MUGUWAR MACE COMPELET HAUSA NOVELS.txt

Author :  HAMIDA SANUSI AHMAD Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   16 / 17

45K to 48K   out of 48.3K words

mai muni,Samira kuma na narka ƙiba abunta kamar mijinta shine mai kashe kuɗin domin ta ji daɗi.....



MUGUWAR MACE.






NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✨✍️




Mai son ci gaba da karanta littafin MUGUWAR MACE ya saka 1k ta 9031416423 Hamidah Ahmad Sanusi Opay. Sai a tura shaidar biya ta 09031416423. Don tsarkin mulkin Allah kada ki sayi littafi na idan za ki yaɗa shi ba tare da kin bari na kammala ba,idan kika yaɗa kamar kin dakushe min sana'a ne.

PAGE 20. LAST FREE PAGE.





Dakan kayan yaji da za su yi miyar dare Salma ke yi a ƙaton turmin tsakar gidan nasu wanda marigayiya matar Malam Jamilu ta yi dakan furar sayarwa a ciki. Gaba ɗaya taɓaryar ta yi wa Salma nauyi da tsawo,a haka ta jure ta ke ta faman daka duk ta haɗa zufa;Samira na yi mata faɗan sanyin jiki da take da shi. Salma na gamawa ta duƙa ta kwashe kayan yajin ta nufi madafi da shi ta buɗe tukunyar dake kan wuta ta zuba. A gajiye ta shiga ɗakin Samira dake hango duk abinda take yi a tsakar gidan ta durƙusa har ƙasa ta ce.

"Yah Samira na gama,akwai abinda zan yi miki?"

Shiru Samira ta yi ta na wani nazari,a cikin ranta ta ce.

'Ya kamata fa na karɓi abinda zan bayar a sunan Hauwa a wajen yarinyar nan,tinda ita ce sabuwar amarya,na tabbata idan na sauka lafiya nima za su rama wa kura aniyarta.'

Muryar Salma ce ta katse ta daga tunanin da ta faɗa ta ce.

"Yah Samira miyar na kumfa me zan zuba?"

"Ki je ki buɗe murfin tukunyar ki saɓa bakin. Yauwa idan kin gama mu je ƙofarki ki buɗe min lefen ki akwai abinda zan ɗauka na kai wa Hauwa na barkatu."

"To Yah Samira."

Cike da ladabi Salma ta je ta saɓa bakin tukunyar kamar yanda Samira ta umarce ta,daga nan sai ta wuce sashenta ita da Samira,su na shiga Samira ta hau leƙe da dube-dube ko za ta ga wani abun da za ta yi faɗa akai ko ta ɗauke. Har uwar ɗaka suka shiga tare,da ƙyar Salma ta iya sakko da akwatunan ƙasa Samira na kallon ta;amma ta ƙi taimaka mata. Ta na saukewa Samira ta zauna a gaban kayan tana ɗagawa,tsabar son zuciya ji take yi da da hali da ta kwashe kayan dika,domin Malam Jamilu bai kashe mata kuɗi kamar yanda aka kashe wa Salma ba. Hannunta ta ɗora akan wata santaleliyar atampa mai kyau,da dikkan alamu ita ce ma mai babban kuɗi a cikin kayan. Turare da breziya Samira ta sake ɗauka sannan ta miƙe tsaye ta ce.

"Maza ki kwashe su ki mayar da su mazaunin su. Ki buɗe kunnen ki da kyau ki ji ni,ko sama da ƙasa za ta haɗe idan an tambaye ki inda atampa take ki ce baki sani ba,idan kika faɗi suna na sai na sa gabanki gabar na yanke da wuƙa. Shegiya mai ido kamar na mage."

Kan Salma ta dangwara sannan ta ɗaga rigarta ta soke atampar da turaren tare da breziya ta fita da sauri. Kai tsaye ɗakinta ta nufa ta cire kayan daga cikinta ta samu leda babba ta saka kayan ta ɓoye. Murna ta dinga yi domin ta samu hanya mafi sauƙi da za ta dinga bada kayan barkatu ba tare da sisinta ya yi ciwo ba.

A wannan azaba da uƙubar Salma ta yi wata biyu a gidan Malam Rabi'u. Watarana da daddare Malam Rabi'u da Salma su na zaune yana jefa lomar tuwon da Salma ta tabbatar masa cewa da kanta ta dafa masa. Murmushi ya yi ya kalle ta ya ce.

