MUGUWAR MACE COMPELET HAUSA NOVELS.txt

Author :  HAMIDA SANUSI AHMAD Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   10 / 17

27K to 30K   out of 48.3K words

suka sanar da Malam Bala ƙudirin Abdulwahab na kai Gwaggo Kande Makka,wani irin kishi,hassada da ƙyashi ne ya taso ya lulluɓe zuciyar Hasiye,ji take yi kamar ta zuga Malam Bala ya hana Kande zuwa Makka,sai dai tana ji ta na gani Malam Ya amince su Abdulwahab suka ɗakko Gwaggo Kande da Salma suka kawo su Kano. A cikin satin suka kai ta aka yi mata international passport da duk wani abu da ya dace. Su na dawowa suka tarar da Ammabuwa na naƙuɗa Layuzah na ta kuka saboda bata san da me za ta taimaka mata ba,gashi zamanin babu waya ballantana ta kira mijinta ta sanar da shi halin da ake ciki.

Ko ajiye hijabi Gwaggo Kande bata yi ba ta kori su Mudassir da suka rikice su na faɗin ta fito a tafi asibiti. Su na fita Gwaggo Kande ta taimaka wa Ammabuwa har ta haifi sankacecen ɗanta kyakkyawa fari tas mai kama da ita. Kukan jaririn ne ya sanar da su Mudassir Ammabuwa ta sauka ƙalau. Murna sosai suka dinga yi shi da Abdulwahab. Layuzah kuwa hamdala ta dinga yi tana maimaitawa bakinta ya ƙi rufuwa. Da yammar Gwaggo Kande ta hura wuta a murhu, nan da nan ta ɗora ruwan wanka ta wanke jariri da mahaifiyarsa. Kafin su gama shiri Abdulwahab ya je wajen mai gashin nama ya siyo nama mai yawa da madarar shanu da dabino ya kawo. Yanda ya dinga hidima da Ammabuwa da jaririnta sai ka rantse Layuzah ce ta haihu. Mudassir har kuka ya dinga yi yana ji a ransa zai iya bada rayuwarsa saboda Abdulwahab. Washegari ya je gidansu Ammabuwa ya sanar da haihuwarta, mahaifiyarta ta so ƙanwarta ta je ta kula da Ammabuwa,amma sai ya ce ai akwai mai kula da ita,domin Ammabuwa da kanta ta sanar da shi bata son kowa ya zo saboda gudun gutsiri tsoma na mutane har a yi abinda zai taɓa zumuncinta da Layuzah.

Abdulwahab shi ne ya sayi ragunan suna manya guda biyu. Dan haka ranar suna Mudassir ya ce yaro ya ci sunan Abdulwahab. Sosai hakan ya yi wa Abdulwahab daɗi sai Layuzah ta ce za su dinga kiransa da Maheer. Ita dai Ammabuwa har a wannan lokacin yaron bai wani shiga ranta ba,shi yasa ko kuka yake idan Layuzah ta kawo mata shi dan ta shayar da shi,sai ta dinga kuka ta na faɗin zai mayar da ita tsohuwa. Sai da Gwaggo Kande ta yi mata wankin babban bargo sannan ta ce za ta je har gidan iyayenta ta faɗi iyashegen da take yi,sannan ta rungumi yaronta ta na bashi kulawar da ta dace duk wata uwa ta ba wa ɗanta.

Bayan suna da sati biyu Gwaggo Kande ta tafi Makka,sosai Salma take taya Ammabuwa rainon Maheer. Idan aka goya mata shi bata sauke shi har sai ya yi kukan yunwa,ya na shan mama za ta ce a goya mata shi,sam bata gajiya da ɗawainiyarsa.

Layuzah na matuƙar jin daɗin zama da Salma,domin yarinya ce ita mai matuƙar natsuwa da hankali tare da sanin ya kamata. Satin Gwaggo Kande biyu a Makka ta dawo cike da tsaraba mai tarin yawa. Domin kuwa duk wasu ƴan kuɗaɗen da za ta ci abinci da Abdulwahab ya bata bata saki jiki ta kashe su ba,Salma kanta sai da ta samu riguna da takalma bakwai. Sannan ta yi wa mutanen Kura tsaraba musamman Malam Bala da dangin mahaifan Abdulwahab na uwa da uba. Kwanan ta uku ta kafe sai ta tafi Kura,kuma da Salma za ta tafi,domin amana ce Atine ta bata,ba za ta rabu da ita ba sai aure ko mutuwa. Salma na jin maganar aure kunya ta kama ta,sai ta dena rikicin ba za ta bi Gwaggo Kande ba ta wuce ta fara haɗa kayanta. Washegari da sassafe Abdulwahab ya saka su a mota suka koma Kura.

