Author : HAMIDA SANUSI AHMAD Category : Romantic Hausa Novels
Kano na sanar da ɗan'uwanta duk abinda kuka ƙulla."
Gaban Kawu Sale ne ya faɗi,nan take nadamar ƙin hana auren Salma da Malam Rabi'u ta kama shi. Sai dai ya baro gini tin ran zane. Kande gida ta koma ta na matsar hawaye tare da hango irin tarin kalubalen da Salma za ta fuskanta a cikin wannan auren. A haka ta kwana da zullumi da fargaba. Washegari da safe ta shirya tsaf da nufin tafiya Kano ta sanar da Abdulwahab abinda yake faruwa. Sai dai lokacin da ta je ta sanar da Malam tana neman izininsa na zuwa Kano sai ya ce.
"Babu inda za ki je ki hure wa yarinya kunne ta bijire wa mijinta. Nan da jibi Hasiye da matar Sale za su je su yi barka sannan su taho da ita."
Hawayen da Kande ke ta riƙewa kada su zuba a gaban maƙiyinta Malam Bala ne suka zubo mata. A daren jiya ta raɗa masa sunan maƙiyi,domin kuwa babu wanda zai aitaka abinda Malam Bala ya aikata a kira shi da masoyi. Ba dan ta so ba dole ta haƙura ta bar ɗakin nasa ta koma ɗakinta ta na sharar hawayen takaici.
A kan idonta Hasiye ta dinga rawar kan zuwa Kano. Tin da safe ta tsefe kanta ta je aka rangaɗa mata sabon kitso,sai kuma ta ɗaura jan lalle a ƙafarta da dare. Gari na wayewa Hasiye ta sheƙa wanka ta saka atamparta sabuwa da suka ci bikin Suwaiba da ita ta fito ta na kallon kanta a ƙaramin madubin hannu ta na gyara zaman mayafinta a kafaɗarta. Washe baki Malam Bala ya yi ya ce.
"Har an fito kenan?"
"Allah Ya yarda Malam. Tinda a yau za mu je mu dawo a yau,ai gwanda mu gaggauta mu yi abinda ya kamata."
"Haka ne Hasiyatu matar fir'auna,waii matar Malam Bala. Kin ga kyan da kika yi har ya ruɗa ni zan sauya miki sunan miji. To ga wannan a yi na mota ko?"
Hannu ya sa a aljihu ya zaro kuɗin mota ya bata yana dariyar samun nasara. Har cikin ransa yake jin daɗin rama wulaƙancin da Abdulwahab ya yi masa na ƙin auren Samira. Sosai ya yaba da shawarar da Hasiye ta bashi na aura wa Malam Rabi'u Salma dan yin ramuwar gayya. Ɗaki ya koma kai tsaye ya zauna ya fara karya wa.
A tasha su Hasiye suka haɗu da matar kawu Sale. Gaisawa suka yi da juna suka samu mota suka shige. A mota banda zuzuta gidan da su Abdulwahab suke a Kanon babu abinda Hasiye take yi,ita a dole ta san kan waje Matar Kawu Sale bata sani ba. Haka suka dinga hira har suka isa garin Kano. Su na isa suka sauka daga mota suka samu taxi suka shiga. Da kwatance motar ta kai su har gidan Abdulwahab. Su na zuwa suka hau buga ƙofa suna faɗin.
"Ohh mutanen birni,su fa yanzu bacci suke yi ko?"
Hannu Hasiye ta sa ta sake buga gidan da ƙarfi. Su na nan tsaye wani ƙaton mutum ya buɗe gidan jikinsa ko riga babu ya kalle su ya na muzurai ya ce.
"Kai ku su wanene kuke damun mutane?"
Yawu Hasiye ta haɗiya a tsorace ta ce.
"Wajen Jikana Abdulwahabu muka zo."
"Waye me wannan sunan kuma? Malama ku ware daga nan nan gidana ne ni ban san wani Abdulwahab ba."
Ƙirji Hasiye ta dafe ta ce.
"Kai ɗannan don Allah kada ka yi mana wasa..."
A hasale mutumin ya zabura ya ce.
"Na yi miki kama da abokin wasanki ne?"
Kai Hasiye ta girgiza ta ja hannun Balaraba Matar Kawu Sale suka fara tafiya. Cike da tsananin damuwa Balaraba ta ce.
