Author : HAMIDA SANUSI AHMAD Category : Romantic Hausa Novels
su. Murmushi Alhaji Kabiru Mai Tumbin Nera yayi sannan ya ce.
"Yanzu ake buƙatar kuɗin ko yaushe? Domin ni a shirye nake da na bada kuɗi,a bani takardu tare da kafa shaidu."
"Idan ka shirya ni ma a shirye nake."
Cikin ƙanƙanin lokaci su Aabid suka gama duk abinda ya kawo su suka yi sallama da Alhaji Kabiru suka tafi. Godiya sosai Malam Sallau ya dinga yi kamar zai kwanta wa Aabid a ƙasa. A haka Aabid ya sauke shi a daidai wajen da zai samu mota ya koma gida shi kuma ya wuce gidansu dake cikin unguwar Ɗanladi na Sidin. A waje ya ajiye motarsa ya shiga cikin katafaren gidan nasu wanda da wayonsa mahaifinsa ya siyi gidan a hannun gwamnati ya rushe shi ya sake ƙera kalar wanda yake so. Gida ne da ya amsa sunansa gida mai part biyu da manyan filayen da aka yi shuke-shuken ƴaƴan itatuwa da flowers domin ƙayata wajen. Gefe ɗaya kuma ƙaton waje ne da aka yi kitchen irin na gargajiya tare da ɗakuna uku na masu aiki. Zagaye Aabid ya dinga yi a gidan yana kallon kowanne lungu da saƙo na gidan yana tuna memories masu daɗi da marasa daɗi da suka faru a gidan. A ƙofar wani ɗaki ya tsaya yana bin ƙofar da kallo. Wani irin abu ya ji ya daki zuciyarsa har sai da ya sanya hannu ya dafe ƙirjinsa.
"Dijahna"
Shi ne sunan da ya ambata kafin ya tura ƙofar ya sanya ƙafarsa ta dama a ciki. Nan take hotunan rayuwar da yayi a baya ta hau gilmawa a idanuwansa. Kansa ya ji yana sara masa kamar zai tsage. Babu shiri ya fita daga ɗakin ya ja ƙofar ya rufe. Da sassarfa ya isa ɗakin Hajiya wadda ke kwance ita kaɗai tana firfita. Kallonta yayi fuska a haɗe kamar bai taɓa dariya ba ya ce.
"Ina wannan yarinyar take na ganki ke kaɗai?"
Da sauri Hajiya ta tashi zaune daga kishingiɗar da ta yi ta kalli Aabid cike da so da ƙauna irin na ɗa da mahaifiya. Murmushi ɗauke a saman fuskarta ta ce.
"Salimah? Ta fita samo mana gawayi mu ɗan ɗora ruwan koko a samu a karya tinda gari ya waye."
Rintse idonsa yayi yana jin jiri na ɗibansa. Mahaifiyarsa ce fa,matar da ko Custard za ta sha sai ya koma fari fat saboda madarar da take zabga masa,ta saka ta ruwa sannan ta ƙara da ta gari,ita ce yau take neman gawayin da za ta dama koko. Mahaifiyarsa wadda take rayuwa kamar sarauniya komai sai an yi mata saboda dukiya da gatan da mahaifinsa da shi kansa suke bata. Kyaɓe baki yayi sannan ya zaro dubu biyu ya ajiye a nesa da ita ya kurɗa kansa cikin ɗakinta,da wani irin farinciki Hajiyan ta ɗauki dubu biyun tana jin kuɗin kamar dubu ɗari biyu a wajenta,yaushe rabon Aabid ya zo gare ta? Yaushe rabon ta samu arziƙin samun wani abu daga gare shi? Lallai wannan babbar nasara ce a gare ta wadda take fatan watarana komai ya koma kamar yanda yake a baya. Bincike yayi sosai kafin ya samu abinda yake so sannan ya fito yana zufa kamar wanda yayi wani aikin wahalar. Kai tsaye ya fice ya bar gidan ba tare da ya ce mata kanzil ba ya faɗa motarsa ya fige ta. A hanya ya haɗu da Salimah hannunta riƙe da tarkacen itacen da ta yo da kanta saboda rashin samun gawayin da bata yi ba. A gabanta ya tsayar da motarsa ya kalle ta ya ce.
"Ke wannan yayin haukan da kika ɗebo fa na meye?"
Cike da jin tsoronsa bakinta ya hau rawa,tsawa ya daka mata tare da sake tambayarta abinda ke hannunta na meye. Cikin rawar murya ta kalle shi ta ce.
