Author : Nimcyluv Zeey Kumurya Category : A Books
nemi wata 'yar ka aura, amma ba 'yar uwar Abra ba".
Mama ta ce "Dan Allah Yallaɓai ka sassautawa yaron nan, kalli yadda ya koma" Abba ya ɗaga mata hannu ya ce "Wannan yaron ba abin tausayi bane, kuma na gama Magana, kuma idan har ka takura sai sun baka yarinyar nan, zan tona maka Asirin irin riƙon da ka yiwa 'yar su" haka Adnan ya dinga kuka wiwi, kamar wanda uwarsa ta mutu.
"Ok Zuwa next week nake son Visa don Allah, abu ne na gaggawa ya taso mini, da yake buƙatar in je da kaina"
Hajiya Saudat ta zubawa doctor ido, tana saurarensa, sai da ya gama wayar sannan ta kalleshi ta ce "Wai ni don Allah doctor, sai yaushe zaka bawa iyayen yaron nan damar zuwa su ganka ne?"
"Sai na dawo daga tafiya"
"Ni ban ma tambayeka ba, ina zaka je naji kana maganar visa?".
Doctor ya gyara zamansa ya ce "Dubai zanje" hantar cikinta ce ta kaɗa, ta dube shi a firgice ta ce "Kaje Dubai kayi me?"
"Wurin wanda na ajiye zani, ai kin fi kowa sanin ina da ajiya a can".
"Me kake nufi? Me kake nema a can da babu a nan?".
Bulama ya ce "Abu mafi mahimmanci da kika sa na wofantar, dole in gano alaƙata da yarinyar da nake bincike a kai, dan haka dole in tafi Dubai"
Gaba daya ta rikice ta ce "Amma ka san zuwanka Dubai na nufin tonuwar Asirinka wataƙila ma da karayar arzikinka?"
"Ban damu ba, ida har abin da na rasa ne zai dawo gareni"
Wayar Hajiya Saudat ce ta fara ringing, jiki na rawa ganin lambar Meenal ce ta ɗaga.
"Muna magana da mahaifiyar Meenal ne?".
"Eh nice"
"Ku zo nan Asibitin Health well, yarinyarki babu lafiya, ana buƙatar sa hannunku ku zo ku biya kuɗ ayi mata aikin gaggawa"
₦300 kacal, a biya kan a karanta dan Allah 08081012143
[11/17, 2:50 PM] Abk: A kiɗime Hajiya Saudat ta ce. "Wacce Meenal ɗin? Ban gane ba bawan Allah, me ya samu ƴata?"
"Idan kika zo za ki fahimta, amma fa ana buƙatar ku yi gaggawar zuwan, saboda gudun kar a rasa rayuwar ta."
Suɓucewa wayar ta yi daga hannunta ta faɗi ƙasa, cikin gigita ta ce. "Doctor wai Daughter ce babu lafiya, tana health well ana buƙatar mu je mu saka hannu za a yi mata aiki." Babu yabo ba fallasa ya ce. "Allah ya ba ta lafiya."
"Haba Doctor, ya na ga kamar ba ka damu ba, ƴarmu fa Meenal nake magana a kai."
"Damuwar da nake ciki ta fi ƙarfin wannan, ki ɗauki ATM ɗina ki je a yi duk abin da ya dace."
Bai jira amsar ta ba ya fice daga ɗakin, zuciyarsa cike da tunanin wanne abu ne yake damun Meenal da har ya kai sai an yi mata aiki ba tare da sun sani ba? Da kallo Hajiya Saudat ta bi shi cikin bugawar zuciya, mamaki da fargaba sun cika mata fal a cikin ranta, yau Bulama ne take masa maganar Meenal tana cikin mawuyacin hali na ciwo amma ya kaɗa ƙafarsa ya yi gaba? Shi da ko ciwon kai take kusan tare suke jinyar saboda yadda yake nuna damuwarsa tare da ba ta kulawa. Lallai dole ta miƙe ta nemi mafita gami da kawar da abin da ya ɗauke masa hankali daga gare su.
Cikin matuƙar tashin hankali ta zari gyalenta da handbag da wayarta dake yashe a ƙasa ta yi waje zuwa asibitin da aka ce mata Meenal tana can.