"To ke da Hasiye kin san baki san gida ba kika rakito mu muka taho ?"
Kai Hasiye ta karkace ta ce.
"Aradun Allah wannan ne gidan. Bayan Abdulwahab ya kama haya a Kano sun dawo shi da matarsa na biyo Kande da za ta kawo musu ziyara. Tin daga nan ko shigowa na yi siyayya sai na biyo na ci na sha na yi warkajami na da abun duniya nake wucewa gida."
"To da dikkan alamu sun canja gida,ko kuma wani abu ya sami Abdulwahab ɗin amma Gwaggo Kande bata sanar da kowa ba."
"Idan ina faɗa muku muguwa ce sai ku dinga ganin laifina,to ai gashi yanzu ta baku misali."
Haka suka ɗauki laifi suka ɗora akan Gwaggo Kande gaba ɗaya. Daga ƙarshe sai suka dinga bi gida-gida suna tambayar inda za su samu gidan Abdulwahab amma basu samu ba. Ganin lokaci ya tafi bar an yi azahar basu dace ba,sai kawai suka yanke shawarar komawa Kura idan Kande ta sanar da su sabon gidan Abdulwahab ɗin sun dawo....
*Ku yi haƙuri bani da caji ne shi yasa kuka ji ni shiru.*
MUGUWAR MACE.
NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✨✍️
PAGE 16.
A matuƙar gajiye su Hasiye suka isa gidan Malam Bala da ke ta zarya a tsakanin cikin gidan da ƙofar gidan Malam Rabi'u dan ganin dawowarsu. Bai jima da fita ba ya dawo ya tarar da Hasiye zube a tsakar gida ita da Balaraba wadda ta kasa ƙarasawa gidanta ta ce sai ta huta ko zuwa dare ne; tinda ba ita ke da girki ba yara sun raka ta. Fuskar Malam Bala ɗauke da mamaki ya hau leƙen ƙofar ɗakin Kande ko zai hango takalman Salma amma ya ga wayam. Kallon Hasiye ya yi ya ce.
"Mutanen Kano an shawo rana,ke Mairo je ki kawo musu farau-farau mana,da dikkan alamu sun yi aswaki da kaji a birni."
Tsaki Hasiye ta ja tana zabga wa Malam Bala harara. Bakinta da ya bushe ta lashe da harshenta da ya ƙafe babu ɗigon yawu a jiki ta ce.
"Ai idan bamu ci kaji ba mun ci uwar wahala. A gaskiya Malam Baƙin halin Kande ya munana babu na biyun ta a mugun hali a kaf cikin ƙauyen nan namu da kewaye."
Waje Malam Bala ya samu ya rakuɓe a jikin gini ya na kallon Hasiye da ta amshe kwanon shan ruwa a hannun Shamsiyya ƙaramar ƴarta ta kwankwaɗe ko kurɓa daya bata rage ba. Tana sauke numfarfashi ta ce.
"Wai ka san kuwa yaron nan Abdulwahabu ba ya gidansa da na sani amma bata damu ta sanar da mu ba;duk da cewa ta san can za mu je mu taho da matar mutane?"
Ido Malam Bala ya zaro waje ya dafe ƙirji sannan ya ce.
"Ki bari dan manzo Hasiye! Wai ki na nufin Abdulwahabu ya sauya muhalli daga wanda muka sani? Ki ce arziƙi ya ci uban na da. Ohhh yanzu fa da shikenan Samira ce a gidan take ta dandalar arziƙi."
"Hummm ai Kande ba macen da za a raɓa a dandali arziƙi bace Malam,ta nuna maka iyakar ka. Yau in da ka ga azabar tafiyar da muka ci da ƙafafuwan nan namu sai ka tausaya mana. Wani ƙato ma ce wa ya yi idan bamu bar ƙofar gidan ba zai lakaɗa mana na jaki,kan dole mu kai ta zagaya unguwar har maƙotan unguwannin da basu da nisa muna tambayar gidan Abdulwahab mai siyar da hatsi,amma bamu samu ba. Yanzu don Allah Malam dubi yanda ƙafar Balaraba ta yi haushi kamar ta me tsohon ciki."
