Author : Aisha Alto Category : A Books
daɗa yaɗuwa tana kuma mamaye ilahirin lungu da saƙon gangar jikin nasa ba.
Wani irin yanayi yau ɗin ya tashi dashi wanda bai taɓa jin irinsa ba, kasancewar a iya tsawon rayuwarsa banda mahaifiyarsa da Imaan bai taɓa jin son wata halitta irin kwatankwacin son da yake yiwa Shatu ba, tunda ya taso kuma bai taɓa haɗuwa da wata macen da ta taɓa burgesa har ta tafi da natsuwarsa lokaci guda irin Shatu ba.
Dan ko Fadwa ya dai aureta ne kawai saboda ya sharewa Abba hawaye akan abubuwan da take yi a lokacin, amma tunda yake bai taɓa jin sonta ba dai-dai da ƙwayar zarra a zuciyarsa, kuma a haka ya zauna da ita ba tare da koda wasa ya taɓa nuna mata cewa baya ra'ayintan ba.
Idanunsa ya ɗan lumshe da sauri sakamakon tunawa da yayi da yanayin surar jikinta da yadda komai nata yake da kyau da matuƙar ɗaukar hankali tamkar itace ta tsarawa kanta komai.
A hankali ya fesar da wani zazzafan numfashi mai cike da zallar shauki da muradi.
Ajiyar zuciya ya sauke saboda wani irin daddaɗan yanayi da yake ji yana yi masa yawo a cikin jikinsa, kafin a hankali kuma ya lumshe idanunsa tare da harɗe hannuwansa ya sake gyara kwanciyarsa a saman doguwar kujerar dake falonsa, wanda kuma tun dawowarsu daga masallaci sallar asuba ne shi dasu Abba ya kwanta anan ɗin yana ta saƙe saƙe, ya kasa tashi ya koma cikin bedroom ɗinsa.
A haka yana ta nazari da tunane tunane har wani daddaɗan bacci yayi nasarar ɗaukarsa, saboda rashin isasshen baccin da bai samu yi ba a daren jiya.
SHATU
Kwance take a saman makeken gadonta wanda yasha shimfiɗa da lallausan zanin gado na alfarma, irin kwanciyar nan ta rigingine ce tayi idanunta na kallon saman ɗakin, yayinda take sanye da wata ƴar shimi mai shara shara mara nauyi a jikinta.
Kyawawan idanuwanta ta lumshe a hankali tare da waresu lokaci ɗaya tana sauke wata sassanyar ajiyar zuciya mai cike da tsantsar farin ciki da jin daɗi.
Juyawa tayi a hankali tana mai saƙawa da kwancewa a zuciyarta, inda yanzu kuma gabaki ɗaya duk haushin kanta take ji.
Can kuma wani sashi na zuciyarta ya fara hasaso mata wasu manya manyan abubuwa dake tattare da Ya Azeez ɗin.
Lallai tabbas ita ɗin mai sa'a ce a rayuwarta, har yanzu kuma ganin abun take tamkar a mafarki, sake juyawa tayi a hankali ta mirgina ƙarshen gadon kana ta cigaba da tunani.
To wai mema ya hanata ɗaukar wayarsa ne jiya daya kirata, gashi yanzu rashin kiran nasa kuma duk ya dameta..? Toh ko dai yaji haushi ne da bata ɗauki kiran nasa jiyan ba..?
Ɗan jim kaɗan tayi tana tunani, kana kuma can sai ta saki ƙaramin murmushi kafin kuma a fili ta ba kanta amsa da cewa "Jan aji mana, kuma ai hausawa sunce mai son ɗan tsuntsu shike binsa da jifa, saboda haka ina kyakkyawan zamana zai nemeni da kansa..."
Ƙarar wayarta dake aje a gefen filonta ne ta katse mata tunanin da take yi, wayar ta ɗauka ganin kuma sunan Ya Abdul ne ke yawo akan screen ɗin wayar yasa ta sakin wani ƙayataccen murmushi kafin cikin hanzari ta ɗaga kiran ta manna wayar a kunnenta tayi shiru ba tare da tayi magana ba.
Daga can ɓangaren Ya Azeez kuwa jin ta ɗaga wayar ne yasa shi sakin wata sassanyan ajiyar zuciya kafin kuma cikin wata irin daddaɗar murya mai taushi yace "Ki fito ina harabar gidanku ina jiranki..." Ya faɗa kai tsaye kana daga haka kawai ya katse wayar.
Da sauri ta buɗe idanunta dake lumshe tare da tashi zaune cike da tsantsar mamaki tana duban agogon dake maƙale ajikin bangon ɗakin, ƙarfe 9am dai-dai ta gani.
