MUGUWAR MACE COMPELET HAUSA NOVELS.txt

Author :  HAMIDA SANUSI AHMAD Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   7 / 17

18K to 21K   out of 48.3K words

cike da rashin samun nasara Aabid ya kewayeta ya fita daga ɗakin. Kanta ta dafe ta saki ƙara a hankali kafin ta mari kuncinta ta ce.

"Da dikkan alamu idan Boka bai gaggauta samar min mafita a wannan lamarin nawa ba zan haukace saboda damuwa."

*Aabid.*

Ya jima yana maimaita kalaman Aabidah a cikin ransa,amma ya gaza gane inda addu'arta ta dosa. A haka ya dinga tuƙi ya na ratsa gidaje da tituna har ya isa ƙofar gidan mahaifinsa. Ya na zuwa ya ga an sabunta fentin gidan tare da yin shuke-shuke a wuraren da aka bari domin shuka. Murmushi ya saki domin yana da yaƙinin babu mai yin wannan aikin sai Maheer. Wata iriyar kewar Maheer ce ta mamaye shi,sai yake jin kamar ya ɗauki wasu shekaru masu tsawo bai gansa ba. Kai tsaye ya dirfafi gate ɗin gidan da zummar shiga ciki. Sai dai ganin wani mutum sanye da kakin soja a jikinsa ne ya sanya shi tsaya wa yana kallonsa cike da neman ƙarin bayani. Shi ma mutumin kallon Aabid ya ke yi tare da faɗin.

"Kai ina za ka je ne kake ƙoƙarin wuce wa ciki ba tare da neman izini ba?"

Wata kafirar harara Aabid ya banka wa sojan sannan ya ce.

"Gidan uban nawa ne zan nemi izininka dan zan shige shi? Kai ɗin waye?"

Murmushi sojan yayi dan ya fuskanci Aabid bai san cewa an siyar da gidan ba. Dan haka cikin ƙanƙanin lokaci ya bayyana masa cewar ai gidan an siyarwa da ogansa ne;a cikin satin ma suka tare. Baki Aabid ya saki yana mamakin wanda zai siyar da gidansu na gado ba tare da izininsa ba. Gefe ya koma ya zaro wayarsa ya danna kiran Maheer. Ta jima sosai tana ringing tare da katse wa ba a amsa shi ba,shi kuwa Aabid ba tare da gajiya wa ba ya sake kira. A haka har dai Maheer ya gaji da nacin Aabid ya ɗaga wayar a hasale ya ce.

'Wai don Allah wannan wanne irin kira kake yi min ne Aabid?'

Da sauri Aabid ya sauke wayar daga kunnensa ya kalli wayar sannan ya mayar da ita kunnensa ya ce.

"Maheer ni ne fa Aabid."

'Sai aka yi yaya dan kai ne Aabid?'

Cike da mamakin sauyawar halayyar Maheer Aabid ya ce.

"Ohhh yanzu na gane komai,dama kai ne ka zuga Mahreen ta siyar mana da gidanmu na gado kenan ko? Dama za ka iya cin amanar zumuncin dake a tsakaninmu Maheer?"

Cike da ƙunar rai Maheer ya ce.

'Excuse me? Me kake nufi da na zuga Mahreen ta siyar muku da gidanku na gado? Ohhh ! Ohhh ta nan kuma ka biyo Aabid? Duk ka manta rashin mutunci da wulaƙancin da ka aikata kenan? Aabid wai kana ma ina ne yanzu haka?'

"Ina ƙofar gidanmu a da;wanda ka shiga ka fita ka siyar da shi. Maheer ka sani ba zan taɓa barin wannan cin amanar ya tafi a banza ba."

Aabid na gama magana ya kashe wayarsa ya shige motarsa ransa a matuƙar ɓace ya nufi hanyar gidansa. A ɓangaren Maheer kuwa ya jima yana nazarin abinda ya faru a tsakaninsa da Aabid kafin ya sanya goshinsa a ƙasa ya yi wa Allah sujjada tare da miƙa godiyarsa a wajen Allah. Ba tare da tunanin duhun dare da ya fara shiga ba Maheer ya shirya yana cike da matsanancin farinciki ya bar gida........


MUGUWAR MACE.





NA: HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✨✍️









PAGE 10.





WAIWAYE ADON TAFIYA....

