Author : Nimcyluv Zeey Kumurya Category : A Books
hana Aure." Wani mugun kallo khamal ya wurga mata sannan ya miƙe ya bar parlour'n. Jijjiga kai ta yi tare da miƙewa ta fice ita ma.
Ɗakin Abra ta je, tarar da ita ta yi ta kifa kanta akan gado tana kuka. A hankali ta ɗago da ita ta rungume ta. Cikin sigar rarrashi ta ce. "Ki yi shiru haka kar kanki ya yi ciwo, ki bar ni da Abbi na san ta inda zan ɓullo masa." Cikin kuka Abra ta ce. "Mami na haƙura tunda Abbi ba ya so, bana son in ga yana fushi da Ni." Da sauri Na'ima ta ce. "A'a Daughter, tunda kina son shi yaron zan yi duk yanda zan yi na ga kin Aure shi, kar ma ki ƙara tunanin za ku rabo, ko ba kya son shi ne?"
"Ina son shi."
"To kuma, abun da nake so dake kawai guda ɗaya ne, ki daina mayar da hankali akan karatunki."
Cikin mamaki Abra ta ce. "Ban gane ba Mami."
Zama ta yi a gefenta ta ce. "Yawwa, abun da nake nufi ki daina karatu, idan an ba ku assignment ki daina yi, ba dai saboda karatun ya ce ba zai aurar da ke ba?" Gyaɗa mata kai Abra ta yi.
"To idan ya ga an kafe result duk kin faɗi dole ya aurar da ke ai."
Shiru Abra ta yi tana nazarin abun da Mami ta ce, anya kuwa za ta iya? Idan ta yi hakan fa tamkar ta watsa wa Abbinta ƙasa a ido ne, wani b'arin na zuciyarta kuma hango mata yake rabuwar su da Adnan, gaskiya ba za ta so su rabu ba, kawai za ta bi shawarar Mami. Cikin rashin wayo ta ce. "Za mu yi text gobe, kar na yi karatun ta kenan Mami?"
"Kar ki yi, idan kin je class an yi muku attendance kar ki kuma yi, ko assignment aka ba ku ki daina yi kin ji yarinyar kirki?" Shiru Abra ta yi tana tunani, ganin kamar ba ta gamsu ba ya sa Na'ima ta gyara zama ta shiga kalailame ta da nuna mata illar rabuwar ta Adnan, har ta samu ta amince da shawarar tata ta daina yin karatu, cikin murmushin mugunta ta rungume ta ajikinta tare da saka mata albarka. Abra har cikin ranta ta yarda da abubuwan da Mami ta faɗa mata, soyayyar Adnan da ta yiwa zuciyarta mugun kamu gami da tsoron rabuwa da shi su suka taimaka gurin ƙara assasa amincewa da hakan, ta manta Abbinta mutum ne mai magana ɗaya gami da kafiya akan abun da ya ce, ko da ba ta mayar da hankali akan karatun ba idan bai so ba, ba zai aurar da ita ba.
Bayan Magriba Na'ima na zaune a parlour suna waya da Ammi tana sanar mata halin da ake ciki. Bayan ta gama Ammi ta ce. "Wacce irin magana ce wannan? Me Babana yake nufi da aikata wannan ɗanyen aikin da yake ƙoƙarin yi? Idan ba a aurar da yarinyar ba saka ta za mu yi a gaba mu dinga kallon ta? Ai aure shi ne mutuncin kowacce mace, kowa na addu'a Allah ya kawo wa yarsa miji na gari shi kuma ya samu zai ce a'a, to bai zai yiyu ba, zan zo har gidan in same shi in nusar da shi illar abun da yake ƙoƙarin aikatawa? Bokon me? da za a ce saboda ita za a jinkirta aure, komai fa lokaci ne da shi, ban da abun Babana ai wannan abin farinciki, addu'a kawai ya kamata ya yi tare da bincike akan yaron da ahalinsa dan tabbatar da nagartar shi."
