Chapter 10 Reading WADATAR ZUCI Complete Book by Aisha Alto.txt Arewa Novels

WADATAR ZUCI Complete Book by Aisha Alto.txt

Author :  Aisha Alto Category :  A Books

Chapter   10 / 38

27K to 30K   out of 113.4K words

wata rana akan abu ƙalilan sai dai kawai ya rufeta da duka, aiko da ranar sai yasan ko ita wacece wallahi dan sai ta nuna masa asalin kalarta.




Da ƙyar take iya haɗiyar miyau saboda yadda maƙoshinta yake raɗaɗi da zugin azaba.
Jin yadda bakinta yake mata raɗaɗin azaba ne shima yasa ta miƙe taje ta ɗauko ƙaramin madubi ta kunna fitilar torch light ɗinsu da suke haska ɗaki ta zauna a bakin gado tana haska fuskarta tana kallon kanta ta cikin ɗan madubin, wani masifaffen kuka ta saki lokacin da taga yadda bakinta ya suntume yayi wani dam kamar ganda ga fuskarta tayi jajir abunka da farar fata wuyanta kuwa inda ya shaƙeta har da shedar farcensa duk ya fito gashi yayi jajir alamar ba ƙaramin matsar azaba wuyan nata yasha a hannunsa ba.
Tunawa da tayi cikin satin nan ne zasu fara bikin ƙanwar Hajiya Lubna yasa ta sake rushewa da kukan takaici da baƙin ciki, sai yanzu ne ta sake tabbatar da cewa Ya Azeez mugu ne na ƙarshen zamani ya iya salon mugunta iri iri.


Wani uban kuka ta saka kafin ta ɗan rage sauti cikin murya ƙasa ƙasa tana faɗin "Wallahi bazan taɓa yafewa ba, mugu kawai mara imani...Allah ya isana kuma uwarka ɗin anƙi a gaishe tan kayi duk abinda zakayi mamugunci kawai munafiki...." Ta ƙarashe faɗa da ɗan ƙarfi ta yadda zai iya jiyota daga inda yake zaune a falon.




Karaf kuwa sai a kan kunnensa ya taso da sauri ya faɗo cikin ɗakin tana ganinsa ta zabura ta matsa gefe, ya matso gabanta ya tsaya a kanta cikin haɗe rai yana watsa mata wani mugun kallo yace "Sake maimaita abinda naji kin ce....?"
Tsit tayi taƙi tanka masa, a zafafe ya sake matsawa gabanta kamar zai kai mata duka yana faɗin "Nace ki maimaita abinda kika faɗa ko...?" Nan ma Fadwa tayi gum taƙi kulasa sai ma ta duƙar da kai ta hau ƙifƙifta idanu kamar wacce ta yiwa sarki ƙarya.


Ganin yadda tai wani tsumu tsumu ne a zaune tana zazzare ido yasa ya fahimci cewa duk a tsorace take da tsaiwar da yayi a kanta, ya zafga mata wata uwar harara lokaci ɗaya yana sakin tsaki kafin ya gyaɗa kai yana cewa "Ashe dai ke ƙaramar mara kunya ce mara mutuncin banza da wofi kawai, ashe iskancin naki kaɗan ne bai wuce cikin cokali ba, baki iya komai ba sai rashin kunyar ƙarya da fitsara..fitsararriya kawai...." Ya ƙarashe maganar a fusace lokaci ɗaya yana ɗaga hannu kamar zai kai mata mangari.


Ɗif tayi tana matsar ƙwallah tare da harararsa ƙasa ƙasa kafin ta ƙara matsawa gefe tana faɗin "To ai nidai babu abinda kaji nace...kuma ma ina ruwanka dani, mutum da bakinsa za'a hana masa magana ne kaji min wata lukutar masifa haka kawai. Allah ya yagawa mutum baki sai a nemi a hana mai magana saboda nuna iko da zalunci...?"
Ta ƙarashe maganar lokaci ɗaya tana murguɗa mai baki ƙasa ƙasa yadda ba zai gani ba.


Bai tanka mata ba ya raɓa ta gefenta ya wuce yana kaɗa kai, ya nufi inda jakar kayansa take yaje ya buɗe ya ɗauko wani farin wandon tree quarter mai kyau a ciki kana ya maida jakar ya rufe ya ajiye wandon akai sai daya cire kayan jikinsa yayi saura daga shi sai ɗan gajeren wandonsa baƙi ya ɗauki bokiti ya cika da ruwa ya fice daga ɗakin.