Gwaggo Kande na tafiya Mahaifiyar Ammabuwa ta matsa akan sai Ammabuwa ta koma gida wanka,domin ta gano babu wani babba da ke yi mata wanka shirmen su kawai suke yi ita da Layuzah a gidan. A daidai wannan gaɓar Layuzah ta shiga damuwa saboda tafiyar Ammabuwa,sai take jin gidan shiru babu Salma,babu Maheer,ga Ammabuwa ƙawa kuma aminiyarta ta koma gidan iyayenta. Wannan damuwar da ta shiga ne ya sanya Abdulwahab bata lokacinsa sosai,har ya zamana watarana ma baya fita aiki ko kasuwa, Mudassir ne kawai yake tafiya ya ji da komai. Ana haka Layuzah ta fara yawan cin abinci da kwaɗayin tsiya,bata yin wani ciwon kuma bata amai ballantana zazzaɓi. Gaba ɗaya basu gane abinda ke faruwa da ita ba har sai da Ammabuwa ta gama wankan gida,danginta suka dawo da ita cikin kwalliya irin ta Buzaye da kayan gara irin na al'ada da ake yi a duk haihuwar fari. A lokacin da za su tafi ne wata Innar Ammabuwa ta ke cewa.

"To Gwaggon Maheer kema Allah Ya sauke ki lafiya. Ku ci gaba da haƙuri da junanku domin zaman ku lafiya na faranta mana rai mu iyayenku. Allah Ya yi muku albarka."

Da haka suka tattara suka tafi suka bar Ammabuwa cikin murnar dawowa kusa da aminiyarta. Bayan sun raka su sun dawo ne Ammabuwa ta ce.

"Ƴar'uwa wai meye sirrin ne na ga kin yi wani irin kyau sai kace yanzu ne kuke cin amarci ke da Yayana?"

Murmushi Layuzah ta yi ta ce.

"Ni kai na ban san me yake damu na ba,kin ganni nan babu abinda na saka a gaba da ya wuce kwaɗayi da yawan cin abinci, sai kuma yawan bacci kamar wata kasa."

"To ko dai maganar Innahta ce za ta zamo gaskiya Maheer zai samu ƙani ko ƙanwa?"

Kunya ce ta kama Layuzah ta ce.

"Habaa babu wani ciki da nake ɗauke da shi ni dai. Da duk ban samu ba sai yanzu?"

"Iyi mana,ai Baban Mudassir ya bani labari irin soyayyar da kuke zubawa a gidan nan kamar wasu tattabaru."

Dariya kawai Layuzah ta yi, ta wuce ciki ta ɗakkowa Ammabuwa abicin da ta dafa mata na musamman. Nan suka zauna su na ta hira Layuzah na riƙe da Maheer a cinyarta ta na jin son yaron na ƙaruwa a cikin ranta saboda kyau da girman da ya sake yi.

Su Layuzah basu tashi sanin tana dauke da ciki ba har sai da cikinta ya kai watanni huɗu a duniya. Ranar da ta fara jin motsi ta gigice ta gigita kowa a gidan. A wannan ranar kuwa Abdulwahab baya gari tafiya ta kama su daga wajen aikinsa. Mudassir ne ya ɗauke ta a kan babur ya kai ta asibiti aka duba ta. Bayan gwaje-gwaje likita ya tabbatar musu da cewar ta na ɗauke da juna biyu har na tsawon watanni huɗu. Murna sosai Mudassir ya dinga yi,ita kuwa Layuzah sai ta ji kunyar Yayan nata ta kama ta har ta ƙi hawa babur ɗinsa sai da ya samo mata bus ta hau aka mayar da ita Ƴankaba. Ta na zuwa gida ta tarar da Mudassir ya riga ta zuwa har ya sanar da Ammabuwa. A ƙofar gida ta tarar da Ammabuwa goye da Maheer ta na ta washe baki. Hijabi ta sa ta rufe fuskarta saboda kunyar da ta ke ji. A haka suka shige gida Ammabuwa na nan nan da ita. Har so take ta ji Layuzah na buƙatar wani abu ta gabatar mata da shi. Bayan kwana biyu Abdulwahab ya dawo daga tafiya aka sanar da shi wannan labarin mai daɗi,farinciki ya dinga yi ya na kumawa tare da godiya ga Allah da ya yi masa wannan kyautar.

