Author : Aisha Alto Category : A Books
amfani a wajen AbdulAzeez, ke ba komai bace a cikin rayuwarsa face banza, baki da wani amfanin da kike yi masa...."
Ya ƙarashe maganar cikin ɗaga murya da hargowa.
Wani kukan baƙin ciki da takaici Fadwa ta fashe dashi kafin ta miƙe itama cikin ihun kuka tana faɗin "Sai me AbdulAzeez...nace sai me..nima ai ba amfanin komai ɗin kake yi min ba, wanene kai..? Meye kai ɗin da har Fadwa zata damu da rashinka a rayuwarta...meye kai me kake dashi, dame kake taƙama wanda har zanyi takaicin ace yau na rasaka..? Kai ɗin banza kai ɗin wofi me ka taɓa tsinana min a zamana da kai..me na ƙaru dashi duk tsawon wannan watannin da nai a tare da kai..?
Ka sakeni tunda bani da wani amfani a wajenka, ka sakeni ka gani AbdulAzeez idan zan ƙara ko da second ɗaya ne a wannan matsiyacin ruɓaɓɓen gidan naka, da kake tutiya dashi kake wani ɗaga hanci kana tinƙaho da ɓaɓatu sai kace naka, ka sakeni ka gani idan daga yau rayuwar Fadwa zata wulaƙanta kota ƙasƙanta...AbdulAzeez ka sakeni nace...!"
Ta faɗa a zafafe cikin hargowa tana ƙara fashewa da kuka.
Da kallo kawai Ya Azeez yake binta lokaci ɗaya kuma sai jikinsa yay bala'in sanyi, wani irin tafarfasa zuciyarsa ke yi idanuwansa kuwa sun kaɗa sunyi jajir saboda tsabar baƙin ciki da tashin hankali, kai kawai ya kaɗa kafin ya juya da sauri zai fice daga gidan, ganin haka yasa Fadwa tashi da sauri tana kuka tasha gabansa tana faɗin "Ina zaka tafi kuma ba tare daka sakeni ba...?" Ta faɗa kai tsaye cikin tsantsar rashin tsoro da bushewar zuciya tana watsa masa mugun kallo.
Matsar da ita gefe yayi a hankali yana ƙoƙarin danne ɓacin ran dake taso masa, ya raɓa ta gefenta zai wuce, da sauri ta sake shan gabansa tana watsa masa wani mugun kallo da idanuwanta da suka kaɗa jajir saboda tsabar kukan data sha, kafin kuma cikin tsananin ɓacin rai tace "Wallahi babu inda zakaje saika sakeni AbdulAzeez, indai kai cikakken ɗan halak ne kuma cikin uwarsa da ubansa ba shege ba, to yau ka sakeni ka sawaƙe min wannan ƙaddararren munafukin auren naka nima in huta da wannan masifaffiyar jarabar ko zanyi rayuwar ƴanci da salama..."
Sosai ran Ya Azeez ɗin ya ƙara ɓaci, dan hatta jikinsa rawa ya ɗauka.
Ƙasa yayi da kansa yana ƙara jin wani ɗaci da tsananin baƙin ciki a cikin ransa, ɗagowa yayi yana kallon Fadwa da idanuwansa da suka ƙara runewa da zallar ɓacin rai da tsantsar damuwa, jikinsa har rawa yake, saboda tsabar baƙin ciki da tashin hankali, yayinda a lokaci guda kuma maganganunta suke ƙara kai kawo a ƙwaƙwalwarsa, cikin ƙaraji kunnuwansa ke masa amsa kuwwar muryarta tana ƙara maimaita masa.
"Indai kai cikakken ɗan halak ne kuma cikin uwarsa da ubansa ba shege ba, to ka sakeni ka sawaƙe min wannan ƙaddararren auren naka nima in huta da wannan masifaffiyar jarabar ko zanyi rayuwar ƴanci da salama...!!!
Sosai idanuwansa suka ƙara kaɗawa jajir, jijiyoyin kansa suka fito raɗa raɗa agaban goshinsa, da ƙyar ya buɗe baki cikin tsananin ɓacin rai ya furta "Kije na sakeki saki ɗaya Fadwa, ki fita ki bar min gida..."
Ya faɗa muryarsa cike da amon sauti mai cike da tsantsar takaici da ɓacin rai.
Rass rass rasss! Gaban Fadwa ya yanke ya faɗi, yayinda a kuma lokaci guda fargaba da tsananin tashin hankali suka ziyarceta, amma sai bata nuna ba tayi ƙoƙarin ɓoye fargabarta da tashin hankalinta.
