Author : Aisha Alto Category : A Books
kyakkyawan matashin saurayi dake fitowa daga cikin falon ya nufosa cike da farin ciki yana faɗin "Oyooyo Ya Azeez, ina ka baro min Umma da Imaan ɗina...?" Ya ƙarashe maganar lokaci ɗaya yana karɓan jakar dake rataye a kafaɗarsa, yana cewa "Muje ciki Mami tana nan..."
Ɗan shafa kansa Ya Azeez yayi a hankali yana murmushi yake faɗin "Masha Allah su Ibrahim yaron Mami an ƙara girma, sai kuma aure tunda an gama karatu ko...?" Ya faɗa cike da tsokana yana kallonsa, da sauri ya rufe fuskarsa da hannuwansa alamar jin kunya kafin yace "Kai Ya Azeez ni fa ba yanzu zanyi aure ba har sai Imaan ta gama makaranta tukunna sai muyi atare..." Ya ƙarashe maganar yana wucewa da sauri yayi gaba, shima Ya Azeez ɗin da Fahad dariyan sukayi kaɗan kana suka bi bayansa a nutse suka nufi ƙofar babban falon gidan.
Wani haɗaɗɗen falo suka shiga mai tsananin kyau da tsari, wanda aka kewayesa da wasu rantsatstsun kujeru na alfarma.
Bakinsu ɗauke da sallama suka shiga cikin falon, inda suka iske wasu hamshaƙan manyan mata zazzaune kota ina a cikin falon kowaccen su taci uban ado na kece raini, suna ganinsu kuwa suka hau faɗin "Oyooyo ango..oyooyo ango kasha ƙamshi..." Suka faɗa a tare suna dariya, a hankali suka ƙarasa gabansu duk suka rusuna suna gaishesu, shi kuwa Ibrahim da sauri yayi gaba yana kiran "Mami..Mami kizo ga Ya Azeez yazo..."
Wata kyakkyawar hamshaƙiyar mata ce mai matsakaicin tsaho ta fito daga wani ɗaki da sauri cikin fara'a tana cewa "Ina AbdulAzeez ɗin yake...?" Ta faɗa fuskarta ɗauke da murmushin farin ciki tana kallon Ibrahim ɗin.
Da sauri Ya Azeez ya miƙe ya isa gabanta cikin nuna tsantsar farin cikin ganinta da yayi ya ɗan rusuna a gabanta yana faɗin "Mami ina wuni mun sameku lafiya...?" Ya faɗa cikin sanyin murya lokaci ɗaya yana sakin murmushi. Cikin tsantsar so da nuna kulawa Mami tace "Lafiya Alhamdulillahi AbdulAzeez, ya Hajiya Hafsatu da Imaan ɗin, fatan duk kuna lafiya ko...?"
Cikin natsuwa ya amsa mata da faɗin "Duk suna lafiya Mami Alhamdulillahi, sunce ma agaisheki..."
Gyaɗa kanta tayi kafin tace "Masha Allah, ina ita iyalin naka ko ba tare kuka zo ba...?" Ta ƙarashe maganar tana ɗan leƙa cikin falon.
Saurin girgiza mata kai yayi da sauri yana faɗin "A'a tana gida can na barota, ba tare da ita muka zo ba..." Ya faɗa lokaci ɗaya yana jin wani irin ɗaci da bala'in haushin jin sunan Fadwa da Mami ta ambata ya ƙara cika masa zuciya.
Dai-dai lokacin kuma Fahad ya ƙaraso gabansu yana faɗin "Mami dan Allah ki tayani ba aboki haƙuri, nayi masa laifi kuma na bashi haƙuri amma yaƙi fahimta ta..." Ya faɗa cikin marairaice fuska yana kallon Ya Azeez daya wani ƙara haɗe rai ya ɗauke kai gefe.