Ƙaramar hukumar Kura da ke a cikin jihar Kano, wacce ke da tazarar kusan kilomita 35 daga birnin Kano,ɗaya ce daga cikin manyan wuraren noma da sarrafa shinkafa a jihar Kano da Najeriya baki ɗaya.

Ana noma shinkafa a kusan dukkanin yankunan ƙaramar hukumar. Kura gari shi ne babban zaure na harkokin noma da kuma masana'antun nika shinkafa (kamar Golden Grains Agro-processing Co. LTD).
Allah ya albarkaci ƙaramar hukumar Kura da ruwa; musamman na kogin Kano da ake amfani da shi wajen noman rani da damuna,suna da ƙasa mai kyau da ta dace da da noman shinkafa da sauran kayan abinci. Mutanen garin Kura sun taso sun ga iyayensu da kakanninsu na noma da cinikayyar amfanin gona daga cikin jihar kano,da sauran jihohin Nigeria har ma da ƙasashen waje.

Musa Abdulwahab Musa Kura wato Aabid ɗaya ne daga cikin mutanen da Allah ya yi wa gam da katar ɗin kasancewa daga cikin tsatson manoman cikin wannan gari mai tarin albarka na Kura. Kakan Aabid wato Malam Musa ɗan asalin Ƙaramar hukumar Kura ne,wanda ya taso da zafin nema da kuma fasaha da ilimin noma da kiwo. Wannan dalilin ne ya sa mutanen garin ke matuƙar girmama shi tare da kiransa duk wani babban project da za a yi na gwamnati domin su amfana da iliminsa. Babban dalilin da ya hana Malam Musa zamowa ɗaya daga cikin manyan masu arziƙi a cikin garin Kura da kewaye shine ƙaddara. Tabbas ƙaddara ce kaɗai za ta hana mutum mai ilimin noma da zafin nema kamar Malam Musa zamowa ɗaya daga cikin masu kuɗi.

Lokuta da dama idan ya dawo daga gona ya gaji ba tare da ya samo wani abun a zo a gani ba;sai ya zauna ya zabga tagumi yana jimamin lamarin. A haka matarsa mai suna Atine za ta kawo masa abincinsa da ruwan sha, da ya buɗe ya ga babu nama ko fikin miya,sai ya yi murmushi ya ce.

"Watakam Atine tsari da hikima irin na Ubangiji daban ne da na bayinSa. Kowanne mai rai da kike gani a duniyar nan an gama rubuta arziƙinsa tin yana cikin mahaifiyarsa. Shi yasa za ki ga wani zai taso a rayuwarsa bai san wahala ba ballanatana neman na kai a cikin zafi,damina da ɗari,amma sai ki gansa da wadata tare da hanyoyin samun kuɗi masu tarin yawa. Wani kuma sai ki ga ya taso yana ta nema kacal wacal kamar zai bada rayuwarsa saboda neman na kai,amma sai ya wuni bai samu ko sisi ba. Wani kuma a kullum sai ya fita ya yi aiki da jikinsa ya saka rayuwarsa a hatsari sannan yake samun abinda zai ci iya na wannan yinin."

A duk lokacin da Malam Musa yayi wannan kalaman nasa sai Atine ta yi murmushi ta ce.

"Maganar ka dutse Malam,domin kuwa mu ɗin nan babban misali ne akan Allah yana azurta duk wanda ya so ne,tinda ni ma ba a zaune nake ba wajen neman na kai,amma har yau gamu nan jiya-i-yau."

Haka rayuwar Malam Musa da Atine take a cikin rashi da ƙuncin talauci har suka haifi yaronsu na farko. Bakwai na zagayowa Malam Musa ya zauna a bakin ƙofar ɗakinsa da asubar fari yana hawaye;sakamakon rashin kuɗin da zai sayi ragon sunan tilon ɗansa. A haka Gwaggon Atine da ke yi mata zaman daɓaro mai suna Gwaggo Kande ta same shi zaune yana zubar da hawaye; bayan ta dawo daga kai ruwan wankan Atine bayi. Cike da tausayawa ta isa gabansa ta zauna a nesa da shi ta ce.

"Malam Musa ka sanya wa zuciyarka haƙuri,domin babu da akwai duk na Allah ne. Ba kuma akan ka aka fara haihuwar fari a rasa abinda za a yanka ranar suna ba,sannan ina da yaƙini da tabbacin ba a kanka za a ƙare ba."