Sannu suka dinga jera wa Balaraba da ke ta kurɓar farau-farau. Kande kuwa ta na ɗaki ta na jin su bata tanka musu ba har aka kira sallar magariba ta fito dan yin alwala. Ko kallon inda suke bata yi ba ta ɗauki butar ta ta zaga. Ta na fitowa ta hau yin alwala ba tare da ta kalli inda suke ba,Malam Bala ne ya isa wajenta a hasale kamar zai kifa. Cike da matsanancin fushi ya warce butar ya yi wurgi da ita ya ce.
"Wato ma kin mayar da mutane mahaukata ko? Ki na fa kallo da jin abinda ke faruwa a gidan nan,amma ko sannu ba za ki iya buɗe baki ki yi wa bayin Allah'n nan ba da suka tafi ɗakko Salma dan a kaita gidan miji ta raya sunnar ma'aiki."
Shiru Kande ta yi bata tanka masa ba ta miƙe daga tsugunnon da ta yi ta ɗakko butarta ta wanke ta sake zuba wani ruwan ta hau yin alwala. Ƙwafa Malam Bala ya yi ya ce.
"To ki buɗe kunnen ki da kyau ki jini. Zan je wajen yaransa da ke kai masa kaya Kanon da kaina mu je har shagonsa,ni da kai na zan je na taho da Salma idan zuciya za ki haɗiya sai ki yi magana a baki ruwa ki kora."
Murmushin takaici kawai Kande ta saki ta miƙe tsaye ta wuce ɗakinta. Ta na shiga hawaye ya zubo mata,nan da nan ta hau tuna irin rayuwar da suka yi da mijinta a baya. Rayuwa ce mai cike da so,ƙauna,tattali,kulawa da mutunta juna. Duk wani abu da zai ɓata mata rai baya son sa. Da yardarta da amincewarta ya auri Hasiye saboda ita bata taɓa haihuwa ba. Sai gashi tinda aka auro ta bata huta ba daidai da rana ɗaya. Gashi yanzu tsufa ya cimmata har ta dena al'ada ballantana ta sanya ran haihuwa. Zama ta yi a bakin gadonta ta rushe da kuka mai cin rai saboda ta tabbatar da cewa wani makircin da muguntar Hasiye ke ƙullawa ƙaramar yarinya kuma marainiya Salma. Gani ta yi kukan ba zai kai ta ko ina ba lokacin sallah na wuce wa. Sai kawai ta miƙe ta nufi saman abun sallarta ta gabatar da sallar magariba ta zauna tana ta addu'o'inta. A can tsakar gida kuwa Balaraba da ta gama cin tuwon dare sai ta miƙe ta na ɗingisa ƙafa ta ce.
"Bari na je na gaida Gwaggo Kande tinda na huta."
A bakin ƙofa ta coge ta ɗage labule ta ce.
"Barka da war haka Gwaggo,mun same ku lafiya?"
Ba tare da Gwaggo ta nuna mata halin da take ciki ba ta saki ranta ta amsa mata,su na gama gaisawa Balaraba ta ce.
"To ni na tafi sai da safe. Allah Ya sanya alheri ya ba su zaman lafiya. Idan amarya ta iso mun zo da su Tsahare da yaran."
"Uhumm Allah Ya kaimu to."
Gwaggo Kande ta faɗa ta na tunanin shin ita ce ƴar'uwarsu Kawu Sale ko kuma Hasiye da Malam Bala ne ƴan'uwansu? Ta na wannan tunanin ta ji yaran Hasiye sun tafi raka Balaraba da kwanon tuwo a hannunsu, wanda Mairo ce ta dafa ta zuba wa kowa nasa. Kallon inda aka ajiye mata nata ta yi sai ta ji ko sha'awar ci bata yi,tin safe farau-farau kawai take kurɓa saboda ɓacin rai. A haka Gwaggo Kande ta kwana cike da damuwa har safiya bata rintsa ba.
Da sassafe ta ji Malam Bala na yi wa Hasiye sallama ko ta ƙofar ɗakinta bai bi ba ballantana ya san ya ta kwana ya fice ya bar gidan. Kai tsaye babbar kasuwar Kura ya nufa inda ake ta hada-hadar loda hatsi a manyan motoci. Yaran Abdulwahab ya nema suka gaisa ya ce shi ma can wajen nasa ai ya nufa shi ne ya ce bari ya zo a rage masa hanya. Sanin matsayinsa a wajen Gwaggo Kande ne ya sanya su amincewa bayan sun gama lodi suka ɗauke shi a saman mota suka tafi da shi.