Sosai mutanen nan uku suke nuna wa Layuzah kulawa har watarana ta kan rasa bakin yi musu godiya. Idan Mudassir na tsokanar Abdulwahab sai ya ce.

"Ni dai na shiga uku da surukin zamani,wai kai ba ka jin kunya ta ne don Allah?"

"Ina fa zan ji kunyar ka tinda dai ni ba a suruki na ɗauke ka ba. Kai ɗin abokina ne,aminina ne kuma ɗan'uwana. Dan haka babu wata kunya a tsakaninmu."

Abdulwahab na jin daɗi a ransa idan ya ji Mudassir na bashi babban matsayi a ransa.

Ana haka cikin Layuzah ya shiga watan haihuwa,gashi Abdulwahab ya na so ya yi tafiya ƙasar Ghana saboda shigar da wasu kaya da suke son su yi. Da jin haka sai Layuzah ta hau kuka ta na faɗin.

"Gaskiya babu inda za ka tafi ka barmu ni da abinda ke ciki na,ko kana son ka tafi ka barni wajen haihuwa na mutu baka nan?"

Da sauri Abdulwahab ya kalle ta ya na jin zuciyarsa na tsananta bugawa. A duniya baya son ya ji Layuzah na kiran mutuwa ko rabuwa a tsakaninsu. Dan haka cike da rarrashi ya ce.

"Ki kwantar da hankalinki,babu inda zan je, bana Yayanki zan tura Ghana duk da baya son tafiye-tafiye,na rasa me yake jin tsoro,amma dai a wannan karon dole shi zai je,idan ba haka ba kuma sai dai mu haƙura da kai kayan gaba ɗaya,tinda ke kin ƙi amincewa na tafi."

Haka suka dinga hira Layuzah na sake jaddada wa Abdulwahab rashin son tafiyar da zai yi. Lokacin sallar Isha'i na yi ya tafi ya yi alwala ya wuce masallaci. Bayan an idar da sallah su na dawowa daga masallaci Abdulwahab ya kawo wa Mudassir buƙatarsa na tafiya ƙasar Ghana kai kaya da yake son ya yi. Ba dan Mudassir ya so ba kan dole ya amince da tafiyar. Su na zuwa gida ya dinga yi wa Layuzah masifa ya na cewa duk laifinta ne ta sa mijinta zai aika shi wata uwa duniyar. Dariya kawai ta yi ta ci gaba da yi wa Maheer wasa. Ammabuwa kuwa sai ta ce.

"To ai gwanda ka yi tafiyar ma ko mutum ya ɗan huta na wasu kwanakin. A yi mutum kullum ya na gida ko tafiyar kwana ɗaya baka taɓa yi ba fa."

Ƙanƙance ido Mudassir ya yi yana kallon Ammabuwa ya ce.

"Au haka ne? Dama duk ƙarya kike zuba min da kike cewa ba kya son in dinga yin nisa da ke? To ai shikenan,Aboki ni fa daga yanzu na koma ɓangaren zirga-zirgar ƙasa da ƙasa."

Dariya sosai suka yi gaba ɗayansu,sannan suka ci gaba da hira mai cike da nishaɗi da barkwanci. A wannan ranar basu rabu da junansu ba sai misalin sha ɗaya da rabi na dare. A daren kuma Ammabuwa ta haɗa wa Mudassir kaya a ƴar ƙaramar jaka ta saka masa duk abinda zai buƙata. Sannan suka kwanta suka raya daren nasu cike da soyayya.

Washegari ana idar da sallar asuba Malam Sallau ya zo da tawagar da za su yi tafiyar a mota. Sallama Mudassir ya yi wa su Ammabuwa da Layuzah dake riƙe da Maheer da ya tashi tun asuba bai koma bacci ba,banda kuka babu abinda yake yi. Su na gama sallama ya bi Abdulwahab suka tsaya a zaure ya bashi wasu ƴan kuɗaɗen da zai yi amfani da su ko da buƙatar hakan ta taso. Rungume junansu suka yi sannan suka yi musabaha hannunsu na riƙe da na junansu Mudassir ya shiga mota yana ɗaga wa Amininsa hannu........


