Author : Aisha Alto Category : A Books
tace "To rayye me kuma nayi maka nida bana girma da laifi a gurinka...?"
Ta faɗa cikin taɓe baki tana harararsa, shiru yayi yana ƙoƙarin danne ɓacin ransa kafin yace "Yanzu ina zakije kike irin wannan kwalliyar kamar wata ƙaramar yarinya..anya kuwa kin san abinda kike shirin aikatawa Maryama...?"
Fuska ta ƙara tamkewa tana watsa mai harara kafin tace "A'a ban sani ba kazallaha saika sanar dani..." Ta faɗa cikin gatse tana watsa mai wani mugun kallo mai kama da harara.
Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace "Ai indai zakice irin wannan muguwar ɗabi'ar taki ta kwaɗayi da son abun duniya zaki ɗore da ita har ƙarshen rayuwarki to kuwa kina da babban aiki ja a gabanki, dan wallahi wata rana sai kinyi danasani mara amfani a nan gaba...kina tsofai tsofai dake ko kunya babu kice ke babu abinda kika iya sai kwaɗayi da son abun duniya..yanzu dan Allah da kike wannan shirin ina zakije...?"
Ɗaure fuska tayi sosai kafin tace "Ikon Allah wai tsofai tsofai dake, a'a kwan lafiya ce ni ƙarewar tsufa, kuji min ɗan mutumi da baƙin ciki da hassada sai kace a kanka nake kwaɗayi da son abun duniyan da zai dameka..." Ta ƙarashe maganar lokaci ɗaya tana ɗaukar ƴar ƙaramar wayarta ƙirar Aitel dake ajiye a kusa da ita, cikin lokaci kaɗan ta lalubo numbern Fadwa wacce tayi saving ɗinta da *KUƊINA.*
Shiru yayi yana bin ta da kallo, ta danna mata kira lokaci ɗaya tana kallon ɗan agogon dake maƙale a bangon ɗakin, ƙarfe 5pm ta gani har ta wuce.
Wayar ta shiga haka ta dinga ringing har ta katse bata ɗauka ba, bata haƙura ba ta sake kiranta nan ma har ta gama ringing ta katse bata ɗaga ba haka ta dinga kira har kusan sau biyar bata ɗaga ba, tsaki taja ta kife wayar tana harararsa kamar shine ya hana Fadwan ɗaukar wayar tata, shi dai bai tanka mata ba da ido kawai yake ta bin ta bai ce komai ba.
Haushin haka ne yasa ta sake ɗaukar wayar a fusace tana faɗin "Duk baƙin cikin mutum dai yau sai naje bikin gidan masu arziki, sai dai ƙyashi da hassada su kashe ɗan baƙin ciki...." Ta faɗa lokaci ɗaya tana sake danna mata wani kiran a karo na shida.
Daga can ɓangaren Fadwa dake gefe cikin wani haɗaɗɗen ƙayataccen garden dake gidan Hajiya Kalsoom daya cika da manyan mata ana ta shagalin biki gurin ya kaure da hayaniya, sai sautin kiɗan dj ke tashi, shigowarsu tsakiyar fili kenan ita da Hajiya Labiba da wata hamshaƙiyar ƙawarsu Hajiya Zalika wacce ke auren wani babban ɗan kasuwa a jihar Kano, zasu fara yiwa amarya liƙi kenan, taji vibration ɗin wayarta dake cikin jaka wacce dama ta sakata a silent ne gudun kar a dameta da kira, ba tabi ta kanta ba sai da suka gama liƙin suka fice daga cikin filin kana ta zura hannu a jakarta ta ɗauko wayar, ganin sunan wacce ke kira ne yasa tayi murmushi kafin ta ɗaga kiran tana faɗin "Hello Mamana...kina jina....?"
Daga can ɓangaren Mama da taji muryar Fadwa ta ɗaga kiran ta washe baki cike da farin ciki gefe guda tana hararar Abba daya saki baki galala yana kallonta kafin tace "Ina jinki ƴar albarka, ya taron...kuna can gurin bikin kenan dan naji hayaniya...?"
Murmushi Fadwa tayi kafin tace "Muna can tun ɗazu guri yayi guri Mama manyan mata an haɗu ana ta shagali sai kin gani wallahi abun gwanin ban sha'awa...." Da sauri ta katseta da faɗin "Yauwa dama abinda nakeson ji kenan shiyasa nake ta kiranki, aiko nima banga ta zama ba yanzu nan zan taho ayi dani insha Allahu ki gaya min sunan unguwar kawai yanzu yanzu zan shirya dan bazan ta zama a gida in cuci kaina ba atoh...."
