Chapter 49 Reading Dare da Duhu Book Complete By Nimcyluv. Zeey Kumurya.txt Arewa Novels

Dare da Duhu Book Complete By Nimcyluv. Zeey Kumurya.txt

Author :  Nimcyluv Zeey Kumurya Category :  A Books

Chapter   49 / 78

144K to 147K   out of 231.7K words

mayar da ni ne? Na umarce ki ki mini abu, amma kin koma gado me kike nufi?".
"Abin da idanunka suka gane maka, shi nake nufi" a sukwane ya yo kan gadon yana cigaba da bala'i "Ke kin isa babanki ya wulaƙantani, kema kice zaki mini rashin mutunci? Wato kin gado halin dabbanci irin na babanki".
"Adnan! Kar ka sake zagin ubana,uba fa bai fi uba ba".
"Kina nufin nima zagina za kiyi kenan?" Yayi Maganar yana nuna kansa da yatsa.
"Allah ya tsare ni in zageka, ni mahaifinka uba na ɗauke shi, uba na gari makuwa, abin tausayi Allah ya bashi azzalumin ɗa mai fuska biyu".

Taku ɗaya yayi, ya fizgota daga kan gadon, zai wanka mata mari, amma yaji jikinta zafi rauu, kamar an kunna wuta, hankaɗata yayi ta faɗa ƙasa ya nuna ta da yatsansa ya ce "Ko ki ɗau ubana uba, koma me kike ɗauke shi, abin da na sani shi ne, ubana yafi ubanki imani da mutunci, kuma na dawo na tarar da kayan nan baki wanke ba, sai na tattaka ki".
Binsa ta yi da ido har ya fice.
Girgiza kai kawai tayi, dan Yanzu zuciyarta ta fara bushewa da lamarin Adnan, dan haka a nan kan tiles ta gyara kwanciyarta, ta yi shiru abubuwa daban-daban na kai komo a kwanyarta.




Hannu ya sa cikin sumarsa ya yamutsa ta, ya rintse idanunsa, a tunaninsa zuwan da yayi ya ga Abra, zai rage masa raɗaɗin da yake cikin zuciyarsa, da samun sassauci akan halin da yake ciki, duk da ya san hakan bai kyautu ba, kasancewar ita matar wani ce a yanzu, kuma ga alƙawarin da yayi, na ba zai sake zuwa Nigeria ba, amma ya kasa daurewa sai da yaje, amma zuwan nasa bai amfana masa Komai ba sai sake jefa shi cikin tarin damuwa da tambayoyi.
Abra tana auren wanda take so amma ta furta masa kalmar so, yayi shiru tare da tuna yadda Adnan ya mari Abra saboda kishi, da yadda ya kira shi da loser "No! Am not a loser" ya faɗa yana dukan kan mirror.

"Abra zata dawo gareni, amma ta yaya how? Wa zai bani goyon baya?"

Can kuma sai wata zuciyar ta gargaɗe shi 'Ina imaninka da iliminka na Addini, duk wani abu da zakai yinƙurin aikatawa, don mallakarta alhalin tana matar wani ya saɓawa Shari'a'

Rintse idanunsa yayi, tare da taune lips ɗinsa na ƙasa, da ya tuna yanzu Yaya ta san wacece ita, ta san matsayinta. Ko wani hali ta shiga lokacin da ta sani? Amma ya a kai ma ta sani, sam wannan bahagon mijin nata, ya hana shi ya samu ya sake da ita su yi hira. A hankali ya taka zuwa baki gado ya zauna, ya sunkuyar da kansa yana tunani.


Abbi ya rasa ta ina ya kamata ya fara binciken iyayen Abra, sai yanzu ya gane cewar yayi kuskure, tsananin son Abra da tausayin ta lokacin da ya tsince ta, ya rufe masa idanu, ya kasa tsayawa yayi bincike a kan su waye iyayen Abra, ba tare da tunanin akwai rana kamar irin ta yau da zata zo ba, wanda dole Abra zata buƙaci sanin haƙiƙanin suwaye iyayenta.
A hankali ya sauke ajiyar zuciya, ya fara laluben wayarsa, sai dai yana dubawa ya ga missed calls ciki har da na su Ammi.
Cikin hanzari ya shiga ƙoƙarin bin kiran Ammin. Ammi na ɗagawa cikin girmamawa suka gaisa. "Babana ina ka shiga ne haka? Ake ta kiranka baka ɗagawa?"