Cikin jin daɗi Na'ima ta ce. "Abun da na yi ta faɗa masa kenan Ammi, amma ya ƙi ji ya yi biris da ni, kuma wallahi Ammi ba ki ga yaron ba nutsatstse ga hankali, daga gani ɗan gidan manyan mutane ne wanda suka san darajar kansu. Gashi ita ma Abran tana son shi sosai, dan baki ga yanda take kuka ba da Khamal ya ƙi amincewa."
Salman da ya fito dan zuwa kitchen ya samarwa kansa abun da zai ci jin yunwa na ƙoƙarin hallaka shi kalaman Mami suka doki dodon kunnansa. Cak ya tsaya cikin wani irin yanayi, a razane ya ce. "What? Mami! Ammi kika sanarwa da wannan maganar?" Hararar shi Na'ima ta yi ta cigaba da sauraren Ammi dake sanar mata gobe da safe za ta yi sammako ta zo ta sami Khamal kafin ya tafi gurin aiki, don ta ba shi umarnin amincewa da batun neman Auren Adnan da Abra.
Dafe kai Salman ya yi cikin takaici, Mami ba ƙaramin gamawa da shi ta yi ba da ta sanar da Ammi maganar nan, saboda yanda Ammi ba ta zance kodayaushe sai na Allah ya kawo wa Abra miji ta yi aure. Amma duk da haka ba zai haƙura ba, matuƙar yana numfashi ba zai bari wani ya auri Abra ba shi ba, dan haka zai fasa ƙwai kowa ma ya san abun da yake faruwa, zai sanar da Abbi cewa yana son Abra zai aure ta a yau ba gobe ba, in ya so duk abun da zai faru sai dai ya faru![10/4, 3:15 PM] Abk: A fusace Salman ya juya kai tsaye kuma Part ɗin Abbi ya nufa, zuciyarsa babu daɗi ji ya ke tamkar zata faso ta tsakiyar ƙirjinsa ta fito, saboda tsananin bugawa da ta ke da ƙarfin gaske.
Gane nufin Salman ya sanya Mami saurin miƙewa tare da shan gabansa, fuskarta sam babu walwala a kaushashe ta ce. "Well-done, wato kana nuna mini ban isa da kai ba? kada ka manta ni na ɗauki cikin ka, nai dakonsa na tsayin watanni tara, na haife ka. Haihuwar da babu shiri, kana na raine ka, na shayar da kai nonona na tsayin shekaru biyu. Amma yau ni nake faɗa maka magana kana yi mini musu? Yarinyar da ba ni na haife ta ba, ta fika yin biyayya a gareni ko Salman"
"Mami ya ya ki ke so na yi da raina? tun da na buɗe idanu da Yaya na fara arba cikin rayuwata, ita ce komai nawa, jin daɗina, farin cikina, kwanciyar hankalina, gaba ɗaya Abra ce silar komai Mami, ko kuka nake zata sanyani dariya, bata bari na cikin damuwa, she love's me, and I love her too, we love each other Mami"
Zuciya ce ta kwashi Mami bata tsaya jiran komai ba, ta ɗauke Salman da wani irin wawan mari wanda ya sanya ya yi saurin runste idanunsa tare da safe kuncinsa, idanunsa ya yi jajur sai ajjiyar zuciya ya ke saukewa.
Da hannu ta nuna shi tana mai girgiza kai ta ce.
"You are lying, if I am alive you will never marry Abra, kai da ita sai dai hange da ga nesa, ba zaku taɓa zama abu guda ba,You want reveal the secret and make your father divorce me"
Kallon ta kawai Salman ya ke, yayin da ya ke jin ƙuncin zuciyarsa na ƙaruwa fiye dana baya.