Murmushin yaƙe ta saki a ƙoƙarinta na son ɓoye razanarta tace "Sai me dan ka sakeni AbdulAzeez..Nace sai me..? Mena tsinta a gidan naka dama in banda baƙin ciki da ƙuncin rayuwa..? Kuma da kake maganar in fita in bar maka gidanka ai naga nan ɗin ba gidanka bane kaima haya ka kama, kuma duk abinka dai dole kaima ka fita ka barwa masu gida gidansu tunda bana gado bane..."
Wani ɓacin rai mai zafi ne ya ziyarci zuciyar Ya Azeez, haɗe fuska yayi ba tare kuma da ya ce komai ba ya juya kawai yasa kai ya fice daga cikin gidan.
Ganin haka yasa ta bishi da sauri har ƙofar gidan, sai dai ko kafin ta cimmasa har ya sha kwana yabi ta lungun bayan gidansu ya fice daga layin gabaki ɗaya.
Dawowa tayi cikin gidan a ƙofar ɗakin ta tsaya, sai a lokacin ne kuma wani kukan nadama ya taho mata, mai cike da tsantsar danasani da baƙin ciki.
"Yanzu fa shikenan Ya Azeez ya saketa ta zama bazawara kenan..? Yanzu ta tashi daga sahun matar aure ta koma bazawara..."
Wani gefe na zuciyarta kuwa cewa take "Toh ai farin ciki ya kamata kiyi Fadwa ba baƙin ciki ba, tunda dama abinda kike muradi kenan, kuma anyi miki kamata yayi ki murna ki nuna jin daɗinki ba ki tsaya kuka ba banza kina ƙara ɓatawa kanki lokaci ba..."
Saurin gyaɗa kanta tayi tana sakin murmushi, kafin ta jinjina kai a hankali tana faɗin "Tabbas kuwa, kuma yanzu ne nake da iko da lasisin da zanyi duk abinda nakeso kuma nake buri..." Ta faɗa a fili yayinda kuma a lokaci guda take jin wani irin sanyin daɗi na ratsa zuciyarta.
A sanyaye ta shiga cikin ɗakin, direct ta wuce uwar ɗaka ta fara harhaɗa kayanta a babban akwatinta, sai data cika akwatin taf da kayanta, sannan ta gyara zaman gyalen dake kanta ta ɗauki ƙaramar jakarta da wayarta ta zura flat shoe a ƙafarta saɓanin ɗazu data dawo da mai tsini a ƙafarta.
A hankali take jawo akwatin har ta fito dashi daga cikin ɗakin, sai a lokacin ne kuma ta samu zarafin duba agogon wayarta ƙarfe 9:20pm ta gani, saka wayar tayi a cikin jakarta kana ta ratayar jakar a kafaɗarta.
Cikin sanyi jiki take jan akwatin da ƙyar, da haka har ta samu ta fice daga cikin gidan.
Koda ta ƙarasa bakin titi ta daɗe a tsaye kafin da ƙyar ta samu napep, sai da ta gaya masa inda zai kaita sannan ta hau yaja suka wuce.
Sai da taga mai napep ɗin ya shiga cikin unguwarsu, sannan ta fara jin tsoron ƙarasawa gidan, zuciyarta ta fara raya mata tana shiga Abbanta korarta zaiyi yace ta fitar mai daga gida, take ta tuna da kalaman daya gaya mata ranar da taje zuwanta na ƙarshe gidan, yayinda wani ɓangare na zuciyarta kuma ke raya mata ba ta yadda za'ayi ya koreta, tunda bata da inda ya fiye mata nan, dole zai yi haƙuri ya barta ta zauna.
Misalin ƙarfe 9:55pm. Mai napep ɗin ya direta a ƙofar gidansu, a hankali ta fito daga cikin napep ɗin bayan ta sauko akwatinta ƙasa ta buɗe jakarta ta zaro ɗari biyar ta miƙa masa, kana ta ja akwatin da ƙyar a hankali ta shige cikin gidan.
Tana gaf da shiga zauren gidan ne kuma sai taja ta tsaya tana tunanin idan ta shiga to meza tace..? Take wani bala'in tsoron haɗuwarta da Abbanta ya cika mata zuciya, ganin tsaiwar tata babu amfanin da zata ƙara mata, sai ma wani laifin da zata ƙarawa kanta yasa tayi shahada kawai tasa kai ta shige cikin gidan kai tsaye.