Major ya ce "Afuwan Ammi, wayarce a silent".

Ammi ta ce "Shikenan, kana gari ne?"

"A'a Ammi, ina wurin aiki".

"To duk abin da kake da ka shigo gari ka zo?".

"Lafiya kuwa Ammi?"

"Idan ka zo ka ji"

"Shikenan dama shari'ar nan ce ta sanya na taho wurin aiki, amma tunda an kammala insha Allah zan biyo jirgin dare in taho".

"To shikenan, Allah ya kawo ka lafiya"

Ya amsa da "Ameen"

Kamar yadda Abbi ya faɗa, a daren ya dawo gida, washegari da wuri ya shirya ya nufi gida, Mintuna kaɗan suka kai Abbi gidansu.
Tun da ya ga Baffa a gidan a daidai wannan lokacin kuma da alama duk shi suke jira, ya sha jinin jikinsa.
Ya gaishesu cikin girmamawa, sannan ya ɗora da Ammi "Gani, Allah yasa lafiya naji kin ce kuna nemana?"

Baffa ya ce "Au tambaya ka ke ko lafiya? Kai ba abin kunya ne ba abin da ka aikata Kamal, da ƙuruciyarka ba ka saki matarka ba sai yanzu, kuma ace ba wanda ka kira ka gayawa wannan maganar? Sai su daga can gidan nasu ne aka kiramu aka sanar mana, me ka aikata kenana Khama? Wane laifi zata aikata maka a yanzu, wanda ba kayi haƙuri a baya ba, da har za ta kai ku ga saki, bayan har 'ya kun kai ɗaki".

"Baffa dan Allah kuyi haƙuri, amma abin da Na'ima tayi mini bani da zaɓin da ya wuce aikata hakan".

"Ka kyauta ai, sai ka tashi mu tafi can gidan nasu, mu zauna mu tattauna, a gano bakin zaren".

Major ya ce "Baffa, zamu iya tattauna komai a nan, in gaya muku duk abin da ya faru".

"Ba shawarar ka muke nema ba, tashi koma menene muje can a tattauna" ba yadda Major ya iya, haka ya tashi suka tafi gidansu Na'ima.

Bacci ne mai nauyin gaske ya ɗauke Abra, sanyin tiles ɗin nan da ke ratsa ta ya sanya zazzaɓi ya ƙara rufeta sosai da sosai.

Sai can azahar sannan ta farka daga nannauyan baccin da ya ɗauketa, har wani duhu take gani, saboda wata irin yunwa da take ji, ga jikinta babu daɗi. Ta kalli gurin da kayan Adnan suke a zube, kallon kayan kawai da tayi ta ji cikinta ya sake yamutsawa, zuciyarta ta fara tashi.
Tsaki tayi ta ɗau kayan, tana toshe hanci, ga jiri na ɗibar ta ta tafi ɗakinsa, tana zuwa ta shiga toilet ɗinsa, ta zuba kayan a bucket ta fice.
Ta nufi kitchen ta shiga buɗe buɗen kwanuka, ba abinda ta girka balle ta ci.
Bredi ta tarar a kan dining, wanda Adnan ya karya ya fita, ta zauna ta dinga ci kamar mayunwaciya, sai da ta ci ta ƙoshi sosai, ta koma fridge ta ɗauko lemo mai sanyi ta sha sai da ta ji babu gurin zubawa komai sannan ta haƙura.

A haka ta ɗora ruwa dan tayi wanka ta ɗora girkin rana, ta ɗan fara gyara gidan, duk da gidan ba wani datti yayi ba, tana yi tana kwanciya saboda gaba ɗaya jikinta babu daɗi. Cikinta ne ya fara juyawa kamar ɗazu da safe, nan ta dinga kwara amai, sai da ta amayar da duk abin da ta ci, ta dawo falo ta kwanta gaba ɗaya ta galabaita.
Tun tana jin aman ta tashi ta tafi banɗaki, har ta koma toilet ta zauna gaba ɗaya, kan kace kwabo, Abra ta fita hayyacinta. Da ƙyar ta iya lallaɓawa ta yi wanka, shima ba sabulu iya ruwa ta watsa, ta dawo tai salla a zaune, ta kwanta. Amma amai bai tsaya ba dan ba ta fasa yinsa ba.



"Kai muke saurara, kayi wa mutane bayani ya aka yi ka aikata wannan ɗanyen aikin, bamu sani ba laifin me tayi maka?".