Hawayensa ya share tare da face majinar dake danƙare a hancinsa ya ce.

"Goggo Kande ba ina jayayya da hukuncin ubangiji bane. Kawai ina mamakin yanda kiwo wannan bai karɓe ni ba kamar yanda sauran ƴan'uwana manoma da dangi suke da ababen kiwatawa. Fisabillahi yanzu da ina da abun kiwatawa zan shiga cikin wannan halin ne?"

Jijjiga kai Goggo Kande ta yi sannan ta ce.

"Sam ba za ka shiga ba Malam Musa. Sai dai ina so ka sani duk abinda ya samu bawa da sanin Allah,ka ƙara haƙuri sannan ka gode wa Allah da ya baka rai da lafiyar nema, ko da baka tara ba za ka fita ka nemi wanda za ka ci kai da iyalanka kuma ka samu."

"To amma Goggo ki na ganin mutanen da nake bawa shawarwarin noma da da kiwo har wanda nake zuwa da kaina na yi musu dabarun da za su samu arziƙi a cikin nomarsu duk sun yi kuɗi sun fi ƙarfin gidansu,ni gani nan abinda za a dafa a ranar sunan ɗana na fari babu, ballantana abinda za a yanka na raɗin suna."

A hankali Gwaggo Kande ta miƙe tsaye tana kaɗe zaninta ta ce.

"In dai wannan ne mun gama tattaunawa da Atine,yau ɗin nan za a kawo mata ragonta na gado da ake kiwata mata a can babban gida,idan yaso sai a bar tinkiya da awakin a ci gaba da kiwata mata. Ni kuma na yi alƙwarin kawo abinda za a dafa a ci a taron suna. Dan haka ka kwantar da hankalinka kada ka saka wa kanka damuwar da za ta jawo maka wani ciwon."

Godiya sosai Malam Musa ya durƙusa a ƙasa yana yi wa Gwaggo Kande kamar zai kwanta mata. A haka Atine ta fito ɗaure da zani ta yafa wani a saman kanta ta riske su. Malam Musa na ganinta ya nufe ta ya hau yi mata godiya akan rufa masa asirin da ta yi. Murmushi kawai ta sakar masa ta tafi bayi.

A wannan ranar Malam Musa ya tattara sauran duk abinda yake da shi na daga hatsi ya kai kasuwa ya siyar ya dawo da cefanen kayan miya;tare da kayan jariri kala uku,sai sabon ɗankwali da sarƙa da ɗankunne na murjani ya kawo wa Atine. Murna Atine ta dinga yi tana sanya masa albarka tare da fatan Allah Ya ninninka masa arziƙinsa ya raya musu ɗansu Abdulwahab.

Bayan sunan Abdulwahab Atine da Malam Musa sun ci gaba da rainon ɗan su cikin kulawa,soyayya da ƙauna irin ta iyaye. Malam Musa sai ya sake dagewa da neman kuɗin da zai ba wa ɗan sa da matarsa ingantacciyar rayuwa. Cikin ikon Allah kuwa sai arziƙinsa ya fara buɗewa har ya fara tara dabbobi yana kiwatawa a gida kamar yanda yake da sha'awa da buri. A hankali Malam Musa ya fara siyan fili yana yadawa. Abdulwahab na kai wa shekara takwas a duniya ya saka kansa a makarantar boko da ya ga yaran garin na zuwa. Sai dai su da sun kammala primary suke tsunduma a harkar noma sai su watsar da karatun. A ɓangaren Abdulwahab kuwa sam bai watsar da karatun bokonsa ba,saboda yana gane duk abinda ake koyar da shi. Bayan an taso daga makarantar boko sai ya wuce ta allo,da yamma ya koma gida ya ci abinci ya yi bitar karatunsa na boko da na arabiyya. Babu jimawa labarin nacin karatu irin na Abdulwahab ya fara karaɗe garin Kura,har wasu daga abokan Malam Musa suka yi ayari su huɗu suka je har gida suka same shi da shawarar;ya kamata ya dakatar da Abdulwahab daga zuwa makarantar boko ya jefa shi a harkar noma kamar sauran yaran garin,gudun kada ya tashi bai iya riƙe fatanya ba. Da jin haka sai Malam Musa ya fashe da dariya ya kalli abokan nasa ya ce.

