Author : HAMIDA SANUSI AHMAD Category : Romantic Hausa Novels
mai ƙarfi sannan ya ce.
"To sai da safe,ina fatan kin san inda bayi yake. Dan bana so ina bacci ki katse ni ki ce za ki zaga,ni da kika ganni idan ina bacci ba a tashi na."
Kai kawai Salma ta gyaɗa masa ba dan ta san akan me ta gyaɗa kan ba. Ita dai babban buri da fatan ta bai wuce na ta ganta ta keɓanta ita ɗaya ba ta samu damar yin kukan da ke danƙare a ƙirjinta. Waje Malam Rabi'u ya fita ya nufi wani ɗaki dake kallon na Salma ya buɗe da makulli ya shiga. Fitilar tocilan ya kunna ya ke haska ɗakin da ita, daga nesa Salma ke hango Malam Rabi'u ya na cire babbar rigarsa,gabanta ne ya faɗi sai ta yi saurin kawar da kanta gefe ta sake takure wa a waje ɗaya. Salma bata da ilimi ko na sisin kwabo akan rayuwar aure,a bakin su Mairo da ƙawayenta ne ta ji wasu abubuwan a lokacin da aka barsu tare. Babban buri da fatanta bai wuce Allah Ya sa kada Malam Rabi'u ya zamo daga cikin ƴan isakan mutanen da ke taɓa jikin ƙananan yara ba. Wani irin kuka ne mai cin rai ya turniƙe ta. Nan take ta hau yinsa ta na faɗin.
"Gwaggo don Allah ki zo ki taimake ni tsoro nake ji."
Haka ta dinga kuka a hankali ta na toshe bakin ta gudun kada wani ya ji ta. Ganin hasken ɗakin Malam Rabi'u ya mutu ne ya sanya ta miƙe wa a hankali ta rufe ƙofar nata ɗakin da sauri. Wani irin tsoro ne ya ke shigarta a hankali. Gado ta haye ta takure a waje ɗaya ta na jin kamar ta ɓace ta ganta a ɗakin Kande. A haka bacci mai daɗi ya ɗauke ta.
*************************
A ɓangaren su Abdulwahab kuwa sai ƙarfe goma na dare suka shiga cikin garin Kura. Su na isa Mudassir ya kafe sai sun je gidan Malam Bala a daren an yi wacca za a yi. Da ƙyar Abdulwahab ya danne shi ya bashi baki kan su bari safiya ta waye a yi komai a ilmance,domin ya kula faɗa da tashin hankali ba zai bashi abinda suka zo nema ba.
A daren suka shiga cikin kasuwa suka samarwa kansu abinda za su ci suka koma gida. Abdulwahab wanka ya yi ya gabatar da shafa'i da wutiri kafin ya nemi waje ya kwanta. Malam Sallau kuwa da Mudassir na nan zaune su na hira kamar ba su ne suka sha gajiya tuɓus ba akan gyaran mota
Washegari da sassafe bayan sun dawo daga masallaci Abdulwahab ya riga su shiga wanka,ya na fitowa Mudassir ya watsa ruwa ya fito. Malam Sallau kuwa gidan su na gado ya wuce dan ƴan'uwansa basu san ya shigo gari ba a daren jiyan.
Ko karya wa ba su tsaya yi ba suka nufi gidan Malam Bala. Su na zuwa suka yi sallama a bakin ƙofa kafin Abdulwahab ya sa kai ya shiga gidan kai tsaye. Hasiye da ke bakin murhu ta na hura wuta ce ta fara arba da fuskar Abdulwahab da ya tamke ta tamau kamar bai taɓa dariya ba. Yaƙe ta fara yi ta hau ƙwala wa mijinta kira da duk wanda sunan sa ya shiga bakinta. Sai take jin ba za ta iya motsa wa ba kada Abdulwahab da ya fusata ya sa ƴan sanda su harbe ta.
Kai tsaye ɗakin Gwaggo Kande Abdulwahab ya shiga. Zaune ya tarar da ita akan abun sallah idanuwanta sun koɗe sun yi jawur saboda kuka. Ta na ganinsa ta sunkuyar da kanta ƙasa ta fashe da wani sabon kukan da yake jinsa a cikin ransa. Durƙusawa ya yi a gabanta ya kamo hannuwanta ya ce.
