Chapter 11 Reading WADATAR ZUCI Complete Book by Aisha Alto.txt Arewa Novels

WADATAR ZUCI Complete Book by Aisha Alto.txt

Author :  Aisha Alto Category :  A Books

Chapter   11 / 38

30K to 33K   out of 113.4K words

da sauƙi dama na dawo ne in duba jikin naki saboda naga kamar bakya jin daɗi ɗazu da safe kuma har na fita daga gidan baki tashi ba shiyasa na dawo in dubaki kuma inji ko kin sha magani...." Ya faɗa lokaci ɗaya tare da zaro gudar dubu ɗaya daga cikin aljihunsa ya ajiye agabanta kana ya juya zai fice daga ɗakin yana faɗin "Sai na dawo, ki kula da kanki Allah ya ƙara lafiya...." Ya ƙarashe maganar lokaci ɗaya tare da ficewa daga ɗakin.




Wata zazzafar ajiyar zuciya Fadwa ta sauke kana ta koma ta zauna lokaci ɗaya tana dialing numbern Hajiya Labiba, kamar kuwa jira take kiran na shiga ta ɗaga cike da masifa tana faɗin "Wai ina kika shiga ne dan tsabar iskanci da wulaƙanci ina ta kiranki a waya kin ƙi ɗagawa...?" Ta faɗa a hasale tana sauke numfashi.




A hankali Fadwa ta sauke numfashin itama kafin cikin ƙasa ƙasa da murya tace "Shine ya shigo shiyasa kika jini ɗif wallahi..amma kiyi haƙuri..."


A fusace Hajiya Labiba ta katseta da faɗin "Dan ya shigo sai akayi ya ya...nace sai akayi ya ya...? Oh ashe dama tsoronsa da kikeji ne yasa har yake takaki yake samun damar yi miki duk iskancin da yaga dama...? Lallai yau na sake raina wayonki ashe dama duk bakinki na banza ne da wofi ban sani ba Fadwa....? Wallahi yau kin bani mamaki na raina ajinki..." Daga haka ta shiga zazzaga mata masifa tana ta faffaɗan mata maganganu akan ta daina jin tsoronsa idan ya zare mata ido itama ta zare masa tunda shi lusarin namiji ne babu abinda yake tsinana mata a gidan da har zaisa ta dinga jin wani tsoronsa haka kawai, ta dage ta kwatarwa kanta ƴanci ta kuma tsaya tsayin daka itama ta nuna masa cewa dashi ko babu shi zata iya cigaba da rayuwarta babu abinda zai sameta.




Fadwa kawai sakin baki tayi tana sauraren masifar da Hajiya Labiba take ta surfa mata sai kace wata uwarta, kawai sai taji duk ranta ya ƙara ɓaci da abinda Ya Azeez yayi mata jiya, taji kamar ta dawo da hannun agogo baya ta yadda zata zagesa ta gaggaya mai magana iya son ranta.


Lallai Hajiya Labiba tayi gaskiya ita banza ce shashasha kuma bakinta ma na banza ne da wofi dole a raina wayonta yanzu ji yadda ya barta da kumburarren baki ya tafi harkokinsa, ita kuma ya barta tsuru a gida kamar wata mayya tana ji tana gani bata da halin fita taje ko'ina, lallai ya kamata ta tashi tsaye domin ta ƙwatarwa kanta ƴanci sannan ta nunawa Ya Azeez cewa itama tasan takan tsiya.


Maganar da Hajiya Labiba ta ci gaba da yi ce ta dawo da ita daga duniyar tunanin data lula ta sake manna wayar sosai a kunnenta kafin tace "Wallahi duk abinda kika faɗa gaskiya ne ƙawata, kuma dole zan tashi tsaye in kwatarwa kaina ƴanci in bi hanyar da nasan zata ɓullar dani, domin kuwa idan na bari muka ci gaba da tafiya dashi a haka ba ƙaramin la'anta min rayuwata zaiyi ba. Wallahi a kullum shiyasa nake ƙara ƙaunarki a raina nake kuma ƙara ganin kima da mutuncin ki a idanuna saboda burinki ako da yaushe shine kiga kin ɗaukaka darajata a ko'ina kin kuma fifita ni fiye da kowa a gareki, na gode ƙawata kuma insha Allahu bazan taɓa baki kunya ba zan gyara daga yau nayi miki wannan alƙawarin dan sai na nuna masa cewa ni ba kanwar lasa bace kamar yanda yake zato, sannan in nuna masa mata ma suna suka tara sannan ruwa ba sa'an kwando ba ne, ko an zubasa sai ya tsiyaye...." Ta ƙarashe faɗa tana sauke numfarfashi kamar wacce ke shirin kokawa.


