Author : HAMIDA SANUSI AHMAD Category : Romantic Hausa Novels
taimakon kujerar dinning table ta saka gogaggun labulayenta masu kyau da tsada wanda Hajiyanta ta siya mata a lokacin aurenta ba tare da sanin Yah Aabid ɗinta ba. Tana tuna wa da su ta ji jikinta yayi sanyi,waje ta samu ta zauna a ƙasa ta hau zuba addu'o'in samun daidaito a tsakanin zuri'ar tasu. Ta na nan zaune aka fara kiran sallar azahar. Da sauri ta hau bi itama,ana gamawa ta yi addu'ar bayan kiran sallah sannan ta yi wa Annabi salati, addu'a ta sake yi sannan ta kalli ko ina ta ga yayi fess. Rufe ɗakin ta yi ta koma sashenta ta shiga wanka. Tana gamawa ta yi alwala ta shiga ɗakinta ɗaure da towel ta hau gyara jikinta. Sallah ta yi kafin ta ɗora abinci wanda ta yi shi mai yawa saboda tana tunanin baƙi za su yi,Yah Maheer bai dai sanar da ita bane kawai.
Bata jima da gamawa ba kuwa ta ji ana buga gate ɗin gidan. Cikin sauri ta nemi Hijabinta ta ɗora a saman shigar atampa riga da skirt ta fita dan ganin wanda ke buga gidan nasu......
MUGUWAR MACE.
NA: HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✨✍️
*Ƴar'uwa kema kin yi ta shan maganin slimming amma har yau ya ƙi karɓar ki? Matso na zo maki da haɗin da zaki sha ki sauke ƙiba da nauyin jiki cikin sauƙi,Shayi ne mai daɗi da ƙamshin da ba zai baki damar yin ƙiwa ba wajen amfani da shi. Bayan haka akwai slimming oil da zai rage maki kitse a duk gaɓar da kike da buƙata a jikinki;kamar tumbi,damtse,kitsen baya,da cinya.*
*Slimming Tea 6k.*
*Slimming oil 3500.*
*Body scrub 3500.*
*Skin oil 2500.*
*Location Kano.*
*Phone No 09031416423.*
PAGE 4.
Motar kamfanin Aabid ta gani ta ɗiban hatsi tsaye a ƙofar gidan ɗauke da kaya,sai direba dake tsaye yana yi mata bayanin daga inda kayan suka fito tare da sanar da ita saƙon Alhaji Maheer. Gyaɗa kai kawai ta yi ta matsa ta basu waje. A gaban idanuwanta suka shigar da kayan ɗakin da ta gama gyarawa sannan suka yi mata sallama suka wuce. Kanta ya ɗaure sosai da wannan sabon lamarin da ta kasa yi wa suna. Shin me yake faruwa ne? Rashin samun amsar tambayarta ne ya sanya ta shige wa ɗakin ta duba kayan da yanda suka jera komai a inda ya dace. A hankali ta ja ƙofar ta rufe sannan ta koma sashenta ta zauna. Tagumi ta zabga tana hasaso abubuwa da dama da za su iya sanya Yah Maheer gyara ɗakin nan kamar wanda za a saka wata amaryar a ciki. Kasa cin abincin da ta dafa ta yi;duk kuwa da irin yunwar da take ji na kartar tumbinta. Kwanciya ta yi a saman doguwar kujera tana hawaye,a haka bacci mai cike da mafarkin Yah Maheer ɗinta ya ƙara sabon aure har ya tare da amaryarsa.
Kiran sallar magariba ne ya tada ita daga nannauyan baccin da ta sha,a gaggauce ta faɗa banɗaki ta yi brush ta ɗaura alwala sannan ta wuce ɗakinta ta tada sallah. Kaya ta sauya zuwa ƙanana masu kyau sannan ta ƙara feshe jikinta da turare,daga nan sai ta wuce parlour ta kunna turaren wutanta mai daɗin ƙamshi,nan da nan gidan ya kiɗime da ƙamshi kamar a Sudan. Sai da ta tabbatar ko ina ya ɗauki ƙamshin sannan ta wuce ɗakin tsakar gida ta kunna turaren wutan ta zauna tana jiran ya gama ta ɗauke.