Da wata ƙatuwar harara Fadwa ta rakasa yana fita ta ɗauke kai lokaci ɗaya tana jan tsaki kana ta tashi da sauri taje ta ɗauko jakarta ta ciro sabuwar wayarta aciki ta kunna data, lambar Hajiya Labiba ta lalubo sai dai tayi rashin sa'a bata hau online ba, amma duk da haka sai da ta bar mata massage kana ta rufe datan ta saka wayar a silent ta mayar da ita cikin jaka ta ajiye, ko ta kan kayan bacci yau bata bi ba ta kwanta da zurmemiyar rigar da tayi sallah a jikinta tana sauke ajiyar zuciya.


Bata jima da kwanciya ba ya shigo ɗakin da bokiti a hannunsa ya ajiye sannan ya ɗauki ƙaramin tawul ɗinta wanda take amfani dashi idan ta fito wanka ya shiga goge jikinsa, tana jinsa tayi banza dashi bata motsa ba, shima bai sake bi ta kanta ba ya ci gaba da goge jikinsa sai da ya gama duk abubuwan daya saba yi kafin ya feshe ilahirin jikinsa da turarensa mai daɗin ƙamshi da sanyaya rai kana ya zura wandonsa ya haye gado ya kwanta a gefenta. Tana jinsa a kusa da ita ta zabura kamar wacce ta ga dodo, tayi sauri ta matsa can ƙarshen gadon ta juya masa baya tana kumbura baki tare da takure jikinta guri ɗaya tana rarraba idanu.
Shi dai ko kulata bai yi ba ya shiga karanto addu'ar kwanciya bacci ya gama ya shafe ilahirin jikinsa kana ya ja bargo ya lulluɓe jikinsa lokaci ɗaya yana lumshe idonsa, dan wani irin bacci ne sosai a idanunsa saboda yau gaba ɗayansa a gajiye yake tuɓus dan yasha aiki gashi ko abincin kirki bai samu yaci ba tun karin safe da yayi kafin ya fita shine har yanzu a cikinsa kasancewar lokacin daya dawo gida da nufin ya ɗan huta sannan ya samu ya ɗan ci wani abun shine ya iske gidan a kulle lokacin Fadwan bata nan, haka ya sake juyawa ya nufi gidansu dake can Unguwar Mu'azu a tunaninsa ko can ta tafi, yana zuwa can ɗin ma kuma ya iske mahaifinta a ƙofar gida ya dawo daga masallaci sallar magriba inda ya tabbatar mai da cewa Fadwa bata zo gidan ba kwata kwata yau, dan rabonta da zuwa ma kusan sati biyu kenan, abun ya matuƙar bashi mamaki sosai dan shi duk a zatonsa nan ɗin tazo bai ɗauka duk abinda ya gaya mata da safe kafin ya fita zai bi ta bayan kunnenta ya wuce bane bai shiga kunnen nata ba.


Shi kuwa Abbanta dama yana ganin Ya Azeez ɗin a irin wannan lokacin yasan tabbas akwai matsala dan haka ya matsa masa da tambayar abinda ke faruwa amma Ya Azeez yaƙi faɗa masa komai sai cewa yayi ba komai dama sunyi da ita ne zata zo gidan ta wuni shiyasa ya biyo dan ya ɗauketa su koma gida.
Ƙin yarda yayi da abinda ya faɗa ɗin dan haka yace masa ya jirasa ya shiga gida ya fito sai su wuce gidan tare yaga abinda ke faruwa, saboda yayi yayi dashi kan cewa ya gaya masa gaskiyar abinda yake faruwa amma yaƙi, shiyasa yace to ya tashi su tafi gidan tare saboda yasan abinda ke faruwa, domin gaba ɗaya zuciyarsa bata kwanta da abinda Ya Azeez ɗin ya faɗa masa ba. Haka dole ba dan yaso ba yana gani ya hau mashin ɗinsa shi kuma ya shiga keke napep ɗinsa suka kamo hanyar zuwa gidan.


Aiko nan suka iske har lokacin Fadwa bata dawo ba, haushi da takaicinta yasa Abbanta yace da Ya Azeez ɗin ya buge kwaɗon su shiga cikin gidan su zauna su jirata har zuwa lokacin da taga dama ta dawo, dan ba zai tafi ba har sai yaga dawowarta.