"Ƙirare ne na samo dan mu yi amfani da shi."
"Ina gawayin da kika je siyowa?"
"Ban samo ba."
Tsaki ya ja mai tsawo sannan ya ja motarsa ya bar wajen a guje kamar zai tashi sama. A hankali ta waiga ta kalli ƙurar da motar ke tadawa sannan ta girgiza kanta ta wuce gida.
Washegari da sassafe ko tashi daga bacci su Hajiya basu yi ba suka ji ana buga gate ɗin gidan nasu da ko arziƙin mai gadi babu. Hajiya da kanta ta sanya mayafinta ta nufi ƙofar gidan da makulli a hannunta tana tambayar waye. Wata murya ta ji wadda bata waye da ita ba tana faɗin.
"Mu ne."
Gabanta ne ya faɗi har sai da ta dafe ƙirjinta kafin ta ce.
"Ku su wa?"
"Alhaji Aabid bai sanar da ke zuwan mu ba ne? Ina ga zai fi kyau ki kira sa a waya ki tambaye sa su waye za su zo war haka."
Cike da jarumta Hajiya ta buɗe ƙaramar ƙofar gidan ta tsaya tana kallon mutanen da bata taɓa gani ba sai a wannan ranar. A guje Malam Sallau da ya tsaya bawali ya ƙaraso yana gyara wandonsa tare da fyace majina ya ce.
"Barka da safiya Hajjaju."
Ajiyar zuciya Hajiya ta sauke sannan ta ɗan yi dariya ta ce.
"Malam Sallau ai har na ji tsoro,ashe ku ne ke tafe. Bismillah ku shigo."
Da jin haka sai suka ɗunguma suka shiga cikin gidan gaba ɗaya su na sake gaisawa. Alhaji Kabiru Mai Tumbin Nera kuwa kallon gidan yake yi yana girgiza kai tare da washe baki. Tafe yake yana buɗe duk wani ɗaki ko ƙofa da ya gani kamar gidansa. Cike da mamaki Hajiya ta ke kallon ikon Allah,ba ta katse da lamarin Alhaji Kabiru ba har sai da ta ga ya nufi ɗakinta ya saka hannu zai buɗe ƙofa. Da ƙarfi ta ce.
"Malam lafiya wai naga kana ta buɗe min ƙofofin gida kana kalle-kalle?"
Malam Sallau ne ya sosa ƙeya sannan ya ce.
"Hajiya wai ko dai kina nufin Alhaji Aabid bai sanar dake abinda ke faruwa bane?"
Cike da mamaki Hajiya ta juya tana kallon Malam Sallau sannan ta ce.
"Malam Sallau me ya samu ɗana? Me yake faruwa wanda ba a sanar dani ba?"
"Baki da labarin Alhaji Aabid ya siyar da wannan gidan Hajiya? Ai jiya da yamma ya kai wa Alhaji Kabiru takardu muka je wajen Mai Unguwa aka saka shaidu ya biya kuɗi da ..."
Wani irin duhu ne ya mamaye ganin Hajiya,nan take ta yanke jiki ta faɗi. Alhaji Kabiru na ganin haka ya hau sauri yana son barin gidan,domin shi mutum ne mai tsananin tsoro da kiyaye duk wani abu da zai haɗa shi da hukuma. Banda nishi babu abinda yake yi a haka ya isa waje ya shige motarsa ya zauna yana yarfe zufa.
Sallau kuwa sunan Salimah ya dinga kira ta fito a gigice kanta babu ko ɗanƙwali. Ganin Hajiya a zube a ƙasa ne ya gigitata ta nufi wajen da gudu ta zube a gefen Hajiyan tana jijjiga ta. Hankalin Sallau ba ƙaramin tashi yayi ba dan haka sai ya miƙe ya lalubo wayarsa ya dannawa Aabid kira. Cikin rashin sa'a kiran ya shiga a daidai lokacin da wayar Aabid ɗin take hannun Aabida tana duba mutanen da yayi waya da su a jiya;wanda murnar ganin gingimemen alert ɗin kuɗi ya mantar da ita dubawa. Ɗauka ta yi cike da gadara. A kiɗime Malam Sallau ya labarta mata abinda ke faruwa. Rai a ɓace Aabida ta ce.