"Mami marina ba zai hana na janye da ga kan ƙudirina ba, me yasa ki ke son a dole ki gyara kuskuren da kin riga da kin aikata?, da ace kin ajjiye cewa Abra ba ƴarki bace a zuciyar ki, baki gaya mini na, da yanzu ban furta kalma SO ba, da ban yadda sonta yayi mini illa na, balle har aje ga batun aure, da har zuwa yanzu zan cigaba da ɗaukar som da nake mata na 'yan uwanta ka, buy it's too late to cry Mami wallahi wallahi I will never stop loving her, and I wan marry her, zan faɗawa Abbi everything dake faruwa zan faɗa masa yadda nake son Angel, wataƙila shi ya fahimce ni"
"Ni kuma faɗa masa daidai yake da in tsine maka albarka!, wallahi ko da wasa ka faɗawa mahaifinka, cewa kana son Abra sai na tsine maka, kabi duniya in huta da Masifa, wannan wace irin jaraba ce? Tunda yarinyar nan ta shigo rayuwarmu komai ya lalace mini"
Sai kuma ta saka kuka tana faɗin "Yanzu Salman a duniya ko ban haifeka ba, nace kada ka aikata abu ba zaka iya yimin alfarmar hakan ba albarkacin riƙon da nayi maka?. Balle kuma ni nasan zafin haihuwar ka, akan mace zaka nuna fifiko akan mahaifiyar ka?"
Idanun Salman cike da hawaye ya ce. "shi kenan, amma duk abun da ya sameni a rayuwa Mami ke ce sila, rasa Angel daidai ya ke da rasa raina"
Yana faɗin hakan ya juya da sauri tare da barin gidan baki ɗaya, domin da zarar yaci gaba da zama komai zai iya faruwa.
Da daddare Abbi na zaune akan kujera sanye da kayan bacci, idanunsa maƙale akan system yana duba wani abu, gefe guda kuma black tea ne wanda aka matsa masa lemon akai.
Mami ce ta shigo cikin bedroom ɗin tana zabga ƙamshi cikin shirinta na kwanciya bacci, a hankali ta zauna gefen sa tana faɗin.
"Barka da dare Yallaɓai"
"Yawwa" ya amsa ba yabo ba fallasa ganin yanayin sa ya sanya ta ce "You are still angry because I told you the truth?"
"Sure"
Ya bata amsa nan ma a gajarce har yanzu kuma bai ɗaga kai ya kalleta ba, sai ma tea ɗinsa da ya ɗauka yana sha a nutse. Cikin damuwa Mami ta ce.
"Na kasa fahimta, kai na ya ɗaure" sai a lokacin ya buɗe baki cikin ko in kula ya ce "ba zaki gane ba daman, bana da tabbacin kuma zaki gane"
"Idan baka bari Abra tayi aure ba, kai ne zaka aureta?" Da shock Abbi ya ke kallon Hajiya Na'ima, jin anun da ta faɗa, sai kuma ya saki Murmushi cikin nutsuwa ya furta.
"Ina tunanin babu haramun a hakan, dani dake kin san ba ƴar cikina bace, so anything can happen as you said"
"Me kake nufi? I can't hear you correctly me kake son faɗa mini?" Juyawa ya yi gaba ɗaya zuwa inda take idanunsa cikin nata kafin ya numfasa ya ce.
"Ina nufin ba zanwa Abra aure a wannan situation ɗin ba, sai ta gama schoo'l ta zama ƴar jarida. Idan da hali ta haɗa komai nata na karatu, ban damu da adadin shekarun da zata ɗauka ba, cikakken ilimi nake son bata wanda za tayi alfahari da shi, sannan innzaɓa mata nagartaccen miji, wannan shine gatan da zan yiwa Abra, wanda zai amfaneta ko bayan raina, don Allah kada ki sake zuwar mini da maganar wani aure i don't like it. Bana jin kuma akwai wanda zai sauya min tunani kada na sake jin labarin kuma wani ya zo ƙofar gidan nan da niyyar zance wajan Abra Khamal Khamis. Idan har kin ɗaukeni matsayin miji"
Yana faɗin hakan ya miƙe tsaye tare da ɗauke system da tea ɗinsa ya nufi cikin library gidan domin samun peace of mind.
Mami kasa motsawa ta yi me hakan ke nufi? Kada fa dace ta jawa kanta, garin neman gira a rasa idanu. Kamar mahaukaciya haka ta miƙe ta nufi part ɗinta.