Daga can ɓangaren kuwa Hajiya Labiba da ta gama saurarenta taja ajiyar zuciya ta sauke cike da jin daɗi kafin tace "Alhamdulillahi dama haka nake son ki zama ƙawata, to yanzu kuma ya maganar shirye shiryen biki ƙanwar Hajiya Lubna kinsan fa ranar juma'ar nan ne bikin yau saura kwana uku kuma tun yau ne za'a fara programs, ga ankon Dinner ɗinki nan ma a hannuna ɗazu na aika direba yaje gidan Lubnan ya karɓo mana ƙarfe 5pm za'a fara a Hall ɗin dake Ahmed Musa Garden, ya za'ayi kenan...?"


Ba tare da tunanin komai ba Fadwa tace "Haba ba damuwa ai dole zanzo ƙawata kema kin sani, ina nan tafe tun ƙarfe uku ki jirani..."


Hajiya Labiba tace "Yauwa to Shikenan, Allah ya kaimu anjiman lafiya sai kinzo ina jiranki...."


Cikin rashin tunani Fadwa ta amsa mata da "Toh sai kin ganni..." Daga haka kawai suka yi sallama akan sai sun haɗun kafin suka yanke kiran.






Sakin baki kawai Fadwa tayi a zaune tana saƙawa da kwancewa kafin ta miƙe da sauri ta shiga uwar ɗaka ta ɗauko gyalenta wanda ya shiga da atamfar jikinta tayi rolling ɗinsa akanta bayan tayi dabara ta janyosa har zuwa kan bakinta ta naɗesa ta yadda zai rufe bakinta da yake a kumbure suntum har lokacin, ta ɗauki jakarta da wayarta cikin sauri ta fice, sai da ta fara kulle ƙofar ɗakin ta jefa ɗan makullin a cikin jakarta sannan ta juya kai tsaye ta fice daga gidan gaba ɗaya, yau ko tsayawa ma batayi ta kulle ƙofar gidan ba, kawai ta janyo ƙofar ta sakaya ta ƙara gaba abunta.




Tana fita dai-dai kan layinsu ta tari ɗan acaɓa ta ɗare abunta dan bata jin zata iya ƙarasawa bustop ɗinsu yau gurin masu keke napep shiyasa kawai ta hau mashin bayan ta gaya masa unguwar da zai kaita ya tada mashin ɗin yaja suka wuce.






Ƙofar wani ɗan madaidaicin ƙaramin gida ginin bulo da bulo mai ɗauke da fenti kalar ruwan madara tasa mai mashin ɗin daya ɗaukota ya ajiyeta, ta sauka ta buɗe jakarta ta zaro kuɗinsa ta bashi kana ta juya ta shige cikin gidan bakinta ɗauke da sallama.


Wata kyakkyawar mata ce wacce a ƙalla shekarunta zasu kai arba'in zuwa da bakwai zaune a ɗan filin tsakar gidan da babu sumunti ko kaɗan sai ɗan diddigen ƙasa ga ƙaton baho girke a gabanta wanda ke cike da curarriyar tunkuza da aka murza, sai wani ɗan katakon mulmula da wasu manya manyan farantan silba wanda idan ta cura tunkuzar ta mulmula take jerawa akai, jin sallamar ƴar tata ne yasa ta ɗagowa da sauri lokaci ɗaya tana washe baki ta amsa mata sallamar haɗe da faɗin "Oyoyo kuɗina..Ƴar halak kenan kin ƙi ambato, yanzu fa muka gama maganarki nida Ilham nake cewa kwana biyu na jiki shiru ban ganki ba Allah yasa dai lafiya...." Ta ƙarashe maganar lokaci ɗaya tana ƙare mata kallo.