Ɗakin Abra Abbi ya sa Salima ta gyara wa Afrah, bayan ta gama ta dawo parlour inda duk suke ta ce. "Our new daughter na kammala miki gyaran dakin, sai ki shiga ki kwanta ki huta." Murmushi Afra dake riƙe da Little ta yi, ba tare da ta ɗago kanta ba ta ce. "Na gode sosai Aunty." Cikin son cusa kai Salima ta ce. "Haba mene abun godiya don Uwa ta yi wa ƴarta abu?" Murmushi kawai Afra ta yi ba ta ce komai ba, sai shafa fuskar little take cikin ƙaunar ta da ta mamaye zuciyarta lokaci ɗaya, farinciki mara iyaka take ji a cikin ranta, yau ta ga jininta a duniya, Allah Sarki Baba, dama yana nan ya ga wannan ranar mai cike da tarin farinciki a gare su. Mami kuwa taɓe baki ta yi jin abin da Salima ta faɗa, Abbi kuwa murmurshi ya yi cikin jin daɗi ya ce. "Daughter, tashi ki je Antinki ta nuna miki ɗakinki." Cikin girmamawa ta ce. "Toh." Salman dake ta kallon ta ya miƙe tare da ɗauke little daga cinyarta, cikin murmurshi ya ce mu je na raka ki yayata." Da sauri ta kalle shi cikin mamakin jin ƙato da shi ya ce mata Yaya, shi ma kallon ta yake, hakan ya sa idanuwansu suka sarƙe cikin na juna, da sauri ta janye nata saboda wani irin abu da ta ji ya daki zuciyarta, bayan ya kai ta ɗakin yana ƙoƙarin fita ta ce. "Ka bar mini ita a nan." Fahimtar da ya yi little take nufi ya sa ya ce. "Kina buƙatar ki yi wanka a yanzu, ita kuma rigima ne da ita, kina ajiye ta za ta iya farkawa tay ta kuka, idan kin yin wankan sai Mami ta kawo miki ita." Gyaɗa masa kai ta yi ba tare da ta bari sun haɗa ido ba har ya fice, haka kawai ta ji suna mata kwarjini shi da Abbi, shi ya sa ta nutsu kamar ba ita ce Ƴar Baba gagarau ba. Bin ɗakin ta shiga yi da kallo, ƙawatuwar shi da yadda ya tsaru ba ƙaramin burge ta ya yi ba, sai tambayar kanta take yi wai wannan haɗaɗɗen ɗakin duk nata ne? Yau ita ce za ta kwana a birni gidan ƴan gayu mai kyau irin wannan, ba don halin kewar su Inna da take ba da sai ta raba dare tana tsallen murna a kan wannan luntsumemen gadon.
"Allah Sarki Innata, na san yanzu suna can suna kuka da alhinin tafiyata ita da Yaya Musana." Ta faɗi haka a fili ƙwalla na cika mata ido. A hankali ta zauna a bakin gado tana ƙara bin ɗakin da kallo, Adnan ne ya faɗo mata a rai, turo baki ta yi kamar yana gabanta, lokacin da ta tuno yadda yake yi mata magiya akan ta so shi.
Salima ce ta shigo ɗakin bakinta ɗauke da sallama, bayan ta amsa mata ta ajiye wata leda mai ɗauke da kayan bacci a kusa da Afra tare da faɗin. "Ga kayan bacci nan idan kika yi wankan sai ki saka." A hankali Afra ta ce. "Toh na gode, amma na taho da kayana ma suna cikin Mota ba a shigo da su ba ne."
"Okay, bara zan yiwa Honey magana sai a shigo miki da su yanzu, ki saki jikinki kin ji, nan ma gidanku ne, bari na kawo miki abinci.'
