Author : HAMIDA SANUSI AHMAD Category : Romantic Hausa Novels
Mudan ya na cewa ai shi ne silar arziƙinka to shi ma zai je ya kafa kansa ya gaji da wahalta maka."
Salati Mudassir ya yi ya duƙar da kansa sai ga hawaye na zuba daga kwarmin idanuwansa. Ya kasa kare kansa domin bashi da kalaman da zai yi amfani da su ya kare kan nasa. Addu'a ya dinga yi Allah ya kare masa mutuncinsa kada ya ba wa maƙiya damar tozarta shi a gaban amininsa. Iliya na gama zuba miyagun kalamansa a kunnen Abdulwahab ya ji saukar mari ta inda bai taɓa zato ba. Idanu ya zaro waje ya na kallon Abdulwahab da ya miƙe tsaye ya na huci kamar wani zaki. Cikin tsananin ɓacin rai ya ce wa Iliya.
"Ka je na sallame ka daga aiki a ƙarƙashi na,sallama ta har abada Iliya. Sannan ka sani idan har baka nemi tafiya akan abinda ka aikata ba alhakin bawan Allah'n nan da ni kai na ba zai barka ka ji daɗi a rayuwarka ba. Sallau maza ku je da shi ya ɗakko takardun filaye na ya baka ka kawo min,ka karɓe duk wani makullin shago na da yake wajensa. Ga wannan kuɗin sallamar ka ne,domin ba zan riƙe maka haƙƙinka ba."
Kuɗi ya ƙirgo a drawer dake kusa da shi ya miƙa wa Iliya da kunya ta gama baibayewa. Malam Sallau kuwa a gaba ya saka shi suka shiga shagon masu aikin,nan fa Iliya ya hau duba kayansa ya na neman takardun da ya adana a cikin kayan amma bai gani ba. Dariya Malam Sallau ya yi sannan ya zaro su daga aljihunsa ya na kaɗa wa Iliya a gaban fuskarsa ya ce.
"An faɗa maka kai kaɗai ne ka iya makirci? Kalle ni nan ka gani Iliya. Duk makircinka na dame ka na shanye,sai dai ni makircina akan irinku yake aiki. Dan haka maza ka kwashe tsummokaranka ka ƙara gaba,ka yi wasa da damarka ta zamowa ƙaramin attajiri a ƙarƙashin mutumin da dukiyarsa bata rufe masa ido ba,baya kuma yi wa na ƙasa da shi mugunta."
Cike da nadama Iliya ya bar shagon da jakar kayansa ya na nadamar abinda ya aikata. Sai dai a yanda ya ga ran Abdulwahab ya ɓaci ya san ba zai taɓa iya tunkararsa ba ballantana ya bashi haƙuri ya mayar da shi bakin aikinsa.
A wannan ranar Abdulwahab kasa ba wa Mudassir haƙuri ya yi. Domin bashi da bakin da zai bashi haƙuri. Sosai ya shiga ƴar wasan ɓuya da shi,baya fitowa daga ɗakinsa sai ya tabbata Mudassir ya bar gidan. Sannan baya dawowa gidan sai ya tabbata Mudassir ya yi bacci. A hankali matansu suka fara gane akwai matsala a tsakanin mazajen nasu har suka zauna suka tattauna akan lamarin. Dan haka a daren ranar Ammabuwa ta turke Mudassir a ɗaki ta hau tambayarsa abinda ke faruwa tsakaninsa da Abdulwahab.Murmushi ya yi ya ce.
"Ohh mata kenan akwai ku da sa ido,to hasahenku da ke da ƙanwar taki bai zamo gaskiya ba. Kun manta shi yana haɗawa da aikin gwamnati bayan kasuwanci? Sannan shi aikin gwamnati kamar aikin noma ne,a damina manomi ya fi aikatuwa da rashin lokacin kansa. Bayan damina ta ja baya ya girbe amfanin gonarsa sai aiki ya sauƙaƙa a gare shi. To haka lamarin yake a wajen Aboki. Ya sanar da ni cewar aiki ya yi masa yawa a office shi yasa kuke ganin kamar ba ma magana sosai kamar da."
Ajiyar zuciya mai ƙarfi Ammabuwa ta sauke kafin ta ce.
"Har na ji wani irin daɗi a raina Baban Maheer da ba saɓani kuka samu da Yayana ba. Allah Ya ƙara haɗa kammu ya bamu zama na aminci da amana."