"Idan ta faɗi mutuwa ta yi? Malam idan za ku yayyafa mata ruwa ta tashi ku yayyafa mata,idan ba za ku yayyafa mata ba ku kuka sani ku barta ta ƙarasa ai dama ta kwana biyu,babu inda mijina zai fito da sanyin safiyar nan yana hutawa."
Tana gama magana ta katse wayar ta ci gaba da abinda take yi..........
MUGUWAR MACE.
NA: HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH. ✨✍️
*Ƴar'uwa kema kin yi ta shan maganin slimming amma har yau ya ƙi karɓar ki? Matso na zo maki da haɗin da zaki sha ki sauke ƙiba da nauyin jiki cikin sauƙi,Shayi ne mai daɗi da ƙamshin da ba zai baki damar yin ƙiwa ba wajen amfani da shi. Bayan haka akwai slimming oil da zai rage maki kitse a duk gaɓar da kike da buƙata a jikinki;kamar tumbi,damtse,kitsen baya,da cinya.*
*Slimming Tea 6k.*
*Slimming oil 3500.*
*Body scrub 3500.*
*Skin oil 2500.*
*Location Kano.*
*Phone No 09031416423.*
PAGE 3.
A rikice Malam Sallau ya kira Yah Maheer ya sanar da shi abinda ke faruwa. Hankali tashe Yah Maheer ya roƙi Malam Sallau da ya nemo abun hawa ya kai Hajiya asibiti ya na nan tafe zai same su a can. Da ƙyar Malam Sallau ya iya barin Hajiya a kwance a ƙasa ya fita saboda tsoron kada ta mutu kafin ya dawo.
Sai da ya ɗauki kimanin mintuna shida kafin ya dawo da ɗan sahu,su biyu suka ɗauki Hajiya suka saka ta a adaidaita sahun sannan suka ja suka tafi asibitin da ake duba Hajiyan a duk lokacin da ciwon ta ya tashi. Su na zuwa likitansu ya fara bata taimakon gaggawa. Kafin Yah Maheer ya iso Hajiya ta dawo tana numfashi yanda ya kamata,sai dai a wannan lokacin bata san wanda yake kanta ba. Har ofishin likita ya je suka zauna,likita yayi ta masa faɗa akan yanda suke wasa da lafiyar Hajiyan. Cike da rashin jin daɗin lamarin likita ya ce.
"Haba Maheer wai me yake faruwa ne kuke wasa da lafiyar Hajiya haka? Ko ka san cewa tashin ta lafiya ba tare da shanyewar ɓarin jiki ba babban lamari ne da za a gode wa Allah akai? Ina Aabid? Ta na farfaɗowa sunansa ta fara kira. Don Allah ku maida hankali ku kula da lafiyar ta. Yanzu ga wannan ka je ka siyo a fara bata,sannan a kawo mata abinda za ta ci,dan har da ciwon ulcer ke damun ta."
Ajiyar zuciya mai ƙarfi Yah Maheer ya sauke kafin ya miƙa hannu ya karɓi takardar da likita ya bashi,cikin sanyin murya ya ce.
"Mun gode Dr. Anas. In Sha Allahu za mu kiyaye daga yau Hajiya ba za ta sake samun attack irin wannan ba."
"Allah Ya bata lafiya."
"Amin Ya Allah."
Da haka Yah Maheer ya karɓi takardar hannun likita ya wuce pharmacy. Malam Sallau na ganin shi ya ruga da gudu ya nufe shi,cike da damuwa ya ke tambayar jikin Hajiya,murmushin yaƙe Yah Maheer yayi masa kafin ya ce.
"Da sauƙi Malam Sallau,da yardar Allah Hajiya za ta tashi lafiya. Na ɗauki alƙawari daga yau Hajiya ba za ta sake shiga damuwa ba in dai ina raye."
Ƙwalla Malam Sallau ya share kafin ya ce.
"Allah Ya jiƙan Alhaji. Ita kuma waccan azzalumar Allah Ya tsine mata,In Sha Allahu ƙarshen ta ba zai yi kyau ba,da yardar Allah sai ta wulaƙanta kafin ta mutu. Aabid na fara kira da abun ya faru amma ja'irar yarinyar nan ta ɗauki wayar ta ce ba zai zo ba hutawa yake,wannan yarinya wannan yarinya Allah Ya..."
"Ya isa haka Malam Sallau bari na je na kawo abinda ake buƙata. Duk wanda yayi na gari ai kansa ko?"
Jinjina kai Malam Sallau yayi ya ce.
