Chapter 14 Reading WADATAR ZUCI Complete Book by Aisha Alto.txt Arewa Novels

WADATAR ZUCI Complete Book by Aisha Alto.txt

Author :  Aisha Alto Category :  A Books

Chapter   14 / 38

39K to 42K   out of 113.4K words

jikinsa sosai sai suka ƙara fito da zallar kyawunsa da kamalarsa a fili, uwa uba haiba da tsantsar natsuwarsa. Da sauri ta tashi zaune tana binsa da wani mugun kallon sama da ƙasa kana taja tsaki a zafafe tana faɗin "Wai lafiya Malam zaka kashe min dodon kunne da wannan ƙatuwar muryar taka, ko kana bina wani bashi ne...?"


Ta faɗa tana wani ƙara haɗe rai lokaci ɗaya tana galla mai harara, ga tarin mamakinta sai ta ga ko kallonta bai yi ba, sai ma ɗauke kai da yayi gefe ya juya yana ƙoƙarin ficewa yake faɗin "A'a bana binki bashin komai, dama dai zan sanar dake ne ga kuɗi nan na ajiye miki ki siya abun kari sannan ga ruwan wanka can idan kin tashi sai kiyi, ni na fita..."
Daga haka kawai yasa kai ya fice daga ɗakin ya barta nan zaune sake da baki tana binsa da kallo cikin sanyin jiki da tsantsar mamakin sauyawarsa lokaci guda, ji yadda yake mata magana kai tsaye ba wani tausasawa ko lallashi kamar ba Ya Azeez ɗin data sani nata mai haƙuri da tsananin tausayinta ba.


















*Ya Allah ka gafartawa mahaifina da sauran Musulmi baki ɗaya🤲*
*WADATAR ZUCCI*




*Wattpad:Aishaalto09*






1️⃣6️⃣






Ta daɗe zaune tana bin ƙofar daya fice da kallo kafin ta kaɗa kai lokaci ɗaya tare da waigawa tana ƙarewa ɗakin kallo, cikin mamaki da al'ajabi take faɗin "To wai meya faru ne daya sauya lokaci guda irin haka...?"


Ta faɗa lokaci ɗaya tana tsurawa guri guda idanu cikin nazari, kafin a hankali kuma ta sauke numfashi tana faɗin "Can da matsalarka wallahi ni dai a sani na babu abinda ya haɗani da kai balle inyi tunanin ko nice na ɓata maka rai, dan haka babu abinda ya dameni ballantana yasha min kai nida zaka taimakeni ma daka sahale min wannan auren naka in rabu da ƙaya, kaima kuma ka huta nauyin yayi maka sauƙi kaji da kanka..da wannan ƴar ya ƙunanniyar uwar taka..." Ta faɗa tana hararar jakar kayansa kamar shine yake zaune a gurin, kana ta saki tsaki tana zuro ƙafarta ƙasa ta sauko daga kan gadon tana gyara ɗaurin zanin dake ƙirjinta ta fice daga ɗakin zuwa falo, bokitin daya fito wanka dashi ta ɗauka ta juye ruwan daya ɗora mata ta sirka sannan ta kashe gawayin dan babu abinda zata ɗora.
Komawa tayi cikin ɗaki ta ɗauko sabon shower cream ɗin da aka raba musu jiya gurin bikin kanwar Hajiya Lubna sannan ta dawo ta ɗauki bokiti da soso ta shige banɗakin.




Sai data kwashe kusan awa guda a cikin banɗakin tana dirzar jikinta kamar wacce zata canza fata, dan har sai da ta soma jin fatar jikinta na mata raɗaɗi da zafi kafin ta haƙura ta fito, ta wanke bakinta sannan ta ɗaura alwala lokacin ƙarfe 7:40am. Dai-dai ta shiga ɗaki ta tayar da sallah.
Koda ta idar bata bi takan neman abun karyawa ba ta ɗauko kayan kwalliyarta ta zauna bayan ta shafa mai ta murje ko'ina na jikinta da wata humrarta mai daɗin ƙamshi da tsadar gaske wacce Hajiya Labiba ce ta kawo mata ita tsaraba lokacin da sukaje Maiduguri gaishe da mahaifiyar mijinta. Shafa hoda tayi sama sama kana ta shafa wet lips ta miƙe ta buɗe akwatinta ta zabo wata doguwar rigar abaya purple mai kyau wacce tasha adon stones manya manya a jiki, sai data fara saka pant da bra farare masu kyau, sannan ta zura rigar a jikinta ta naɗe kanta da mayafin.