Washe gari bayan sallar Subhi Abra na zaune tana azkar kamar yadda ta saba, lokacin ƙarfe 6:10 wayarta ce ta ɗauki vibration alamar notification ya shigo. Hannunta har rawa yake wajan buɗewa musamman da idanunta ya sauka akan number _Unknown_ mutumin da a koda yaushe take jin tsananin faɗuwar gaba idan ta riski saƙonsa, rashin ganin saƙon kuma ya kan jefata tunanin a wane hali yake ciki.
Fararen idanunta dake cike da bacci ta lumshe a hankali kuma ta buɗe su, tare da sauke ganinta saman screen ɗin wayar.
Message ne rututu daga na _I love You_ sai na _I miss You_ tare da jaddada kalmar _LOVE_
Saƙon farko ta buɗe a hankali ta fara karantawa kamar haka.
_Your love splashes on my mind, I cannot do without thinking of the moments that concern us both. You are my laughter, joy, and peace. Anytime I can find you beside me, it means I am deprive of these virtues. I know I am not that strong enough to come see you right now, but I have you in my heart beating in a speed of light._
Idanunta ne ya cicciko da hawaye, a fili ta furta "Who are you? Mene yasa kake ɓoyewa? Maybe Adnan Aliyu Matawalle ne? Anya mutumin da kai tsaye ya bayyana mini abun da ke ransa, mai zasa ya dinga yi mini wasa da hankali?" saƙo na biyu ta duba mai ɗauke da faɗin.
_Kiyi haƙuri da rayuwa a duk sanda ta zo maki, ina ji a Zuciyata ke ta musamman ce, ke abar alfahari ce, burina ki ai jirani soona or later zan bayyana a gareki Abra, ban san ya zan kwatanta maki yadda matsayinki yake a zuciyata ba, zan baki misali da wanda aka ce yau ya wayi gari zuciyar sa ta daina aiki. You're a darling. Anna Uhibbukiiii_
Jikinta na rawa ta duba buɗe saƙo na ukun mai ɗauke da crying na Emoji da kuma heart, sai double kiss sama da ashirin tare da sticker ta hug.
"Ba'a wasa da kalmar soyayya, don Allah ka bayyana a gareni kada ka sanya zuciyata ta buga" cikin sauri take typing ɗin tana gamawa ta danna _Send_ ya tafi sai kuma ta yi shiru tana tunani, mai yasa ta damu da wannan unkown ɗin bayan ga Adnan ɗinta?.
Babu jimawa ya yi mata reply da _Just pray_ kasa reply tayi tunani duk ya addabi zuciyarta.
Shiru tayi ta shiga kogin tunani, yau tana da test, gashi Mami ta hanata karatu.
' Mami ki kewa karatun? Kin san ambition ɗin da mahaifin ki yake da shi akan ki? Kin kyuta masa ke nan?' wata zuciyar ta gargaɗeta
ita kanta ta san ba daidai bane, dole ta san abun da ta ke, ba zata taɓa yarda ta ɓatawa Abbi rai akan soyayyarta da Adnan ba. This is not fair.
Sai Yamma suka dawo da ga makaranta, duk tsayin lokacin da sukai a school tsakaninta da Salman Idanu, sai ya zauna ya yi ta Kallonta ko kuma da sun haɗa idanu ya lumshe nasa idanun,ya zama wani so silent duk surutun nan nasa babu, ko littafi ya ɗauka zai karatu sai ya tafi tunani.
Ammi ce zaune a Parlourn dake part ɗin Abbi, bata samu zuwa ba sai yamma, yayin da Abbi ke zaune ƙasan carpet kansa a ƙasa yana sauraren abun da take faɗa masa. A sanyaye ya ce.
"Ammi ban hana Abra aure ba, ban kuma ce ba zata ba, abun da ka sani shi ne sai ta kammala makaranta zan aurar da ita, nasan yarinyata zatai mini biyayya ba zata taɓa watsa min ƙasa a idanu ba"
"Ni kuma a matsayina, na uwa a gareka wacce ta kawo ka duniya nace dole a Aurar da Abra, kuma ka bayar da dama ga wanda ya ke son nata ya turo magabata ai magana, ka faɗa mini inda aka ce karatu ne gaba da aure? banda Aƙidar banza da wofi ma mene wani karatu, wallahi akan maganar nan sai na saɓa maka"
Kamar Abbi zai kuka haka ya buɗe baki da ƙyar ya ce. "Shi kenan Ammi, zan yi bincike akan yaron sai na bashi dama, kiyi haƙuri na janye kalamai na"
Murmushi ta yi ta ce "Ma sha Allah, Ubangiji ya yi maka albarka dakai da zuri'ar ka, Allah ya sanyawa auren albarka"
"Amin" ya ce yana Miƙewa tsaye tare da barin parlourn zuciyarsa babu daɗi sam.