Zuro ƙafafuwanta ƙasa tayi da sauri ta sauka daga kan gadon ta zura bedroom silifas ɗinta kana ta juya tana ƙoƙarin kwance igiyoyin rigar baccin dake jikinta lokaci ɗaya tana sake duban agogon bangon dake ɗakin.
Tuna abinda yace ne kuma yasa ta juyawa kai tsaye ta shige toilet da sauri dan yin wanka.
Sanin da tayi cewar yana jiranta ne kuma yasa bata wani ɓata lokaci a wajen yin wankan nata ba ta fito.
Koda ta fito kuwa mai kawai ta ɗan shafa ajikinta, sai ƴar hoda kaɗan da ta ɗan mutstsuka sannan ta shafa lipstick a kyawawan laɓɓanta masu taushi da tsantsi.
A gurguje ta feshe ilahirin jikinta da sassanyan body spray ɗinta masu sanyin ƙamshi da sanyaya zuciya.
Ƙarasawa tayi gaban wardrobe ɗinta ta buɗe inda ta zaro wata haɗaɗɗiyar doguwar rigar material na yadin roba roba mai kyau kalar sararin samaniya ta zura ajikinta, kana ta saka wani takalmi mai tsini fari a ƙafarta, sannan ta yane kanta da wani ɗan madaidaicin gyale shima fari.
Murmushi ne ya bayyana akan kyakkyawar fuskarta, saboda ganin irin kyaun da kayan suka yi mata lokacin data kalli kanta a cikin madubi.
Wayarta ta ɗauka ta riƙe a hannunta kana ta juya ta fice daga cikin ɗakin, a falo ta samu Ummi da Zahra a zaune suna hira, wanda bayan sun kammala breakfast ne kuma suka dawo falon suka zauna suna hira.
Ƙarar takun takalminta da suka ji ne kuma yasa su juyowa a tare suka zubo mata idanunsu gaba ɗaya suna kallonta.
"Masha Allah Aunty Shatu kinyi kyau sosai, wallahi kamar kin sauko daga Saudiya..."
Cewar Zahra da ta wani hangame baki da hanci tana kallon Shatun.
Ita kuwa Shatu ƙarasa saukowa cikin falon tayi tana hararar Zahran da har lokacin bakinta ke hangame tana kallonta.
Ganinta cikin shirin da sukayi ne kuma yasa Ummi cewa "Ina zakije haka kuma tunda sassafe ko karyawa ba kiyi ba...?"
Ɗan kwaɓe fuskarta tayi tana ƙarasowa gaban Ummin ta ɗan rusuna, kafin a kunyace tace "Zan ɗan fita ne gurin Ya..uhmm Ya Abdul tun ɗazu yazo yana jirana...."
Wani tsalle Zahra tayi ta miƙe tsaye cikin tsananin farin ciki tana faɗin "Innalillahi kai Aunty Shatu amma shine baki gaya min ba inje in gaishesa..? Gaskiya baki kyauta min ba nidai ban ji daɗi ba..."
Ta faɗa a shagwaɓe tana turo baki.
Zafga mata harara Shatu tayi kafin tace "Ba dole in gaya miki ba, tunda gurinki yazo..."
Ummi kuwa har a cikin ranta Allah ya sani taji daɗin abun sosai, dan haka da saurin ta ta miƙe tsaye tana faɗin "Zahra tashi maza ki ɗauki key kije ki buɗe masa falon baƙi ki kaishi, ke kuma ƴan mata tsaya ki tafin mai da breakfast..." Ta faɗa tana wucewa kichin da sauri.
Itako Zahra da gudu ta haura sama taje ta dauko makullin falon baƙin tazo ta fice da hanzari, Shatu kuwa tana nan tsaye Ummi ta fito riƙe da ɗan madaidaicin farati a hannunta, ƙarba Shatun tayi kana tasa kai ta fice daga falon.
Tana ƙarasawa falon kuwa tun kafin ta shiga take jiyo surutun Zahra duk ya cika gurin, girgiza kai kawai tayi kafin ta tura ƙofar lokaci ɗaya ta shiga cikin falon bakinta ɗauke da sallama.
Dai-dai lokacin kuma Ya Azeez wanda ke zaune akan ɗaya daga cikin kujerun dake facing ɗin ƙofar shigowa falon ya ɗago kansa kenan fuskarsa ɗauke da murmushin dake ƙara masa wani tsantsar kyau da haiba yana kallon Zahra.