Tana ƙoƙarin fesa turare a jikinta taji ƙarar wayarta dake cikin jaka, da sauri ta ƙarasa inda jakar take rataye ta buɗe ta ciro wayar, sunan Hajiya Labiba ta ga yana yawo akan screen ɗin wayar, da hanzari ta ɗauka ta manna a kunnenta tana faɗin "Ƴar halak kin ƙi ambato, yanzu fa nake zancenki a zuciyata na gama shiri kenan zan taho gidanki..."


Daga can ɓangaren Hajiya Labiba tace "Yauwa ƙawata yi sauri ki taho dan Allah tun ɗazu nake ta zuba ido ina saurarenki na jiki shiru ba labari, shiyasa nace bari in kiraki kinsan yau dai muna da abubuwan yi da yawa dan har ƙunshi nake son ayi mana, gashi zamu shiga kasuwa inaso zan ƙarasa siyayya sannan zamuje gidan Hajiya Kalsoom dan acan ne yau za'ayi bridal shower ɗin..."


Ajiyar zuciya Fadwa tayi tace "Ok gani nan zuwa yanzun nan insha Allahu mashin ma zan hau dan yafi min sauri..."


Hajiya Labiba tace "Ok sai kin ƙaraso nima bari in tashi in shirya kafin ki iso..."


Ta faɗa tana katse wayar, a gurguje Fadwa ta ƙarasa fesa turaren kana ta ɗauki handbag ɗinta ta sagala a gefen kafaɗarta, wayarta kuma ta riƙeta a hannu ta fice daga gidan bayan ta jawo ƙofar ɗakin ta kulle haka nan ba tare data saka kwaɗo ba, dan saboda yau ma tasan suna da abubuwan yi da yawa wataƙila bazata dawo gidan da wuri ba sai dare, shiyasa kawai ta bar mai ƙofar ɗakin data gidan duka a buɗe bata kulle ba, domin bata son ta dinga dawowa kullum tana iskesa tsaye a ƙofar gida yana dakon jiran dawowarta kamar wani almajiri.






*******




A ɓangaren Ya Azeez kuwa yana fita daga gida direct cikin gari ya nufa inda ya saba shiga yayi sana'arsa, sai dai yau abun yazo masa da wani irin salo mai matuƙar ban mamaki da al'ajabi dan tunda ya fito daga gida yake ta haɗuwa da jama'a kota ko'ina gashi tunda ya tashi yau yake jin kansa wani iri kamar bashi ba, dan duk wani ƙunci da baƙin ciki da damuwa daya kwana dasu a ransa daren jiya tuni sun kau, sai wani farin ciki da walwala da yake ji from no were da jin daɗi suna taso masa tun daga can ƙasan zuciyarsa har zuwa cikin ransa.


Sosai yau ɗin ta kasance mai ta musamman dan tunda ya auri Fadwa bai ƙara tsintar kansa a irin wannan yanayin mai daɗi ba, irin na yau gashi tunda ya fito yake ta aiki bai samu ya huta ba, dan har rana ta fito bai samu ya tsaya ba ballantana ya huta har ya samu ya ɗan ci wani abu, gashi yau ko karyawar daya sabayi a gida kullum kafin ya fito bai samu yayi ba, haka ya dinga zirga zirga a tituna da unguwannin dake cikin garin har ƙarfe 1pm. Ta buga aka kira sallahn azahar, sai a lokacin ne ya tsaya ya samu wani masallaci dake kan titin Raɓa Road ya shiga yayi sallah kana bayan an idar ya fito ya tsallaka gefen masallacin inda ya hango wani mai shagon provision ya shiga ya siya biredinsa babba da coke ɗinsa mai sanyi sosai, ya fito ya zauna kan bencin dake bakin shagon ya dinga yagar biredin yana korawa da coke ɗin, sai da yasha yayi nak abinsa sannan ya ɗan zauna jim na ƴan wasu mintoci ya huta kafin ya tashi ya yiwa mai shagon sallama kana ya tsallaka inda ya ajiye keke napep ɗinsa a bakin masallacin yaja ya wuce abinsa.








****



Fadwa kuwa dasu Hajiya Labiba da Hajiya Lubna gaba ɗayansu suna can wani haɗaɗɗen shagon saloon na isassun mata dake cikin gari ana yi musu gyaran jiki, sai da aka gama musu gyaran jiki da na kai tsaf sannan aka kira mai ƙunshi tazo ta tsantsara musu lafiyayyen ƙunshi mai kyau da burgewa, kana aka yi musu fixing eyelashes da nails ƴan dai-dai masu kyau da ban sha'awa.