YA AZEEZ
Acan ɓangaren Ya Azeez kuwa sai da yaga fitarta daga gidan, sannan ya fito daga maɓoyarsa ya koma cikin gidan da tunanin Allah yasa dai gida ta nufa, kar kuma tace zata tafi gidan ƙawayenta a wannan daren, ɗakin ya shiga ya zauna a falo ya dafe kansa yana ƙoƙarin daidaita numfashinsa, sake ɗago kansa yayi yana kallon tsakar ɗakin kafin kuma ya sake matsawa sosai ya jingina kansa da jikin bangon ɗakin ya ɗaga kansa sama yana jin nauyin daya dabaibaye zuciyarsa lokaci ɗaya yana sauka a hankali a hankali.
Sai daya daɗe a zaune yana saƙawa da kwancewa sannan ya fara tunanin da wane ido zai kalli Abba..? Me zai faɗa masa..? Taya zai fara tunkararsa yayi masa bayani..? Anya zai fahimcesa kuwa..? Toh idan ya tuhumesa dalili me zai faɗa masa..? Yace masa bata zaman gida ne ko kuwa tun matsalar da ya sani dai tun farko itace dalilin da yasa har ya kasa haƙuri ya saketa..? Ko kuwa zai faɗa masa cewa ta tafi bikin ƙanwar ƙawarta ne tayi kwana da kwanaki, shi kuma haushin hakan yasa ya saketa..?
Can sai ya miƙe tsaye da sauri ya fara kai kawo yana zagaya ɗakin, sai a lokacin ya ƙara shiga kogin danasani.
Tabbas bai kyautawa Abba ba, bai kuma cancanci irin wannan sakayyar daga garesa ba, to shi me ma ya harzuƙasa ne da har ya yanke wannan hukuncin ba tare da yayi tunani mai zurfi ba, bai kuma duba abinda zai je ya dawo ba..?
Da sauri ya girgiza kansa yana ɗan saurarawa kafin kuma cikin sanyin jiki ya furta "Iyayena fa ta zaga, tace idan ni cikakken ɗan halak ne cikin uwarsa da ubansa ba shege ba, in saketa..." Ya faɗa a fili lokaci ɗaya yana ƙara jin wani tsantsar ɓacin rai da baƙin ciki na sake bijiro masa tamkar a lokacin Fadwa ke zagin iyayen nasa.
FADWA
Tana saka ƙafarta cikin gidan tai arba da Abba da Mama dake zaune a tsakar gidan kan tabarma suna hira.
Cikin rashin kuzari ta taka a hankali ta isa gabansu ta durƙusa, da sauri duk suka ɗago kai a tare suka kalleta, kafin kuma Abba ya juya da sauri ya kalli akwatin data shigo dashi, girgiza kansa kawai yayi cikin tarin takaici da tsantsar damuwa yana faɗin "Lallai yau da ganin alamu Fadwa kin ƙure haƙurin AbdulAzeez, tunda gashi har ya gaji da halinki ya sakoki..."
Cikin rashin jin daɗin maganarsa Mama tace "Haba Abban Fadwa wannan wace irin magana ce kake yi haka, daga tafiya fa ta dawo yau, ka sani ko dare ne taga yayi yasa ta taho nan ta kwana gobe da sassafe sai ta wuce gidanta..? Amma shine saboda baka son zaman lafiya daga ganinta zaka fara mana jaye jayen wata lukutar masifa da daddaren nan kana son jajibo mana ja'iba...?"
Maman ta faɗa tare da kallon Fadwa data sunkuyar da kai lokaci ɗaya tana jin jikinta na ƙara yin sanyi.
Da kallon takaici Abba ya bisu lokaci ɗaya yana ƙara nazarin Fadwan, bai dai ce komai ba ya kaɗa kai kawai ya miƙe tsaye ya wucesu da sauri ya nufi ɗakinsa ya shige ya turo ƙofa.
Ganin haka yasa Fadwa matsawa da sauri ta zauna a kusa da Mama tana sauke numfashi kafin kuma cikin yin ƙasa ƙasa da murya tace "Mama da gaske fa Ya Azeez ya sake ni..." Ta faɗa tare da juyawa lokaci ɗaya ta kalli ƙofar ɗakin da Abban ya shige.
Zaro idanu Mama tayi cike da tsantsar mamaki tace "Ya sake ki..shi AbdulAzeez ɗin ne ya sake kin Fadwa...?"
Da sauri Fadwa ta rufe mata baki da hannunta tana girgiza mata kai, kafin kuma cikin yin ƙasa da murya tace "Kai Mama kiyi a hankali dan Allah kar Abba ya jiyoki..."