Gyaɗa mata kai ta yi ta ce. "Ina zan ɗebo ruwan da zan yi wanka da alwala?" Murmushi Salima ta yi ta ce. "Duk akwai a cikin toilet, mu je na raka ki, ki gani." Miƙewa ta yi ba tare da ta ce komai ba, duk wannan kanbanbar da Salima take ba ta wani yi mata ba, sai ta ji ta fi son farar matar nan mai kama da Salman. A toilet ɗin ma lalacewa ta yi wajen kallon yadda aka ƙawata shi, kasa ɗaurewa ta yi ta ce. "Yanzu nan ne bayin gida kamar wani ɗaki? Taɓ, ai da ni kaɗai na shigo fita zan yi na ce ban ga bayan gidan ba, na saba da namu na ƙauye ko rufi babu balle siminti." Murmushi Salima ta yi ta nunnuna mata duk abin da ta san zai mata wahalar ganewa da yadda za ta yi amfani da shi. Bayan ta fita ta ce. "Wai aljannar duniya, har da wani fanfon ruwan zafi? To shi daga ina yake zuwa kuma? Ko ta cikin ƙasa ake dafa shi?"
"Khamal wai me kake nufi da ni a gidan nan ne? Ina cikin damuwar rashin Abra amma mai kama da ita ta zo sai kaita tura waccan matar tana yi mata abubuwa? Alhalin gani a zaune."
"Na sani ko ita ma za ki ce ƴata ce karuwa ta haifa mini? Ki azabtar da ita kamar yadda kika yi wa Abra."
Cikin hawaye Mami ta ce. "Me ya sa kake son dawo da abin da ya wuce ne? Ai babu wanda ba ya yin kuskure a rayuwarsa." Wani kallo ya watsa mata ya fice ba tare da ya kuma magana ba. A zuciye Mami ta ce. "Kuma yarinya a gurina za ta zauna ba a gurin wata baƙar yarinya ba, sai dai a yi duk abin da za a yi. Ban da neman fitina yarinyar kusan sa'ar ta amma ita za ta riƙe ta, ita ma shegiyar da neman gindin zama har da wani ce mata ƴarta, ko a gidan uwar wa ta haifi kamar ta oho?" Ta ƙarashe maganar tare da jan tsaki.
"Doctor me yake damun ƴata da har ya kai a yi mata surgery without knowing us?" Hajiya Saudat ta tambaya a gigice.
"Mu ƙarasa office mana sai mu yi maganar."
"Ba ni da nutsuwar ƙara taku ko nan da can? Please tell me what happened to my daughter?" Ta yi maganar cikin kuka.
Cikin tausawa likitan ya ce. "Ki dai daure mu ƙarasa office ɗin, kin ga nan reception ne, bai dace mu yi magana ba."
Ba ta kuma magana ba ta bi shi suka tafi. Bayan sun shiga sun zauna ya ce mata. "An yi mata abortion ne, sai kuma aka samu matsala ta samu raptured utherus, mahaifarta ta ragargaje gabaɗaya, yanzu za a yi mata aikin gaggawa a cire t....."
"Innalillahiwa'inna'ilaihirrajj'un, na shiga uku! Meenal ɗin za a cirewa mahaifa? Mahaifa fa ka ce Doctor?"
"Eh, ta sha maganin abortion ne wanda ya wuce ƙa'ida, hakan ne ya janyo mata wannan matsalar, ba don da wata Nurse da take aiki a nan asibitin suka zo ba ma da ba za mu karɓe ta ba."
Gumi ne ya shiga yankowa Hajiya Saudat ta ko'ina a jikinta, cikin rawar murya ta ce. "Doctor, kuma babu wani abu da za a iya yi dole sai dai a cire mahaifar?"
"Babu." Ya faɗa a taƙaice.
A dole ba bisa son rai ba Hajiya Saudat ta saka hannu aka yi wa Meenal aiki, wadda ke cikin mawuyacin halin ciwo.
Ba ƙaramin tashi hankalin Hajiya Saudat ya yi ba da ta ga Meenal, Saboda yadda ta ɗashe ta yi fari fat alamun babu jini a jikinta, ga wata rama da ta yi kamar wadda ta daɗe tana jinya, tsabar galabaita ko magana ba ta iya yi, sai hawaye kawai take.
Washegari bayan Salima ta gama haɗa breakfast ta shiga ɗakin Afra don ta taso ta. Tarar da ita ta yi har lokacin tana kwance tana bacci, saboda jiya ba ta yi bacci da wuri ba, kewar Inna da baƙunta sun hana ta. A hankali ta tashe ta, bayan ta shiga toilet ta fice ta ɗauko mata sabuwar abaya da undies a cikin kayan lefenta, ta haɗo da su lotion da powder ta kawo mata. Cikin mintuna ƙalilan Afra ta shirya, kasancewar ta mai kazar-kazar ba kamar Abra ba. Sosai ta yi kyau cikin bak'ar abayar da ta haska farar fatarta. Kallon kanta ta tsaya yi a mirror cikin murmurshi, gani take ba kamar ba ita ba saboda kyawun da ta ga ta yi. Sai da Salima ta ƙara dawowa ta kira ta sannan suka fita tare.