A hankali ya sauke ajiyar zuciya kana ya sake shigewa cikin ɗan yalolon bargon nasu lokaci ɗaya yana gyara kwanciyarsa, kafin ya matsa kusa da ita ya saka hannuwansa duka ya juyo da ita gaba ɗaya ya sakata cikin jikinsa, a hankali ya ɗago kanta ya ɗan sumbaci goshinta kana ya ƙanƙameta sosai yana sauke numfashi. Fadwa dake idanuwanta biyu duk tana jin abubuwan da yake mata amma tayi ɗif kamar mai bacci bata motsa ba.


A hankali a hankali tana jinsa yake ɗan shasshafa bayanta yana hura mata iskar bakinsa a cikin kunnenta da haka har bacci ya ɗaukesa ta fara jin saukar numfashinsa a gefen wuyanta, sai data bari baccin nasa yayi nisa sosai sannan a hankali ta zare jikinta a nasa ta matsa can ƙarshen gadon ta gyara kwanciyarta bayan ta lumshe idanunta da haka itama baccin yayi awon gaba da ita.








Washegari kuwa da ƙyar Fadwa ta iya tashi sakamakon wani zazzafan ciwon kai daya saukar mata tun cikin dare sai nishi take, wuyanta da maƙoshinta kuwa zafi suke mata, bata ko iya haɗiyar miyau saboda shaƙa da matsar da Ya Azeez yayi mata, a daddafe ta ita gabatar da sallar asuba wacce sai gurin ƙarfe 8am na safiya sannan tayi ta wanda shima saboda takurawar Ya Azeez da matsawarsa ne yasa ta lallaɓa ta tashi ba dan taso ba taje tayo alwala tazo ta gabatar da sallahn, tana idarwa kuwa ko hijabin jikinta bata tsaya cirewa ba ta koma gado ta kwanta ta ƙudundune tana jan ajiyar zuciya, ba jimawa ta sake komawa wani baccin.


Sai ƙarfe 11am sannan ta tashi lokacin shi kuwa Ya Azeez ya daɗe da ficewa gurin sana'arsa, gaban madubi taje ta tsaya tana ƙarewa bakinta kallo wanda har lokacin yake a suntume bai koma dai-dai ba, ga wani azababben raɗaɗin azaba da yake mata, hannu ta kai ta shafa saman inda yayi suntum ɗin kamar zata fashe da kuka tace "Wallahi Allah ya isana bazan taɓa yafewa ba, mugu kawai azzalumi mai baƙin hali..." Ta faɗa tare da fashewa da wani matsanancin kuka, kana ta wuce taje ta ɗauki bokiti ta ɗebi ruwa ta fice daga ɗakin zuwa banɗaki.
A haka tayi wankan tana ta mita da masifar yadda ya suntume mata baki ta koma kamar wacce aka naushe gurin kokawa, bata ƙara tsinkewa da lamarin ba kuwa sai lokacin da tazo yin brush taji wata azaba ta ziyarceta ba tasan lokacin da wasu sabbin hawaye suka soma silalowa kan fuskarta ba, dan ji tayi kamar ta ɗora hannu akai ta rushe da kuka saboda baƙin ciki. Haka nan dai ta daure ta lallaɓa ta wanke bakin tsaf sannan ta tashi ta koma ɗaki.


Sai data gama shafa mai sannan ta ɗauko wata atamfarta Avogan wacce aka yiwa ɗinkin doguwar riga da tasha adon stones a jiki kalarta brown da milk ne sai ɗan ratsin orange kaɗan a jiki ta zura, kayan sun mata kyau sosai sun zauna a jikinta sun mata ɗas, dan ɗinkin rigar irin mai ɗan matsewar nan ne daga sama daga ƙasa kuma ya buɗe, bata ɗaura ɗankwalin kayan ba ta fesa turare kawai ta ɗauki wayarta ta fita falo.


Wata ɓaƙar leda taci karo da ita ajiye a tsakar dakin sai wani ɗan madaidaicin ƙaramin kofin flas, ɗan taɓe bakinta tayi tare da watsawa kayan harara kafin ta zauna ta janyo kofin flas ɗin gabanta ta buɗe ruwan lifton ne a ciki sai titiri yake yana tashin ƙamshin kanumfari da citta, sakin tsaki tayi kana ta tashi taje ta ɗauko kofi da cokali sannan ta dawo ta zauna ta zuba lifton ɗin kana ta rufe flas ɗin ta jawo ledar ta buɗe, buredi da ƙosai ta gani a ciki sai wata ƴar guntuwar siga kaɗan a farar leda.