Karaf kuwa idanunsu suka sarƙe a cikin na juna, da sauri ta maida kanta ƙasa dan bata jin zata iya jurar kallon cikin ƙwayar idanunsa masu matuƙar kashe mata jiki su saukar mata da kasala.
Tunda ta duƙar da kanta bata ƙara ɗagowa ba daga bakin ƙofar ta coge ta sunkuyar da kanta, Zahra kuwa ganin haka yasa ta miƙe ta matsa kusa da ita ta karɓi farantin dake hannunta taje ta ajiye a gabansa, kana ta ɗago ta kallesa tana faɗin "Ya Abdul bara na shiga ciki tunda amaryar ta ƙaraso idan ka fito sai muyi sallama, Aunty Shatu a fito lafiya..." Ta faɗa tana ficewa daga cikin falon da hanzari tana dariya.
Sun kusan mintuna goma a haka tun bayan fitar Zahra Shatu bata ɗara daga inda take ba, ganin kuma bata da niyyar ƙarasowan ne ta zauna yasa Ya Azeez miƙewa a hankali ya ƙaraso inda take, wanda kuma Shatu kwata kwata bata san da ƙarasowar tasa ba kawai sai jin amon daddaɗar muryarsa tayi haɗe kuma da sassanyan ƙamshi turarensa daya gauraya da numfashinta suka saukar mata da wani daddaɗan yanayi mai wuyar fassara.
Cikin wani irin yanayi yake kallonta shima kafin kuma ya ƙara matsawa kusa da ita sosai yana faɗin "Pls mana Eishatuna, dan Allah horon ya isa haka, ki sassauta min ba dan halina ba..." Ya faɗa cikin marairaice murya yana kallonta.
Wani irin sanyi taji ya ziyarci zuciyarta, wanda hakan kuma yasa ta ɗagowa da sauri tana lumshe kyawawan idanunta, a cikin ranta kuwa faɗi take "Nima dauriya kawai nake, amma tuni soyayyarka ta riga da ta gama min kamun kazar kuku ta fatattaka zuciyata, tayi mata dalla dalla..." Ta faɗa tana turo ɗan ƙaramin bakinta gaba kamar zatayi kuka.
"Pls na roƙeƙi ki daina wahalar dani ta hanyar yiwa kunnuwana rowar jin daddaɗar muryarki dan Allah Eishatunaaa..."
Ya ƙare maganar cikin wata iriyar kasalalliyar murya da shi kansa bai taɓa sanin zai iya irinta ba.
Shatu kuwa jin abinda ya faɗa ɗin ne yasa ta sake yin ƙasa da kanta, tare da lumshe idanunta, kafin kuma ta ɗan buɗe a hankali tana faɗin "Ina kwana...?"
Idanunsa ya ɗan lumshe saboda wani irin abu na musamman da yaji ya taɓa zuciyarsa kana a hankali kuma yana ratsa dukkan ilahirin lungu da saƙon gangar jikinsa.
Ɗan ƙaramin bakinta ya kalla kafin kuma cikin kasalar da muryar tata ta saukar masa yace "Lafiya Alhamdulillahi Eishatuna, yasu Ummi da Abbie...?"
A hankali ta amsa da Lafiyarsu ƙalau, kana kuma tace "Muje ka zauna in zuba maka abincin kar yayi sanyi..."
Ta faɗa tare da wucesa ta ƙarasa tsakiyar falon inda Zahra ta ajiye farantin abincin ta zauna a ƙasan kafet ɗin daya mamaye falon bayan ta tanƙwashe ƙafafunta ta buɗe kulan tare da ɗauko filet ta zuba mai soyayyen dankali da kwai, sai source ɗin hanta da taji albasa kaɗan da ta ɗan zuba mai daga gefe guda, kana ta haɗa mai tea mai kauri ta aje a gabansa.
Ƙarasowa yayi ya zauna akan kujerar dake kallonta, kana ya ɗauki kofin data haɗa masa kakkauran tean a ciki ya kai bakinsa ya soma kurɓa a hankali a hankali yana lumshe idanunsa cike da nishaɗi.
Shatu kuwa har lokacin kanta na ƙasa bata ɗago ba sai faman wasa take da yatsun hannunta.
Bai wani ci dankalin sosai ba kaɗan kawai ya ɗan tsakura ya ci, sai tean daya shanye tas.
Bayan ya gama ne kuma ta tattare kayan ta matsar da farantin gefe kana ta koma kujarar kusa dashi ta zauna ta sunkuyar da kanta ƙasa tana wasa da adon zaren dake jikin gyalenta.
Ajiyar zuciya Ya Azeez ya sauke, kana kuma cikin tsananin so da ƙaunarta yace "Ɗago kanki ki kyalleni pls..." Ya faɗa cikin taushin murya yana kallonta.