"Inyeee an Salamemen Gwaggo hannu yana ta faɗawa. To ga wannan ki sayi sha ka laɓe ki sha abunki."

Hannu ya saka a aljihunsa ya zaro nera ɗari sabuwa kar ya bata. Murna Salma ta dinga yi ta na yi masa godiya. A hankali Malam Rabi'u ya tsaya yana kallon ta shi ma yana murmushi, sai dai bai jima yana murmushi ba fuskarsa ta koma ta jimami,cike da kulawa ya kalli Salma ya ce.

"Salma ko dai akwai abinda yake damunki ne a gidan nan da baki sanar da ni ba? Gaba ɗaya kin rame kin yi baƙi kamar ba ke ba,ni kuma na san ina bakin ƙoƙarin na ga na kawo miki duk wani abu na jin daɗin rayuwa,domin a yanzu na yarda na amince bani da wata ko wani da ya dace da ya ci dukiyata da nake ta tarawa da ya wuce ki. Ki na da hankali,natsuwa da tarbiyya,ki na da kawaici da juriya akan halin da kike ciki,shin ko dai har yanzu ba kya so na ne na mayar dake wajen Gwaggo na haƙura da auren? A ƙalla dai duk wanda ya kalle ni zai tuna cewa na taɓa yin aure a rayuwata ko sau ɗaya ne."

Tinda Malam Rabi'u ya fara magana jikin Salma ya yi laushi idanuwanta ke zubar da hawaye. Tsabar azabar da Samira ke gana mata ko sunan ta aka kira sai gabanta ya faɗi ta zaci na Samiran aka kira. Ganin hawaye na zarya a kuncinta ne ya sanya Malam Rabi'u kiranta wajensa. Babu musu ta tashi ta isa gare shi ta zauna a saman cinyarsa kamar yanda ya fara sabar mata. Ba dan yana jin wata sha'awa ba haka kawai yake jin daɗi idan Salma ta zauna a jikinsa,ya na ƙaunarta sosai saboda natsuwarta da kamewarta,bata da hayaniya da kwaramniya irin ta yara. Cike da sigar lallashi ya ce.

"Sanar da ni abinda kike so Salamatuna. Ko akwai abinda yake damunki?"

Kai ta girgiza masa alamar babu komai,sake tambayarta ya yi a karo na babu adadi,da ƙyar ta iya buɗe baki ta ce.

"Ina so na ga Gwaggona. Tinda na zo gidan nan sau ɗaya ta zo ta kawo min kayana,ni kuma ban samu damar zuwa na ganta ba. Kuma ina son ganin Aabid,Aunty Layuzah ta yi min alƙawarin za ta zo yawon arba'in Kura amma bata zo ba gashi har sun yi wata uku zuwa huɗu."

Murmushi Malam Rabi'u ya saki,bai san dalili ba sai zuciyarsa ta ji daɗi da Salma bata ambato matsala a zaman su tare ba,duk damuwarta mai sauƙi ce a wajensa. Kanta ya shafa sannan ya ce.

"In dai wannan ne matsalar ki to ki shirya a daren nan zan kai ki wajen Gwaggo ba zan bari ki kwana baku gana ba. Wajen Aabid kuwa ki yi haƙuri ki ƙara ko da wata guda ne sai na kai ki,dan kin san al'adar garin nan amare ba sa yawo idan basu cika shekara ba. To mu dai za mu fara take doka daga yau ko?"

Bakinta ta rufe ta na dariya cike da ƙuruciya. Shi ma dariyar ya taya ta,daga ƙarshe ya ƙarasa cin tuwonsa ya na bata a baki har suka cinye. Salma ce ta kwashe kwanukan ta kai waje,ta na fita ta ji kamar an ruga da gudu an bar sashen nata,ta ji tsoro sosai a ranta,amma kuma ta tabbata ko ma wanene ba zai wuce Yah Samira ba,dan ba sau ɗaya ko sau biyu ta kama ta tana yi musu laɓe ba. Hannunta da bakinta ta wanke ta koma ɗakin. Malam Rabi'u kuwa sai da ya zaga bayi sannan ya wanke bakinsa ya kulle ko ina ya miƙa wa Salma sabon hijabi da takalmi ya ce.