Har Mahreen ta kammala duk wani abu da za ta yi ta zauna,shiru Yah Maheer bai dawo ba bai kuma kira ta a waya ba kamar yanda ya saba. Jin shirun yayi yawa ne ya sanya ta ɗaukan wayarta ta kira shi. Haka wayar ta karaci ringing bai ɗauka ba,jikinta ne yayi sanyi sosai ta sanya hannunta a baki tana cizon farcenta ta ce.
"Ni fa wannan sabon lamarin dake faruwa ya fara bani tsoro,ina mijina ya tafi tun safe har yanzu bai dawo ba;kuma bai kira ni a waya ba?"
Tsaye ta miƙe ta hau sintiri a parlourn tana jin yanda cikinta ke kukan yunwa amma ta bawa banza a jiyarsa. Duk yanda Mahreen ta so ta daure kasawa ta yi,cike da damuwa ta hau rubutawa Yah Maheer saƙo. Kafin ta tura ta ji horn ɗin motarsa,wurgi ta yi da wayar tata ta fita da gudu zuwa tsakar gidan sanye da hijabi a jikinta. Gate ta buɗe masa tana ta washe baki saboda farincikin dawowarsa. Sai da ya parker motar a inda yake ajiye wa sannan ta kula da Hajiyanta da Salimah a baya. Cikin sauri ta ƙarasa rufe gate ɗin ta nufe su,a daidai wannan lokacin Yah Maheer ya riƙo hannun Hajiya yana taimaka mata ta fito daga motar. Damuwa kwance a fuskar Mahreen ta hau jero musu tambayoyin da suka sanya Hajiya sakin murmushin baƙinciki. Yah Maheer ne ya kalli Mahreen dake a cikin ruɗani ya ce mata.
"Baby ki yi haƙuri mana mu shiga ciki sai na baki amsar tambayoyinki. Yanzu kafin nan maza ki je ki haɗa wa Hajiya ruwan wanka da abinci."
Da sauri ta wuce sashenta ta ɗora ruwan zafi a gas zuciyar ta cike fal da tarin tambayoyi. Ruwan na tafasa ta juye a bokiti ta sirka ta kai banɗakinta,ta na kai wa Hajiya ta tashi da ƙyar Salimah na riƙe da hannunta Mahreen ta isa wajensu ta kama Hajiyan suka kai ta banɗaki,cike da kulawa Mahreen ta ce.
"Ko na tsaya na taya ki wankan?"
Kai Hajiya ta gyaɗa alamar eh,dan haka Salimah sai ta fita ta basu waje. Wanka mai kyau Mahreen ta yi wa Hajiya wanda ya bata ƙarfin jiki suka fito. Kai tsaye saman dinning table ta zaunar da Hajiya ta hau zuba mata abinci ta fara bata a baki,ganin ƙwalla a idon Hajiya sai ya karya zuciyar Mahreen. Cike da kulawa ta sanya hannu ta share mata wadda ta gangaro saman kuncinta. A haka Yah Maheer ya tarar da su shima ya zauna ya zuba abincin ya fara ci. Salimah na fitowa daga wanka itama ta zauna ta ci nata. Kallon Mahreen Yah Maheer yayi ya haɗe fuska ya ce.
"Me yasa baki ci abinci ba yau?"
Tura baki ta yi ta ce.
"Ba kai bane ka ɗaga min hankali? Ka fita tun safe babu waya babu saƙo,sannan baka yi min bayanin abinda ke faruwa ba."
Murmushi yayi sannan ya ce.
"Wannan halin naki na yawan shiga damuwa akan abu ƙalilan shi yasa na ƙi sanar dake abinda yake faruwa. Yanzu dai ki tabbata kin zuba abinci kin ci kin ƙoshi. Idan kin gama sai mu raka Hajiya ɗakinta ta huta."
"Dama Hajiya ka gyarawa wancan ɗakin?"
Mahreen ta faɗa cike da farinciki maɗaukaki. Kai Yah Maheer ya gyaɗa mata yana murmushi,tsallen murna ta daka ta rungume Hajiya dake kusa da ita tana murmushi. Zama Mahreen ta yi ta hau cin abinci tana zuba musu surutu suna amsa mata. Tana gamawa suka raka Hajiya sabon ɗakinta sannan Yah Maheer ya tsaya a gaban idonsa aka bata magungunanta ta sha ta kwanta tana ta zuba masa godiya da sanya albarka. Sai da bacci ya fara ɗaukanta sannan suka yi wa Salimah sallama suka koma nasu sashen.