Mami kuwa riƙe baki tayi da sauri tana faɗin "A'a rufa min asiri kunfi kusa, nima tare na ganku, kuje can ku ƙarata..." Ta faɗa lokaci ɗaya tana murmushi kafin ta juya tana duban Ibrahim dake tsaye har lokacin da jakar Ya Azeez sagale a kafaɗarsa tace "Kaje ka kai masa jakar ɗakin yayanku mana ya samu yayi wanka ya ci abinci, sai ya ɗan huta kafin kuma Abbanku ya dawo ko...?" Ta faɗa tare da kallon Ya Azeez ɗin tana ci gaba da faɗin "Tashi ku shiga ciki ka watsa ruwa, yanzu za'a kawo maka abinci..." Ta ƙarashe maganar lokaci ɗaya tare da juyawa ta nufi kichin.
Koda suka isa ɓangaren Fahad ɗin wanda ƙofar shiga cikinsa ke kusa da falon mahaifinsa, ajiye jakar Ibrahim yayi ya wuce toilet yaje ya haɗa masa ruwan wanka kana ya fito ya fice daga ɗakin da sauri dan zuwa ya karɓo masa abinci kafin ya fito wankan.
A hankali ya miƙe tsaye ya fara ƙoƙarin tuɓe kayan jikinsa dan ya samu ya ɗan watsa ruwa kafin yazo ya gabatar da sallar la'asar data kuɓuce masa, wanda kuma a dai-dai lokacin Fahad ya shigo cikin ɗakin da sauri shi da wani abokinsa, ya zauna saman wata sofa guda ɗaya dake tsakiyar ɗakin ya dafe kansa cike da damuwa.
A hankali Ya Azeez ya waigo ya kallesa kafin ya matso kusa dashi ya riƙo hannunsa cikin nuna kulawa wanda kuma har a lokacin fuskarsa take ahaɗe yace "Meya faru kuma..ko wani abun akayi maka...?"
Da sauri Fahad ya riƙe hannunsa yana faɗin "Wallahi na rasa ta yadda zanyi ne in fahimtar da kai dalilina na ƙin sanar da kai ɗaurin aurena da ban yi ba, na san nayi maka kuskure ban kyauta ba, amma..."
Saurin rufe masa baki Ya Azeez yayi lokaci ɗaya yana fashewa da wata irin dariya wacce ya daɗe rabon da yayi irinta, sakin baki kawai galala Fahad da abokinsa sukayi suna kallonsa, kana suka juya suka kalli juna, kafin kuma cikin wani irin rauni Fahad ɗin yace "Amma dai kai ɗan iska ne ko aboki..to meye abun dariyan kuma...?"
Bai kulasa ba sai da yayi mai isarsa sannan ya tsagaita yana faɗin "Shege Dude..ai dama nace yau sai nayi maganinka ɗan iska tunda kai baka da mutunci, amma ni komai ya riga ya wuce a gurina, dama ban riƙeka ba tuni na manta. Amma idan ka ƙara ko...?" Ya faɗa tare da yin ƙwaffa kafin ya ci gaba da faɗin "Sai na bala'in ɓata maka rai wallahi..." Ya ƙarashe maganar lokaci ɗaya yana wani ƙara haɗe fuska irin ya ci serious ɗin nan.
Dunƙule hannunsa Fahad yayi ya kai masa duka a ƙirji yana sakin murmushin farin ciki, kafin ya faɗa jikinsa lokaci ɗaya suka rungume juna atare suna ƙara fashewa da dariya.
Ya Azeez ne ya fara janye jikinsa a hankali yana murmushi, kafin yace "Ina zuwa bari in watsa ruwa idan nayi sallah sai ka kaini gurin amaryar tamu in ganta..." Ya faɗa tare da juyawa ya shige toilet.
