Author : Nimcyluv Zeey Kumurya Category : A Books
Adnan ɗin da ya ci burin ganin wannan ranar da za ta kasance a gidansa, amma me ya yasa ya yi mata haka? Me yasa tana yi masa magana ya share ta? Ko dai something bad happened to him? Tunanin hakan ya sa ta matsawa kusa da shi da niyyar ta ji abun da yake damun shi. Wata uwar harara da ya ɗago kai ya banka mata yasa ta tsayawa cak a inda take cikin bugawar zuciya. "Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un." Abun da ta ambata a fili kenan. Rasa abun yi ta yi hakan ya sa ta koma ɗakinta cikin sauri, faɗawa kan gado ta yi tare da sauke wani wahalallen numfashi. So take ta tuno ko ta yi wa Adnan wani lefin amma ta kasa, hakan ya sa ta fashewa da kuka. Sai da ta yi mai isarta sannan ta tashi ta shiga toilet ta wanke fuskarta. Bayan ta fito ta tsaya a gaban mudubi tana kallon kanta, cikin ƙoƙarin son gano ko wani abun Adnan ya gani a jikinta da bai masa ba, amma ba ta ga komai ba. Duk da ita ba ma'abociyar son kwalliya ba ce amma haka ta zage ta tsantsara ta tare da kafa ɗaurin ɗankwali mai kyau, ita kanta ta san ta yi kyau, duk da yanda take jin wata irin fargaba a cikin zuciyarta amma sai ta murmusa, ta san dole kwalliyar tata ta burge Adnan. Daddaɗar humra mai daɗin ƙamshi ta shafe jikinta da ita, sannan ta fita zuwa ɗakin Adnan. Sai da ta fara shiga kitchen ta haɗa masa breakfast wanda aka ajiye dan shi sannan ta nufi ɗakin nasa. A zaune ta tarar da shi a kan gado yana operating system. Cikin sanyin jikinta ta yi masa sallama, ko d'agowa bai yi ba balle ya amsa mata. Hakan ya ƙara tsinkar mata da gaba, zuwa yanzu kam ta gane da akwai matsala. Kanta a ƙasa ta ce. "Ga abinci." Nan ma bai kula ta ba, kawai sai ta fashe da kuka cikin rashin sanin abun yi. Ta daɗe a duƙurshe tana kuka mai tsuma zuciya, yana jin ta amma ko tari bai yi ba, ƙarshe ma tashi ya yi ya ɗauki car key ya fice ya bar mata gidan. Hasbunallahu..... kawai Abra take maimaitawa, a ranta tana tambayar kanta me yake shirin faruwa da ita ne? Me Adnan yake nufi da ita? Jiki a saɓule ta miƙe ta koma ɗakinta ta kwanta akan gado ta cigaba da kukanta, kewar Faris da Abbi da Mami na nuƙurƙusar zuciyarta, wani azababben ciwon kai ne ya far mata lokaci ɗaya, cikin dauriya ta janyo bargo ta lulluɓe jikinta, saboda yanda take jin wani sanyi na ratsa gaɓoɓin jikinta, tamkar wadda za ta yi zazzaɓi, a haka wani wahalallen bacci ya ɗauke ta.
Sai Azhar ta farka, shi ma ƙarar doorbell ya tashe ta, cikin sauri ta miƙe ta shiga toilet ta wanke fuskarta da ruwa sannan ta fito ta saka hijabi ta fita. Mata ne kusan su takwas ta gani, cikin fara'a ta tarɓe su tare da yi musu iso. Bayan sun zauna sun gaisa ta kawo musu drinks da kayan garar ta, anan suke gabatar mata da kansu. Dukkansu cousins ɗin Adnan, Ƴanmata shida sai matan aure biyu. Ta ji daɗin zuwansu ba kaɗan ba, dan ba ƙaramin ɗebe mata kewa suka yi ba. Sai dai duk bayan sakanni idan ta tuna Adnan da yanayin da ya nuna mata ɗazu sai gabanta ya faɗi. Da abinci suka zo, hakan ya sa ba ta yi girki ba shi suka ci, ita ɗan caccakalar abincin ta yi kaɗan ta ci ba don daɗi ba. Sai kusan Magriba suka tafi suna ta tsokanar ta wai kar Ango ya dawo ya same su ya yi musu korar kare, ita dai murmurshin yaƙe kawai take, sai ta ji dama kar su tafi.