"Amin Ya Allah Ummu Maheer."
Daga nan suka sauya salon hirar tasu har Ammabuwa ta samu bacci. Waje ya samu ya zauna domin kuwa yana so a wannan ranar ya kawo ƙarshen wasan ɓoyon dake gudana a tsakaninsa da abokinsa. Ya na nan zaune gyangyaɗi na ɗibansa ya ji dawowar Abdulwahab. Cikin sauri ya buɗe ƙofar ɗakinsa a hankali ya fita. A lokacin da Abdulwahab ya gansa sai da ya razana. Da sauri ya kafe babur ɗinsa ya ce.
"Ah Aboki baka yi bacci ba?"
"Ina fa zan yi bacci ƴan jarida sun fara ɗaukan rahoto akan irin zaman da muke yi da ni da kai a gidan nan?"
Cikin rashin fahimta Abdulwahab ya ce.
"Ƴan jarida kuma? Wa ya basu labarin abinda ya faru?"
"Mu je ƙofar gida mu tattauna."
Jiki babu ƙwari Abdulwahab ya bi bayan Mudassir suka je ƙofar gida suka zauna a dandamalin dake ƙofar gidan nasu. Shiru ne ya ratsa a tsakaninsu kafin Abdulwahab ya buɗe baki ya ce.
"Na rasa da wacce fuska zan kalli idonka na baka haƙuri akan abubuwan da na dinga yi maka a baya. Don girman Allah abokina ka yi haƙuri akan dikkan abinda ya faru a tsakaninmu. Har yanzu na kasa yafe wa kaina irin kallon da na dinga yi maka,da tozarci tare da kyarar ka da nake yi ma a kasuwa duk kuma a gaban mutane."
Murmushi Mudassir ya yi ya ce.
"Ban haƙurin ka ya karɓu Aboki,ina so ka sani tun kafin ka bani haƙuri na yafe maka,domin na san cewa zuciya bata da ƙashi,zama kuma ya gaji haka,zo mu zauna ne,kuma zo mu saɓa duk zaman da za ka ga ba a samun saɓani komai ƙanƙantarsa to ka bincika ɗaya yana munafurtar ɗaya ko yana yi masa zagon ƙasa. Sannan abinda ka aikata ai ba laifinka bane ziga ce irin ta maƙiya kawai ta shiga zuciyarka kai kuma ka yi aiki da ita."
"Hakane Aboki. Ka na da kyakkyawar zuciya. Allah Ya ƙara mana haƙurin zama da juna ya kare mu daga sharrin shaiɗanun mutane. Malam Sallau shi ne ya same ni har gida ya min bayanin komai,sannan ya yi min nasiha akan ruko da zumuncin da muka gina tin kafin wannan lokacin."
"Da yardar Allah sai mun samu lada da Aljannar da Allah ke ba wa bayinSa da suka yi zumunci dominSa Abokina. To wai ni ina ka je yau da na ga ka fi kowanne lokaci jimawa a waje?"
"Kura na je na gaida mutanen gida na kuma ga Salma. Na so na taho da ita Gwaggo Kande ta hana, ta ce sun kusa jarabawar common entrance na jira har ta gama sai na ɗauke ta ta min hutu mai yawa. A nan nake samun labarin wannan sakarar Samira ta gaji da jira na ta yi aure."
Dariya Mudassir ya yi sannan ya ce.
"Ai kuwa ka ga da ka aure ta ta gyara wa shagwaɓaɓɓiyar matarka zama a gidan nan."
"Allah Ya yi min tsari da auren Samira, a barwa matata shagwaɓarta ina son ta a haka."
Daga nan hira ta ɓarke a tsakaninsu har basu san dare ya tsala ba;sai da Mudassir ya fara hamma sannan suka shiga gida suka kulle kowa ya yi ɗakinsa.
Da asuba bayan su Abdulwahab sun tafi masallaci naƙuda ta kama Layuzah. Kafin su dawo ta haihu lafiya a gida da taimakon Ammabuwa. Ko da suka dawo suka ji kukan jariri sai suka yi zaton Maheer ne. Mudassir ne ya ce.
"Kai anya wannan kukan na Maheer ne kuwa? Ko dai Layuzah ce ta haihu?"