Ta faɗa tare da sake waigawa tana zare idanu, kafin ta juyo a hankali tana gyaɗa mata kai tace "Wallahi kuwa Mama Ya Azeez ya sakeni kuma sakin wulaƙanci, wai saki ɗaya, gashi har da marina wai in fita in bar mai gida, sai kace wata karya, baya son ganina bani da wani amfani a gurinsa, dama darajar ubana nake ci kuma ya gaji, in tafi baya son ƙara ganina..bakiji cin mutunci ba iri iri, wallahi yau Mama nayi mamakin abinda Ya Azeez ya rufe ido yayi min, ban taɓa zato ba..."
Taɓe baki Mama tayi tana faɗin "Ai kaɗan kenan daga iskancin talaka, dan shi jaki koya kikayi dashi sai yaci kara, amma in ba dan haka ba har AbdulAzeez ya isa ya kalleki yace wai darajar ubanki kike ci, ai shi ya kamata a gayawa haka ba ke ba banzan bazara kawai matsiyaci, bai san dama can rufa masa asiri mukayi kawai kike zaune dashi ba, amma inda yayi tunani ai daya gano cewa ruwa ba sa'an kwando bane dan ko an zubasa sai ya tsiyaye, daƙiƙin banza da wofi kawai ɗan iska..." Ta ƙarashe maganar lokaci ɗaya tana kumfar baki.
Haka dai suka zage sukai ta zagin Ya Azeez, wanda yana can gida shi bai ma san me sukeyi ba.
Mama nata aibantasa tana ta faɗan maganganu marasa daɗi akansa da mahaifiyarsa, Fadwa kuwa sai biye mata take itama tana tayata suna zaginsa.
Sai da suka gaji dan kansu sannan suka miƙe, Mama taja akwatin Fadwan ta shigar mata dashi ɗakin kannenta, kana ta fito ta ɗauki bokiti ta cika mata shi da ruwa ta kai mata har banɗaki ta fito ta sake ɗaukar soso da sabulu ta kai mata, ta dawo ta bata zani ta ɗaura bayan ta tuɓe kayan jikinta tace "Jeki ɗan watsa ruwa ko kyaji daɗin jikinki, kafin ki fito na gyara miki gurin kwanciyan..." Ta faɗa tare da ficewa zuwa ɗakinta, kafin itama Fadwan ta fice zuwa banɗakin dake tsakar gidansu domin tayo wankan.
*********
A ɓangaren Ya Azeez kuwa ya daɗe idonsa biyu ya kasa bacci, gaba ɗaya idanuwansa sun gama bushewa zuciyarsa kuwa har lokacin tafarfasa kawai take saboda ɓacin rai.
Sai juyi yake yana ta tunane tunane yana jin wani abu mara daɗi na masa yawo a zuciya, ta wani ɓangaren kuwa har lokacin tunani yake ta yadda zai iya tunkarar Abba ya iya kallon idonsa idan yasan cewa ya saki Fadwa, ƴar cikinsa duk irin halaccin da yay masa.
Sake juyawa yayi a hankali yana sakin tsaki, kafin a fili a furta "Abba ka gafarceni na kasa control ɗin kaina da zuciyata ne akan irin abubuwan da Fadwa ke yi min, kuma ina fatan ka fahimceni insha Allahu zan dawo da ita ɗakinta, kuma nayi alƙawarin kome tai min zan daure in jure in cigaba da zama da ita a yadda take..."
Ya ƙarashe maganar tare da gyara kwanciyarsa lokaci ɗaya ya lumshe idanunsa yana sauke ajiyar zuciya.
*********
Washegari misalin ƙarfe 8am. Ya Azeez ya fito cikin shirin fita, sai daya kulle ƙofar ɗakin sannan ya fita daga gidan, da ƙafa ya taka yaje gidan bulon da yake kai ajiyar napep ɗinsa ya ɗauka, bayan ya fito ya nufi unguwar Mu'azu.
Tafe yake a cikin napep ɗin sai saƙe saƙe yake a ransa, tunani kawai yake yadda zai fuskanci Abba idan ya isa gidan, dan sosai yake matuƙar jin matsananciyar kunyar Abban a zuciyarsa, anya kuwa zai iya fuskantarsa..? Ko dai ya juya ne yaje ya ɗauko Umma su taho tare..?
Haka har ya isa gidan bai gama yanke shawarar ba, ya fasa zuwa gidan ne ko kuma ya koma ya ɗauko Umman..?