"Ƙwarai da gaske ma kuwa Alhaji Maheer."
Daga haka Yah Maheer bai sake cewa komai ba ya tafi Pharmacy ya siyo magungunan da aka rubuta,sannan ya shiga wajen siyar da abinci ya siyo abinci mai rai da lafiya da ruwan sha ya koma ɗakin Hajiya. Kwance ya tarar da ita tana bacci wanda da ka gani cike yake da azaba da wahala. Zama yayi a kujerar dake kusa da gadon ya kifa kansa a jikin gadon yana jin yanda zuciyarsa ke tsananin zafi. Motsin da ya ji ne ya sanya shi ɗaga kansa cikin sauri ya kalli Hajiya dake kiran sunan Aabid hawaye na zubowa daga gefen idanuwanta. Da sauri Yah Maheer ya tashi ya tsaya a gabanta ya ce.
"Sannu Hajiyarmu Allah Ya baki lafiya. Ki yi haƙuri ki kwantar da hankalinki a samu jininki da ya hau ya sauka,daga baya sai mu samo solution akan matsalar da ke gabanmu. Bari na je na kira likita na dawo."
Da sauri Hajiya ta riƙo hannunsa ta ce.
"Maheer Aabid zai kashe ni da baƙincikinsa...Aabid...Ya siyar...da gidan da nake ciki....ba tare da ya sanar da ni ba.....Aabid ya siyar da gidan da mahaifinsa ya gina...min cike da soyayya....tsarin ginin gidan da duk abinda....yake ciki...ni na zaɓa da kaina...me na yi wa Aabid a duniya yake azabtar....da ni haka? Laifi ne da na zamo a matsayin....mahaifiyarsa?.....Aabid ɗina ya halaka Maheer...ko mutuwa na yi bana so...ya zo kan gawata....na yafe wa Aabida shi....na yafe wa duniya shi."
Hawaye ne masu tsananin zafi suka hau zubowa daga idanuwan Yah Maheer. Da ƙyar yake iya buɗe bakinsa ya bawa Hajiya haƙuri,sai dai shi kansa ya sani ban haƙurinsa a daidai wannan lokacin ba zai yi tasiri ba. Da sauri ya fita ya kira likita suka dawo tare da nurse. Abinci suka tursasa Hajiya ta ci kaɗan sannan suka bata magunguna,daga nan nurse ta sauya mata ruwan da ke shiga jikinta sannan suka tafi suka barta tana sambatu. A haka bacci mai cike da mafarkai marasa daɗi ya ɗauke ta.
Yah Maheer na ganin ta samu bacci ya leƙa ya kira Salimah ya ce mata.
"Ki zauna da ita bari na je na dawo. Malam Sallau mu je na ajiye ka a gida ko?"
Da sauri Malam Sallau ya tashi yana matse ido ya bi bayan Yah Maheer wanda fuskarsa ta sauya daga mai yawan fara'a da sanyin hali zuwa wani mutum mai tsananin fushi. Ya na ajiye Malam Sallau ya wuce gidansa. Ƙamshin da ya daki hancinsa ne ya sanya shi lumshe ido ba tare da ya shirya ba. Ƙamshi ne na turaren wuta mai daɗi da kwantar da hankali wanda Mahreen ke haɗawa da kanta saboda ta san irin ƙamshin da mijinta yake so. Ya na ƙarasa shiga gidan ya tarar da ita ta sanya guntun wando da ƴar ƙaramar riga sai zabga ƙamshi take. Ajiye food flask ɗin hannunta ta ƙarasa yi a saman dinning table kafin ta tafi da gudu ta faɗa jikinsa. Kyakkyawan ruƙo Yah Maheer yayi wa Mahreen sannan ya taka da ita a hannunsa suka zauna a ɗaya daga cikin kujerun dake jere a parlourn. Cike da shagwaɓar da ta san tana burge gwarzon nata Mahreen ta ce.
"Ina ka tafi da sassafe ina bacci ba tare da ka sanar dani baaa?"
Murmushin yaƙe yayi kafin ya ce.
"I am sorry my rigimatu,a yi min afuwa ba zan sake ba. Yanzu mu je ki bani abinci na ci yunwa nake ji kin ji tauraruwa ta?"