Major yayi ajiyar zuciya ya ce "Tun da na auri Na'ima, muka yi auren soyayya muke zane lafiya da ni da ita, har zuwa lokacin da na tsinci Abra, wanda tun daga wannan lokacin ta dinga bijiro mini da wasu irin halaye akan yarinyar, tana iƙrarin ni na haifi yarinyar da karuwa a waje, kuma ba zata riƙe ta ba. Idan ban manta ba a wancan lokacin na yi mata wani furuci na cewa, idan har ta bari wani yasan ba ni na haifi Abra ba daga gareta a bakin Aurenta. Sai ta dinga nuna mini bakomai, a gabana ta kula da Abra a bayan idona ta cutar da ita, wanda na daɗe da fukantar hakan amma nayi shiru na ƙyle. Ashe matar nan ta riga ta sanar da ɗanta cewar bamu muka haifi Abra ba, ina wurin aiki, na samu wayar mijin Abra ya haɗani da ita, yarinyar tana kuka ta sanar mini da cewa wai ashe bamu muka haifeta ba? Wanda na san ba mai gayamata sai Na'ima, kuma na dawo gida na tarar da wasiƙar da Salman ya bari a kan cewar ba zai sake dawowa Nigeria ba, ashe ya san Abra ba 'yar uwassa bace, ya fara sonta kuma ta sani duk ta munafunce ni, Wallahi Ammi bakiga a mawuyacin halin da na baro Abra ba, dan haka taje tayi rayuwarta nima in yi tawa, zan tabattar da samun farincikin yarana".

Na'ima ta fashe da kuka tana faɗin "Wallahi ni ban gaya mata ba"

Ammi ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, yanzu kana nufin Abra ta san ba kai ka haifeta ba?".

"Ta sani Ammi, ba kiga a yadda na baro ta ba, cikin matsanancin tashin hankali da damuwa, yanzu irin tsananin soyayya da shaƙuwar da ke tsakaninta da Salman da wani abu da ba a so ya shiga tsakaninsu fa a dalilin sanin su ba 'yan uwa bane? Duk bata kalli wannan ba amma ta sanar musu, ba yadda ban da Abra ba a kan ta gaya mini wanda ya gaya mata amma taƙi, wanda nasan dama ba zata gaya mini ba, saboda ba ta san ace ga laifin Na'ima dan ita uwa ta ɗauketa".

"Wallahi ni bani na gaya mata". Ta sake Maganar cikin raunin murya.

Baffa ya ce "Kuskure ne dai an riga an yi shi, amma kayi haƙuri ka maida yarinyar nan ɗakinta, ba shawara ba ce umarni ne".

Abbi yayi jimm, yayin da ƙanin mahaifin Na'ima shima haƙurin yake bayarwa.

Khamal ya ce "Shikenan, batun ɗan ta da ta sa na tura China kuma, sai taje ta nemo shi da kanta, dan dama ita tace a kai shi can, tun da yace ba zai dawo ba shikenan, dama mugunta ai fitsarin faƙo ce".

Ammi ta ce "A'a ai duk ba za'ai haka ba, haƙurin dai shi zaka yi" aka haɗu akai ta bawa Abbi haƙuri, ya amince Mami ta koma ɗakinta.

SP Adnan a gajiye ya dawo gida, saboda wani ƙauye suka je aiki, ya sha zirga-zirga, salla kawai yayi, ya duba fridge ya samu sauran juice da Abra take haɗawa ya sha.
Bai nemi wurin da Abra take ba, ya shige ɗakinsa ya faɗa toilet dan yayi wanka, amma ya ga kayansa a cikin bokiti a banɗaki.
Jinjina kai yayi da jinjina yadda Abra ta koyi taurin kai, wankansa yayi da niyyar ya kammala ya ci Abinci, ya ci ƙaniyar Abra.
Sai dai bai ƙara tsinkewa da lamarin Abra ba, sai da ya duba ya ga ba tayi girki ba, ya duba kitchen ma bakomai.
  A fusace ya nufi ɗakinta, yana zuwa ya tarar da ita a duƙunƙune cikin hijjabi tana ta bacci. Ƙafarsa ya sa yana takata ta tashi, amma ko motsi ba ta yi ba, baccinta kawai take.
Yasa hannu ya ɗagota yayi wurgi da ita, zafin buguwar da ta yi ne ya sanya ta farka cikin wani irin razani. Adnan ta gani a gabanta yana wani irin zazzare idanu.
"Dame kike taƙama har kike mini wannan iskancin a gida? Baki girki da safe ba, na bar miki wanki ba kiyi ba, dan kin mai da ni ɗan isaka, shine kika kai kayan banɗakina kika watsar, kuma still ba ki girki ba, me kike nufi?" Ikon Allah kawai take kallo, yadda yake ta zazzaga bala'i, babu alamar ma zai bata damar kare kanta.
Sai da yayi ya gama ba tace uffan ba, ta miƙe a hankali ta fara ƙoƙarin gyara zaman towel ɗin jikinta.
"Am i not talking to you Abra?" Ya sake tambayarta cikin tsawa.