Ana cikin wankewa Fadwa ƙunshin ƙafarta ne Sadeeq telanta ya kirata a waya yake sanar da ita cewa gashi a gidan Hajiya Labiba yazo kawo mata ɗinkinta amma mai aikinta ta sanar dashi basa nan dukkansu sun fita, ya jirata ne zasu dawo yanzu ko ya bar wa mai aikin Hajiya Labiban kayan ne kawai ya wuce..? Ɗan jim Fadwa tayi kafin tace "Ok ba damuwa Sadeeq ka bar mata kayan kawai ka wuce abinka, na gode sosai sai mun sake haɗuwa..."




Ta faɗa lokaci ɗaya tana katse wayar, Hajiya Lubna dake zaune a gefenta ana ƙarasa saka mata nails a yatsun ƙafarta ta ɗago tana kallon Fadwa lokaci ɗaya tana ƙare mata kallo kafin tace "Gaskiya ƙawata kinyi masifar yin kyau..ke kin ganki kuwa wallahi na tabbata yau idan Azeez ɗinki ya ganki da wuya ya iya ganeki saboda komai naki ya canza kin ƙara wani haske da kyau kamar wata tauraruwa..."


Fadwa da taji kanta ya ƙara mata wani girma ta washe baki cike da jin daɗin yabon da Hajiya Lubnan tayi mata tana faɗin "Dan Allah fa ƙawata..amma ai ban kaiku ba..."


Ta faɗa tana duban Hajiya Labiba wacce ta sakar mata harara tana faɗin "Lallai ne ma ƙawata, ai wallahi da nice nake da kyaunki da yanayin tsarin halittar jikinki da ba ƙaramin abu zanyi ba..dan ko miji ne wallahi sai na zaɓi haɗaɗɗe wanda yaci naira ya tada kai da ita sannan zan yarda in aura, dan irin wannan haɗaɗɗen jikin naki bana talaka faƙiri bane..."


Fadwa ta saki tsaki cikin tsantsar baƙin ciki da takaici tana faɗin "Uhmmm ki bari kawai ƙawata ai ni kam an gama cutata da aka haɗani da jigari jigarin miji wanda bai da wani abinda ya mallaka duk faɗin duniyar nan sai keke napep wanda itama ba tasa bace tausayinsa kawai akaji aka ara masa dan ya dinga samun ɗan na kashewa da siyan abinci..amma dan Allah ki dubeni yanzu waye zai ganni yayi tunanin cewa ni matar ƙaramin mutum ce irin Ya Azeez..? Gaba ɗaya an gama kashe min rayuwata da kuncin talauci, ɗan kyaun da nake taƙama dashi ma so ake aga ya dusashe sannan za'a san zaman da nakeyi dashi kwata kwata bai kamace ni ba kuma duk da hakan wai mahaifina ya kasa ganewa, shi dai babban burinsa kawai in cigaba da zama dashi in ƙarashe rayuwata cikin baƙin talauci da ƙuncin rayuwa..yanzu anyi min adalci kenan dan Allah...?"


Ta ƙarashe maganar lokaci ɗaya da sigar tambaya tana wani kwaɓe fuska kamar zata fashe da kuka, saurin girgiza mata kai Hajiya Lubna tayi tana faɗin "Gaskiya kam har ga Allah ba'a kyauta miki ba Fadwa, amma kiyi haƙuri ki ci gaba da zama dashi a yanda yake wataƙila Allah yayi masa kyakkyawan tanadi wanda yafi wannan a nan gaba, kema sai kiga wata rana kin tsinci ribar haƙurinki..domin gaba ɗayanmu nan babu wanda yasan me gobe zata haifar, ballantana muyi wani hasashe a kansa da abinda zai faru da rayuwarsa nan gaba..."


Wani dogon tsaki Fadwa taja lokaci ɗaya tana hararar Hajiya Lubna kafin tace "Oh ashe ke har wani tunanin kyakkyawar rayuwa kike yi masa a nan gaba...?"


Cikin sauri Hajiya Lubna ta kaɗa mata kai cike da tabbatarwa tana faɗin "Of course..ko kin manta ne a dare ɗaya Allah kanyi bature...?"


Fadwa ta girgiza kai cikin takaici tace "Amma yana a faƙirin matsiyaci wanda bai ajiye komai ba kuma bai ba wani ajiya ba har kike tunanin zai iya zama wani abun arziki a nan gaba...?"