Da sauri suka ƙarasa shiga cikin gidan. Su na zuwa suka tarar da zannuwan da Ammabuwa ta goge jini da su a rataye a igiya tana ta shanya wasu. Gefe ɗaya kuma ga ƙatuwar tukunya nan ta ɗora ta na dafa ruwan zafin da za ta yi wa jariri da Mamansa wanka. Farinciki ne ya mamaye zuƙatansu sai suka hau godiya ga Allah suna tambayar abinda aka samu. Cike da murna Ammabuwa ta ce.
"Addu'a ta ce ta karɓu Maheer ya yi aboki shima kamar iyayensa."
Cikin tsananin farinciki Abdulwahab ya shiga ɗakin ya ga Layuzah kwance a gado ta tasa jaririnta a gaba tana kallo cike da so da ƙauna. Su na haɗa ido ta tashi zaune ta na miƙa masa jaririn da aka naɗe cikin zani. Hawayen farinciki ne suka sauka a kuncin Abdulwahab ya karɓi yaron ya yi masa kiran sallah,cikin rawar murya ya ce.
"Mahaifina Malam Musa ya yi takwara Layuzah. Ya Allah ka sa yaron nan ya yo gadon kyawawan halayyar masu sunansa. Allah ka yi masa albarka Ka raya mana shi akan tafarki madaidaici."
"Amin Ya Allah Baban Aabid."
Kallonta ya yi cike da tsokana ya ce.
"Tooo Aabid kuma?"
Kai Layuzah ta gyaɗa ta ce.
"Ƙwarai da gaske,ai na ji labarin yanda Abbanku yake da yawan ibada da dogaro ga Allah a wajen Gwaggo Kande. Shi yasa zan dinga kiransa da Aabid saboda shima ya yo gadon yawan ibada da tsoron Allah."
Waje Abdulwahab ya fita da yaron ya kai wa Mudassir tare da sanar da shi sunan da ya raɗawa yaron. Addu'a shima ya yi wa Aabid sosai sannan ya yaba da sunan da za a dinga kiransa da shi. Ruwa na tafasa Ammabuwa ta haɗa ruwan wankan jariri ta je ta karɓe sa a hannun iyayen nasa da ke ta murna. Tambayar Maheer Abdulwahab ya yi,sai Ammabuwa ta ce.
"Ai yau sarkin rikicin ya san ƙaninsa ya zo duniya ya zama babba. Ya na can yana bacci bai tashi ba."
Dariya suka yi gaba ɗayansu ta shige ciki ta fara yi wa yaro wanka. Ta na gamawa ta shirya sa da ɗaya daga cikin kayan jariran da Abdulwahab da Mudassir ke yawan siyo wa a duk lokacin da suka fita wata ƙasar ko suka shiga kasuwa suka gani. Ta na gamawa ta kai wa mazan jaririn ta kwashe wa Layuzah ruwan wanka suka shiga banɗaki ta yi mata wanka tsaf suka fito. Sosai Ammabuwa ta dinga mamakin yanda Layuzah ta jure ruwan zafi bata yi raki ba kamar yanda ita ta yi a lokacinta.
Gari na wayewa Abdulwahab ya aika Sallau can Kura ya taho da Gwaggo Kande. Da zuwanta ta karɓi aikin kula da wankan yaro da kuma Layuzah'n kanta.
Bayan suna Salma ta gama jarabawarta Malam Sallau ya je ya ɗakkota ya kawo ta gidan. Sosai ta dinga murnar ganin yaron. Bacci,wanka,sallah da cin abinci ne kawai ke raba ta da Aabid idan ta ɗauke shi. Lokacin da Gwaggo Kande ta zo komawa sai Salma ta kafe ba za ta bi ta ba har sai sakamakon jarabawarsu ya fito sannan za ta koma. Kan dole Gwaggo Kande ta koma ba tare da Salma ba. Ta na isa gidan bayan ta huta Malam Bala ya same ta har ɗaki riƙe da kwalin chewing gum,minti da goro yana washe baki. Cikin rashin fahimta Gwaggo Kande da ke ƙarasa ninke zanin kayan da ta cire a jikinta ta ce.
"Ah ah! Malam wannan kuma fa? Ko dai Mairo aka yi wa baiko da bana nan?"
Washe baki Malam Bala ya sake yi sannan ya ce.
"In banda abinki Kande nawa Mairon take? Ai yayarta aka ɗaurawa aure ɗazu a masallacin Juma'a. Liman har ma da manyan garin nan duk sun shaida kuma sun saka wa abun albarka."