Fadwa tace "Toh..." Nan ta gaya mata sunan unguwar daga haka suka yanke kiran, cikin sauri Mama ta ajiye wayar ta miƙe ta fara ƙoƙarin shiryawa cikin wata atamfarta mai sauƙin kuɗi wacce Fadwan ta ɗinka mata ita tun ƙaramar sallahn data wuce, inda tasa Sadeeq telanta yayi mata ɗinkin doguwar riga Ashape mai kyau wanda yaji stones irin na zamani masu walwali da ɗaukar ido ta saka, kana ta ɗauki ɗankwalin atamfar ta zauna ta saita madubi ta kafa ɗaurin Maryam Babangida a kanta wanda ya zauna daram, sannan ta wani turosa gaban goshi ta ɗan karkata shi yayi gefe irin na ƴan matan zamani.
Shi dai Abba sakin baki kawai yayi yana kallon ikon Allah, dan sosai zuwa yanzu lamarin na Mama ya fara bashi tsoro, domin yaga alamar abun nata ƙara gaba gaba kawai yake kwata kwata babu alamar wata saduda a tattare da ita, Mama kuwa ko a jikinta shirinta kawai take yi abin ta ko kallon inda yake bata yi.
Sai data gama shiryawa tsaf har ta yafa gyalenta kana ta ɗauki ƴar jakar pos ɗin da take zuba cinikin ƙuli ƙuli da kayan miyanta ta buɗe ta jefa wayarta a ciki ta riƙe a hannunta lokaci ɗaya tana gyara zaman gyalenta tana wani yatsina fuska.
Abba dake ta kallonta cikin ƙufuluwa da baƙin ciki yace "Wai yanzu kina nufin da gaske bikin ƙanwar ƙawar ƴarki zaki kama hanya ki tafi gotai gotai dake Maryama saboda rashin tsoron Allah....?"
Ya faɗa cikin son kwantar da fushinsa duk da ya kasance mai tsananin haƙuri da yakana.
Banza dashi tayi tasa kai zata fice daga ɗakin, da sauri ya miƙe yana faɗin "Babu fa inda zakije Maryama...kuma a matsayina na mijinki nake baki wannan umurnin, dan haka ki dawo ki zauna tun kafin ranki ya ɓaci...."
Ta buɗe baki a fusace zatayi magana kenan wasu kyawawan ƴan mata guda biyu masu tsananin kama da ita suka shigo ɗakin hannuwansu rungume da litattafai wanda da ganin alamu daga makarantar islamiyya suka dawo, dan dukkansu sanye suke da dogayen hijabai har ƙasa iri ɗaya.
Ganinsu baisa ta fasa abinda tayi niyya ba sai ma ƙara buɗe murya da tayi ta taso mai cikin masifa da bala'i tana faɗin "Wallahi sai na tafi sai dai duk abinda zai faru ya faru...kai ya ma daɗe abun bai faru ba, sai naje ɗin kayi duk abinda zakayi kaji...!?"
Ta faɗa kai tsaye tana ƙoƙarin raɓawa ta gefensa ta wuce, cike da mamaki ƴan matan suke kallonta kafin ɗaya daga ciki tace "Haba..Mama wannan wace irin rayuwa ce kika zaɓarwa kanki tsakani da Allah...? Wannan abun da kikeyi fa sam bai dace ba har ga Allah nidai na gaji da ganin irin wannan wulaƙancin da kike yiwa mahaifin mu tunda ba'a kansa kaɗai aka sauke talaucin duniya ba kuma ba wai Allahn da ya yishi baya sonsa bane daya barshi a haka...idan kuma kin gaji da zama dashi ne sai ki nemi ya sawwaƙe miki ba ki dinga cin zarafinsa a gaban ya'yansa kina neman zubar mai da mutunci ba...."
Ta ƙarashe maganar kai tsaye tana kallon cikin ƙwayar idanunta cike da rashin kunya, zaro idanu waje ta kusa da ita tayi cike da tsoro kafin cikin sanyin muryarta tace "Subhanallahi Ilham ki daina mata rashin kunya mana dan Allah, kar fa ki manta ita ɗin mahaifiyar mu ce bai kamata kina gaya mata duk maganar data fito daga bakinki ba...."