"Allah mai iko! Ku yanzu akan makarantar da yaron nan yake zuwa kuka yo ayari haka kuke sanar da ni na hana shi zuwa? Ina kuke lokacin da nake cikin gararin talauci da babu? Ina kuke ranar sunansa lokacin da nake neman ragon da zan yanka a sunansa dan na sauke nauyi da kuma kare mutuncin ɗana da ni kaina da iyalina? Ina kuke lokacin da yaron nan ya dinga yawo babu suturar arziƙi a jikinsa ballantana takalmin da zai saka ya shiga cikin tsaransa?"

Idon da ya zuba musu yana neman ƙarin bayani ne ya sanya su sauke kawunansu ƙasa cike da jin nauyi da kunyarsa. Murmushi yayi sannan ya ce.

"Idan baku da amsar bani ku je ku ci gaba da kula da yaranku ta hanyar da kuke ganin ita tafi dacewa da rayuwarku;nima ku barni na kula da nawa yaron ta hanyar da nake ganin tafi dacewa da rayuwar da nake so yarona ya taso a cikinta."

Cike da borin kunya suka kaɗe rigunansu suna faɗin.

"Ai shikenan,dama shi gyara kayanka ba ya zamowa sauke mu raba,shawara ce dai muke baka,dan mu dai bamu ga wanda biro da takarda suka ciyar ba,riƙo da fatanya muka gada kaka da kakanni,ita ce ke bamu abinda muke kai wa bakin salati."

"To ku je ku ci gaba da riƙe fatanyar shi kuma ya riƙe bironsa,Allah Ya bawa kowa sa'a akan abinda ya sa a gaba."

Tin daga wannan ranar abokan Malam Musa suka janye jiki daga gare shi,sannan duk wata harkar noma ta samun ci gaba idan ta shigo garin suke kashe tauraruwarsa su ƙi sanar da shi. A duk lokacin da ɗayansu ya neme shi to ta tiƙe masa ne babu yanda zai yi sai ya nemi shawara ko taimakon Malam Musa. A hankali samun Malam Musa ya fara ja baya,amma duk da haka bai karaya ba,sai ya koma noma filayensa guda uku da ya mallaka da kansa,idan abunda ya noma yayi sai ya je ya siyar. A haka Abdulwahab ya kammala ƙaramar sakandire har ya rubuta jarabawar shiga babbar sakandire. A tsakanin hutun da ya samu ne na rubuta jarabawar shiga senior secondary school ya fara bin mahaifinsa kasuwa yana ganin yanda ake gudanar da kasuwanci. A kuma wannan lokacin ne sha'awar siye da siyarwar kayan abinci ta shiga ransa. Bayan ya koma makaranta sai Malam Musa ya hana shi zuwa kasuwa ya ce ya mayar da hankali akan karatunsa.

Abdulwahab na da shekaru goma sha biyar a duniya Atine ta haifa masa ƙanwarsa mai suna Salma. Sosai Atine ta wahala saboda jimawar da ta yi ba tare da ta haihu ba,jinin da ta zubar sai ya sake rage mata kuzari da karsashi. Wannan dalilin ne ya sa ita kanta yarinyar bata samun cikakkiyar kulawa daga mahaifiyarta yanda ya kamata. Bayan suna da wata ɗaya Atine ta rasu sakamakon rashin jini a jikinta. Malam Musa ya shiga ɗimuwa da zaucewa saboda rashin masoyiyarsa. Ya jima sosai bai koma noma ba ballantana ya girbe amfanin gonarsa ya kai kasuwa. A haka suka ci gaba da rayuwa cikin ƙunci da kewa tare da maraicin rashin Atine a rayuwarsu. Sosai Malam Musa ya so a bar masa Salma su ci gaba da kula da ita shi da Abdulwahab,amma sai Goggo Kande da sauran ƴan'uwan Atine suka ƙi amincewa da hakan suka ɗauke ta ta koma ƙarƙashin kulawarsu.