Mamakin kalaman Malam Bala ne suka sanya Kande zama a bakin gadonta ta karɓi abubuwan da yake miƙa mata ta ajiye a gefenta sannan ta ce.
"Malam ka na ta yi min magana a duƙunƙune,dan Allah ka fito fili ka yi min bayani,domin ni dai a iya sani na Samira ce kawai ta girmi Mairo a gidan nan;kuma an yi mata aure. To wacece kuma Yayar Mairo da aka aurar babu baiko balle saka rana?"
"Ke dai ba kya cin ribar zance Kande. To auren Salma ta wajenki aka ɗaura yau a masallacin Juma'a da Rabi'u ƙanin mijin Samira."
Wani irin faɗuwar gaba da tashin hankali ne ya dirarwa Gwaggo Kande wanda ya sanya ta jin jiri na ɗibanta daga wajen da take zaune. Cike da tashin hankali ta kalli Malam Bala ta ce..........
MUGUWAR MACE.
NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✨✍️
PAGE 15.
Cikin tsananin ɓacin rai Gwaggo Kande ta kalli Malam Bala ta ce.
"Lallai kuwa za ka je duk masallaci ko ƙofar gidan da aka ɗaura wannan ƙaddararran auren a kunce shi;dan ba zan taɓa amincewa a cuci yarinya ƙarama a aura mata tsoho kamar Malam Rabi'u ba."
Tsayuwa Malam Bala ya gyara ya ce.
"Kayya! Kande wai dika-dika Malam Rabi'un nawa yake? Ƙanin ƙanin bayana ne fa."
A hasale Kande ta ce.
"Mutumin da ko za ka girme shi bai wuce ka bashi shekara uku zuwa huɗu ba shi ne yaron? Kada fa ka manta Salma bata wuce shekara sha biyu zuwa sha uku ba."
Cikin sauri Malam Bala ya ɗaga wa Kande hannu ya ce.
"To kin ga kenan ta yi gadon ki. Ai idan ban manta ba kema da waɗannan ƙananan shekarun aka aura min ke."
"Malam wancan zamanin da wannan da muke ciki akwai banbanci,sannan kuma lokacin da muka yi auren ina da ƙananan shekaru ai kai ma ba wani babba bane."
"Banbancin na menene Kande? Tuwon hatsin aka dena ci ko kuwa shinkafar? Ko kuma kwanciyar sunnar aka canja? Matan ne suka koma na gwal ko me? Bayan haka Kande indai da kara ba karaya ba ni ai uba nake a wajen Salma,a zato na zan iya zartar da komai a kanta. Dama Hasiye ta faɗa min idan kika dawo sai kin yi tijara na karyata ta saboda na sanki da biyayya. Ashe ta sauya zani ban sani ba."
"Malam babu zanin da ta sauya,har gobe da jibi ina nan a Kanden da ka sani mai yi maka biyayya akan dikkan umarninka matsawar bai saɓawa Allah ba. Amma wannan abinda ka yi ba zan taɓa yi maka biyayya akansa ba ballantana kara,yanda ka je aka ɗaura aren nan babu sanin dangin uwa da uban yarinya dole ka je a warware."
A hasale Malam Bala ya tsaya a gaban Kande ya na zazzaro mata ido waje ya ce.
"Ke ba na son shashanci fa. Wa ya faɗa miki dangin uwa da uba basu sani ba. A gaban kawunanta, Sarkin garin nan liman da duk wani mai faɗa a ji na ƙauyen nan aka ɗaura,kada ki so ki ga yanda akai ta saka miki albarka da ita kanta yarinya,ko babu komai kun yi taimakon musulunci "
"Ka ce haka mana Malam tinda an ɗaura wa yarinya aure da tuzuru. Ina son ka sani duk wani mummunan abinda ya sami Salma ba zan zauna da kai ba na gama auren ka kenan Malam. Habaa ta ya za a yi wa yarinya aure sai kace wata ƴar tsana? Idan gaskiya ne abun naka ai ka na da wata ƴar ka bashi mana,sai a haɗa ta da ƴar'uwarta gida ɗaya su yi zaman aure,amma ba wai a ɗauki marainiya a kai ta gidan da na san da biyu ka ƙulla auren dan kawai a cutar min da ita ne."
