kansa yana kallon cikin idonta ya ce.

"Na amince zan yi miki duk abinda kike so matsawar ba za ki rabu da ni ba har abada."

A sheƙe Aabida ta kalli Aabid kafin ta juya masa baya ta harɗe hannuwanta a ƙirji ta ce.

"Ban yarda da kai ba,dan na san halinka sarai da tausayi,ba lallai ka iya cika min burina ba,dan haka mu rabu kawai Aabid na je na auri wanda zai...."

Cikin sauri Aabid ya ja ta jikinsa ya rungume ta ya na kuka yana jaddada mata kalmar.

"Na sake yi miki alƙawari a karo na babu adadi Aabida,zan cika miki duk wani burinki a rayuwa ko da hakan zai yi sanadiyyar rasa rayuwata ne."

Wani irin ƙayataccen murmushi Aabida ta saki,domin ta tabbata a wannan karon za ta samu biyan buƙatar ranta da ta jima tana fata. Dan haka sai ta rungume Aabid tana yi masa wani irin salon da ya sanya shi sauke ajiyar zuciya da sauri da kuma ƙarfi. Cike da farinciki suka kwanta har aka kira sallar asuba aka shiga sallah a dikkan masallatan dake unguwar Aabid bai farka ba ballantana ya yi sallar akan lokaci. Ba su suka farka ba sai da gari ya waye tarwai sannan Aabid ya farka a gigice ya faɗa banɗakinsu ya yi wanka ya tsarkake jikinsa sannan ya fito ya shirya. Sallahr asubar da ta wuce shi ya rama sannan ya kalli saman gadon da Aabida ke kwance tana ta sauya wuri kamar a lokacin ta fara jin daɗin baccin da take yi,sake rufe ta ya yi da bargo yana jin soyayyarta na ratsa kowacce kafa da ɓargon jikinsa. Kitchen ya nufa ya haɗa mata abinci sannan ya jera a saman dinning table kamar yanda ya saba,sannan ya ɗebi nashi ya ci a gaggauce,zuciyarsa na bugawa cike da matsananciyar damuwa da tsoron yanda zai tunkari Hajiyansa a wannan ranar. Da ƙyar ya tura dankalin da ya soya ya kora ruwan shayi ya ɗauki makullin motarsa ya bar gidan cike da fargaba da tsantsar damuwa.................


MUGUWAR MACE.





NA:HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✨✍️.


*Ƴar'uwa kema kin yi ta shan maganin slimming amma har yau ya ƙi karɓar ki? Matso na zo maki da haɗin da zaki sha ki sauke ƙiba da nauyin jiki cikin sauƙi,Shayi ne mai daɗi da ƙamshin da ba zai baki damar yin ƙiwa ba wajen amfani da shi. Bayan haka akwai slimming oil da zai rage maki kitse a duk gaɓar da kike da buƙata a jikinki;kamar tumbi,damtse,kitsen baya,da cinya.*

*Slimming Tea 6k.*
*Slimming oil 3500.*
*Body scrub
3500.*
*Skin oil 2500.*
*Location Kano.*
*Phone No 09031416423.*



PAGE 2:



Karkata kan motarsa yayi ya ɗauki hanyar unguwar Ƴankaba. A daidai ƙofar wani gida na masu matsakaicin ƙarfi ya tsaya. Ya jima sosai a cikin motar kafin ya fito tare da zaro wayarsa da ke cikin aljihunsa ya hau latsawa. Jiki a mace ya kara wayar a kunnensa,ko sallama bai yi wa wanda ya kira ba ya ce.

"Ka same ni a ƙofar gidanka yanzu."

Kashewa yayi ya jingina da jikin motarsa yana jin ƙafafuwansa sun masa nauyi kamar ba zai iya ci gaba da tsayuwa ba. Cikin abinda bai fi minti biyu ba wani siririn dattijo ya fito daga gidansa ya na saɓa tsohuwar babbar rigarsa a kafaɗarsa,kaki yayi ya zubar sannan ya ƙarasa wajen Aabid dake tsaye. Sallama yayi wa Aabid tare da naɗe hannuwansa a cikin babbar rigarsa ya duƙar da kansa ya ce.

"Ranka ya daɗe lafiya dai ko na ga ka zo har gida ba ka kira ni can kamfani ba."

Ajiyar zuciya mai ƙarfi Aabid ya sauke kafin ya ce.

"Lafiya ƙalaou Malam Sallau. Na zo ne akan maganar nan da muka taɓa yi da kai da jimawa daga baya kuma na ce na fasa. To yanzu ina so ka sake tuntuɓar mutumin ka ji if he is still interested i am willing to...."

Cikin hanzari Malam Sallau ya katse Aabid ta hanyar washe baki ya ce.

"Ai Alhaji ko yanzu muka je na san zai amince. Wannan mutumin ai kusan sana'arsa kenan,dan haka duk lokacin da ka shirya kawai zuwa za mu yi mu same shi har gida a daddale magana."

"Ok idan dai haka ne kawai mu je yanzu."

Har Malam Sallau ya kama hannun motar Aabid ya buɗe zai shiga,sai kuma ya ja ya tsaya. Cike da sanyi tare da mutuwar jiki ya ce.

"Ranka ya daɗe ba zan ce maka ban ji daɗin wannan harƙalla da za a ƙulla ba,saboda ko babu komai ta nan nake samun nawa abincin da wasu buga-bugar. Amma kuma ina ganin kamar abinda za ka aikata bai dace ba,kada ka manta fa...."

Hannu Aabid ya ɗaga wa Malam Sallau rai a ɓace ya ce.

"Za ka kai ni ne ko na samo wani?"

Da sauri Malam Sallau ya saka hannunsa guda biyu ya zuge laɓɓansa sannan ya faɗa mota ya zauna. Cikin ƙiftawar Ido Aabid ya bar unguwar su Malam Sallau suka nufi unguwar Ɗanladi na Sidi. Da kwatance Aabid ya kai su gidan Alhaji Kabiru Mai Tumbin Nera. Gida ne kadaran kadahan domin kuwa gaba ɗaya unguwar shi ne gidan da bashi da gate da kyawun sifa kamar sauran manyan gidajen dake jere a unguwar reras gwanin ban sha'awa. Malam Sallau ne ya fita ya je ƙofar gidan ya dinga kwaɗa sallama. Babu jimawa wata yarinya ƙarama ta leƙa tana tambayar waye. Washe baki Sallau yayi ya ce mata.

"Ki ce wa gyatuminki yayi manyan baƙi ya hanzarta ya fito kada ya ɓata wa Alhaji lokaci."

Da gudu yarinyar ta koma cikin gidan ta sanar da zuwan su Malam Sallau ga mahaifinta wanda ke tsaye yana sanya takalmansa tare da tura uban tumbi gaba yana nishi tsabar ƙiba. Kai kawai ya gyaɗa mata ya nufi waje. A tsaye ya tarar da su Aabid ya miƙa musu hannu suka gaisa. Babu ɓata lokaci Sallau ya kora masa bayani akan dalilin zuwan

1 / 17