*Ya Allah ka gafartawa mahaifina da sauran Musulmi baki ɗaya🤲*
[12/23, 10:18 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI*
*Wattpad: Aishaalto09*
2️⃣4️⃣
Yana fitowa daga wankan ana kiran sallahr Magriba, da sauri ya sake komawa cikin toilet ɗin ya ɗauro alwala kana ya fito shima Fahad ya shiga yayo, sannan abokinsa. A gurguje ya buɗe jakarsa ya zaro wata farar jallabiyarsa ya zura kana ya ɗan fesa turare ya ɗauki casbaha ya fice daga ɗakin yayinda Fahad da abokinsa ke biye dashi a baya zuwa masallacin dake cikin unguwar.
Basu dawo ba sai da suka sallaci sallar isha'i sannan gurin ƙarfe 7:40pm suka shigo gidan.
Koda suka shigo sun iske Ibrahim ya kawo abinci yana ajiyewa suna shigowa cikin ɗakin, da sauri Fahad ya nufi ɗan madaidaicin teburin da Ibrahim ɗin ya jera abincin akai ya zauna, filet ya ɗauka tare da spoon ya buɗe kular farfesun kayan cikin rago dake ta tashin ƙamshi ya fara zubawa yana faɗin "Zoka zauna kaci abinci aboki, dan nasan tun kafin ka taho ƙila rabonka da abinci..." Ya faɗa yana ƙoƙarin zuba masa farfesun, a hankali Ya Azeez yazo ya zauna a ƙasan kafet ɗin dake malale a tsakiyar ɗakin tare da tanƙwashe ƙafafuwansa lokaci ɗaya yana kallon tarin kulolin dake jere kan ɗan teburin cin abincin kafin ya juya ya kalli gefen da abokin Fahad ke zaune yana faman danna waya yace "Ya ka koma nan kuma..? Matso mana kaima kaci abincin..."
A hankali ya taso shima ya ƙaraso ya zauna kusa da Ya Azeez ɗin kana ya tanƙwashe ƙafafuwansa kamar yadda yaga Ya Azeez ɗin shima yayi.
Fahad ne yayi Sarving ɗinsu da kansa kana ya turawa kowa filet ɗin abincin gabansa, kafin shima ya ajiye nasa agabansa suka fara ci shida abokinsa, shi ko Ya Azeez bai ko kalli abincin da Fahad ɗin ya zuba masa ba, ya ɗauki kofi ya soma ƙoƙarin haɗa tea, ɗagowa Fahad yayi ya kallesa kafin yace "Ya haka kuma aboki, tea naga kana haɗawa abincin kuma fa...?"
Ɗan kwaɓe fuskarsa Ya Azeez yayi ya lumshe idanunsa kafin yace "Tea ɗin kawai zan iya sha Dude, shi kaɗai ya isheni..." Ya faɗa kai tsaye yana ɗaukan kofin daya haɗa kakkauran tean a ciki ya kai bakinsa.
Kai Fahad ya ɗan jinjina ba tare kuma da ya cewa komai ba, ya ci gaba da cin abincinsa, saboda yasan halinsa farin sani tunda yace tea ɗin kawai zaisha to shi ɗin kuwa zaisha ba zai ci abincin ba.
Koda suka kammala cin abincin Ya Azeez ne ya fara miƙewa tsaye lokaci ɗaya yana kallon Fahad cikin tarin gajiya yace "Kawai mu bari sai zuwa gobe muje gurin amaryar nan tamu dan yanzu kam dare yayi kusan 8:30pm ake nema, kuma duk a gajiye nake wallahi baka ji jikina ba ko'ina ciwo yake min, mu bari goben kawai..."
Ya ƙarashe maganar lokaci ɗaya yana nufar hanyar toilet ya shige, a hankali Ibrahim ya turo ƙofar ɗakin ya shigo yana kallon Fahad dake tsaye a tsakar ɗakin yana ƙoƙarin tuɓe kayan angoncin dake jikinsa ya ɗago ya kallesa kafin yace "Yauwa dama yanzu nake shirin kiranka ka kwashe kayan nan ka fita dasu..." Ya faɗa yana ƙarasa tuɓe babbar rigar shaddar dake jikinsa ya sagale a cikin wardrobe ɗinsa, shi kuwa Ibrahim duƙawa yayi ya soma tattare kayan yana faɗin "Dama Mami ce tace inzo in kira mata Ya Azeez yazo su gaisa da Abba ya dawo tun ɗazu yana falonsa..."