"Gwaggo ki kalle ni,ki dena saukar da kanki ƙasa kamar wadda ta aikata wani laifi."
Cikin kuka Gwaggo Kande ta ce.
"Na aika babban kuskure Abdulwahab. Na yi nadamar zamowata matar Malam. Ji nake yi kamar na mutu saboda baƙinciki. Ina soyayya da tausayin da Malam ya nuna min a tsawon rayuwarmu? Me ya sa ya zaɓi ya ƙuntata wa zuciya ta a cikin ƙanƙanin lokaci irin wannan? Salma ita ce farinciki na ya kuma san da hakan,sai gashi ya yi amfani da ita wajen rusa wannan farincikin nawa na shekara da shekaru kamar wanda dama can yana jin haushi na. Babbar damuwata yanzu bata wuce zaman Salma da Samira a waje ɗaya ba,Samira bata ƙaunar Salma ko kaɗan,tun su na nan gidan ta saka ta a gaba ban dai taɓa faɗa bane saboda nima bana bari idan ta yi mata abu,to yanzu da suke su kaɗai wa zai rama mata idan Samira ta zalunce ta?"
"Allah shi ne zai rama mata Gwaggo,ina so ki dena damuwa dan ba laifinki bane abubuwa suka kasance a haka. Na san laifi na ne ya shafi Salma,ko kin manta ni ne na ƙi auren ƴarsu? Shi ya sa suka biyo ta nan dan su rama abinda na yi musu."
A hasale Mudassir dake tsaye yana kallon su ya ce.
"To ana so dole ne? Wa ye ya basu dama da ƴancin aurar da yarinya ƙarama babu izinin magabatanta?"
Muryar Malam Bala ce ta daki dodon kunnen Mudassir dake tsaye a bakin ƙofa;kamar saukar aradu.
"Ni ne nan na ba wa kai na izinin aurar da ita,domin a ƙarƙashi na take,idan tarbiyyarta ta yi kyau ni ne,idan tarbiyyarta ta ɓaci ni ne. Me ya sa lokacin da nake kula da ita cinta,shanta,suturarta da duk wani abu da ya shafi rayuwarta baku ce wa ya bani izinin yin hakan ba,sai yanzu da na ga dacewar na aurar da ita ga mutumin da na san zai kula da ita ko bayan ranmu shi ne na yi laifi?"
"Tsohon da ko yau ana iya sanar da mutuwarsa kake maganar zai kula da Salma ko bayan ranmu? Kai Malam ka fa yi son zuciya dole ne kuma a warware wannan auren ko kana so ko baka so."
"Kai kuma a wa da kake ta baloƙoƙo kamar wani kwarton ƙadangare?"
A hasale Mudassir ya isa gaban Malam Bala yana huci kamar zai kai masa duka,sosai hakan ya tsorata Malam Bala da Hasiye da ke laɓe a jikin labule ta na sauraron duk abinda ke faruwa. Baya Malam Bala ya ja Mudassir ya ƙara binsa ya na zaro ido waje,ji yake yi ba dan tsufan Malam Bala ba da tini ya ɗaga shi sama kamar yanda suke wa buhun shinkafa ya lafta shi da ƙasa. Sai da Abdulwahab ya gama lallashin Gwaggo Kande da bata baki sannan ya fito ya tarar da fusataccen amininsa da Malam Bala a tsaye carko-carko kamar zakarun dake shirin kacame wa da dambe. Tsakiyar su ya shiga ya raba kallon kisan kan da Mudassir ke bin Malam Bala da shi. Sassanyar ajiyar zuciya Malam Bala ya sauke ya yi gyaran murya. Kafin ya ce wani abu Abdulwahab ya ce.
"Na ji labarin a gaban sarkin garin nan aka ƙulla auren Salma da Tsohon da ka zaɓa mata ko?"
Da sauri Malam Bala ya ce.
"To abinda Sarkin ne ma ya wakilci ɗaurin auren tare da sanya masa albarka? Ai kada ka...."
Katse masa hanzari Abdulwahab ya yi ya ce.
"To ya kamata mu je gaban sarki domin a warware abinda aka ƙulla babu son yarinya da danginta."