Ba ta zauna ba sai da ta tsaftace gidan ta saka turaren wuta a burner, hakan ya sa gidan gabaɗaya ya karaɗe da ƙamshi. Bayan ta yi Sallah ta yi wanka ta shirya cikin wani tsadadden yadi mai kyau maroon color, ya yi mata sosai ya haska farar fatarta. Parlour ta fita ta jera abinci akan dinning sannan ta koma ta yi Sallar Isha'i da aka fara kira. Tana idarwa ta janyo wayarta dan ta kira Abbi amma ta tarar wayar a kashe, ta manta tun jiya wayar babu chaji ta mutu. Chajin ta jona ta zauna jiran ya ɗan yi, Salman ne ya faɗo mata a rai. A fili ta ce. "Kana ina My Faris? Me kake yi yanzu? Me ya sa ba ka kira ni ba tunda ka tafi? Yaushe zaka dawo ka zo gidana in gan ka ɗan ƙanina? Na yi tsananin kewar ka." Daga haka ta fashe da kuka.
Khamal na zaune a parlour'nsa shi da Na'ima wadda zuciyarta ke cike da tsananin farinciki, jin ta take kamar a mafarki yau Allah ya yi Abra ta bar mata gida, shikenan fargabarta ta ƙare. Sai dai tuno letter Salman da ta gani ya sa gabanta fad'uwa da ƙarfi, ta rasa me ya sa abun ya dame ta? Dan da farko shirme ta ɗauki abun, saboda sanin komai daren daɗewa dole Salman ya neme su, ba kuma zai taɓa iya yin zuciya da su ba, letter da ya yi mata dan yana cikin ɓacin rai ne, abun yana cin shi a lokacin shi ya sa, amma ta san idan tafiya ta yi tafiya komai zai wuce. Khamal yana duban ta ya ce. "Komai lokaci ne, kamar ba yau ake zancen bikin Daughter ba, ga shi har an yi an gama, ta tafi ta bar mu da kewar ta. Cikin kissa Na'ima ta ce. "Ta bar mu da kewa kam, don gidan babu daɗi yanzu ko kaɗan, ga ba Salman." Khamal ya nisa ya ce. "Har kin tuna mini kuwa, na kai sati ina trying his number ba ta shiga, amma na kira mutumin da ya kira ni da numbern shi lokacin da ya sauka a garin, ya ce mini neighbours suke, idan sun haɗu zai kira ni ya haɗa mu." Murmushi Na'ima ta yi ta ce. "Allah Sarki yaron kirki, Allah ya tsare mana shi." Khamal ya amsa da Amin tare da zaro wayarsa daga aljihu ya kira layin Abra amma sai aka ce masa a kashe, tun rana yake kira ta ba ta shiga. Numbern Adnan ya kira, dan ya san duk sabon ango i yanzu yana gida. Bayan ya ɗaga suka gaisa cikin mutuntawa, Khamal ya tambayi Abra, Adnan ya tabbatar masa tana nan ƙalau, wayarta kuma babu caji ne shi ya sa bai same ta. Khamal ya buƙaci Adnan ya ba wa Abra wayar, sai ya ce ya ɗan fita, idan ya koma gidan zai haɗa su, daga haka suka yi sallama.