Ta faɗa cike da mamaki tana kallonta, cikin yaƙini da sake tabbatarwa kuwa Hajiya Lubna ta kaɗa kai tana faɗin "Sosai kuwa wallahi wata rana sai kinyi mamakin yadda Azeez ɗinki zai zama a rayuwarsa nan gaba, domin duk ɗan hakin daka raina wata rana shi zai tsole naka ido..shiyasa nace kibi komai a sannu dan dole wata rana in dai muna raye komai zai zamo labari, ke dai ki jira lokaci..."


A zafafe Fadwa ta taso mata da faɗa tana faɗin "Eh saboda ke kina cikin daula kina jin daɗin rayuwarki kina zuba mulkin da kika ga dama a gidanki ba..ai dole ni kiyi min fatar dawwama cikin tsiya da ƙuncin rayuwa, to insha Allahu ta Allah ba taki ba..kina nan mugun bakinki zai biki dan nima Allah ya kusa kawo min mafita ta alkhairi sai dai ɗan baƙin ciki ya mutu..."
Ta ƙarashe faɗa lokaci ɗaya tana huci.


Ran Hajiya Lubna ya ɓaci sosai da kalamanta amma sai bata kulata ba tayi banza da ita.
Ita dai Hajiya Labiba duk tana jinsu amma bata tsoma musu baki ba, sai ma wayarta data fito da ita daga cikin jaka take ta latsawa tana sakin murmushi. Dan ita Allah ya sani bata ganin laifin Fadwa ko kaɗan akan irin tsanar da ta yiwa Azeez saboda an tauye mata hakki da yawa an durƙusheta sosai an hana mata ci gaba, shiyasa take bala'in jin tausayinta domin zama da matsiyaci sai wanda ya daure ya kai zuciyarsa nesa.


Haka har aka gama musu babu wanda ya sake magana a cikin su, suka miƙe ko wacce ta ɗauki jakarta Fadwa sai hararar Hajiya Lubna take tana sakin tsaki, ita ko Hajiya Lubna ko bi ta kanta bata sake yi ba ta wuce taje ta biya duka bill ɗin komai da akayi musu kana suka fice daga saloon ɗin.
Kasancewar dama dukkansu a motar Hajiya Lubna suka je saloon ɗin dan koda sukaje gidan Hajiya Lubnan Hajiya Labiba acan ta bar tata motar, shiyasa direct daga saloon ɗin suka wuce gidan Hajiya Lubnan sai da Hajiya Labiba ta ɗauki tata motar kana suka wuce kasuwa ita da Fadwa dan Hajiya Lubna tace bazata je ko'ina ba zata tsaya a gida ta ƙarasa wani aiki.










*BAYAN AWA HUƊU*




Fadwa ce tsaye a tafkeken ƙayataccen bedroom ɗin na Hajiya Labiba tana shiryawa cikin wani haɗaɗɗen lufaya mai tsadar gaske yellow mai flowers blue ajiki sai rigar da tasa long sleeve itama blue sannan tasa takalmi mai tsini blue shima sai ƙaramar jakarta ƴar madaidaiciya data sagala a tsintsiyar hannunta mai kyau kalar blue itama.


Bata yi wani kwalliya sosai a fuskarta ba yau sai hoda kaɗai da janbaki da ta ɗan shafa amma idan ka ganta sai ka ɗauka wata shuwa arab ce saboda bala'in kyaun da shigar tasu tayi mata ga ƙunshin ƙafarta da hannayenta ya sake fitowa raɗau yayi jajir dashi sai tayi sharr da ita kamar wata sabuwar amarya.


Hajiya Labiba dake gefenta a tsaye tana ƙoƙarin naɗa lufayan itama a jikinta ta buɗe baki galala kawai tana kallonta, cikin wani irin taku Fadwa ta ƙaraso gabanta ta tsaya fuskarta ɗauke da wani ƙayataccen murmushi take faɗin
"Nayi kyau kuwa ƙawata...?"


Hajiya Labiba tayi murmushi kana tace "Haba ana magana ma! Ai kinyi masifar yin kyau tawan..na tabbata yau kinfi jiya haɗuwa da tsaruwa dan baki ga yadda kike wani walwali da ɗaukar ido bane..kamar a saceki a gudu..."


Cikin tsananin jin daɗi Fadwa tace "Na gode tawan, wallahi har kinsa kaina ya ƙara wani girma da wannan yabon naki..."