Duk yanda Mahreen ta so ta ji dalilin dawowar Hajiyanta gidan Yah Maheer ya ƙi sanar da ita gaskiyar lamarin. Kan dole ta haƙura ta kwanta ranta fal murnar dawowar Hajiyanta kusa da ita kamar yanda take fata a koda yaushe.
A ɓangaren Yah Maheer kuwa yanda ya ga rana haka ya ga dare,domin kuwa hankalinsa a matuƙar tashe yake,yana jiye wa Aabid tsoron yin mummunan ƙarshe sakamakon wulaƙanta mahaifiyarsa da yake yi a rayuwa. Babbar damuwarsa bai wuce a ce har a wannan lokacin Aabid bai kirasa ya sanar da shi abinda ya aikata ba,sannan bai nemi ya san ina Hajiyansa ta shiga ba. Me yake tunani da ya siyar da gidansu na gado ba tare da sanin kowa ba? Ko babu komai Mahreen na da haƙƙi akan dukiyar mahaifinta. Me zai yi da maƙudan kuɗaɗen da ya siyar da gidan? Shin ko dai Aabid yana cikin wata matsalar rashin kuɗi ne? Kansa ya shafa zuwa fuskarsa tare da furzar da wani irin zazzafan huci. Zama yayi a kujerar dake cikin ɗakin nasu ya furta.
"Kamfaninsa na samun riba mai tarin yawa,ban ga dalilin da zai sa ya aikata wannan mummunan abun ba ba tare da yayi shawara da ni ba."
Jingina yayi a kujerar yana ci gaba da jera wa ƙwaƙwalwarsa tambayoyin da ya tabbatar da babu mai amsa masa su face Aabid da kansa. Da wannan tunanin ya miƙe ya buɗe ƙofa ya leƙa su Hajiya,jin shiru babu motsin komai ya tabbatar da bacci suke yi,sai ya koma ɗakinsa yana tunanin sanya musu solar a gidan ko dan matsalar wuta da ake fama da ita,ga kuma tsananin zafi da ake zubawa,sannan Hajiya ta saba da solar saboda yanayin jikinta bata son zafi.
Ɗakinsu ya koma ya shiga banɗaki ya ɗaura alwala ya fito. Abun sallah ya shimfiɗa ya hau ya tada sallah,ya jima yana jera nafilfilu kafin ya zauna yayi addu'a. Yana idarwa ya hau gado ya rintse ido yana fatan ya samu bacci ya ɗauke shi ko babu yawa. A hankali ya furta.
"Ya Allah ka bani ikon samun sallar asuba akan lokaci kada na makara sakamakon jimawa da na yi ban rintsa ba."
Yana gama faɗin haka ya runtse idonsa,sai dai tunanin dake cikin kansa ya hana shi samun abinda yake so. A haka aka yi kiran farko yana ta tasbihi a cikin ransa.
Da misalin huɗu da arba'in Mahreen ta farka ta shiga banɗaki,brush ta yi ta ɗaura alwala ta fito ta tada nafila. Tana idarwa Yah Maheer yayi shirin masallaci ya tafi. Bayan ta yi sallar asuba ta shiga kitchen ta fara haɗa musu abun karyawa,tana tsaka da aiki Salimah ta shiga ta hau taya ta,nan da nan suka kammala soya doya da ƙwai tare da dama kunun gyaɗa,sai suka gyara gidan. Ta so ta zuba musu anan su ci dika,sai Salimah ta ce.
"Hajiya ta ce na sanar dake,daga yau idan kin yi abinci a dinga kai mana namu can."
"Ohhh Hajiya,to Yah Maheer ɗin baƙonta ne?"
Murmushi kawai Salimah ta yi wanda ya sanya Mahreen ƙure ta da ido tana murmushi,a hankali ta ce.
"Kamanninki da Addah Dijah sai suka bayyana da kika yi murmushin nan."
Ƙwalla ce ta taru a idon Salimah ta miƙe da sauri ta bar sashen. Kai Mahreen ta dafe ta na jin babu daɗi a cikin ranta da ta tuna wa Salimah abinda ita kanta yana damun zuciyarta ballantana Salimah da ta fi ta kusanci da Dijah. Jiki a sanyaye ta kwashe abincin da ta zuba ta kai ɗakin Hajiyar. Rashin ganin Salimah a wajen da kuma ƙarar ruwa da ta jiyo a banɗakin ne ya tabbatar mata da wanka take yi,sai kawai ta zauna ta gaishe da Hajiya ta zuba mata abici ta kai mata gabanta. Godiya Hajiya ta yi mata tare da sanya musu albarka sannan ta ja kunun gyaɗar ta hau sha.