Abdulwahab na zana jarabawarsa ta ƙarshe a sakandire mahaifinsa majinginarsa kuma katangarsa ya faɗi ya rasu. Sosai mutuwar Malam Musa ta girgiza mutanen garin Kura da kewaye. Domin kuwa shi ɗin mutumin kirki ne,kuma su na amfana da shi matuƙa gaya a ɓangaren noman rani da damuna. Rasuwar Malam Musa ta sanya Abdulwahab zamowa yaro mara son magana da kuma kaɗaice kansa daga cikin al'umma. Lokuta da dama yafi tafiya cikin gonar mahaifinsa ya kwanta ya sha kukansa,daga ƙarshe bacci ya ɗauke sa,sai idan an aika yara nemansa ne ake samo shi a gona. Sosai Gwaggo Kande take tausayawa rayuwarsa saboda ta fi kowa sanin irin gata da kulawa tare da soyayyar da iyayensa suka bashi. Ganin yana neman ya lalata rayuwarsa ne ya sanya mijin Gwaggo Kande shige masa gaba a lokacin da sakamakon jarabawarsa ya fito; Result ya yi kyau sosai,sai ya biya masa kuɗi ya rubuta JAMB a wannan shekarar. Cikin ikon Allah ya samu makin da ake nema domin shiga jami'a. Malam Bala shi ne yayi tsaye tsayin daka ya saka Abdulwahab a makarantar jami'a ta kano wato Ado Bayero University Kano State. Ranar da Abdulwahab zai tafi makaranta Gwaggo Kande da Salma sai kuka suke yi,shi kuma yana jin wani irin farinciki a ransa zai bar garin Kura ya je wajen da zai yi nesa da inda ya yi rayuwa da iyayensa da ya rasa. Har tasha Malam Musa ya ɗauki Salma suka raka Abdulwahab da kayansa a cikin Ghana most go da leda ViVa. 

Bayan tafiyar Abdulwahab makaranta Malam Bala ya ci gaba da kula da shi da buƙatunsa har ya kai level 200. Sai dai zugar abokai da danginsa ce ta sanya shi fara ja da baya tare da cire duk wani tallafi da yake bawa Abdulwahab. Lokacin da Abdulwahab ya samu hutu ya leƙa garin Kura mutanen garin suka gansa fes da shi gwanin sha'awa,sai suka ƙara tinzira Malam Bala suna yi masa nuni da ya zauna yana ta kashe kansa shi da yaransa su na gina yaron da bai san zafin nema ba. Tin suna maganar a ɓoye har magana ta shiga kunnen Abdulwahab. A lokacin da ya ji sai ya ƙi amincewa Malam Bala zai ɗauki zugar masu zuga har ya daina tallafa masa kamar yanda ya saba. Lokacin komawa makaranta na yi ya tinkari Malam Bala da maganar kuɗi,a nan ne fa Malam Bala ya murza wa idonsa toka ya ci wa Abdulwahab mutunci tare da yi masa gori kala-kala. Sosai kalaman Malam Bala suka ƙona wa Abdulwahab zuciya,amma sai ya tuno da alkhairin da ya yi masa a baya. Godiya ya yi masa ya shiga wajen Gwaggo Kande ya sanar da ita zai koma. Sanin halin da ake ciki ne ya sanya ta miƙe wa ta shiga ɗakinta ta ɗakko wata baƙar leda ta dawo ta zauna a gefensa ta ajiye masa a saman cinyarsa ta ce.

"Karɓi wannan,kuɗin awakin mahaifiyarku ne da na sa a siyar tin wancan satin. Kasancewar na fuskanci Malam ya fara ɗaukar zugar mutane ya sa na ce to meye amfaninsu? Shine na ba wa Kawunka Sale na ce a siyar a kawon kuɗin. Ka ƙara haƙuri Audu watarana sai labari. Allah Ya yi maka albarka Ya sa a mori wannan ilimi da kake ta fafutukar nema."

"Amin Ya Allah Gwaggo na gode,Allah Ya ƙara miki lafiya da nisan kwana mai albarka in kai ki makka da Madina ke da Baba da Salma."

Guɗa Gwaggo Kande ta zabga tana murna,domin ko Abdulwahab bai kai ta Makka da Madina ba ya biya ta tinda ya sa hakan a niyyarsa. A wannan karon Abdulwahab da kansa ya nemi Salma ta yi masa rakiya tasha ta riƙe masa ƴar ƙaramar jakarsa ta goye suka tafi su na hira tana ta zuba masa surutu irin na yara masu wayo da baki. Da za su rabu ya siya mata kayan kwalama irin na yara a tasha ya tsaya a bakin tashar har ta ɓacewa ganinsa. Gani yayi ana ta loda

7 / 17