Ya na gama magana ya yi gaba, Mudassir kuwa sai ya ƙi tafiya ya tasa ƙeyar Malam Bala a gaba suka mara wa Abdulwahab baya. Su na zuwa fada sai suka tarar da mutane ana ta kwasar gaisuwa a wajen sarki ciki har da Malam Rabi'u da Malam Jamilu Yayansa. Su ma zubewa suka yi suka kwashi gaisuwa,daga nan sai Abdulwahab ya gabatar da kansa da kuma ƙorafin da yake tafe da shi. Malam Rabi'u da ke bin su da kallo tin shigowarsu fadar ne ya saki murmushin da yake dabi'arsa ya sunkuyar da kai,kalmar tsoho da ake yawan kiransa da shi tun da ya auri salma ta na yi masa ciwo a rai;ba dan be yarda shi ɗin tsoho bane,amma kafin ya aure ta abokansa kullum yabon kyan jikinsa da yanda jikin nasa baya nuna shekarunsa suke yi,wasu ma sai suka ce ko dan be yi aure bane shi yasa tsufansa ƙin bayyana,wasu kuma suka ce aljanar da ta aure shi ne take son ganinsa da yarinta shi yasa take sabunta masa fatarsa duk shekara,kwatsam sai gashi auren Salma ya jawo masa tuni akan shi ɗin fa tsoho ne da ya yi jika da ita. Kamar daga sama ya ji sarki na gabatar da shi a matsayin mijin Salma. Murmushin dai ya sake sakar musu ya miƙa wa Abdulwahab hannu suka gaisa, Mudassir kuwa kawar da kai ya yi yai kamar be ga hannun Malam Rabi'u ba. Janye hannunsa Malam Rabi'u ya yi yana murmushi ya koma mazauninsa. Bayan sun gaisa Sarki ya ce.
"To Alhamdulillahi. Kamar dai yanda kowa ya sani a garin nan kaf Malam Rabi'u ya sha wahala wajen neman matar aure,tausayi da kuma zaman amana tare da ceton rai ne ya sanya Malam Bala baiwa ƙanin amininsa auren Salma. Domin kuwa a ranar da aka fasa aurensa a karo na barkatai suma ya yi anan saboda damuwa,dan haka ina mai roƙon ku da Allah ku kwantar da hankulanku,ku bar wannan aure ya rayu domin bamu san alkhairin da Allah ya jefa a cikinsa ba."
Cikin sauri Malam Bala ya tari numfashin Sarki ya ce.
"Kuma shi irin wannan auren Allah Ya baka yawan rai,idan mutum ya matsa sai an raba sai Allah ya raba shi da rayuwarsa gaba ɗaya."
Harara Mudassir ya danƙara wa Malam Bala ya yi ƙwafa. Shi dai har a wannan lokacin ransa bai risina ba,nasiha sosai Sarki ya yi musu wadda daga ƙarshe ta ratsa su ta sanya su yin haƙurin dole ba dan sun so ba. Har gidan Salma Malam Rabi'u ya kai su,su na zuwa suka tarar da ita ta na cin fuffuken kazar daren jiya da bata ci ba,duk da cewa sai da Samira ta shiga ta ɗebi mai yawa ta na faɗin.
"Abunka da mai juna,ina zaune jikina ya bani akwai abun motsa baki a nan,to gani na zo a bani kason maƙotaka. Sannan daga yau idan aka kawo miki abun motsa baki ko na kari ki tabbata kin ajiye min na zo na taɓa nima,idan ba haka ba zan yi miki azabar da tunda uwarki ta haife ki baki taɓa ganin an yi wa wani irinta ba."
Miƙa mata ledar gaba ɗaya Salma ta yi ta ɗebi son ranta ta bar mata wajen da babu wani nama sosai. Da sauri Salma ta ture ledar dake gabanta ta nufi Yayanta ta rungume shi ta sanya kuka mai taɓa zuciya. Abdulwahab rungume ƙanwarsa ya yi a jikinsa sosai yana jin kamar ya raba jikinsa biyu ya saka ta ciki. Ji yake yi sam be bata rayuwa mai inganci ba kamar yanda ya kamata,sai gashi an datse mata ƙuruciyarta ta hanyar aura mata tsoho. Da sauri Mudassir ya fita ya na sharar ƙwallar tausayawa Salma. A ƙofar shiga sashen Salma ya gamu da Malam Rabi'u ya na ba da kuɗi a siyo wa Salma abun kari. Har ƙasa Mudassir ya durƙusa yana hawaye ya ce.