Ta faɗa lokaci ɗaya tana ƙara jin wani alfahari da farin ciki suna mamaye zuciyarta, murmushin itama Hajiya Labiban tayi tana faɗin "Ai kinfi duk yadda zan kwatanta ki aminiyata, dan ke ɗin ta musamman ce wallahi..samun irinki a wannan zamanin zaiyi matuƙar wahala saboda ke mai tsada ce sai mai babban rabo, shiyasa nake tayaki baƙin ciki da takaicin kasancewarki matar talaka faƙiri mai jan keke napep wallahi..."


Ɗan taɓe baki kawai Fadwa tayi ba tare da tace komai ba ta matsa inda wani haɗaɗɗen ƙaramin show glass yake ta buɗe, turaruka ne kala kala masu matuƙar tsada ƙamshi jere reras a ciki ta ɗauki turaren sweet baby da lovely ta feshe ilahirin jikinta dasu tsaf kana ta ɗauki wayarta ta zura cikin jaka sannan ta kwashi awarwarayen gwal manya manya guda huɗu da Hajiya Labiba ta zube mata yau ma ta zura a hannunta, kana ta juya tana kallon Hajiya Labiba dake fesa turare a jikinta tana faɗin "Muje dan Allah ƙawata, wallahi duk na ƙosa mu isa gurin in ga irin manyan jiga jigan matan da Hajiya Kalsoom ta gayyata dan nasan tabbas taron yau sai yafi na jiya tara manyan mata saboda ita mai tarin jama'a ce..."


Hajiya Labiba tace "Ai kuwa dai kamar kin sani yau gidan na can cike maƙil da jama'a sai wanda ya gani..."


Ta faɗa tana duƙar jakarta itama kalar flowern jikin lufayanta ta riƙe a hannunta tace "Muje ko..?"


Ta faɗa tana yin gaba yayinda Fadwa ta rufa mata baya suka fice daga bedroom ɗin, haka suka fita harabar gidan gaba ɗayansu suna baza ƙamshin turare irin na manyan mata masu aji da yarari, direba yana ganinsu ya taso da sauri ya iso gabansu kamar zai kifa ya rusuna yana faɗin "Barka da fitowa Hajiya..fita zamuyi ne...?"


Fadwa dake kallonsa sama da ƙasa a wulaƙance tace "A'a ba fita zamu yi ba, zamu zauna ne a bakin ƙofa..." Ta faɗa tana jan tsaki kana taja hannun Hajiya Labiba tana faɗin "Muje dan Allah ni kar ya ɓata mana lokaci muna da abun yi mai muhimmanci a gabanmu..."


Cikin sauri yace "Allah ya huci zuciyarki ƙawar Hajiya..." Ya faɗa yana wucewa da hanzari yaje ya buɗe musu wata dalleliyar sabuwar mota baƙa wuluk ƙirar Bugatti.
Cikin rawar jiki Fadwa ta ƙarasa da sauri ta shige zaraf ta zauna lokaci ɗaya tana ƙarewa motar kallo dan sosai ta gama tafiya da imaninta, itama Hajiya Labiban kanta ganin yadda Fadwan tayi sai data kalleta ta murmusa kana ta girgiza kai ta shiga ta zauna a kusa da ita, sai da ya rufe musu ƙofar kana ya juya cikin sauri ya shiga gurin zamansa ya zauna ya tada motar yaja maigadi ya wangale musu get ya silala motar a hankali suka fice daga gidan.






















*Ya Allah ka gafartawa mahaifina da sauran Musulmi baki ɗaya🤲*
*WADATAR ZUCCI*




*Wattpad: Aishaalto09*






1️⃣7️⃣




Abba ne zaune a ɗan filin tsakar ɗakinsu ya zuba uban tagumi yana kallon Mama dake riƙe da wani ɗan madaidaicin madubi a hannunta tana shafa hoda a fuskarta, lokaci ɗaya tana ƙara kallon kanta a madubin tana sakin murmushi.
Kaɗa kai Abba yayi a hankali yana kallonta kafin ya juya cike da takaicinta ganin ta ɗauko janbaki zata shafa a leɓenta yayi murmushin da yafi kuka ciwo yana sake kallonta cikin mamaki da al'ajabinta yake faɗin "Yanzu Maryama rayuwar da kika ɗaukarwa kanki kina ganin mai ɓullewa ce..kamar ke ace kina babba dake tsofai tsofai amma kina abu sai kace wata ƙaramar yarinya...?"


Da sauri ta ajiye madubi da janbakin dake hannunta tana yatsina fuskarta cikin ƙosawa

14 / 38