Cikin baƙin ciki da damuwa wacce aka kira da Ilham ɗin tace "Amma baki ji itama mahaifinmu ne take gayawa duk maganar data fito daga bakinta ba....?"
Bata bata zarafin magana ba ta cigaba da faɗin "Dan haka ki ƙyaleni dole zan faɗa Amatullah! Kaf unguwar nan babu uwa kamar tamu, sam ba wanda kake jin kansa da mijinsa a cikin gidansa sai ita itace duk abinda akayi bazata barwa cikinta ba sai ta amayar...kina kallo dai komai mahaifin mu yayi a cikin gidan nan sai ta nuna bai isa ba saboda tsabar rashin godiyar Ubangiji da kwaɗayi haka take ta zubar mai da mutunci a gurin mutanen unguwa ake kallonsa wani iri....amma wallahi Amatullah kowa ya sani mahaifin mu bai da zuciyar kwaɗayi da son abun duniya, yana da WADATAR ZUCCI da jajircewa yaga ya nemi na kansa..amma Mama kullum hakan baya yi mata akoda yaushe ita gazawarsa take gani, meye laifinsa Amatullah...shine ya ɗaurawa kansa talaucin ko akwai wanda yafi ƙarfin shima Allah ya ɗora masa ne....? Bansan kuma me takeso yayi ba....." Ta ƙarashe maganar lokaci ɗaya ƙwallar tausayin kansu dana mahaifinsu na taruwa a idanunta.
Wani mugun kallon banza Mama ta watsa mata a wulaƙance tana faɗin "To kisa ya sakeni mana dan uwar ubanki ki gani idan zan ƙara ko second ɗaya ne a wannan ƙaddararren baƙin gidan nasa....shegiya kawai mai matacciyar zuciya wacce ta kwaso mugun halin dangin ubanta na baƙin talauci da muguwar zuciya...."
Ta buɗe baki kenan a tsiwace zata sake bata amsa Abba ya ɗaga mata hannu cikin sanyin muryarsa yana faɗin "Fita ku tafi ɗakin ku Ilham, kuma daga yau kar in sake ji idan muna magana da mahaifiyarku wani daga cikinku ya sake saka mana baki...domin wannan ba itace irin tarbiyyar da muka yi muku ba kunji ko....?"
A sanyaye duk suka gyaɗa mai kai kana suka juya ba tare da sun sake cewa komai ba suka fice daga ɗakin.
Cikin ɓacin rai Mama tace "Kash ai da baka katse mata hanzari ba da ka barta ta ƙarasa zagina tunda ita tantiriya ce ƴar iska gantalalliya...."
Lokaci ɗaya Abba yaji wani abu na taso mai tun daga ƙasan ransa ya tokare mai maƙoshi ya tsaya mai ƙyam a ƙahon zuciya, shi dai Allah ya sani bai yi dace da uwar ya'ya ta gari ba, cikin ƙoƙarin danne fushi da ɓacin ran da yake ji suna taso masa yake kallonta kafin yace "Kull! Daga yau karki sake jifan ƴaƴana da wata mummunar kalma makamanciyar wannan, domin kome sukayi miki kece kika jawo...saboda a gurinki suke ganin komai kuma kece ke ɗaurasu akan hanya...."
Wani ƙasƙantaccen kallo ta watsa masa tana faɗin "To ko zaka kirata ta dawo ne sai ku rufeni da duka gaba ɗayanku tunda naga kamar hakan shine zai sanyaya muku zuciya da kai har itan...?"
Ta faɗa cike da masifa tana kumfar baki, ko tanka mata bai yi ba ya raɓa ta gefenta zai fice, har ya kai bakin ƙofa ya tsaya ya juyo yana kallonta kafin cikin bada umarni yace "Ban baki iznin fita ko nan da can ba kuma idan kika fita bada izinina ba ban yafe miki ba tunda ke bakin san abinda ya dace ba...."
Daga haka yasa kai ya fice daga ɗakin ya barta nan tsaye tana binsa da kallon mamaki. Wai yau itace Abban Fadwa yake gayawa irin waɗannan maganganun...Yanzu har ta kai lalacewar da zai tasata gaba yana gindaya mata wasu shegun sharuɗansa marasa tushe ballantana makama..? Aiko wallahi sai yasan yayi da Maryama ɗiyar Malam Audu da Fulera in ma yana tunanin tayi sanyi ne to tana nan daram a yadda ya santa tun tali tali kuma sai ta nuna masa kuskurensa.