MUGUWAR MACE.





NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✨✍️






*Yanzu muka fara wannan labari na MUGUWAR MACE mai cike da sarƙaƙiyar rayuwar zaman aure,makirci,butulci,sihiri,tare da cikakken ilimin zaman duniya. Idan ki na son a ci gaba da yin wannan tafiya tare da ke sanya 1k ɗinki ta wannan account ɗin 9031416423 Opay Hamidah Ahmad Sanusi. Sai ki tura shaidar biya ta 09031416423. Don girman Allah idan har kin san za ki siyi novel ɗin nan ne da niyyar ki yaɗa shi a group ɗin da idan kika bari suka siya a waje na nima zan samu alkhairi to ki yi haƙuri kada ki siya,domin idan kin siya kin yaɗa kin kashe min kasuwa. Don Allah mu so juna domin Allah kada mu dinga zalintar junanmu.*✨✍️


PAGE 14.





Zuwan Mudassir ƙasar Ghana ya sanya idamuwansa sake buɗewa akan kasuwanci ƙwarai da gaske. Lokacin da za su dawo gida Nigeria bai yi shawara da kowa ba ya saro wasu daga abubuwan da suke da shi a can wanda mutanenmu na Nigeria ke da buƙata suka kamo hanya da sauran yaran Abdulwahab suka dawo. A wannan lokacin ne ɗaya daga cikin yaran Abdulwahab mai suna Iliya ya kai masa gulmar yanda Mudassir ya dinga facaka da dukiyarsa a Ghana. Nan take shaiɗan ya yi uwa ya yi makarɓiya ya dasa wa Abdulwahab wani ƙulli a cikin zuciyarsa game da aminin nasa kuma Yaya ga matarsa. Tin daga wannan ranar alaƙarsu ta fara sauyawa,sai ya zamana kafin Abdulwahab ya kira Mudassir sau ɗaya ya kira Iliya sau biyar. Mudassir na kula da hakan sai ya ja baya ya koma yin ayyukan da ba lallai ne sai ya nemi izinin Abdulwahab ba,sannan ya kame bakinsa bai sanar da matarsa ko ƙanwarsa sauyin da yake gani a tattare da abokin nasa ba.

Sosai Mudassir ya kai zuciyarsa nesa game da yanda Abdulwahab ya dinga ɗaure masa fuska da nuna masa iyakarsa,sai Mudassir ya nuna sam bai ma gane abinda yake yi ba,harkar gabansa kawai ya sa a gaba tare da ƙoƙarin kawo cigaba a cikin kasuwancin da suka sha wahala wajen ginawa. A hankali Malam Sallau ya kula da abinda ke faruwa a tsakanin aminan junan. A matsayinsa na amintaccen yaron Abdulwahab sai ya tsaya ya tsananta bincike akan lamarin,babu jimawa kuwa ya gano abinda ke faruwa. Ba tare da sanin kowa ba ya ɗana wa matashin dake son ya ture Mudassir daga rayuwar Abdulwahab shi ya kafa tashi kujerar tarko.

Watarana Malam Sallau ya karɓo takardun wasu filaye da ya siyo wa Abdulwahab sai ya je shago ya bawa Mudassir a gaban Iliya da mutanen shagon ya ce ya bawa Abdulwahab,babu ɓata lokaci Mudassir ya karɓa ya saka su a cikin jakar da yake zuwa da ita shagon nasu da niyyar idan Abdulwahab ya taso daga aiki ya biyo shago sai ya bashi,idan kuma bai biyo ba in sun je gida sai ya bashi,daga nan sai ya ci gaba da harkar gabansa. Malam Sallau na zaune ya na ta hirarsa amma gaba ɗaya hankalinsa ya na kan Iliya da ke ta kallon mutane ya na zuge jakar Mudassir. A hankali ya zare takardun ya fita daga shagon da sauri ya nufi shagon da suke kwana ya ɓoye,ya na gama ɓoyewa ya dawo ya ci gaba da aikinsa kamar babu abinda ya aikata. Da ganin haka sai zargin da Malam Sallau yake yi akansa ya tabbata. Sai da ya bari an tafi sallar magrib ya shiga shagon su Iliya ya ɗauke takardun. Da dare bayan Abdulwahab ya koma gida Malam Sallau ya je ya bashi labarin duk abinda yake faruwa da kuma hasashen da yake yi akan Iliya. Cike da tsantsar nadama da danasani tare da jin nauyi da kunya Abdulwahab ya ce.