Wani rau rau Fadwa da tayi da idanu kamar zata fashe da kuka kafin ta yatsine fuska cike da shagwaɓa tana faɗin "Wallahi lafiya ƙalau Mama muna ta shirye shiryen bikin ƙanwar ƙawata ne Hajiya Lubna, shiyasa kika jini shiru gaba ɗaya kanmu ya ɗauki zafi, muna ta zirga zirga kullum ina kan hanyar zuwa gidan Hajiya Labiba da Hajiya Lubnan, kwata kwata bana samun zama sai dare sannan nake komawa gida kuma dana koma kwanciya kawai nake yi saboda na gaji shiyasa ko samun damar kiranki ma bana yi...." Ta faɗa lokaci ɗaya tana janyo kujera ƴar tsugunne ta zauna akai.
Baki Maman ta washe cike da fara'a tana faɗin "Ikon Allah kice har bikin ya matso...? Amma kuwa gaskiya Fadwa baki kyauta min ba ko kaɗan da kika ƙi gaya min tunda wuri dan in samu in tanadi sabon ɗinkina na kece raini in shiga taron manyan mata nima in samu a fantama dani...koda yake ai duk da haka ma bata ɓaci ba yaushe ne za'a fara bikin dan in san abinda zan tanada...?" Take faɗa tana kallon Fadwa da take ƙoƙarin cire gyalen jikinta kafin ta cigaba da cewa "Kinga sai ki haɗani kawai da ita uwar Hajiya Lubnan nima mu dinga mutunci abun mu kinga zumunci ya ƙara ƙulluwa kenan a tsakani...."


Fadwa data linke gyalenta ta ɗora akan jakarta dake ajiye a gabanta ta ɗago kai tana faɗin "Aiko Hajiya Turai akwai ta da jin kai da ɗagawa Mama, da wuya ku shirya da ita saboda akwai ta da gadara sosai dama dai Hajiya Kalsoom ce ita babbar yayar su Hajiya Lubnan..."




Mama kuwa da taji abinda Fadwa tace dan da nan ta gimtse fuskarta tana faɗin "To sai me nidai kawai ki haɗani da ita, duk wata ɗagawarta ba damuna zatayi ba nidai kawai in dangwali arziki kuma in barshi a mazauninsa atoh..shine kawai..." Ta faɗa tare da ɗaga hannuwanta sama alamar ko a jikinta ita dai kawai a kaita.


Gyaɗa kai Fadwa tayi tana faɗin "Aiko zaki ga matan manya Mamana, dan wallahi har da matar gwamnan jihar Kaduna zata zo bikin, ni ba dan ma wannan algungumin ya kumbura min bakina ba ai da tun tuni ina can abuna muna ci gaba da shirye shirye, amma da yake azzalumi ne mugu ji yadda yayi min da baki sai kace wacce tayi kokawa da ƙatti..." Ta faɗa lokaci ɗaya tana ƙara jin zafi da tsanar Ya Azeez ɗin a ranta.


Da sauri Maman ta kalli bakin ta ga yadda ya wani suntume yayi jajir abunka da farar fata gashi har lokacin bai saɓe ba yana nan a yadda yake sai ma ƙara hawa da yake tayi yana ƙyalli, take taji gabaki ɗaya ranta ya gama ɓaci gwiwarta tayi sanyi tace "Meya faru kuɗina...wane ɗan iskan ne ya nemi ya canza min kyakkyawar hallittarki lokaci ɗaya da duka haka...? Kuma dan saboda tsabar wulaƙanci da rashin mutunci ya rasa inda zai kai hannu ya doka a jikinki sai bakinki saboda yana baƙin ciki da kasancewarki mai magana ba kurma ba kome...?"


Cike da tsantsar takaici Fadwa dake jin wasu irin zafafan hawaye masu raɗaɗi na shirin ziraro mata tace "Ya Azeez ne fa ya matse min baki ya shaƙe min wuya ya dinga gana min azaba da mugunta iri iri haka kawai ba abinda nayi masa, kuma bayan yaje ya haɗo min munafunci a gurin Abba ya ɗauko Abba suka zo har gida ina dawowa na samesa a gidanmu ya mammareni sannan shi kuma ya ɗora min da nasa...dubi yadda ya maida min bakina kamar wata mara galihu....."


Ta ƙarashe maganar lokaci ɗaya tana matsar ƙwalla, a fusace Mama ta miƙe tsaye cikin tsananin tashin hankali da masifa take faɗin "Kan uban nan kai...lallai Malam ya shahara da mugunta, yanzu saboda tsabar mugun abu yaje har gidanki ya ware wannan kafcecen hannun nasa mai kama da guduma babu tausayi ballantana imani ya kafta miki shi a tattausar fuskarki haka kawai...? To wallahi anzo dai-dai inda ba zan iya haƙuri ba, kuma tunda abinda suka tsiro dashi kenan bazaki koma gidansa ba kin barosa kenan sai dai suyi duk wacce zasuyi, amma bazan taɓa zuba idanu ina kallo a ƙara kassara min rayuwarki ba bacin wanda akayi na farko, bari Malam ɗin ya shigo ina nan ina jiransa za'ayi duk wacce za'ayi amma auren wannan matsiyacin kam kin barshi har abada kin gama shi dan bazan lamunci mugunta ba..."