Ɗagowa tayi a hankali ta kallesa, kafin kuma ta maida kanta ƙasa tana jin wani baƙon yanayi mai saukar da farin ciki yana ziyartarta.
Kallonta Ya Azeez ɗin yayi kafin yace "Pls mana Eishatuna kinji...?" Ya faɗa cikin wata irin narkakkiyar murya kana lokaci ɗaya yana sakar mata manyan idanuwansa.
Da sauri Shatu ta ɗago kai tana kallonsa, kafin kuma kai tsaye ta tsinci kanta da furta "Na daina bazan sake ƙin ɗaukar wayarka ba, kayi haƙuri..."
Ta faɗa a hankali tare da rufe idanunta tana murmushi.
Saurin riƙo hannunta yayi ya matso kusa da ita ya zauna a gefenta yana faɗin "Nagode Eishatuna..." Ya faɗa cike da tsantsar farin ciki yana kallon kyakkyawar fuskarta.
Ɗan janye jikinta tayi a nasa ta matsa gefe tana murmushi, ganin kuma yadda tayi ne yasa shi ɗan matsawa gefe shima yana murmushin.
Wanda kuma a dai-dai lokacin wayarsa dake cikin aljihun rigar tsadaddiyar shaddar jikinsa ta ɗauki ƙara, zaro wayar yayi ganin sunan Fahad yasa ya kwaɓe fuska kafin ya ɗauka ya manna a kunnensa yayi shiru ba tare da yayi magana ba.
Daga can ɓangaren Fahad kuwa jin ya ɗaga wayar yayi shiru ne, yasa ya hau faɗa yana cewa "Wai dan Allah kana ina ne, tun fa ɗazu ina ofis ina jiranka amma har yanzu baka fito ba, kuma ka sani yau zamu gana da baƙin mu da suka zo daga Lagos ƙarfe 10am amma shine har gashi yanzu ƙarfe 9:45 baka fito ba, kuma Abba da Mami sun tabbatar min da cewa tun ɗazu ka fita, amma shine har yanzu baka ƙaraso ba..to wai gidan uwarwa ma ka tsaya ne, ina kaje tunda sassafen nan...?"
Ɗan kwaɓe fuska Ya Azeez yayi kafin yace "Karka cika min kunne dan Allah Malam ina gurin amaryata..."
Ya faɗa kai tsaye kana daga haka ya katse wayar ya mayar cikin aljihu.
Shatu kuwa da tunda ya fara wayar take ta kallonsa tana murmushi sakamakon duk ta jin abinda Fahad ɗin ya faɗa, kasancewar kuma a handfree Ya Azeez ɗin ya saka wayar, yayinda kuma ganin ya gama wayar ne ya ƙara gyara zama alamar bai da niyyar tafiya yasa tace "Pls mana Ya Abdul tashi kaje ana jiranka..."
Juyowa yayi ya ɗan kalleta kafin kuma cikin kwaɓe fuska yace "A'a nidai ba inda zanje yau ina nan tare da Eishatuna..."
Kallonsa tayi kafin tace "Pls mana Ya Abdul kaje dan Allah ai zamuyi waya..."
Ta faɗa cikin magiya tana kallonsa, ganin yadda ta wani marairaice masa ne kuma yasa ya miƙe ba dan yaso ba gashi sai faman narke masa take tana ƙara kashe masa jiki da zuciya da salon soyayyarta mai matuƙar tsayawa arai da zuciya.
"Kin tabbatar dai zamuyi waya ko...?" Ya Azeez ɗin ya faɗa murya a sanyaye yana tsura mata idanu.
Gyaɗa masa kai tayi cike da tabbatarwa kafin ta miƙe tsaye tana cewa "Insha Allahu da kaina ma zan kiraka karka damu..."
Cike da jin daɗi ya amsa da Toh ina jira, kana daga haka ya juya suka fice daga falon, har gurin motarsa ta rakosa wanda sai da taga ficewarsa daga cikin gidan sannan ta juya bayan ta ɗauko farantin ta kulle falon da key ta wuce cikin gida.
FADWA
Sosai suke shan soyayyarsu ita da sabon saurayinta, wanda yanzu kusan kullum sai yazo gidan taɗi gurinta, yayinda kuma kullum idan zaizo sai ya taho musu da kayan ciye ciye iri iri ya kawo musu.
Duniya sabuwa a gurin Mama da Fadwa, an samu abinda akeso babu abinda ya damesu yanzu sha'anin gabansu kawai sukeyi.