"Baba don girman Allah ka riƙe mana Salma da amana,ka tausaya mata ka ririta maraicinta,ka kuma bata kulawa da gatan da bamu samu damar bata ba,Baba don Allah kada ka bari a cutar da Salma. Mun baka amanar Salma idan ka ci amanar ta amanar Allah za ta ci ka."
Jikin Malam Rabi'u ne ya yi sanyi ƙalau,hannu ya miƙa wa Mudassir don ya tashi amma ya girgiza masa kai yana sake haɗe hannayensa biyu yana roƙon Malam Rabi'u akan ya kula musu da amanar Salma. A haka Salma da Abdulwahab suka same shi. Hannu Malam Rabi'u ya miƙa wa Salma ya kira ta gare shi. Sakinta Abdulwahab ya yi ta ƙarasa wajen Malam Rabi'u ta tsaya daga ɗan nesa da shi. Mudassir Malam Rabi'u ya kalla ya dafa kan Salma ya ce.
"Gata nan ku tambaye ta daga jiya zuwa yau idan akwai abinda na yi mata wanda ya nuna ni Rabi'u zan yi mugun zama da ita. Kana ji na ko samari? Wannan yarinyar ƙaddarata ce,hukuncin ni zan aure ta ita za ta aure ni a halin da nake ciki ya tabbata babu mai canja hakan. Na yi muku alƙawari da sani na ba zan taba cutar da Salma ba,idan kuma yanzu ta ce bata son aure na a gabanku zan tsinke igiyar da ta ɗaure mu ni da ita."
Cikin sauri Abdulwahab da Mudassir suka kalli Salma tare da fatan ta ƙi wannan aure. Ita kanta Salma a zuciyarta tana son furta kalmar saki,amma a zahiri tana jin kamar idan ta bar auren ko ta bar gidan za ta iya mutuwa,wani irin hali ta shiga na firgici da tsoro tare da azabar ciwon kai mai tsanani. Dariyar Samira ce ta sanya su juyawa gaba ɗaya su na kallonta. Takowa ta yi gaban su ta ce.
"Ni fa mamaki kuke bani gaba ɗayanku, wai shin akan Salma aka fara aure da ƙarancin shekaru;ko kuwa akanta ƙaramar yarinya ta auri babban mutum? Kun bi kun damu kanku kun ishi mutane da abu ɗaya,aure dai ya riga ya ɗauru,kuma da alama rabo ne ya kira Salma gidan nan, duk wanda ya nemi ya datse igiyar aurenta to da alama tashi rayuwar zai datse."
Ta na faɗan haka ta kalli Salma dake jin kamar da ita ta yi maganar ƙarshe,domin kuwa ji take yi idan ta nemi saki za ta mutu. Mudassir ne ya kalli Abdulwahab yana neman ƙarin bayani,da laɓɓansa ya yi masa nuni da ita ce Samira. Girgiza kai ya yi ya na jinjina ƙarfin hali irin nata. Daga ƙarshe dai ɗakin Salma su Abdulwahab suka koma suka zauna suna ta bata haƙuri tare da lallashinta akan ta yi biyayya da yardar Allah za ta ci riba anan gaba. Kuɗi mai yawa Abdulwahab ya bata ya ce.
"A duk lokacin da kika ji zaman gidan be yi miki ba,ki je tasha ki hau mota ki zo waje na kin ji ko? Ai zaki gane Ƴankaba ba sai na sake yi miki kwatance ba ko? Sannan duk abinda kike so ki siya da kuɗin nan,idan sun ƙare Malam Sallau zai kawo miki wasu,dan zan dinga aiko miki shi akai-akai."
Abdulwahab na gama magana Mudassir ya ce.
"Ko kina son wani abu ne Salma? Idan da abinda kike so kuma ki sanar da mu kafin mu tafi."
Kai ta girgiza tana murmushi. A hankali ta ce.
"Babu abinda nake so Yayah Allah Ya saka da alkhairi,don Allah ku ce wa Gwaggona ta kwantar da hankalinta,wannan Baban ba mugu bane,ta yi min addu'a Allah Ya sa kada ya dake ni ko ya min faɗa. Sannan ku gaishe min da yarana idan Baban nan gidan ya barni zan zo na gansu."