Abbi na zaune a dinning suka shiga parlour'n, ɗagowa ya yi yana kallon su tare da amsa sallamar, cikin girmamawa Afra ta tsugunna ta ce. "Ina kwana?"
"Lafiya ƙalau, ya kwanan baƙunta?" Ya amsa cikin fara'a.
"Alhamdulillah." Ta faɗa cikin sanyin muryar da ta ara daga jiya, don sosai ta ji jikinta ya yi mata wani irin sanyi ba tare da ta san dalili ba.
"Ƙaraso mu karya." Cewar Salima tana nufar dinning area.
"Bari na fara gaishe da Mami idan ta tashi."
Cikin jin haushin abin da ta faɗa Salima ta ce. "Ai ko da ƙyar in ta tashi."
"Ta tashi, mu je na raka ki." Abbi ya faɗa cikin jin daɗin yadda ta nuna girmamawa ga Mami.
Da kallo Salima ta bi su zuciyarta cike da baƙin ciki, ta gama yi wa yarinya hidima sannan tana fitowa ta ce wani za ta gaishe da Mami? Lallai dole ta tashi tsaye don ganin ta ja Afra jikinta sosai, ta san hakan zai ƙara ninka ƙaunar da Abbi yake mata.
Mami tana shirya little suka shigo ɗakin, da fara'a ta ɗago tana duban Afra, Abbi kuwa juyawa ya yi ya koma parlour.
"Daughter har kin tashi?"
Gyaɗa mata kai ta yi tare da gaishe ta, rungume ta Nai'ma ta yi hawaye na cika mata ido saboda tuno Abra da ta yi, don ganin Afra cikin abaya ba ƙaramin ƙara kamar su da Abra ya yi ba, kasancewar ta ma'abociyar saka ta.
"Lafiya ƙalau daughter, dafatan kin tashi lafiya?"
"Lafiya ƙalau." Ta amsa tare da ɗaukar little, kamar wadda aka faɗawa yarinyar sai ba ta yi mata ƙiwa ba, sai ma dariya da ta shiga bangala mata. Socks Mami ta ɗauko ta fara saka mata tare da faɗin. "Lallai yarinyar nan, wato ke ba kya yi wa iyayenki ƙiwa ko? Da wani ne ya ɗauke ta da tuni kin cika ɗakin nan da kuka da ciccilla ƙafafuwa." Murmushi Afra ta yi tare da shafa sumar kan little, tana jin duk duniya babu abin da take so sama da yarinyar. Tare da suka koma parlour da Mami, lokacin har Salima da Abbi sun fara karyawa. Cikin son gwaninta Salima ta miƙe ta yi serving ɗinsu, don a gaban Abbi biyayya da girmamawa take yi wa Nai'ma. Ciki-ciki Mami ta ce. "Thanks." Abbi bai ji daɗin hakan ba, amma ya danne saboda Afra dake gurin bai nuna ba, fahimtar hakan ya sa Salima sakin murmushi cikin jin daɗi, dama abin da take so kenan a kodayaushe, Abbi ya dinga ganin lefin Mami a zamantakewar su.
Tsurawa kayan breakfast ɗin ido Afra ta yi, a kallon farko da ta yi masa ta ji yawunta ya tsinke, ga ƙamshinsa da ya cika mata hanci, tun kafin ta ci ta san ba ƙaramin daɗi zai yi ba. Inna da Yaya Musa ne suka faɗo mata a rai, ji ta yi dama a ce tare da su za su kwashi wannan daɗin, ga masoyin nata bread ƙatoto a gurin. A hankali ta ɗauki cup ɗin da Salima ta haɗa mata tea ta yi Bismillah ta fara sha, daidai lokacin Salman ya shigo parlour'n. Gabansa ne ya yanke ya faɗi ganin Afra, don gani ya yi tamkar Abra ce zaune a gurin, hakan ya tuno masa lokuta da dama da suke yin breakfast exactly like this da Abra. Addu'a ya yi mata sannan ya ƙarasa dinning area ɗin cikin sanyin jiki. Bayan ya gaishe da su Abbi ya ɗauki little dake bacci sannan ya zauna. Kamar yadda Salima ta yiwa kowa haka ta tashi ta yi serving ɗin shi. Ba yabo ba fallasa ya yi mata godiya. A hankali Afra ta ɗaga kyawawan idanunta ta kalle shi tare da sakar masa murmushi, mayar da mata murmushin ya yi tare da yin ƙasa da murya ya ce mata. "Morning Angel, da fatan kin tashi lafiya?"