A ɓangaren Fadwa kuwa yanzu burinta ya gama cika ta gama samun abinda takeso, shiyasa yanzu da gayya take shiga cikin ƙawayenta tana fankama saboda yanzu gaba ɗayansu babu wacce zata nuna mata wani abu, dan hatta da tsadaddiyar wayar da take riƙewa irin ta hannun Hajiya Lubna ce da Hajiya Labiba, shiyasa yanzu ko bi ta kansu bata cika yi ba.
Dan har gwara gwara Hajiya Labiba ma ta kan ɗan je gidanta wani lokacin, amma Hajiya Lubna kam tun ranar da tayi mata faɗa tace ta koma gidan Ya Azeez domin shine rufin asirinta, Fadwa ta rufe ido tayi mata kaca kaca, kuma tace daga yau ta fita harkarta babu ruwanta da ita kowa yayi ta kansa, saboda ita a ganinta yanzu duk wanda zai ga irin cigaban da take ciki yazo yana mata maganar komawa gidan Ya Azeez to ba masoyinta bane, cikakken maƙiyinta ne, domin ya nuna mata tsantsar hassada da baƙin ciki.
Toh tun daga wannan ranar da sukayi haka kuwa basu sake haɗuwa ba, sai wata rana da tasa Alhajinta ya kaita gidan Hajiya Labiba suka haɗu da Hajiya Lubnan acan, tana shiga kuwa ko zama ba tayi ba ta juya ta koma gida, dan acewarta bata son duk wani abu da zai sake haɗata inuwa ɗaya da Hajiya Lubna da take yi mata kallon babbar maƙiyiyar a yanzu.
Wanda kuma duk waɗannan abubuwan da suke faruwa Abba bai da masaniya ko kaɗan akai, dan kullum idan ya fita kasuwa tun safe baya dawowa gida sai dare, inda kuma zuwa lokacin sosai harkar kasuwancinsa ya ƙara haɓɓaka, dan zuwa yanzu gaba ɗayansu sun san cewa ya samu aikin tsaron shago a kasuwa, dan ko da wasa bai taɓa gaya musu cewa shagon mallakinsa bane ballantana kuma su san cewa Ya Azeez ne ya samu kuɗi har ya buɗe masa shi.
Sai dai kuma zuwa yanzu yanayin samun Abban yana matuƙar ɗaure musu kai da basu mamaki, domin yanzu duk wata yake siyo musu tilin kayan abinci ya kawo ya aje musu sannan ya siyo musu komai da yasan zasu buƙata, ga abubuwa sosai daya canja musu a cikin gidan, dan hatta da makarantar boko da islamiyya yanzu ta kuɗi su Ilham da Amatullah suke zuwa, sannan duk abinda yasan zasu buƙata ba sai ya jira sun tambaya ba haka yake siyowa yazo ya ajiye musu, shiyasa yanzu babu abinda suka nema suka rasa.
Wanda kuma hakan kwata kwata bai taɓa ɗaɗa Mama da ƙasa ba, domin duk wannan kyautatawar da yake musu ko ajikinta bata gani, ballantana taga ƙoƙarinsa.
Ita kawai babban burinta yanzu shine taga Fadwa ta auri Alhaji Zailani, shine kawai hankalinta zai kwanta idan tasan cewa ƴarta na gidan arziki tana auren mai kuɗi suna damawa yadda suke so suna abinda suka ga dama.
Shiyasa ma tuni ta watsar da sana'ar ƙuli ƙuli da kayan miyan da take yi, dan yanzu gani take tafi ƙarfin wannan sana'ar ta wuce da saninta kuma, yanzu jira kawai take idan komai ya gama daidaita tsakanin Fadwa da Alhaji Zailani yayi mata Visa ta dinga fita ƙasashen waje tana harkar Saudi da Dubai, itama ta faso gari tana damawa da manyan mata.
*********
*BAYAN WATA UKU*
Zuwa lokacin haka abubuwa sukayi ta gudana da daɗi ba daɗi.
A ɓangaren Shatu da Ya Azeez kuwa komai yana ta tafiya dai-dai, domin yanzu har ta kai basu iya ɓoye irin tsananin soyayyar da suke yiwa junansu ko a gaban waye.
Wani lokaci ita kanta Zahra har mamaki take idan taga Shatu na yin wasu abubuwan, ballantana idan taga yadda take faman rawar jiki akan Ya Azeez abun har ɗaure mata kai yake yi.
Haka kuma shima a ɓangaren Ya Azeez ɗin gaba ɗaya ya gama susucewa akan Shatun.
Sosai suke gudanar da tsaftatacciyar soyayyarsu hankali kwance babu abinda ya