Sai data zuba sigan ta jujjuya kana ta ɗaga ta kai bakinta ta fara sha tana haɗawa da buredi da ƙosan, a haka ta cika cikinta taf sakamakon mugun daɗin da taji lifton ɗin yayi mata sosai dan sai data ƙara cika kofi ta shanye tas sannan taji cikinta yayi mata dam ta saki gyatsa kana ta ture flas da kofin gefe ta sake gyara zamanta sannan ta ɗauki wayarta ta lalubo numbern Hajiya Labiba ta danna mata kira.
Tana ta ringing bata ɗauka ba, haka har sai da ta kira kusan sau uku tana yankewa ba'a ɗauka ba, ana huɗun ma ta jima tana ringing dan har sai da ta cire rai dan tana gaf da tsinkewa taji an ɗaga cike da farin ciki ta sauke ajiyar zuciya tana faɗin "Hello Ƙawata kintashi lafiya..Allah yasa dai bani ce na tasheki ba..dan naga tun ɗazu nake ta kira baki ɗauka ba....?"




Daga can ɓangaren kuwa Hajiya Labiba wacce kiran wayar Fadwan ne ya tasheta daga bacci tana kwance akan makeken gadonta da yaji shimfiɗa da wani haɗaɗɗen lallausan zanin gado sai wani tattausan bargo data lulluɓe rabin jikinta dashi tayi luf ga sanyin Ac kota ko ina yana kaɗawa a cikin haɗaɗɗen bedroom ɗin nata wanda ya gaji da haɗuwa.
A hankali tayi juyi ta sake manna wayar sosai a kunnenta lokaci ɗaya tana ƙara gyara kwanciyarta kafin cikin muryar bacci da ƙosawa tace "Aiko dai kece kika tasheni da wannan shegen nacin kiran naki wallahi...." Ta ƙarashe faɗa tana sakin hamma alamar baccin bai gama isarta ba aka katse mata shi.


Murmushi kawai Fadwa tayi kafin tace "Ai wallahi na kasa haƙuri ne Ƙawata, duk na ƙagara in gaya miki abinda wannan azzalumin yayi min shiyasa nake ta kiranki, amma kiyi haƙuri ban san kina bacci ba na tasheki nasan bakyaso ana tashinki idan kina bacci...."


Da sauri Hajiya Labiba ta tashi zaune kafin tace "Kamar ya...? Ban gane ba meya miki kuma...kar dai ace fara dukanki yayi Azeez ɗin...?"


Fadwa da taji wasu hawayen baƙin ciki da ɓacin rai sun cika mata ido tasa hannu da sauri ta share kana ta girgiza mata kai kamar tana ganinta tace "A'a marina yayi kuma ya shaƙe min wuya ya matse min baki da maƙogwaro kamar zai kasheni sannan ya dinga zagina yana ta ce min kwaɗayayya mai bin gidajen ƙawaye maula, ba kiji cin mutunci ba iri iri haka ya dinga min, har yanzu wuyana kuwa in banda zugi da raɗaɗi babu abinda yake min, gashi bakina ya suntume leɓena yayi ƙato baki gani ba kamar ganda...wallahi mutumin nan mugu ne na bugawa a jarida, ba kiga irin muguntar da yayi min ba..." Ta ƙarashe maganar lokaci ɗaya tare da fashewa da kuka.




Wani uban ashar Hajiya Labiba ta mulmulo cike da ɓacin rai tace "Dan kutumar ubansa ance masa ke ɗin jaka ce da zai ware ƙwanjinsa a kanki kamar wata tsararsa saboda shi ɗan iska ne mugu salon yaje ya raunataki ya illata miki rayuwa, shine ya rasa inda zai gwadawa muguntarsa a jikinki sai fuskarki tunda yana baƙin ciki da kyaun da Allah yayi miki har da kumbura miki baki...? Ni da har ina tausaya masa ki gansa wani simi simi dashi kamar na Allah ashe shima ƙwallon shegen ne a ƙunshe ba'a sani ba, To wai uwar me ma kikayi masa da zai miki irin wannan rashin mutuncin...? Aiko wanda ya isa da gidansa ma bana jin zai iya yiwa matarsa wannan iskancin, ke ko zaginsa kikayi ba ki cancanci yayi miki wannan muguntar ba, banza kawai wawa..."
Ta ƙarashe maganar cike da masifa tana sauke numfarfashi.