Yah Maheer na dawowa daga masallaci ɗakinsu ya shige ya hau rama baccin da bai samu ba a daren Jiya. Mahreen kuwa ta so ta zauna su yi hira da Hajiya a haka har ta bigi cikinta ta sanar da ita dalilin dawowarsu nan da zama,amma Hajiya ta kora ta wajen mijinta,kan dole ta tafi ba dan taso ba.
*************************
A ɓangaren Aabid kuwa tunda ya siyar da gidansu na gado aka tura wa Aabida kuɗin ta account ɗinta kai tsaye ya samu sauƙin matsin lambar da take yi masa. Wata iriyar soyayya take zuba masa wadda yake jin sa kamar shi kaɗai ne yayi dace da sa'ar macen aure a duniya. A ɓangaren ɗaya kuma kullum da tunanin halin da Hajiyansa take ciki zuciyarsa ke kwana ta tashi,sai dai duk da damuwar da yayi da lamarin baya marmarin zuwa ya ga halin da take ciki ballantana ya san a ina take kuma a wanne hali take.
Bayan sati biyu Aabida ta kammala zuba kayan da ta yo order daga ƙasashen waje a sabuwar plazar da ta siya,da kanta ta jagoranci ma'aikatanta suka zuba kayanta da take siyarwa tana ta posting a social media tare da sanar da ƙawayenta Alhajinta ne yayi mata kyautar wajen. Aabid kuwa idan ya ga posting ɗin da ta yi sai ya tsaya yana kallon wajen yana tunani kala-kala a cikin ransa.
Yau ma kamar ko da yaushe tun da asuba da Aabid ya farka bai koma bacci ba. Abun karyawa yayi musu sannan ya haɗa wa gimbiyar tashi ruwan wanka mai cike da kayan gyaran jiki kamar yanda take so. Sai da ya tabbatar komai yayi daidai yanda take so sannan ya haura sama ya taso ta. Miƙa ta yi tana hamma tare da yamutsa fuska kamar wadda ta ga kashi. Da kallo Aabid yake binta yana jin wata iriyar soyayyarta zazzafa na ƙara huda kowanne sashe na jikinsa. Kallon Aabid ta yi daga sama har ƙasa ta ɗaure fuska ta ce..........
MUGUWAR MACE.
NA: HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✨✍️
*Ƴar'uwa kema kin yi ta shan maganin slimming amma har yau ya ƙi karɓar ki? Matso na zo maki da haɗin da zaki sha ki sauke ƙiba da nauyin jiki cikin sauƙi,Shayi ne mai daɗi da ƙamshin da ba zai baki damar yin ƙiwa ba wajen amfani da shi. Bayan haka akwai slimming oil da zai rage maki kitse a duk gaɓar da kike da buƙata a jikinki;kamar tumbi,damtse,kitsen baya,da cinya.*
*Slimming Tea 6k.*
*Slimming oil 3500.*
*Body scrub 3500.*
*Skin oil 2500.*
*Location Kano.*
*Phone No 09031416423.*
PAGE 5.
"Wai ni don Allah Aabii ban hana ka tashi na kana tsamin dauɗa ba? Ka wuce ka je ka yi wanka bana son ƙazanta."
Yawu Aabid ya haɗiya yana kallon kansa a madubin da ya mamaye ɗakin ta ko ina,a hankali ya sunsuna kansa ya kalle ta ya ce.
"Sai da fa na yi wanka kuma..."
"Don Allah dakata min bana son surutu,idan ka ga dama kada ka yi wankan ka zauna da dauɗa ba abinda ya dame ni bane. Ka haɗa min ruwan wankan?"
Da sauri ya gyaɗa kai ya ce.
"Na gama komai,sai dai yau ina so na fita da wuri akwai kayan da za a kawo daga Kura,ina so a sauke su akan idona."
Taɓe baki ta yi sannan ta ce.
"Duk saurin ka dai ka san ba za ka fita ba sai na gama abinda nake yi na fita,dan haka ka je ka jira ni."
"Amma ina za ki je da safe? Ko yanzu da safe za ki dinga buɗe plaza ɗin?"
"Yaushe muka fara ƴar tinke a tsakanin mu Aabii? Ko kuwa dan zan je na ga Innaji dole sai na faɗa maka inda zan je? Ka ga matsa ni bani da energy ɗin surutu da safen nan."