Tana zaune takure a bakin gado ta yi tsumu cikin alamun tsoro, ita kaɗai a gida har tara ta yi amma babu Adnan babu labarin shi. Ƙwaƙwalwarta har ta gaji da tunanin dalilin da ya sa Adnan yake yi mata haka, kanta kamar zai tsage saboda ciwo. Unexpected ta ji an buɗo ƙofar ɗakin an shigo, lumshe ido ta yi cikin jin daɗi dalilin shaƙar ƙamshinsa, a hankali ta buɗe idonta ta kalle shi, yanda ta ga ya murtuke fuska ne ya sa gabanta mummunar faɗuwa, amma duk da haka ta daure cikin raunin murya ta ce. "Sannu da zuwa." Ta ƙarashe maganar hawayen da take ƙoƙarin ɓoyewa suna zubo wa. Bai kula ta ba, wayarta dake chaji kawai ya ɗauka ya fice. Da ido ta bi shi cikin kokawa da numfashinta dake barazanar ɗaukewa. Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un ta shiga maimaitawa hannunta dafe da kanta, wani irin raɗaɗi da zafi take ji a cikin zuciyarta. Tambayar kanta ta shiga yi, dama haka Auren yake? Ko kuma ita kaɗai ta fara da matsala? Ina tarin ƙauna da soyayyar da Adnan yake yi mata? Ina tanadin kulawa da tattalin da ya ce ya mata? Ko dai mafarki take yi? Ta rasa da wanne za ta ji, da rashin Faris a kusa da ita ko kuma da kewar su Abbi ko da abun da Adnan yake mata? Sunan Allah ta dinga ambata har ta ji sauƙin radad'in da zuciyarta ke mata. So take ta tashi ta je gurin Adnan ta ji me ta yi me masa? Amma a yanda take jin jikinta kamar ba nata ba ta san ba za ta iya tashi ba. Kwanciya ta yi saboda juyawar da kanta yake yi mata.
Wannan shi ne dare mai tsayi da muni da Abra ta gani a rayuwarta, dan bacci duk iya satarsa bai sace ta ba. Nasihar Ammi da ta ce ta dinga tashi cikin dare tana yin Sallah ko raka'a biyu ce ta dawo cikin kwanyarta, hakan ya sa ta lallaɓa ta tashi ta shiga toilet ta ɗaure alwala ta raya daren, ta kai wa Ubangiji kukanta tare da roƙon ya kawo mata ɗauki. Bayan an yi Sallar Asuba ta ɗauko alƙur'ani mai girma ta karanta, bayan ta gama ta yi azkar ɗinta. Hakan ya sa ta ji sauƙin damuwar dake cunkushe a cikin ranta. Sai kusan takwas ta fita parlour bayan ta yi wanka. Gyaran gidan ta fara yi cikin matuƙar sanyin jiki, tana cikin yi Driver'n gidan Hajiya Mama ya kawo breakfast, ta karɓa ta yi masa godiya ta kai dinning ta ajiye. Tana zaune har 10 tana jiran fitowar Adnan amma shiru ko motsinsa ba ta ji ba.
Wasa-wasa yau har Magriba ba ta ɗora Adnan a idonta ba, sauƙinta yau ma ta yi baƙi har sau biyu sun ɗebe mata kewa. Sai bayan Magriba ya shigo gidan, lokacin tana zaune a parlour ta kunna kallo, a ƙoƙarinta na son ya ɗebe mata kewa, sai dai damuwar dake cikin ranta ta hana ta gane me firlm ɗin ma ya ƙunsa.
Duk yanda yunwa da ƙishirwar son ganin shi suka cika mata zuciya amma sai ta kasa ɗaga ido ta kalle shi, ƙasa ta yi kanta tana sauraren yanda zuciyarta ke bugawa. Karon farko tun bayan da aka kawo ta, ta ji muryarsa ya yi mata sallama, sai dai ba a yanda ta so jin maganar tasa ta ji ba, ba cikin soyayya da kulawa ba. Fuskarsa a murtuke tamkar aka yiwa saƙon mutuwa, cikin isa da gadara kamar an masa dole ya ce. "Je ki ɗauko hijabinki." A hankali ta ɗago ta dube shi idanunta cike da ƙwalla, kafin ta kai ga yin magana ya juya ya shige ɗakinsa. Kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki haka ta miƙe ta je ta ɗauko hijabin ta saka, tana cikin kashe kayan kallon ya fito daga ɗakinsa ya yi hanyar waje ba tare da ya kalli inda take ba. Bin bayansa ta yi cikin sanyin jiki tana sharar hawaye.