Fadwa ta buɗe baki zatayi magana kenan suka tsinkayi muryar Abbanta dake tsaye tun ɗazu a bakin ƙofa kamar daga sama yana faɗin "Ai kuwa aure tsakanin AbdulAzeez da Fadwa yanzu aka farashi, dan haka ban ga wanda ya isa ya guntulesa ba har sai lokacin da Ubangijin al'arshi yaso kuma yaga dama, dan haka ki sakawa zuciyarki haƙuri da salama kawai ki cire bakinki a maganar aurensu, in kuma ba haka ba to tabbas zaki iya jawa kanki matsala..Ke kuma..." Ya faɗa lokaci ɗaya yana kallon Fadwa da tai wani tsumu tsumu a zaune tana muzurai yace "Ki tashi cikin mutunci ki koma ɗakin mijinki tun kafin ranki ya ɓaci, kuma daga yau kar in sake ganin ƴar ƙafarki a gidana indai ba tare da mijinki zaku zo ko da wani ƙwanƙƙwaran dalili ba..."




Gaba ɗayansu suka zaro idanu a tare suna kallonsa cike da mamaki, ganin irin banzan kallon da yake binsu dashi ne yasa gaba ɗaya jikin Fadwa ya ƙara yin sanyi ta shiga ƙoƙarin miƙewa lokaci ɗaya ta ɗauki jakarta da gyalenta ta yafa a sanyaye tana zumɓuro baki ta juya zata wuce, Mama tai caraf ta riƙe mata hannu tana faɗin "Wallahi babu inda zakije tunda gidan ubanki ne nan dan haka babu wanda ya isa ya koreki daga cikinsa sai dai a haɗa har dani uwar data haifeki a kora atoh..." Ta faɗa cike da masifa tana karɓe jakar a hannunta.


Fadwa kuwa ji tai wani tarin baƙin ciki ya ƙara cika mata zuciya, ta fizge jakarta a zafafe tana faɗin "Mama nidai dan Allah ki barni in tafi tunda yace in bar masa gidansa..."


Mama tana numfarfashi take faɗin "Ai wallahi bai isa ba indai ni uwarki ina cikin gidan nan dole zai ganki a cikinsa, sai dai nima idan zai sallameni ne in kama gabana kinga ba wanda zai sake gani a cikinmu kuma sai in tayi dalili, yo me zai ma kawo wani dalilin da har zaisa mu haɗu dashi ko a hanya ne..? Ai kuma hanyar jirgi daban ta mota daban tunda babu haɗin fura da kashi..."
Tamke fuska Fadwa tayi tana faɗin "Ni dai ki daina faɗin haka dan Allah Mama, kawai bani jakata in tafi zan kiraki a waya idan na isa gidan bikin..."


Ƙin bata jakar Mama tayi, ta sake riƙeta ƙam ta rungume tana harararta kafin ta juya shima ta ƙara galla masa harara, duk yana kallonta amma bai ko saurareta ba ballantana ya tanka mata. Hakan kuwa ya ƙara ƙular da ita ta fizgi hannun Fadwan da ƙarfi tana faɗin "Muje in rakaki ki tafi ƴar albarka ta..." Ta faɗa lokaci ɗaya tare da ɗauke kai tana wani harare harare.


Shi dai Abba ko kaɗan bai sake tanka musu ba yayi gum da bakinsa har suka ƙaraso inda yake tsaye, suna ƙarasowa gabansa Fadwa ta ɗan zame hannunta ta rusuna a gabansa tana faɗin "Abba na tafi sai anjima..."


Ɗan dubanta yayi a hankali yana kaɗa kai, kafin yace "Toh madalla Allah yayi albarka ki gaida gidan dashi AbdulAzeez ɗin..." Yana gama faɗin haka kawai yasa kai ya wucesu ya nufi ɗakinsa.


A zafafe Maman ta ƙara fizgar hannunta tana faɗin "Dalla muje ni in rakaki ki wuce ki tafi inda zai fissheki, kin tsaya sanabe da iyayi..." Ta faɗa tare da janta da sauri suka fice daga gidan.


