Da wannan tunanin ta cire gyalenta ta koma ta zauna a tsakar ɗakin bayan tayi wurgi da ƴar pos ɗin dake hannunta gefe ta rafka tagumi cike da baƙin ciki, Allah ya sani yau taci burin zuwa gidan bikin nan sosai dan har ta gama tsara irin abubuwan da zatayi a gidan idan ta isa, amma gashi yanzu a karin banza an rusa mata tsari.
*******
A ɓangaren Ya Azeez kuwa ƙarfe 5:30pm nayi ya wuce kasuwa domin ya yiwa Ummansa da Fadwa siyayyan kayan abinci kamar yadda ya saba yi musu duk bayan sati biyu zuwa uku, Ummansa ya fara haɗawa komai da yasan zata buƙata na kayan abinci, sannan ya siyawa Fadwa taliya da indomie itama kana ya siya kwai rabin kiret ya haɗa mata har da kayan tea kasancewar yasan sune kawai abinda take iya ci a gidan suma kuma dan tasan ba wani wahalar dafawa zatasha sosai ba domin ko ruwan lifton wani lokacin ganin ƙyashin ɗorawa take a gidan ballantana akai ga dahuwar indomie ko wata taliya da take ganin ɓata lokaci ne kawai indai itace zata tsaya ta dafa da kanta to ta gwammace ta wuni da yunwa ko ta tafi gidan ƙawayenta taje can ta ci lafiyayyen abincinta wanda ranta yake so tayi hani'an, in kuma da safe ne kafin ya fita sai dai shi da kansa ya ɗora tukunya ya dafa mata tana zaune tana kallonsa ya gama ya ɗauka ya kai mata ba kunya ba tsoron Allah tasa hannu ta ƙarɓa kuma taci ta ƙoshi abin ta hankali kwance ba godi bare na gode.
Sai daya gama haɗa mata komai da yasan tana buƙata dan har cornflakes da yaga tana yawan sha, sai daya siyan mata sannan yaje gurin masu kayan miya nan ma yasa aka haɗa masa mai ɗan yawa ya biya kuɗin yasa aka raba masa gida biyu ko wanne aka ɗaure a ledarsa daban daban, ya kwashi kayan ya zuba a napep ɗinsa ya wuce.
Daga nan direct K/Mashi ya wuce gidan Ummansa yaje ya kai mata nata, sosai taji daɗi ta dinga saka masa albarka kafin ta tashi ta zubo masa jallof ɗin shinkafa da wake da tayi saura da suka dafa da rana ta kawo masa, kana ta ɗebo masa ruwan randa mai sanyi ta ajiye masa ya zauna ya ci ya ƙoshi yasha ruwan yayi hamdala.
Sun daɗe suna tattaunawa da Ummansa akan rayuwa kafin ya koro mata zancen Fadwa da abinda take yi mai wanda har yanzu bata canza ba, sai da ta bari ya kai ƙarshe sannan tace "Toh yanzu me kakeso kuma ince maka...?"
Ta faɗa tana kafesa da ido, rausayar da kai yayi kana ya ƙara matsawa gabanta sosai ya tanƙwashe ƙafafuwansa, kafin cikin sanyin muryarsa yace "Umma Fadwa ta gama rainani bata ganina da mutunci ko kaɗan, ban isa in gaya mata magana taji ba duk abinda ta ga dama shi take yi babu ruwan ta da zaiyi min daɗi ko ba zai yi min ba..ta fita duk lokacin da taso ta dawo lokacin da ta ga dama, tamkar wacce take zaman kanta haka Fadwa ta maida rayuwarta babu abinda ya dameta da damuwata. Kullum idan ta saka ƙafa tun da sassafe ta fita tabar gidanta sai can dare sannan zata dawo, ko cikin kwanakin nan sai ƙarfe 12am na dare take dawowa wai suna bikin ƙanwar ƙawarta..taya hakan zaiyi min daɗi har hankalina ya kwanta Umma...?"
Ya ƙarashe maganar yana duƙar da kansa ƙasa, shiru Umma tayi tana kallonsa kafin tace "Naji Yayan Imaan..amma dole yau ma haƙurin dai shi zan kuma baka, tunda bayan hakan babu abinda zan iya gaya maka..."