Dariya sosai Mudassir ya fashe da ita ya na kallon Malam Rabi'u da ke haɗe fuska a duk sanda Salma ta kira shi da Baba. Cike da shaƙiyanci Mudassir ya ce.
"Ai wannan Baban na kula ya na da kirki gaskiya."
Da sauri Malam Rabi'u ya kalle shi ya sake tamke fuska. Ganin cewa Mudassir zai fara sakin layi sai Abdulwahab ya miƙe ya ce.
"To mu mun tafi sai watarana ko Salma."
Idanuwanta ne suka kawo ruwa ta gyaɗa masa kai kawai. Har bakin ƙofa ta raka su ta dawo. Sallama suka yi da Malam Rabi'u suka wuce gidan Gwaggo. Suna tafiya aka kawo abun karyawa Malam Rabi'u ya karɓa ya shige musu da shi sashen su.
A zaune ya tarar da Salma tana kuka. Ba tare da ya lallashe ta ko ya hana ta kukan ba ya ajiye mata abun karyawarta a gabanta,wanda yake shayi ne da bread da ƙosai. Nashi ya ja gefe ya ɗauki kofuna biyu a kwandon kwanikan da yake nashi tun yana shi kaɗai ya juye shayinsa itama ya juye mata nata ya tura mata gabanta. Ganin ba za ta dena kukan bane ya sanya shi sassauta murya ya ce.
"Ɗauki abincinki ki ci,su yayun naki ai ba za su so su ganki zaune da yunwa ba ko?"
Kai ta ɗaga sama ta na jan majina ta ja abun karyarwarta ta fara ci,ta na tsaka da ci ta tuna da gargaɗin da Samira ta yi mata na rage mata duk wani abu da ta ci,da sauri ta ture abincin ta koma gefe ta na zare ido. Malam Rabi'u bai kula da abinda ke faruwa ba,yana gama karyawa ya miƙe ya bar gidan gaba ɗaya. Fitarsa ke da wuya Samira ta afka sashen na Salma,cikin zare mata ido ta ce.
"Ina abinda aka bawa Tanimu ya siyo miki?"
Da sauri Salma ta ce.
"Gashi Yaya Samira."
Ɗauka Samira ta yi ta leƙa ledar ta na washe baki ta ce.
"Yauwaa yarinyar kirki,idan ki na ajiye min irin wannan lafiya lau za mu zauna a gidan nan ni da ke babu mai jin kammu. Miƙo kofin can na tarfa miki shayin. Ko kuma bari ina zuwa."
Ledar ta tattare tai gaba,babu jimawa sai ga Tanimu ɗan mijin Samira wadda mahaifiyarsa ta rasu ta bari ya shiga da wani kwano duk ya yi lamba ya ba wa Salma ya fita. Salma na buɗawa ta ga wani irin tuwo baƙiƙƙirin da koriyar miya fatau. Ture wa ta yi gefe ta zabga tagumi tana tunanin yanda rayuwarta ta koma.
A ɓangaren su Mudassir kuwa sai da suka lallaɓa Gwaggo suka kwantar mata da hankali sosai tare da tabbatar mata sun tarar da Salma yanda basu yi zato ba,suna kuma fatan ta tabbata cikin farinciki a gidan nata. Daga ƙarshe suka ajiye mata ƴan kuɗaɗen da za ta yi wa Salma siyayyar duk abinda bata da shi suka tafi.
Haka rayuwar Salma ta kasance a gidan Malam Rabi'u cikin ƙuncin da shi kansa bai san ƴar ƙaramar amaryar tasa tana cikinsa ba. Domin kuwa duk wata hanya da Samira ta san za ta goge sawun musguna wa Salma da take yi a gidan ta goge. Dan haka Malam Rabi'u da Malam Jamilu har alfahari suke yi da zaman lafiyan da su Samira ke yi. Lokuta da dama idan ya kawo nama ko kifi Samira yake bawa ya ce ta yi musu dabge saboda Salma ta ci ta ji daɗi. Ba tare da saninsa ba sai dai ta zuba wa Salma romo kaɗan ta bata,ita ta zauna ta cinye naman ko kifin. A hankali Salma ta dinga rama