"Bana tamtama akan abinda ka sanar da ni Malam Sallau,amma ina so don Allah ka taimaka mini domin kama Iliya hannu da hannu domin na ji daɗin hukunta shi akan abinda ya sa na aikata."

"Yauwaa Alhaji an zo wajen. Ina so gobe da safe a gaban Iliya ka tambayi Malam Mudan takardun nan da na nuna maka,da ka tambaya ka bar min komai a hannuna."

Sallama suka yi da Malam Sallau Abdulwahab ya koma cikin gida cike da nadama,a wannan ranar ya gane cewa lallai matansu sun yi ƙoƙari da suka riƙe zumunci suka ƙi ba wa ƴan gulma damar shiga tsakaninsu. Tunani ya fara yi ta yaya ma har ya bari wani bare zai raba shi da mutumin da ya fara taimaka masa a rayuwa? Duk dukiyar da ya tara yake alfaharin zamowarta tasa da taimakon Mudassir ya tara ta. A wannan daren kasa bacci Abdulwahab ya yi. Asuba na yi ya watsa ruwa ya yi alwala ya tafi masallaci. Bayan an idar da sallah kafin Mudassir ya fito daga masallacin Abdulwahab ya gudu gida,domin kunya yake ji ya haɗa ido da shi ballantana har su yi magana. Ya na kwanciya bacci mai daɗi ya ɗauke shi har Mudassir ya shirya ya samu Layuzah ya tambaye ta ko Abdulwahab ya farka kuwa? Sanar da shi ta yi bai farka ba,dan haka sai ya tafi kasuwa da zummar idan Abdulwahab ya je zai bashi takardun a can.

Abdulwahab na farkawa Layuzah ta sanar da shi zuwan Mudassir,shiru ya yi kamar wanda ruwa ya cinye,gani yake yi kamar kowa ya san abinda ya aikata a gidan. Sai kawai ya ɗakko mata zancen zuwan Gwaggo Kande domin ta kula da ita har ranar da za ta haihu. Cike da jin kunya Layuzah ta ce.

"Ni dai gaskiya bana son Gwaggo Kande ta zo ta karɓi haihuwa ta. Dama ina a can Kuran ne idan ta karɓi haihuwar babu komai,amma ina a nan gaskiya ni dai a barta kawai,idan na sauka lafiya sai ta zo ta dinga yi wa jariri wanka."

Murmushi ya yi ya shafa ƙaton cikin nata da suke wa laƙabi da cikin ƴan biyu. Ba tare da ya ce komai ba ya ƙarasa shirin fita ya buga babur ɗinsa ya wuce kasuwa.

Ko da ya isa ya tarar da manyan shagunan nasa guda huɗu dake jere da juna sun ɗauki harami ana ta cinikayya. Shigarsa wajen ke da wuya yaransa suka je suna ta gaishe shi yana amsawa. Malam Sallau dake zaune a gefe ma ya gaishe shi yana kallon Mudassir dake zuwa shagon hannunsa riƙe da jakar bakkonsa da yake saka kayansa a ciki. Ya na zuwa ya fara gaishe da Abdulwahab wanda sai a wannan lokacin ya gane irin sauyawar da ya yi ashe ba kaɗan bace. Su da suke caccafkewa da abokinsa kuma amininsa su zauna a waje ɗaya,yau shi ne Mudassir ke risinawa ya na gaishe shi a ɗarare gudun kada a ce ya yi wani laifin. Nan take ƙwalla ta taru a idanuwansa yana jin kamar ya kurma ihu. Da ƙyar ya danne abinda ke taso masa a rai ya ce.

"Aboki ina takardun da Man Sallau ya baka jiya ka bani."

Cikin rawar jiki Mudassir ya isa gaban Abdulwahab ya na duba jakarsa ya hau neman takardun. Wani irin tausayinsa ne ya kama Abdulwahab. Kafin ya dawo cikin hayyacinsa Iliya ya isa gaban Abdulwahab ya ce.

"Ai Alhaji ba zai iya baka waɗannan takardu ba. Domin kuwa jiya ya zaci na wuce gida sai wani mutum ya zo ya bashi takardun shi kuma mutumin ya bashi maƙudan kuɗaɗe. A nan ne ma na ji shi Malam

10 / 17