Buɗe ƙofar toilet ɗin da Ya Azeez ɗin yayi ne ya dawo da hankalin Ibrahim ɗin kansa inda yake faɗin "Yauwa Ya Azeez dama Mami ce ta aikoni wai kazo Abba ya dawo yana falonsa..."
Da sauri Ya Azeez yace "Ok muje..." Ya faɗa tare da yin gaba da hanzari yayinda Ibrahim ɗin kuma ke biye dashi a baya hannunsa riƙe da babban farantin daya kwashe kwanukan da suka gama cin abinci dasu suka fice daga ɗakin.
Ƙofar wani haɗaɗɗen falo dake can tsakiyar babban falon gidan suka nufa, tsayawa Ibrahim yayi daga bakin ƙofar ya buɗe Ya Azeez ya kutsa kai cikin lafiyayyen falon bakinsa ɗauke da sallama, yana shiga shi kuma Ibrahim ɗin ya juya ya nufi kichin dan kai kayan dake hannunsa ya ajiye.
Wani kyakkyawan mutum ne mai cikar haiba da kamala ke zaune a tsakiyar falon kan wata ƙatuwar darduma da aka shimfiɗa, gabansa wani babban farati da aka jere masa kulolin abinci akai, sai gefensa kuma Mami ce zaune cikin shiga ta alfarma tana ƙoƙarin zuba masa abinci, ganin shigowar Ya Azeez ɗin ne kuma yasa Alhaji Sale Musawan ɗagowa fuskarsa ɗauke da ƙayataccen murmushi ya buɗe masa hannayensa cikin tsananin farin ciki da jin daɗin ganinsa yana faɗin "Barka da zuwa yarona, yaka nan..." Yake faɗa yana ƙara sakin murmushin jin daɗin ganinsa da yayi.
Da sauri Ya Azeez ya ƙarasa gabansa ya rusuna tare da faɗawa jikinsa cikin tarin farin ciki da wata tsananin kewar mahaifinsa da yake ji lokaci guda tana bijiro masa yace "Barka da dare Abba, fatan na sameku lafiya...?" Ya faɗa tare da yin tsam a jikinsa yana sauke ajiyar zuciya a hankali, kafin kuma ya janye jikinsa a hankali ya matsa gaban Mami yana faɗin "Sannu da gida Maminmu..."
Jinjina masa kai Mamin tayi tana murmusawa kafin tace "Yauwa sannunmu yaron kirki, ya gajiyar tafiya...?"
Ta faɗa tana ƙarasa haɗawa Abban abincinsa ta tura gabansa kana ta sake ɗaukar wani filet ɗin ta fara ƙoƙarin haɗa wani tana faɗin "Me za'a zuba maka AbdulAzeez...?"
Da sauri yace "Wallahi a ƙoshe nake taf Mami, yanzu ba daɗewa muka gama cin abincin da Ibrahim ya kai mana..." Ya faɗa lokaci ɗaya tare da ɗan shafa cikinsa yana sakin murmushi.
Dariya Abba yayi irin tasu ta manya kafin yace "Da dai ka daure ka ƙara ci ɗin, tunda naga alamar so Mamin taku take taga kayi ƙatoton tumbi ƴan mata su dinga gudunka, suna basa son mai tumbi..."
Ya ƙarashe maganar lokaci ɗaya tare da yin dariya, itama Mamin dariyar tayi kafin tace "Aiko babu budurwar da duk haɗuwarta zatayi tozali da yarona tsalele dashi santalele ta kushesa, sai dai idan bata kula da kyau ta kallesa ba. Amma irinsu kam ai su ake kira da one in town nake gaya maka..." Ta ƙarashe maganar da iya gaskiyarta tana murmusawa.