Fadwa kuwa wani mugun daɗi ne ya lulluɓeta lokacin da taji irin masifar da Hajiya Labiba take yi akan irin abun da Ya Azeez yayi mata, dan tana bala'in son taga ana tausaya mata akan irin zaman ƙunci da takurar da takeyi a gidan aurenta, domin ita har ga Allah ba ko da yaushe bane take ɗaukan kanta a matsayin matar Ya Azeez, ita gaba ɗaya ma auren gani take kamar bata dashi.


Saboda haka ta sake marairaice fuska kamar tana gabanta tace "Wallahi idan kika ga irin wulaƙancin da yayi min jiya sai kin tausaya min, ke saboda tausayina da zakiji wallahi har kuka sai kinyi min...kamar fa wata jaka haka ya dinga matse min baki yana shaƙe min wuya kamar zai kasheni, kuma wai duk don kawai nace bazan gaisa da uwarsa ba shikenan sai masifa, sai kace gaisawar da ita ance dole ne, aiko na ƙi nace ai ba uwata bace kuma bazan gaishe tan ba, na kafe na nuna mai kalan nawa taurin kan na ƙeƙashe naƙi karɓan wayar nai ta faɗar maganganu kuma nasan duk makirar uwar tasa tana jina, itama munafuka mai fuska biyu. Ni wallahi Allah ma ya gani bana ƙaunar matar nan kwata kwata kamar yadda bana ƙaunar ɗan....."


Ƙamshin turaren data shaƙa ne yasa ta
ɗago kai a razane ba tare data ƙarasa maganar da tayi niyyar faɗa ba, ido huɗu sukayi dashi yana tsaye a bakin ƙofa ya harɗe duka hannuwansa duka a ƙirji ya zubo mata ido, zabura tayi ta matsa baya da sauri tare da zaro idanu waje cike da tsoro, kafin cikin firgici da tashin hankali ta soma ƙoƙarin tashi tsaye jiki na rawa ta saki wayar dake hannunta ta fara ja da baya da baya tana girgiza kai cike da matsanancin firgici da tashin hankali.
























*Ya Allah ka gafartawa iyayenmu da kakanninmu kasa aljanna fiddausi ta zamo makoma agaresu damu baki ɗaya 🤲*
[12/23, 10:16 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI*




*Wattpad: Aishaalto09*






1️⃣2️⃣






A hankali ya shiga takowa inda take yana ƙara kusantarta yayinda kuma har lokacin idanunsa ke tsaye ƙam a kanta ko ƙiftawa ba ya yi.


Ita kuwa Fadwa hakan yasa ta ƙara gigicewa ta kiɗime ta fara ɗaga hannayenta sama a tsorace tana faɗin "Nidai ai ba da kai nake ba kuma baka ji nayi maganarka ko na ambaci sunanka ba, kuma wallahi Allah ma ya gani iya abinda nasan kayi min jiya shi kawai nake bada labari....amma shine zaka wani zo ka tsatstsareni da ido kamar ka kama wata mai laifi....to kai mema kaji na faɗa tsakani da Allah nidai gaskiya karka ce zaka sake matsemin baki ko ka shaƙe min wuya in ba haka ba wallahi na rantse gidanmu zan tafi dan bazan zauna kaita min mugunta ba kamar ka samu jaka...."
Ta ƙarashe maganar a tsorace tana galla mai harara.


Ba tare daya tanka mata ba ya ƙarasa gabanta kawai ta ga ya duƙa ya ɗauki wayarta dake yashe a ƙasa ya ɗago a sanyaye yana jujjuya wayar a hannunsa cike da mamaki yayinda gefe guda a ransa kuwa tsantsar al'ajabinta ne ya ƙara cika masa zuciya, ɗago kai yayi a hankali yana kallonta dai-dai lokacin kuma kiran Hajiya Labiba ya shigo wayar, ga mamakinta kawai sai gani tayi ya miƙo mata wayar ba tare da yace mata komai ba ya juya ya matsa gefe guda yana yi mata alama data ɗauki kiran.


Tsaye kawai Fadwa tayi riƙe da wayar a hannunta tana binsa da kallo mai cike da mamaki, har kiran ya yanke ta kasa ɗagawa haka aka sake kira a karo na biyu nan ma ta kasa ɗagawa, duk yana kallonta da ya fahimci ganinsa ne ya hanata amsa wayar kawai sai ya saki murmushin yaƙe kafin ya juya lokaci ɗaya yana faɗin "To ni dai zan koma gurin sana'ata tunda naga jikin naki

10 / 38