Su na isa Kano suka nufi Ƴankaba domin sauke wa Abdulwahab kayansa. Su na zuwa suka tarar da yaran shago na ta shara tare da ba da space domin kayan da za a kawo. Da taimakon matasan wajen Malam Bala ya diro daga saman motar ya ƙarasa gaban shagon Abdulwahab yana gaisawa da mutanen wajen. Malam Sallau ne ya sanar da shi cewa ai Abdulwahab bai iso ba sai rana ko yamma yake shigowa kasuwa. Malam Mudan ne kawai ke zuwa da safe amma kuma shi ɗin ma bai iso ba. Da sauri Malam Bala ya ce.
"Ni da da yanda za a yi a kai ni can gidan nasa ma ai da kun kyauta. Dama rashin sanin muhallin da ya koma ne ya sa na biyo ta nan."
"Ah bari to na jawo babur na kai ka gidan yanzun nan.'
Albarka Malam Bala ya dinga sanya wa Malam Sallau. Malam Sallau na jawo babur ya buga shi ya ce wa Malam Bala.
"Bismillah Baba mu je."
Cikin ƙanƙanin lokaci suka isa gidan Abdulwahab wanda ke tsaka da shirin fita office. Sallama Malam Sallau ya rafka sau uku,a na huɗun Mudassir ya fito ya na faɗin.
"Man Sallau kai ne a gidan namu war haka?"
Hannu Malam Sallau ya miƙa masa suka hau gaisawa,sannan Mudassir ya durƙusa ya gaida Malam Bala. Cike da fara'a ya ce.
"Shigo ciki mana Baba,ka tsaya daga waje? Aboki na ciki ya na shirin tafiya aiki,bari na sanar da shi zuwanka."
Sallama Malam Sallau ya yi musu ya koma kasuwa. Su na shiga ciki ya nufi parlourn da suke ajiye baƙi zai buɗe masa kenan Salma ta fito daga ɗakin Layuzah bayanta goye da Aabid. Gabanta ne ya yi mummunan faɗuwa har bata san sanda ta furta kalmar.
"Wayyo Allah na shiga uku." Ba.
Washe baki Malam Bala ya yi kamar bai ji ta ba ya ce.
"Lallai ne Salma zaman birni ya karɓe ki ƙwarai da gaske. Kin ga yanda kika murje kika ƙara kyau da girma kuwa? Kwanto min yaron na gansa."
Jiki a mace Salma ta isa gaban Malam Bala ta durƙusa har ƙasa ta gaida shi. Amsa wa ya yi cikin sakin fuska ya karɓi Aabid da ya fara kuka,sama Malam Bala ya wurga shi yana masa tawai kafin ya miƙa wa Salma yaron ya shige parlourn da aka buɗe dominsa. Ya na shiga ya kama baki ya na faɗin.
"Inyeee! wato bayan wancan gidan da suka shaƙe da kayan alatu suka barwa aljanu suna dabdalarsu a ciki a can ƙauye,nan ɗin ma sai da suka cika shi da dukiya. Lallai yaron nan ba ƙaramin baƙinciki ya yi mana ba. Yanzu da Samira ce a gidan nan ai mu da talauci sai dai mu hango shi a maƙota."
Zama ya yi a kujera ya ji ya lotsa saboda laushi,sai ya sake miƙe wa tsaye ya zauna da ɗan ƙarfi kamar wani ƙaramin yaro. Ya na nan yana zancen zuci da na fili Abdulwahab ya shigo parlourn cikin shirin fita office. Gaisawa suka yi cike da girmamawa sannan Abdulwahab ya ƙwala wa Salma kira ya ce a kawo musu abun karyawa shi da Malam Bala. Layuzah ce ta yi sallama riƙe da babban faranti ta shiga ta ajiye a tsakiyarsu sannan ta koma gefe ta tsugunna. Gaida Malam Bala ta yi tare da tambayar mutanen gida. Nan ya dinga shirga ƙarya ya na faɗa musu yanda Kande ta yi kewarsu har ta tashi da zazzaɓi ta na ta cewa a kawo mata Salma amanarta,shi yasa ya yi mata alƙawarin zuwa ya tafi da Salmar. Cike da tausayawa Layuzah ta tambayi jikin Gwaggo Kanden,Malam Ya ce da sauƙi,ya dai kula kawai kewar Salma ke damunta,da an kai mata Salma za ta ware,fatan samun sauƙi Layuzah da Abdulwahab suka yi mata ta miƙe ta fita ta basu waje.