"To bismillah amaryar Malam Rabi'u mu je ko?"

Bakinta ta toshe tana dariya ta yi gaba yana biye da ita. A haka suka isa har gidan Malam Bala. Malam Bala dake ƙoƙarin shiga gida ne ya ga Malam Rabi'u tafe da Salma su na hira a cikin hasken farin watan da ya mamaye ilahirin garin Kura. Sam ransa bai yi masa daɗi ba da ya gan su cikin nishaɗi. Sai ya kawar da kai ya yi kamar be gansu ba zai shige gidan. Cikin sauri Malam Rabi'u ya kira sunansa,washe baki Malam Bala ya yi yana fara'a kamar babu abinda ke damun zuciyarsa. A ɗarare Salma ta durƙusa ta gaishe shi,haɗe fuska ya yi ya ce.

"Ince dai Ja'irar yarinyar nan ba wani mugun abun ta gunguma ba ka dawo da ita gida? Ina so ki sani muddin kika kaso auren nan ba dai gida na ba,sai dai ki nemi inda za ki je."

Da sauri Malam Rabi'u ya tari numfashin Malam Bala ya ce.

"Allah na tuba me wannan halitta mai tsarkin za ta yi min na ɓacin rai? Yarinya kamar ba a cikin shekarun biri take ba. To ka ganta nan da zan ce mata ta haɗiye min ruwa in ji ƙoshi a cikina za ta yi tsabar yanda take yi min biyayya. Gwaggonta na kawo ta ta gani,ka san abun yaro sai ana lallaɓa shi."

Ƙwafa Malam Bala ya yi ya saki yaƙe ya ce.

"Maza ki tashi ki shiga ciki,kuma kada ki jima,tinda sarai kun sani ai mace bata fita daga gidan miji sai ta shekara,wata ma sai ta haihu idan za ta je wankan gida take zuwa gida ita da abinda ta haifa."

Da sauri Salma ta miƙe tsaye ta shige cikin gida cike da murna. Malam Rabi'u kuwa sai ya tuntsire da dariya yace.

"Wannan yarinyar kam ai sai dai a yi mata uziri ta yi abinda take so,dan kuwa nan kusa dai ban ga yanda za ta samu juna biyu ba ballantana ta haihu."

Kai Malam Bala ya karkace ya ce.

"Ban gane nan kusa ba,wai kana nufin har yanzu baka shiga gonar yarinyar nan ba?"

A karkace shima Malam Rabi'u ya kalli Malam Bala ya ce.

"Habaa Malam! Wannan yarinyar ai ta yi ƙanƙanta da wannan al'amari,kai dai kawai Allah Ya sa mu na da rabon alkhairi a gaba."

"Kada ka duba yarintarta fa Rabi'u. Mata nawa aka yi wa aure da shekarunta kuma suka haihu? Ka duba kai iya tsawon shekarun da ka ɗauka a duniya,idan ban ɓata lissafi ba wannan bazarar da za ta zo za ka cika shekara Hamsin da uku a duniya,ka faɗa min wata matar za ka aura nan gaba idan baka tara da wannan ba?"

Kyaɓe baki Malam Rabi'u ya yi ya ce.

"Ni fa na riga da na yarda da maganar mutane,da dikkan alamu aljana ce ta aure ni,dan bana samun nutsuwa a ko ina sai a cikin bacci na. Na raina wannan yarinyar sosai Malam Bala bata da abinda za ta bani a yanzu dai,ban sani ba ko nan gaba."

Cike da takaici Malam Bala ya bar wannan tattaunawar ya ɗakko wa Malam Bala zancen gona. A cikin ransa yana saƙa tsiyar da zai shukawa Malam Rabi'u a nan gaba.

A ɓangaren Salma kuwa ta na shiga cikin gidan ta shiga ɗakin Gwaggo ta na murna. Gwaggo ma na ganinta ta saki kaɗin da take yi ta rungume Salma ta na faɗin.

"Maraba maraba jikalle na kin fiye min ɗa daɗi."

Sai da suka gama murna Kande ta ce.

"Ke salma garin ya aka yi kika zo war haka bayan baki cika shekara da aure ba? Ko dai gudowa kika yi bai sani ba? Me yake faruwa a gidan naki na ga kin rame kin yi duhu?"

Cikin dariya Salma ta ce.