Hannayenta biyu ta sanya ta toshe kunnuwanta, dan ji take kamar a cikin kanta yake wannan ihun. Ganin ta toshe kunne ya sanya ya kuma harzuƙa, ya sauketa mata wani wawan mari a kan hannunta da toshe kunnen, wani irin zafi ya ratsata ta shiga zubar da hawaye, amma taƙi ce masa uffan, hannunsa ya sanya ya shaƙeta yadda ba zai mata illa ba ya ce "idan har kika cigaba da ƙoƙarin bijirewa umarnina a cikin gidan nan, Wallahi wahala zaki sha a gidan nan, sai kin gwammace kiɗa da karatu". Ai yana tsaka da maganar ta kyalayo masa amai a jikinsa, kallon Abra yayi cikin tsananin baƙin ciki ya hankaɗeta ta faɗi ƙasa, ta cigaba kakarin amai, sai dai babu komai a cikinta.
Ya kalli hannunsa da jikinsa da ta ɓata amai, cikin takaici ya ce "Ƙazamar banza mara hankali" Ko ɗaga kaia ba tayi ba balle ta tanka masa, ya ƙare mata zagi ya fice.

Gefe ta koma ta kwanta tana haki, saboda yadda ilahirin jikinta ke ciwo, tunani ta shiga yi a ranta, anya ba zata gudu ba, ko ta sanarwa Abbi irin halin da take ciki ba, sai kuma tayi tunanin dole Abbi zai shiga damuwa ya ga daga aurar da ita, har an fara samun matsala dan ta san tabbas sai ya kashe Auren nan. Tayi tunanin ko ta gayawa Abbi Adnan ya san waye mahaifinta, sai kuma taga idan har ta gayawa Abbi, to lallai fa zai gane irin zaman da take da Adnan, wanda hakan ne bata so, ba zata so ace daga yin Auren ace har Auren nata ya mutu ba, a fara lissafa mata Aure.

"Ohhh Allah, Allah ka bani mafita. Faris come back to me, i need your help, kar wannan macucin ya kashe ni, bana son ɗagawa Abbi hankali, da saina kashe Auren nan" ta ƙarasa Maganar tana jin zafi a ƙirjinta.

Na'ima Allah ya taimaketa ta koma gidanta, sai dai sam Major Khamal yaƙi bata fuska, ƙarewa idan ya fice tun sassafe ba zai dawo ba, sai can dare, ta shirya ta tafi sashinsa da nufin bashi haƙuri kamar yadda ta saba idan sun samu saɓani, amma ya koreta ya ce ta fita ta bashi guri.
Gaba ɗaya zaman gidan sai yayi mata babu daɗi, ta san da yaran nan suna nan ko dan Albarkacin su kar su gane Akwai abin da yake faruwa zai haƙura, amma Yanzu da yake ba kowa sai ita kaɗai yaƙi saurarar ta, dan da alamu yayi fushi sosai da ita a wannan karon.
Babban abin da ya sake jefata cikin damuwa shi ne yadda ya ce sai dai taje China ta nemo Salman, dan ba abin da yayi masa zafi da cewar da Salman yayi ba zai sake dawowa Nigeria ba. Gashi yanzu ta hankalta ta dawo daga rakiyar shawarwarin Anty Suwaiba dan ba in da shawarwarin na ta ke kai ta sai tashar Nadama!.