*Ya Allah ka gafartawa mahaifina da sauran Musulmi baki ɗaya🤲*
[12/23, 10:17 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI*




*Wattpad: Aishaalto09*








1️⃣3️⃣






Har zauren gidan nasu Maman ta rakota suka tsaya ta miƙa mata jakarta ta ƙarba ta buɗe ta zaro kuɗi ƴan ɗari biyar biyar sababbi fil guda goma ta miƙa mata, da sauri tasa hannu ta karɓe lokaci ɗaya tana washe baki take faɗin "Allah yayi miki albarka ɗiyar ƙwarai, shiyasa akoda yaushe nake ƙara alfahari dake ke ɗin ta musamman ce. Dama kamar kin sani ɗan jarin ƙuli ƙulin da kayan miyan nawa duk mun taru mun cinye nida ƙannenki da mahaifinki, jarin ya karye ɓagas saboda wani lokacin a ciki muke zarar wani abu muke yin cefane mu samu mu ci abinci dan ni ban ga amfanin facin da mahaifinki yake yi ba, wani lokacin fa sai a fi wata da watanni bai shigowa da ko asi gidan nan amma koda yaushe yana kan hanya yana gararanba a tsohon mashin zuwa bakin titi sai kace wani abun azo a gani yake tsinanawa kansa da iyalinsa, wallahi abun bala'in bata min rai yake, kinga yanzu dai wannan ƙulin da nake curawa nan da zuwa anjima ina soyawa zaki ga har an siye ya ƙare amma ƙarshenta sai kiga ban tsira da ko sisi ba na kwashe kuɗin duk mun yi cefane saboda rufawa kai asiri amm...."


Fadwa tai saurin tarar numfashinta da faɗin "To ai rufin asirin kenan dama Mama, yanzu da baki yin sana'ar ai da ba'a san kuma wane irin hali zaku shiga ba, amma a hakan ma ai sai a ƙara godewa Allah ko...?" Take faɗa cikin takaici da jin haushin irin maganganun da Maman ke faɗi akan mahaifinta. Tasan mahaifiyarta farin sani shegen kwaɗayi gareta da rashin godiyar Ubangiji ga bala'in son abun duniya, shi kuwa mahaifinta tuni tayi masa kyakkyawan sani shi mutum ne wanda ke da tsantseni da WADATAR ZUCCI kuma baya taɓa hangen abun hannun wani, amma ita sam ba ta san ya kamata ba shiyasa wani lokacin take jin haushin abinda take yi.


Ƙaramin tsaki Fadwan taja kana ta juya lokaci ɗaya tana ƙoƙarin fita daga zauren take faɗin "Ni zan wuce ki gaidasu Ilham da Amatullah idan sun dawo..." Tana gama faɗin haka kawai tasa kai ta fice daga zauren ba tare data tsaya sauraren addu'ar da Maman ke mata na fatan sauka lafiya ba ta wuce abun ta.




Maman kuwa ko a jikinta ta juya itama ta koma cikin gidan tana mita da faɗin "Ai sai kiyi kuma, baƙin rai kuwa sai ki ta yi kin daɗe baki yi ba zaki gaji ne wata rana..haba ina dalili yarinya sam bakya so a faɗi laifin ubanki. Ke kenan indai ana so a ga ɓacin ranki to a ambaci ubanki yayi ba dai-dai ba kuma ya yin sai kawai aƙi faɗi saboda jin tsoro, ai kuwa kin daɗe sai dai kije kiyi ta ƙuncinki da nunƙufurcinki dan ni dai kam sai na faɗa kuma koda a gabanki ne..Atoh....."
Take faɗa cikin masifa da jin haushin yadda suka rabu da Fadwan, dan ita so tai suyi magana tai mata kwatancen gidansu Lubna dan jibi ta cakare ta tafi biki, amma daga maganar gaskiya ta bi ta murtuke fuska tana ta faɗin maganganu har da su tsaki.


Tana cikin masifar Abbansu Fadwan ya fito daga cikin ɗakinsa riƙe da buta a hannunsa zai yi alwala ya kalleta ya ɗauke kai bai ce mata komai ba ya wuce ta gabanta ya shige banɗaki abunsa.


Sai da ta kallesa ta watsar kafin ta bi bayansa da wani banzan kallo ta ɗauke kai lokaci ɗaya tana jan tsaki ta kwanto haɓar zaninta ta ƙulle kuɗin da Fadwa ta bata kana ta jawo kujera ta zauna ta ci gaba da curin ƙuli ƙulinta hankali kwance.


Haka koda ya fito ma bai kalli inda take ba ya matsa can gefe guda ya tsugunna ya ɗaura

11 / 38