"Gwaggo da shi fa muka zo yana waje yana jiran mu gaisa na je mu koma gida. Kuma ni babu abinda yake faruwa da ni a gidan sai alkhairi. Gwaggo na yi kewar ki sosaiiii."

Kai Gwaggo ta jinjina ta na nazari,can sai ta yi ƙasa da muryarta ta ce.

"Ko dai kun fara kwana a ɗaki ɗaya da Malam Rabi'u ne Salma?"

Da sauri Salma ta kame baki tana zaro ido waje,cike da tsoro ta hau ja da baya,dan bata so Gwaggo ta gane tana sakar masa jiki har ta hau cinyarsa ta zauna. Ganin irin kallon da Gwaggo ke binta da shi ne ya sanya ta fara kuka ta ce.

"Ki yi haƙuri Gwaggo zan faɗa miki gaskiya,dama...dama...uhumm shine yake ɗora ni a cinyarsa,ko ya ce na hau,amma Gwaggo ni ban taɓa kwana a ɗakinsa ba,shima kuma bai taɓa kwana a ɗakina ba."

Salma ta ƙarasa maganarta cike da yarinta da tsoro. Murmushi Kande ta yi ta ja Salma jikinta,a hankali ta dinga warware mata duk wani tsoro da ta dasa mata a ranta akan maza. Cikin sauƙi take sanar da ita duties ɗin matar aure a wajen mijinta. Lokacin da ta zo kan gaɓar bayani akan kwanciyar aure sai Salma ta hau jin tsoro jikinta ya ɗauki rawa. A haka Gwaggo ta yi mata bayanin komai yanda za ta fahimta. Daga ƙarshe Kande sai ta tashi ta hau haɗa mata kayan cimar da Abdulwahab ke kawowa a kai wa Salma bata samu damar kai mata ba. Hotunan Aabid da aka ɗauka aka wanko Kande ta bata ta ce.

"Wannan saƙo ne daga ɗanki. Yana can duk kayansa sun yi masa kaɗan saboda girma."

Dariya Salma ta yi kafin ta ce.

"Amma Gwaggo me ya sa Yah Audu bai zuwa gani na? Kuma Aunty Layuzah ta yi min alƙawarin zuwa amma har yau bata je ba."

"Hidima ce ta yi wa Layuzah yawa saboda Ammabuwa na ɗauke da juna biyu mai wahalar laulayi,ga yaronta bai yi wani ƙwarin a zo a gani ba,shi kuma Yayanki baya son zuwa gidan ne saboda Samira,ina fatan za ki yi masa uziri."

Ɗaga kai Salma ta yi ta buɗe baki za ta yi magana,muryar Hasiye ta katse ta ta yi sauri ta juya tana kallon bakin ƙofa. Washe baki Hasiye ta yi ta ce.

"Ah ah! Yau amare ne a gidan namu babu ko sallama ballantana mu ji zuwan baƙi? In ji dai ba wani laifin ta yo ba ya koro ta?"

"Sai dai ki ga kora a kan taki ƴar amma ba akan jika ta ba."

Guɗa mai ƙarfi Hasiye ta rafsa sannan ta ce.

"Yo su waye suka yi silar auren har da za a yi wa mutane firirita? In ce dai ni ce na shiga na fita na haɗa auren? Kuma naga da ai cewa kuka yi ba kwa so,yanzu kuma sauya zani ta yi da zaki ce haka Kande?"

Banza Kande ta yi da ita ta gama ƙulle wa Salma kayan da ta haɗa mata kaf. Har Salma za ta ɗauka sai ta tuna yanda Samira ke yi mata iko da ƙwacen kayanta. Cikin sauri ta durƙusa ta kunce ɗaurin kayan ta kwashi hotunan Aabid da abinda ta san za ta iya cinye wa kafin su isa gida ta kwasa da gudu ta yi waje. Duk kiran da Gwaggo ke yi mata bata waiwaya ba ballanta ta amsa ta. A nan ta bar Hasiye na san barka da yanda ta ga rama da duhun fatar da Salma ta yi.

A ƙofar gida ta tarar da Malam Rabi'u da Malam Bala,kai tsaye wajen Malam Rabi'u ta je ta ci burki ta ce.

"Baba taso mu tafi gida."

Harar wasa Malam Rabi'u ya sakar mata ya ce.