Abdulwahab da kansa ya buɗe food flask ɗin masa ya zuba wa Malam Bala,sannan ya ɗauki kwanon miya ya zuba masa miyar gyaɗa da ta ji naman rago. Kunun gyaɗa Abdulwahab ya zuba masa a babban mazubi sannan ya saka madara da sugar mai yawa ya juya masa ya ajiye masa a gabansa. Yawun Malam Bala kamar zai zubo haka ya dinga magana yawun na tsartuwa. Babu ko bismillah ya danna hannu ya hau ci yana zuba surutu, a cikin surutun nasa ne yake sanar da Abdulwahab zai wuce da Salma gida idan ya bada izini. Ba tare da Abdulwahab ya kawo komai a ransa ba ya ce.
"Babu damuwa Baba,ai dama ko randa za ta tafi ta so ƙwarai ta tafi da Salman yarinyar ce ta ƙi amincewa."
"Ai sha'anin yaro sai shi,ka duba ka ga yanda suke da Kande,a gani na ai bai kamata ta ƙi binta ba ballantana har ga dinga nuna rashin jin daɗi dan za ta koma can,ta na abu sai kace wata wadda ake yi wa wani abun a can. Wa Salma take da shi yanzu dai a duniya da ya wuce kai da Kande? To sai kuma danginku na uwa da uba."
Murmushi kawai Abdulwahab ya yi ya ci gaba da cin abincinsa. A haka suka gama ba tare da kowa ya sake cewa komai ba. Sosai Malam Bala ya ci abincin nan har a ransa ya na tunanin da ace Abdulwahab zai ɗan fita da sai ya samu leda ya ƙulle sauran.
Kiran Salma Abdulwahab ya yi ya ce ta haɗa kayanta ta bi Baba. Cikin kuka ta tashi ta koma ɗakin da ta sauka ta fara haɗa kayanta. A haka Layuzah da Ammabuwa suka same ta tana kuka. Tsaraba sosai suka haɗa mata sannan Layuzah ta rungumeta ta ce.
"Ki yi shiru ki dena kuka ƙanwata. Na yi miki alƙawari a Kura za mu yi yawon arba'in saboda mu nuna wa dangi Aabid. Ina komawa kuma zaki tattaro ki dawo waje na har sai mun yi watanni biyu ko uku sannan za mu dawo."
Ammabuwa ce ta kalli Layuzah ta ce.
"Inyee ashe kun gama tsara bari na ni kaɗai a gidan ba tare da kun sanar da ni ba ko?"
"Haba ke kuwa ai kema kin san dole na sanar da ke,yanzun ma maganar ta zo ne ba tare da shiri ba."
"Humm shikenan Allah Ya nuna mana lokacin."
"Amin Ya Allah."
Da wannan lallashin Salma ta saki ranta ta fito saɓe da jakarta da su Layuzah suka shaƙe mata ita da kaya. Malam Bala ne ya fito daga parlour ya na ta tura hannu a aljihu yana zuba wa Abdulwahab godiya kamar zai kwanta. Shi kuwa sai ya bi bayansa kawai yana kallon Salma tare da karantar yanayin da take ciki. Ya riga ya gama tsara yanda zai ɗauke ƙanwarsa da zarar burinsa na gina katafaren gidan da za su tattare su koma ya cika.........
MUGUWAR MACE.
NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✨✍️
*Yanzu muka fara wannan labari na MUGUWAR MACE mai cike da sarƙaƙiyar rayuwar zaman aure,makirci,butulci,sihiri,tare da cikakken ilimin zaman duniya. Idan ki na son a ci gaba da yin wannan tafiya tare da ke sanya 1k ɗinki ta wannan account ɗin 9031416423 Opay Hamidah Ahmad Sanusi. Sai ki tura shaidar biya ta 09031416423. Don girman Allah idan har kin san za ki siyi novel ɗin nan ne da niyyar ki yaɗa shi a group ɗin da idan kika bari suka siya a waje na nima zan samu alkhairi to ki yi haƙuri