Abra baiwar Allah, kwana biyun nan haka tayi su cikin tsananin ciwo, zazzafan zazzaɓi da amai ba ƙaƙƙautawa, ga bata iya cin komai, dan komai ta ci sai tayi amansa, Adnan kuwa ya daina ko zuwa in da take, idan ma ya zo sai dai ya tsaya daga bakin ƙofa ya zazzage mata masifa ya barta.
Da safe ya shiga ɗakinta, ya tarar ta fito daga wanka, tana zaune a bakin gado, duk ta zabge ta rame sai idanuwa, so take ta shafa mai a jikinta amma ta kasa, hawaye ne kawai ke fita daga idanunta, kanta kamar zai tsage, dan bayan zazzaɓi har da damuwa ke damunta, saboda haryanzu zuciyarta na ƙuna akan rashin sanin haƙiƙanin suwaye iyayenta, ga Adnan ya sani amma azabar muguntarsa ya sanya ya ce na zai bari ta haɗu da su ba, kuma ko ta sanar da Abbi cewar Adnan yasan in da iyayenta suke, Adnan zai iya ƙaryatawa, dan ba ƙaramin makiri bane.

"Ke! Nifa na gaji da wannan halin naki, ba zai yiwu na ajiye ki a gida, amma kullum sai na nemi abin da zanci ba, saboda baki da lafiya dole ki mini Abincin breakfast yau na gaji".

Ɗauke kanta tayi, ta juya masa ƙeya, mai ɗauke da uban gashinta baƙi siɗik da ya sauka a kan gadon bayanta.

"Ina miki magana kike juyowa mini wannan banzan gashin naki?".

"Me kuma gashi na yayi maka, ko da yake ba abin mamaki bane, maybe burgeka yayi".

"Meye abin birgewa a jikin duk wani abu da ya danganci zuriyarku, masu kyan ɗan maciji, miyagu azzalumai, ai duk wani abinda ya shafi mahaifinki muninsa ya ƙazanta".

Cikin ƙarfin hali ta ce "Ai da yake gwano ba ya jin warin jikinsa, kai meye marabarka da miyagun maganganun da kake suffanta mahaifina da su? Wataƙila ma gara shi, baya neman matan banza, kai kuwa fa har karuwa ka kawo cikin gidanka dan abin kunya da.....
Damƙe gashin kanta yayi, wanda azaba ya sanya tayi shiru, saboda tsananin zafi da ciwon da kan yake mata. Cikin tsantsar mugunta da rashin imani, ya cire towel ɗin jikin Abra, ya fara ƙoƙarin kwanciya da ita, duk da yadda yake jin wani irin hucin zafi da jikinta yake mata saboda ciwo.
Kuka take sosai tana ƙoƙarin ƙwatar kansa, tare da kai masa duka, amma jikinta babu ƙwari, yayi abin da ransa yake so, cikin zallar mugunta tana kuka tana wani irin kakari na wahala, amma ko a jikinsa, sai da ya gama ya kalleta yana wani shu'umin murmushi ya ce "Idan nace zan gwada miki irin mugunta da zaluncin da mahaifinki yake yi, to mutuwa zaki yi, dan ba zaki rayu ba, zaluncinsa ya wuce duk wani tunani naki, ki sa a ranki ni ban iya komai ba a kan mahaifinki"
Ido shine kaɗai abin da Abra ta iya raka Adnan da shi, ba ta san da ya zata misalta irin uƙubar da yake mata ba. 'Haka zaki zauna abubuwa na cigaba da kwaɓewa?' wata zuciyar ta tambayeta.
Tana jinsa ya tada motarsa ya bar gidan, ta kai awa biyu a kwance, ko ƙwaƙwaran motsi ta kasa, daga bisani ta tashi da ƙyar ta shiga banɗaki ta gyara jikinta ta sanya kaya, ta duba tana da kuɗin da aka babbata lokacin da za'a kawota, ta zuba a jakarta ta nufi gate ta fice, wanda tun da aka kawota bata taɓa fita ita kaɗai ba.

LITTAFIN KUƊI NE, KU SIYA KAFIN KU KARANTA.
0808102134
09047871750
[10/25, 4:54 PM] Abk: Tana tafe a hanya kamar za ta kifa, unguwar kamar quaters take, ita ko maƙotanta ba ta sani ba, dan Adnan bai bata damar ko sallama tayi musu ba da aka kawo ta, da ƙyar ta kai titi, dan ta huta babu adadi.


Duk wasu shedu da yakamata, an tattara su a kan General Ibrahim mai retire,ya tabatta shine ya kashe karuwarsa a Hotel, kuma shike maƙarƙashi na bayyanar da sirrin tsaron ƙasa, dan haka yau Litinin

49 / 78