Ganin ya shiga Motor ta buɗe front seat ta shiga, wai mugun kallo ya watsa mata tare da faɗin. "Kar ki bari na ƙara ganin wani abu mai kama da hawaye a fuskarki." Ba ta ce komai ba ta share hawayen tare da lumshe idonta. Gidan Hajiya Mama suka je. Abba da Hajiya Mama sun karɓe ta cikin fara'a da soyayya, sai nan-nan suke da ita. Ita kam kanta na ƙasa kunya duk ta ishe ta, idan an yi magana sai dai kawai ta murmusa. Adnan kuwa sai shagwaɓa yake musu wai yanzu sun daina son shi Abra suke so. Abun da ya ba wa Abra mamaki yanda ya dinga yi mata magana cikin kulawa da sakin fuska a gabansu Abba, hakan ya jefa ta cikin tunanin me Adnan yake nufi da ita?
A nan suka yi dinner tare da su Abba, tun tana jin kunyar su har ta ɗan ware, saboda su babu ruwansu, musamman Abba he is so friendly, yanata jan ta da hira. Sai ta ji dama Adnan ɗinta ne haka. Hajiya Mama ta lura da yanayin Abra kamar wani abu yana damun ta, idanuwanta ma sun nuna alamun ta yi kuka. Ba ta yi tunanin komai game da hakan ba, sai ta alaƙanta hakan da kewar gida take yi da kuma rashin sabo na mu'amalar Aure. Kafin su tafi Adnan ya sanar da su zai yi tafiya zuwa Abuja akan wani muhimmin aiki da ya taso masa, za su tafi tare da Abra. Addu'a fatan isa lafiya sukai musu. Sai wajen 10 suka dawo gida. Bai ko kalle ta ba bayan ya yi parking ya buɗe Motar ya fice. Bin bayansa ta yi kallo cikin wani irin yanayi na ƙuncin zuciya. Ajiyar zuciya ta sauke tare da buɗe Motar ta fita. Tun daga lokacin ba ta ƙara saka shi a idonta ba sai washegari bayan Sallar Asuba ya shigo ɗakinta.
Time ɗin tana karatun Alkur'ani, bayan ta kai ajiye ta rufe tare da gaishe shi cikin girmamawa. Bai amsa mata ba sai bin ta da wani wulaƙantaccen kallo da ya yi. Cikin ƙaunshin murya ya ce. "Zan yi tafiya yanzu, ba na zo kuma dan in sanar miki ba ne saboda ba ki kai wannan matsayin ba a gurina, na zo in ja miki warning ne akan ko da wasa kar wani ya ji labarin ba da ke na yi tafiyar ba, idan kunne ya ji jiki ya tsira." Ya ƙarashe maganar tare da jan tsaki. Cikin kukan da ya taho mata ta ce. "Dan Allah kar ka tafi ka bar ni, ni kaɗai, wallahi tsoro nake ji."
"Abun da kike jin tsoron ya kashe shi."
Ya faɗi haka tare da juyawa da niyyar ficewa."
"Please where is my phone, ka dawo mini da ita Dan Allah." Ta faɗa cikin matsanancin kuka.
Ko juyowa bai yi ba ya yi ficewarsa abunsa.
Kifa kanta ta yi akan cinyoyinta ta shiga rera kuka mai ban tausayi. Why Adnan? Me nake yi maka da ka zaɓi mu yi irin wannan rayuwar mai cike da ƙunci da damuwa? Ya Allah ka kawo mini ɗauki akan sabon babin ƙaddarata da ya buɗe, Allah ka sassauta mini. Abun da take faɗa a ranta kenan cikin tsantsar damuwa.