Kallonta Abba yayi da murmushi akan fuskarsa yana faɗin "Banda dai cika baki atoh, kuma suzo suyi kwantai anan gaba, duk da shima wancan ɗayan tuzurun an samu da ƙyar da suɗin goshi yau an ɗaura, dan har gwara wannan ɗin ma yana da nashi iyalin tun tuni..wai ina take nema..ko ba tare da ita kuka zo bane...?" Ya faɗa tare da kallon Ya Azeez ɗin daya sunkuyar da kai yana murmushi.
Suna cikin haka Fahad ya shigo cikin falon bakinsa ɗauke da sallama wanda dawowarsa kenan daga rakiyar abokinsa da yayi ya tafi, da sauri ya ƙaraso gaban Abban ya rusuna cikin girammawa ya yiwa Abban nasa barka da dare haɗe da yi masa ban gajiyar taro, kafin ya juya ɓarayin Mami itama yayi mata.
Amsawa sukayi dukkansu cike da kulawa, kafin kuma Abban yace su tashi su koma babban falo su jirasa idan ya kammala zai fito akwai maganar da yake so dama zaiyi dasu.
Jinjina kai sukayi dukkansu kana suka miƙe atare suka fice daga falon zuwa babban falon gidan kamar yadda Abban ya umurcesu.
Suna nan zaune Abban ya fito sanye da farar jallabiya ajikinsa wanda da alamu sai daya sake yin wanka kafin ya fito, ƙarasowa yayi ya zauna saman ɗaya daga cikin kujerun falon yana fuskantar su.
Wanda da sauri dukkansu suka zamo daga saman kujerar da suke zaune akai lokaci guda suna daidaita zamansu a ƙasan kafet ɗin dake tsakiyar falon cike da girmamawa suna yi masa barka da fitowa.
Amsawa yayi cike da kulawa, kafin ya ɗago kai a hankali ya kalli Ya Azeez daya sunkuyar da kai yana wasa da zoben azurfan dake hannunsa.
Yace "AbdulAzeez ya gurin aikin naka, ina fatan dai komai yana tafiya dai-dai yadda ya kamata ko, ba wata matsala...?"
Da sauri Ya Azeez ɗin ya ɗago kai jin irin tambayar da Abban yayi masa, kafin yace "Eh Abba Alhamdulillahi komai yana tafiya dai-dai yadda ya kamata mun gode Allah..."
Jin irin amsar da Ya Azeez ɗin yaba Abban ne kuma yasa Fahad juyowa da sauri yana galla masa harara kafin yace "Wallahi ƙarya yake Abba, babu wani aikin da yake yi kawai ɓoye maka yake saboda bayaso kasan takamaiman abinda yake yi acan ɗin..."
Wani kallon banza Ya Azeez ya ɗago kai ya watsa masa yana faɗin "Malam bada kai ake magana ba kayi mana shiru..faɗi ba'a tambayeka ba..." Ya faɗa lokaci ɗaya tare da zafga masa harara.
Abba da tunda suka fara maganar ya kafesu da idanu kawai yana sauraren su, yayinda shi kuma Fahad ya ƙara matsawa gaban Abban da kyau yana faɗin "Wallahi Abba ƙarya yake yi kek..."
Da sauri Ya Azeez ya katsesa da faɗin "Ka kiyayeni wallahi ka fita daga harkata, tunda ba kai aka tambaya ba, saboda haka ka barni inyi mai bayani da kaina..."
Fahimtar da Abba yayi cewa akwai abinda Fahad ɗin ke son sanar dashi ne amma Ya Azeez ke ta kakkarewa yana hanasa, yasa ya ɗago kai ya kalli Ya Azeez ɗin da yay sauri ya sunkuyar da kansa ƙasa yana faɗin "Sharri kawai yake son ƙulla min a gurinka Abba kum..."
Ɗaga masa hannu Abban yayi yana faɗin "Ina jinka Fahad..." Ya faɗa kai tsaye cikin tsare gida yana kallonsa.