"Ba na ce ki dena ce min Baba ba? Ni mijinki ne,dan haka kada ki sake kira na da Baba,daga yau ki dinga kira na da Mijin Salma,idan ba za ki faɗi haka ba ki dena kira na da kowanne suna bana so."

Dariyar ƙuruciya ta yi ta buɗe ledar biscuit ta fara ci a gabansu ta na rausaya kai cike da jin daɗin abinda take ci ɗin. Tsaki Malam Bala ya ja cike da hassada da baƙin cikin bai samu yanda yake so ba,sallama ya yi musu ya shige cikin gida ya samu Hasiye na ta yi wa Kande rashin kunya. Har a wannan lokacin yana son Kande sosai a ransa,kuma ya na ganin girmanta,shi kansa yana rasa dalilin da ya sa yake rufe ido ya karta mata rashin mutunci. Tsawa ya daka wa Hasiye ya ce.

"Ke bana son rashin ta ido,Kanden sa'ar ki ce? Na ce sa'arki ce da zaki sa ta a gaba kina yi mata rashin ta ido? Wuce ki tafi ɗakinki."

Ko shiga ɗakin Kande bai yi ba ya wuce nashi ɗakin ya hau rage kayan jikinsa yana ƙulla mugunta a cikin ransa. A haka Hasiye ta shiga ɗakin ta na kumbura baki ita a dole fushi take yi da Malam Bala yayi mata tsawa a gaban kishiya. Zama ta yi ta na ɓata rai,sai ta ba wa Malam Bala dariya,nan ya zauna ya bata labarin gidan Malam Rabi'u. Ranta ne ya ɓaci ta ce.

"Yo me aka yi kenan Malam? Ai ni so nake ace ya yi mata fata-fata ya yayyaga ta ta yanda sai an ɗinke ta kamar ƙwarya. Gaskiya da sakel,ai ni ban yi wannan gamin dan Salma ta zauna lafiya a gidan miji ba."

Shiru suka yi na wani lokaci kowannensu na tunanin irin gadar zaren da zai haɗa wa Salma domin daƙile farincikin da take samu a gidan aurenta.

Bayan wata ɗaya Salma ta saki jiki sosai a gidan miji,Malam Rabi'u ya fara dawowa cin abincin rana a gida,wannan dalilin ne ya sa dole Samira ta rage musguna wa Salma gudun kada mijinta da Malam Rabi'u su gani. A hankali Salma ta fara cika  haskenta na dawowa. Watarana har ƴar bireziyar da Samira ta rage mata guda ɗaya take ɗauka ta dinga gwadawa ta na dariya ita kaɗai a ɗaki. Fatanta bai wuce watarana itama ta shiga cikin sawun matan da ke sanya bireziya ba.

A ɓangaren girki kuwa ta ƙware sosai,domin Samira sakar mata komai take yi,sai dai ta dinga nuna mata abinda za ta yi,ita ke share sashenta ta share na Samira,wankin banɗaki da wanke-wanke dik aikinta ne. Ɗiban ruwa a rijiya ta cika randuna na daga cikin aikinta. Idan Malam Jamilu ya ga aikin ya yi wa Salma yawa ya yi magana sai Samira ta dafe ciki ta hau karairaya ta na cewa.

"Yanzu Malam me tsohon juna me za ta iya yi? Ai idan aikin ya min yawa sai na haihu lokaci bai yi ba."

Kan dole yake ƙyale ta ba dan ya so ba,tinda ai lokacin da tsohuwar matarsa na raye da cikin Tanimu babu abinda bata yi.

***********************

Yau ma kamar kowacce rana tun safe Salma ta tashi take aikin gida. Wanke-wanke ta fara yi,sannan ta yi shara,daga nan ta wanke banɗaki. Ta na gamawa ta kwashe ɗumamen tuwon da ta aza ta ɗora ruwan kunu. Lokacin da ta gama komai Malam Rabi'u har ya yi wanka yana zaune yana jiran a kai masa kayan karyawarsa. Babu jimawa Salma ta shiga ɗakinsa da babban faranti mai ɗauke da kwanon tuwo,kofin kunu da kwanon sha cike da ruwan randar sanyi. Ajiye wa ta yi ta miƙa masa butar ƙarfensa,daga nan inda yake zaune ya wanke bakinsa ya watsa ruwan waje,sannan ya

16 / 17