Da sauri ta ɗaga shi ta wuce wajen cin abincin ta hau zuba musu soyayyan dankalin hausa da ta yi da miyar attaruhun da ta ji albasa da kayan ciki sai zabga ƙamshi take yi. Ajiye wa ta yi a center table sannan ta koma ta haɗa musu shayi ta kawo da bread da soyayyan ƙwai ta zauna a gabansa ta na bashi a baki. Bata jima tana bashi abincin ba ya ji duk ya fice masa akai,sai dai dole ya daure ya ci tare da ɓoye damuwarsa kafin rigimammiyar tasa ta fahimci akwai matsala ta saka shi a gaba da kukanta da ba ya iya jure sauraro. Sai da suka gama cin abincin tas sannan ta kwashe komai ta kai kitchen ta ajiye ta koma wajen Yah Maheer da ya zurfafa a tunanin halin da ya baro Hajiya a ciki. Zama ta yi a kusa da shi tare da ɗauke masa tagumin da ya zabga ta sumbaci hannunsa ta ce.
"Tun da ka shigo na fuskanci akwai damuwa a tattare da kai,a tunani na kyautatawar da zan yi maka kaɗai ta isa ta wanke maka damuwarka,sai dai da dikkan alamu abinda ke damunka ya fi ƙarfin kulawata ballantana ta taimaka ta yaye maka damuwar. Sanar dani abinda ke faruwa ko akwai wani taimako da zan iya yi akai."
Zuciyarsa ce ta karye da tausayinta,sai kawai ya ja ta jikinsa ya rungume. Ya jima a haka kafin ya miƙe tsaye ya ce mata.
"Zan fita na je na dawo,ban sani ba ko zan jima ko kuma zan dawo da wuri,ki tabbata kafin na dawo kin gyara ɗakin dake tsakar gida ki wanke banɗakin sannan ki saka labulayenki masu hasken nan,ki goge ƙurar cikin ɗakin da kyau,idan da hali ki saka masa wannan ƙamshin naki mai daɗi."
Jikin Mahreen ne ya ɗauki rawa,nan take ta hau jin wani sanyi na lulluɓe ta. Cikin ranta ta hau ayyana.
'Shikenan! Ta faru ta ƙare,Yah Maheer yayi aure ba tare da ya sanar dani ba. Kuma shine dan cin mutunci zai saka ni gyara wa amaryarsa ɗakin da za ta zauna. Babu komai,zan yi duk abinda ya ce domin umarninsa a koda yaushe gaba yake da buƙatata. Ya Allah ka sassauta min wannan zazzafan kishin da nake ji yana taso min a cikin zuciyata.'
Mahreen ta yi nisa a cikin tunaninta tare da zubar da hawaye ta ji hannun Yah Maheer ɗinta abun ƙaunarta ya na share mata hawayen. Da sauri ta sanya nata hannayen ta na sake share hawayenta tare da sanya murmushin yaƙe ta juya za ta shiga ɗaki. Hannu Yah Maheer ya saka ya dawo da ita ta tsaya a gabansa kanta a ƙasa ta na tsiyayar da hawaye. Murmushi yayi sannan ya ce.
"Sarkin kishi,ki kwantar da hankalinki domin ba abinda kike zargi bane. Na rantse maki da wanda ke busa min numfashi har yau ban ga macen da ta kai ki ba. Ke kaɗai nake gani a matsayin mace,kuma ke kaɗai ce wadda na yarda na amince ta san sirri na,a wajen ki kawai natsuwata take. Dan haka ki kwantar da hankalinki. Trust me my love ba zan taɓa aikata abinda zai dame ki ba. Bari na yi sauri na je ana jira na,ki yi abinda na ce please ki saka labulen nan naki mai shara-shara saboda zafi ake yi yanzu."
Kai Mahreen ta ɗaga masa kawai tana jin wata iriyar nutsuwa na shigarta,a hankali ta sakar masa murmushi suka yi sallama ya wuce asibiti. Ya na fita Mahreen ta hau gyaran ɗakin da ya gina a matsayin na mahaifiyarsa sai kuma ta rasu tun kafin a kammala ginin. Tun daga nan idan Yah Maheer na so ya tsokani Mahreen sai ya ce mata ai inda zai saka mata abokiyar zama kenan tinda Innah bata yi nisan kwanan da za ta rayu a ciki ba. Lokuta da dama sai dai ta yi dariya ta yi ta cika masa bakin bashi da chance ɗin ƙara aure a duniya,ya dai jira su je ƙiyama a bashi na aljannah. Cikin ƙanƙanin lokaci Mahreen ta wanke banɗaki ta wanke ɗakin tass sannan ta goge shi. Da