Ɗan kallon gefen da Ya Azeez ɗin yake Fahad yayi kafin ya gyara zamansa da kyau lokaci ɗaya yana faɗin "Bai aikin komai fa Abba, keke napep kawai Abban Fadwa ya ƙarban masa a hannun wani mutumi yake ja..kuma tun..."
Ɗaga masa hannun shima Abban yayi cikin ɓacin rai kafin yace "Amma tunda nake da kai ka taɓa sanar dani irin aikin da yake yi acan ɗin kenan...?"
Da sauri Fahad ya girgiza masa kai cikin sanyi jiki kafin yace "A'a ban taɓa gaya maka ba Abba, amma shida kansa ya hanani yace kar in gaya maka..wai baya so ya takuraka kuma..."
Wata uwar tsawa Abba ya daka masa a fusace yana faɗin "Tashi ka fita ka bani guri..mutumin banza kawai..." Ya faɗa a zafafe lokaci ɗaya yana nuna masa ƙofa, cikin sanyi jiki Ya Azeez ya ɗago kai da sauri yana kallonsa, kafin cikin hanzari ya ƙara matsawa gabansa ya duƙar da kai yana faɗin "Dan girman Allah Abba kayi haƙuri ka gafarceni, wallahi ba laifinsa bane laifina ne nine na hanasa ya gaya maka, amma kayi haƙuri ka fahimceni ban yi hakan da wata niyya ba, sai domin bana son in sake ɗora maka wani nauyi akanka bayan wanda kake fama dashi..." Ya ƙarashe maganar a sanyaye yana ƙara sunkuyar da kansa.
Abba da tunda ya fara maganar ya kafesa da ido baya ko ƙiftawa, gaba ɗaya jikinsa sai yayi bala'in yin sanyi da maganganunsa.
Domin tabbas yasan indai har AbdulAzeez cikakken ɗan Alhaji Naseer Arabi ne kuma jininsa yana yawo a jikinsa, to dole zaiyi gadon halayyarsa na rashin son dogaro da kowa sai Allahn daya haliccesa, shi dai burinsa a kullum a kuma koda yaushe shine ya nemi na kansa ya tsaya da ƙafafunsa baya son ya kasance mai dogaro da wani ɗan Adam balle har ya zame masa kaya ya ɗora masa nauyin kula da wasu al'amuransa, wanda kwata kwata hakan ba ɗabi'arsa ba ce kuma har ya koma ga mahaliccinsa bai taɓa damun kansa da neman wani abu a gurin kowa ba sai a gurin Allah.
Lallai yau ya ƙara tabbatar da cewa AbdulAzeez jajirtaccen namijin duniya ne mai ƙwazo, da son dogaro da kansa.
A hankali ya kalli Ya Azeez ɗin cikin natsuwa kafin yace "Na fahimceka AbdulAzeez..sai dai kuma inaso zan yanke wani hukunci a kanka, wanda nake fatan zai faranta maka kuma zaka karɓesa hannu bibbiyu bazaka taɓa yi min musu akai ba...?" Ya faɗa kai tsaye yana tsaresa da idanu.
Kai Ya Azeez ɗin ya jinjina masa tare da cewa "Insha Allahu Abba, babu hukuncin da zaka yanke min wanda har zan ƙi karɓarsa koda kuwa hakan bai yi min ba..."
Kai Abba ya jinjina shima cike da gamsuwa kana yace "Alhamdulillahi naji daɗin kalamanka, kuma tabbas hakan na min nuni da cewa ka ɗaukeni tamkar mahaifinka..dan haka kai tsaye nake roƙonka daka ajiye wannan ƙudirin dake zuciyarka a gefe ka karɓi abinda nake son gaya maka yanzu..." Ya faɗa a hankali yana mai ƙara nazarin hukuncin daya yanke a zuciyarsa yanzu, kuma yake son furtawa a fili.
A hankali ya gyaɗa