Ya so ya sanar da ita muhimmancin fitarsa da wuri,amma rashin ganin fuska ne ya sanya shi komawa parlour ya zauna yana duba wayarsa. Ba tare da tunanin komai ba ya danna kiran Maheer. Wayar ta jima tana ringing kafin Yah Maheer ya amsa. Cikin yin ƙasa da murya Aabid ya ce.
"Don Allah Ɗan'uwa ka je office da wuri a sauke kayan nan akan idonka. Ina da ɗan wani uziri ba zan samu damar fitowa da wuri ba."
Takaici ne ya mamaye zuciyar Maheer har bai san sanda ya ce.
'Aabid kana da hankali kuwa? Wai me yasa kai rayuwar duniya kawai ka saka a gaba kana mantawa da cewa watarana za mu mutu mu je lahira mu girbi abinda muka shuka?'
"Me ya faru kake yi min waɗannan maganganun Maheer? Na aikata maka wani kuskuren ne ko saɓon Allah ka kama ni ina aikatawa?"
Cike da takaici Maheer ya haɗiye yawu ya ce.
'Shikenan zan je office da wuri,sai anjima. Allah Ya ganar da kai gaskiya.'
Jujjuya wayar Aabid yayi a hannunsa yana mamakin kalaman Maheer. Taɓe baki yayi sannan ya shiga ɗakinsa ya sake yin wanka kamar yanda Aabida ta buƙata. Shadda gezna ya sanya ash color ya ɗauki hular da ta dace da kayan ya sanya. Gaban madubi ya tsaya ya hau ɓarin turare tare da buɗe wajen da yake ajiye agogo ya ɗauki wanda ya dace da kayansa ya sanya a tsintsiyar hannunsa. Kallon kansa ya tsaya yi a madubi ya na shafa dogon gemunsa da ke ƙarawa kyakkyawar fuskarsa kyau. Taku ya sake yi zuwa gaban wata ƙofar glass ya buɗe ta,takalma ne kala-kala masu kyau da tsada. Babu ɓata lokaci ya cire na ƙafarsa ya sanya wanda ya dace da adonsa sannan ya rufe wajen ya fita zuwa parlour. Ko da ya isa dinning room bai ga Aabida ba kamar yanda yayi tsammani. Waje ya samu ya zauna yana jiranta. Ta na fitowa ya hau serving ɗinta abinci ya na kallon kwalliyar da ta yi kamar mai shirin zuwa gasar zaɓen sarauniyar kyau. Ido suka haɗa ya sakar mata murmushi tare da faɗin.
"A gaskiya dole na gode wa Allah da ya bani ke a matsayin matar aure na. A koda yaushe kika saka sutura kyau kike yi mata kamar domin ke aka yi ta. Idan kuwa kika saka kwalli sai idanuwanki su dinga fitar da wani haske da sheƙi mai ban sha'awa. Ba dan kar na yi ƙarya ba zan iya cewa duk duniya babu macen da ta kai ki kyau."
Wani irin ƙayataccen murmushi ta yi wanda yake nuna tsantsar jin daɗin yabon da ta samu daga wajen mijin nata. Sai da ta ɗebi abinci za ta kai bakinta sannan ta yi fari da idanuwanta ta ce masa.
"Ai idan ka yi ƙaryar ma ba laifi bane,domin a soyayya komai ka yi daidai ne kuma ya halatta."
Da haka Aabid ya zauna a gaban Aabidah ya na kashe ta da kallon ƙauna har sai da ta kammala cin abincinta sannan ta saɓi jakarta da wayoyinta tare da makullin motarta za ta fita. Gani yayi yau ko arziƙin yafa siririn mayafin da take yi a saman kanta bata yi ba sai ta saƙala shi a hannunta irin yanda ƴammata ke yi,kamar zai ƙyale ta sai ya ji ya kasa,wani irin matsanancin kishinta yake ji kamar ya ɓoye ta daga idanun duniya. Gyaran murya yayi ya na kallonta kamar mai jin tsoron yin magana ya ce.
"Amma Baby a haka za ki fita yau ko abun tatar kokon ba za ki yafa a saman kanki ba sai a hannu za ki riƙe?"
Da wani irin mugun kallo ɗauke a idanuwanta ta juya ta na dubansa,nan take Aabid ya sauke ƙwayar idanuwansa ƙasa. Ganin yanda ya