Ta faɗa fuskarta cike da tausayinsa, murmushi yayi ganin yadda ta nuna jin tausayinsa a fili ƙarara kafin yace "Toh shikenan Umma na gode kuma insha Allahu zan cigaba da haƙuri da halayen Fadwa kamar yadda kikace har zuwa lokacin da Allah zai kawo min mafita..."
Ya faɗa cikin sanyin muryarsa yana kallonta, kaɗa kai tayi a hankali kafin tace "Da yardar Allah kuwa Allah zai kawo maka kyakkyawar mafita ta alkhairi anan gaba wacce sai kowa yayi mamaki, kai dai kai ta haƙuri kana nuna komai ba komai bane insha Allahu wata rana sai labari..." Ta faɗa a sanyaye cike da tausayinsa, dan ita kanta ta sani ɗanta yana da bala'in haƙuri sosai shiyasa bata fatan ace haƙurinsa ya gaza wata rana zuciya ta ɗebesa ya yanke hukuncin da bai kamata ba.
Haka suka daɗe suna hira har Imaan ta dawo daga islamiyya ta samesa a gidan, yana nan zaune sai ƙarfe 7pm bayan yayi sallar magriba sannan ya bar unguwar.
*******
Yau ma kamar kullum Fadwa sai dare sannan ta baro gidan bikin ta koma gidanta shima sai da Hajiya Lubna ta haɗata da yayar ta Hajiya Kalsoom ta kirata tayi mata faɗa sosai sannan tace ya kamata ta tafi gida haka nan dare yayi kar mijinta ya riga ta komawa gida ya iske bata nan ransa yazo yana ɓaci gobe tana son fitowa kuma ya hanata, domin kwata kwata ita bata san irin zaman da Fadwan takeyi da mijinta ba shiyasa take hasashen hakan, wanda ita Fadwa anata son ran so tayi ta kwana a gidan Hajiya Kalsoom ɗin, amma ganin babu yadda ta iya yasa ta haƙura ba dan taso ba ta tashi Hajiya Kalsoom da kanta tasa direbanta ya ɗauketa a motarta ya kaita gida.
Ƙarfe 11:50pm. Dai-dai direban Hajiya Kalsoom ya dire Fadwa a ƙofar gidanta kamar yadda ta kwatanta masa, sai dai sosai tayi baƙin cikin kasancewar unguwar tasu shiru cikin layinsu babu kowa mutane duk sun shige gidajensu sun kwanta sai ƴan tsirarun dake bakin titi suna harkokinsu amma taso ace koda mutum ɗaya ne ta haɗu dashi a lokacin dan ya ƙarar a gaba cewa ya taɓa ganinta a motar matar mataimakin gwamnan jihar Kaduna sukutum an kawota gida ko banza za'a daina mata kallon matar matsiyaci a dawo ana mata kallon ƙawar matar mataimakin gwamnan jihar Kaduna daga nan darajarta ta ƙara ɗaguwa a idanun jama'ar unguwa a dawo a riƙa mata kallon hamshaƙiyar mace ƙawar manyan mata masu faɗa aji.
Yana yin parking ya fito da sauri yaje ya buɗe mata tana ta wani yauƙi da iyayi ta zuro ƙafafuwanta waje cike da yanga sannan ta fito riƙe da wayarta da ƙaramar jakar handbag ɗinta a hannunta kana ta juya ta ɗauki ƙatuwar ledan data cikota da kayan ciye ciye iri iri danginsu snacks da drinks kala kala da gasassun kaji waɗanda aka rarraba a gurin bikin sister's day ɗin ta riƙe a ɗayan hannunta ta juya ko waiwayen direban ba ta tsaya yi ba kawai ta ɗaga masa hannu tasa kai ta shige cikin gida abin ta, shima direban bai ce komai ba ya shiga motar yaja yabar unguwar.
*Ya Allah ka gafartawa mahaifina da sauran Musulmi baki ɗaya*🤲
[12/23, 10:17 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI*
*Wattpad: Aishaalto09*
1️⃣8️⃣
Ya Azeez kuwa koda ya baro gidan Ummansa bai tsaya a ko'ina ba direct ya wuce unguwarsu, dan sosai ya gaji gaba ɗaya jikinsa ciwo yake yi tamkar wanda aka yiwa dukan tsiya, shiyasa ya ƙosa ya isa gida ya watsa ruwa a jikinsa ko zai ɗan ji dama dama ga wani azababben ciwon kai mai tsanani daya saukar masa lokaci guda, yana neman ya hanasa sukuni.
Yana fitowa dai-dai kan babban titin