Salman dake bakin ƙofa yana jin duk abinda ake faɗa, jikinsa na rawa ya buɗe ƙofar zai shiga Mami tayi saurin kama hannunsa tare da jansa zuwa part ɗinsa. Idanunta cikin nasa ta ce.
"Da kyau, Ammin zaka je ka faɗawa kana son Abra kana son aurenta ko? To jeka ban hanaka ba, amma kasan abinda zuwan naka ke nufi"
Tana faɗin hakan ta fice daga ɗakin tare da banko masa ƙofa, Salman ji yayi wani zazzaɓi na neman kama shi ga wani ciwon kai dake neman tarwatsa masa ƙwaƙwalwarsa.
Sama da marwa kawai yake a cikin haɗaɗɗan bedroom ɗin nasa, tunanin mafita yake amma ya gagara samu gaba ɗaya. "What should I do? Ko na faɗawa Granny nasan she most do something" zubewa ya yi a kan gadon, ya na dafe kansa.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, Hasbunallahu! Ubangiji ka kawo mafita" shiru ya yi yana tunani a fili ya sake ce wa "If na gayawa mayen na Abra gasky tare da faɗa masa ina son ta, nine kuma zan aureta fa?" Girgiza kai ya yi yana sauke numfashi ya ce.
"Mami zata tsine min, she's my mother ban son hakan ya kasance" ganin ya rasa mafita ya ɗauki wayarsa tare da ƙorawa photon Abra kallo, Murmushin da ke shimfiɗe akan fuskar ta shi kaɗai ya isa ya sanya ya samu nutsuwa.
Kwanciya ya yi yana ƙanƙame wayarsa a ƙirjinsa kamar da wasa kuma zazzaɓi ya rufesa tare da ciwon kai mai zafi.
Mami na fita ta kira Anty Suwaiba a waya cikin damuwa ta ce "Ni yaron nan ke son tonawa asiri Anuty Suwaiba?. Babbar matsalar da ya faɗi komai Uban sa sakina zai yi, bana son hakan ta kasance gaba ɗaya na rasa yadda, al'amarin na son fin ƙarfina"
Anuty Suwaiba ta cikin wayar ta saki dariya sai da tayi mai isarta kafin ta ce "akwai shawara, ki bawa mahaifin nasa shawara a kan ya fitar da shi ƙasar waje karatu tun da Abra aure za tai, kuma kina da tabbacin ba zai mai da hankali ya yi karatun da ake buƙatar ya yi ba, idan ya so yana can sai ayi mata Auren idan ya dawo dai duk jarabarsa ta zama matar wani"
Jinjina kai Mami ta yi cike da gamsuwa kafin ta ce "shawara mai kyau, ban yi tunanin hakan ba shi ya sa nake son kawo maki damuwata thank you Anty" tattaunawa suka sakeyi a kan lamarin.
Washe gari da safe bayan Abbi ya yi breakfast, Hajiya Na'ima ta je masa da maganar ta inda ya shiga bata ban yake fita ba, kamar ya ari baki saboda masifa.
"Ban san me kike nufi dani ba, ban san kuma abinda ya ke kan ki ba Na'ima, karatun Salman kuma yanzu ki ke son lalatawa, shirme da haukan na ki har akan ɗan da kika haifa na gaji na gaji" fuuuu! Ya yi waje rai ɓace.
Cikin tashin hankali Mami ta kira Anty Suwaiba "wallahi ba zai yarda ba Anty yanzu yaya zan yi? Ya fara ɗaukar zafi, dama a ƙule yake dani na haɗa shi da mahaifiyarsa"