*Ya Allah ka gafartawa mahaifina da sauran Musulmi baki ɗaya🤲*
[12/23, 10:19 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI*
*Wattpad: Aishaalto09*
_Nagode ƙwarai da sharhinku ina matuƙar jin daɗin yadda kuke nuna kulawarku akan littafina, nagode sosai da sosai Allah ya saka da alkhairi ina godiya sosai Allah yabar Ƙauna._
2️⃣9️⃣
Koda ya shiga cikin gidan Ilham kaɗai ya samu a tsakar gidan tana shara, yayinda Amatullah kuma ke kichin tana ƙoƙarin dama musu koko.
Ganinsa ne yasa Ilham ɗin ajiye tsintsiyar dake hannunta da sauri ta matso gabansa, dan tana ganin yadda ya shigo gidan tasan ba lafiya ba, domin tun bayan aurensa da Aunty Fadwa ba kasafai yake zuwa gidan ba balle kuma yau ɗin data ganshi tunda sassafe, aiko ba lafiya, tunda taga ita karan kanta Aunty Fadwan jiya a gidan ta kwana.
"Ya Azeez ina kwana...?" Ta faɗa a sanyaye bayan ta amsa sallamarsa.
Ƙarasowa yayi cikin gidan bayan ya amsa mata gaisuwar tata, kafin kuma ya ɗora da faɗin "Abba ya tashi kuwa...?" Ya faɗa tare da ɗan juyawa yana kallon ƙofar ɗakin nasa.
Gyaɗa masa kai tayi kafin tace "Ya tashi tun ɗazu, yana cikin ɗaki karatu yake, bari inyi masa magana..." Ta faɗa tare da juyawa da sauri ta nufi ɗakin, ba daɗewa sai gata ta fito tace "Yace ka shiga..."
Ta faɗa tare da wucewa ta ɗauki tsintsiya ta cigaba da shararta.
Shiko Ya Azeez a hankali ya ƙarasa ƙofar ɗakin yayi sallama, inda daga ciki Abba ya amsa masa tare kuma da bashi iznin shigowa.
Cikin natsuwa ya ɗaga labulen lokaci ɗaya ya saka kansa cikin ɗakin, karaf kuwa idonsa ya sauka ana Mama dake zaune a gefen Abba, kauda kai yayi da sauri tare da ƙarasawa gaban Abba dake zaune akan darduma ya rusuna yana faɗin "Barka da safiya Abba..."
Ɗagowa Abba yayi da murmushi a fuskarsa yana faɗin "Barka dai AbdulAzeez, lafiya dai ko na ganka yau tunda sassafe...?" Ya faɗa cikin fargaba, yayinda ya tsaresa da idanu lokaci ɗaya gabansa na faɗuwa, domin haka nan tun jiya da yaga Fadwa hankalinsa ya gaza kwanciya zuciyarsa kuma gabaki ɗaya taƙi natsuwa da zuwan nata shiyasa yanzu da yaga Ya Azeez ɗin tunda sassafe zuciyarsa ta ƙara shiga ruɗu da tashin hankali.
Mama kuwa zabga masa wata muguwar harara tayi ba tare kuma data amsa gaisuwar da yake mata ba tace "Yo ba dole ka ganshi a gidan tunda sassafe ba ya dako uban sammako, tunda yasan tsiyar daya ya tsula maka..."
Ɓata fuska Abba yayi kafin yace "Wace irin tsiya kuma, wai ke meyasa kwata kwata rayuwarki babu lissafi da tunani ne..? Ana zaune lafiya ke dai dole sai kin jajibo abinda za'a yi fitina sannan hankalinki zai kwanta, yanzu tsakani da Allah wace irin tsiya yayi miki daga zuwansa...?"
Fuskar Mama ba walwala tace "Sakin ƴata yayi ya mayar min da ita ƙaramar bazawara..."
Ta faɗa kai tsaye tana harararsa.
Galala Abba yake kallonta kafin kuma ya juya ya dubi Ya Azeez wanda ya duƙar da kai ƙasa yace "Da gaske ne ka saki Fadwa AbdulAzeez...?"
A ƙufule Mama tace "Yo ya saketa mana, meye na wani bin ba'asi kuma...?" Ta faɗa tana wani kumburo baki sai kace wata ƙaramar yarinya.
Shiko Ya Azeez gaba ɗaya ji yayi ya gama muzanta a gaban Abban, gabaki ɗaya ya rasa da wane ido zai iya kallonsa me zai ce masa..?
Riƙo hannunsa da Abban yayi ne yasa ya ɗago kai da sauri ya kallesa, kafin kuma ya sake duƙar da kansa dan baya jin zai iya kallon cikin ƙwayar idanunsa saboda tsabar kunyarsa da yake ji gaba ɗaya ta gama lulluɓesa.
Bai gama jin kunya ba sai da ya jiyo muryar Abban kamar daga sama yana