Ta na gama maganarta ta fito waje fuuuu cike da fushi. Karo ta yi da Hasiye da ke yi musu laɓe ta na jin duk abinda suka yi magana akai. Cike da borin kunya Hasiye ta tsugunna tana ɗaukan duk abinda hannuwanta suka hau kai. Murmushin takaici Kande ta yi ta ce mata.
"Na dawo na ga tuggu da munafurcin da kika ƙulla Hasiye,dan kuwa na sani sarai ke ce za ki zuga Malam ya yanke wannan mummunan matakin akan Salma. Ina so ki sani da yardar Allah Salma za ta ba ki mamaki. Sai kin yi nadamar wannan haɗin auren da kika yi ko ba jima,ko ba dade."
Harara Hasiye ta banka wa Kande ta tsirtar da yawu sannan ta ce.
"Eh ɗin ni ce nan matar da ta isa da miji da gida,uwar magada mai mulkin gidan Malam Bala. Har ke kin isa Ƴata ta nuna tana son auren jikanki ki hana ta? To bari ki ji Samira ba ta yi auren tsoho a banza ba,kema dole ne taki jikar ta je can ta ɗanɗani zama da sa'an ubanta. "
"Ba kanta farau ba Hasiye,kuma na tabbata ba za a gama akanta ba,dan ta auri tsoho ba shi ne yake nufin ƙarewar numfashinta ba. Kuma ina so ki dinga tinawa da mugunta dai fitsarin fako ce,kuma idan za ka gina ramin mugunta ka gina shi gajere."
Haka su Kande su ka dinga musayar yawu ita da Hasiye har ta ga rashin dacewar biye mata su yi ta hayaniya. Ɗaki ta shiga ta killace tsarabar da ta zo da ita ta zari mayafinta ta saka ta kulle ƙofarta ta nufi gidan Kawu sale. Ta na zuwa ta dinga doka sallama a tsakar gida domin ko ɗaki bata jin za ta iya shiga. Yanda suka haɗa kai da Malam Bala aka aurar da Salma ba da saninta ba dole ne su je duk inda za su je a warware wannan auren. Ta na nan tsaye Kawu Sale ya fito ya na suɗe hannu tare da haɗe su waje ɗaya ya murtsuke. Washe baki ya yi yana kallon Kande ya ce.
"Ah ah Gwaggo yau ke ce a gidan namu war haka?"
Harara ta banka masa sannan ta ce.
"Da abinda ya fi war haka ma za ka ganni Sale,tinda baku ƙulla gaskiya ba da kai da wancan azzalumin. Yanzu Sale amanar da aka bar mana ita kuka wulaƙanta? Ina laifin ku aura wa Salma matashi wanda ƙarfinsu zai yi ɗaya, kurum sai ku aura mata sa'an ubanta?"
Tsayuwa Kawu Sale ya gyara sannan ya tsotse haƙorinsa ya ce.
"Don Allah Gwaggo Kande ki yi haƙuri da abinda ya faru. Matsala aka samu gagaruma . Wato auren Malam Rabi'u aka fasa saboda yarinyar da zai aura iyayenta sun ji labarin Yayansa dika yara mata yake haifa,kuma yaran ne ke zuwa masa gona su yi duk abinda yaro namiji zai yi,watarana ma har marigayiyar matarsa yake ɗauka ya kai ta gona su yi aiki su dawo. A taƙaice dai sun ji ƙishin-ƙishin ɗin aikin gona da na gida ne ya yi ajalin matar wansa. To shi ne fa Malam Rabi'u da be taɓa aure ba hankalinsa ya tashi da jin wannan mummunan labari sai ya yanke jiki ya faɗi. Da ƙyar aka zuba masa ruwa ya farfaɗo aka kai shi can asibiti aka saka mas ruwa. Ni dai ban san ya aka yi ba bayan kwana biyu an tashi sallar Juma'a sai ga Malam Bala ya zo muna tare da Sarki a idar da sallah ya ce wa Malam Rabi'u ya bashi ƴarsa Salma ya aura idan yana so."
"Shine kuka amince ba tare da yin tunanin zaluntar yarinya marainiya da ake son a yi ba ko?"
Kai Kawu Sale ya sosa ya na faɗin.
"A yi haƙuri Gwaggo ƙaddara dai ta riga fata yanzu."
"Humm Allah Ya kyauta,gobe da sassafe zan koma