"Lafiya ƙalau"
Mami dake lura da su ta yi gyaran murya, hakan ya sa Salman haɗiye abin da yake son faɗa, sanin da ya yi ƙa'idar Abbi ne idan ana cin abinci ba a magana idan ba dole ba, gyaran muryar da Mami ta yi kuma ya san tuna masa hakan take. Bayan kowa ya gama cin abincin Abbi ya dubi Afra ya ce. "Yata a ina kika tsaya da karatu ne?"
"Na yi Candy."
Gyaɗa ya yi ya ce. "Da kyau, islamiyya fa?"
"Muna izifi Ashirin."
"Masha Allah, yanzu kina da takardun WAEC da NECO?"
"Eh, na taho da ita ma, Inna ta haɗo mini a cikin kayana, amma NECO kawai na yi."
"Okay." Abbi ya faɗa tare da mayar da duban shi ga Salman ya ce. "Idan Allah ya kai mu gobe Monday ka je ka yi mata registration a school ɗin English Academy, saboda ta samu bakinta ya faɗa a Turanci kafin ta shiga University, idan an fara registration na JAMB sai a yi mata, Islamiyya ma ka kai ta wadda kuka yi ta cigaba da karatun a can."
"Insha Allahu Abbi."
Cikin matuƙar farinciki Afra ta ce. "Na gode sosai Abbi, Allah ya ƙara girma da arziƙi."
"Amin Daughter, babu komai. Yanzu sai ka kai ta, ta gaishe da su Ammi, idan kun dawo sai ku je tare da Auntinku ku yi mata shopping na kayan sawa da sauran abubuwan amfani." Ya ƙarashe maganar idanunsa a kan Salman.
Godiya sosai Afra ta yi masa har da hawayenta, ta so a ce Baba yana raye ya ga wannan ranar, don ba shi da buri da ya wuce na ganin ta yi karatu mai zurfi na addini da na boko, karamcin da Abbi ya nuna mata a yanzu ya ƙara tabbatar mata da an yi wa ƴar'uwarta riƙon mutunci a gidan, hakan ya ƙara kwantar mata da hankali akan zamanta a gidan.
Daren jiya Adnan bai samu ishashshen bacci ba saboda damuwar dake cunkushe a cikin ransa gami da fargabar rasa Afra. Raba dare ya yi yana kallon hotunan Abra cikin zubar hawaye tare da surutai, ta tafi ta bar shi cikin tsananin kewa da ƙaunar ta, ya samu wacce yake ganin za ta ɗebe masa kewar ta amma ita ma yana ƙoƙarin rasa ta. Sai bayan Sallar Asuba wani wahalallen bacci ya ɗauke shi, bai farka ba sai da goma ta wuce, ko sakkowa bai yi daga kan gadon ba ya lalubi wayarsa ya kira Mami, bayan sun gaisa ya ɓukaci ta ba wa Afra saboda muryar ta kawai yake son ji ko zai samu nutsuwa a cikin zuciyarsa, lokacin su kuma sun tafi gidan Ammi, cikin rashin jin daɗi ya yiwa Mami sallama, a ransa yana ƙudirce dole gobe ya yi wa Kano dirar mikiya.
Littafin kuɗi ne, don neman ƙarin bayani: 09047871750
[11/20, 7:09 AM] Abk: Washegari kamar yadda Adnan ya sanya a ransa haka ne ya kasance. Tun asuba ya shirya cikin wata shadda shampoo maroon colour ya murza hula duk da bata dame shi sosai ba, amma ganin weather ya sanya