Yau kwana biyar da kai Abra gidanta, wadda waɗannan kwanakin suka kasance kwanaki mafi muni da tsaho a cikin rayuwarta. Gabaɗaya ta rame ta fita daga hayyacinta, ga babu waya balle ta kira su Abbi ko ta ji sauƙi a cikin ranta, ga kewar Salman da kullum ƙara yawaita take a cikin zuciyarta. Alkur'ani shi ya zamto abokin hirar ta akodayaushe, sai kuka da kullum sai ta yi shi ba adadi.
Misalin ƙarfe goma sha biyu na rana tana kwance a parlour akan carpet, idanunta a lumshe hawaye na zirara ta ƙasansu. Tana jin yanda cikinta yake ta ƙugin yunwa amma ta kasa tashi ta samar wa kanta abin da za ta ci, ga wani azababben ciwon kai da ya aure ta, kullum da shi take kwana take tashi. Kamar a mafarki ta ji an buɗe ƙofar parlour'n an shigo, ko ba a faɗa mata ta san Adnan ne ya dawo, saboda da zai tafi ya kulle ƙofar parlour'n ta waje, ta gane hakan ne a lokuta da dama da ta yi yunk'urin fita harabar gidan ko za ta ga abun da zai ɗebe mata kewa damuwar zuciyarta ta ragu. Ko matsawa ba ta yi ba da niyyar tarɓar shi, sanin da ta yi ko ta masa magana ba amsawa zai yi ba. Sai dai jin kamar ba shi kaɗai ya shigo ba ya sa ta buɗe idonta da sauri tare da goge hawayen fuskarta ta tashi zaune. Abun da ta yi tozali da shi ne ya sa numfashinta ɗaukewa na wucen gadi. Adnan ne tare da wata mace wadda kallo ɗaya za kai mata ka gane ƴar duniya ce ta ƙarshe, duba da yanayin shigar jikinta da uban bleaching ɗin da ta ci, ga kitson attachment a kanta gami da gashin ido maƙale a saman idanunta. Wannan duk ba shi ne abun da ya fi ɗagawa Abra hankali ba, jakar matar da Adnan ya riƙo a hannunsa da kallon da yake jifan ta da shi mai nuni da tsantsar soyayya, a ƙarshe kuma ya tsugunna yana cire mata hill shoe ɗin dake ƙafarta.
Littafin kuɗi ne,biya ₦300 via 0116886423 Sulaiman Na'ima s union Bank... Idan katin waya ne zaka Turo 500 shaidar biya 09047871750 or 08081012143.[10/13, 2:20 PM] Abk: Cikin rawar murya Abra ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, you are lying Sp, ba zai taɓa yiwuwa ba".
Adnan ya ce "Ban gaya miki dan ki yarda ba, na gaya miki ne dan ki san irin zaman da zaki yi a gidana, Abra akan ki zan ɗau fansar abun da mahaifinki yayi mini, mummunan tabo mai raɗaɗi da ke cunkushe a zuciyata, ina son ya ɗanɗani abun da na ɗanɗana ya ji idan da daɗi"
Ƙirjinta ne ya dinga wani irin bugu, kamar zai tsage, da gaske Adnan yake abun da ya faɗa? Kai wannan ƙarya ce, ta yaya ma haka zata kasance ta yaya za'ace ba Abbi ne ya haifeta ba?.
Adnan na ƙoƙarin barin ɗakin, yaji timmm.
Yana waiwaya wa, ya ga Abra ta kai ƙasa, ta faɗi a sume, tunowa yayi yadda Abbi ya taɓa yi masa bayanin irin wannan ciwon da take fama da shi, taɓe baki yayi yai ficewarsa ya bar ta, ba tare da wani tausayi ko jin ƙai ba.
Karatun su Faris yayi nisa, sai dai ba shi da wata walawala, ya kasa sakewa da kowa, balle ya saba da halin da ya tsinci kansa a ciki, kullum tunanin Abra na cikin zuciyarsa, yadda take bashi kulawa da tarairayarsa, ba ta san damuwarsa ko kaɗan.
Tabbas da Mami ta bashi goyon baya,ya san Abra ba zata ƙi Aurensa ba, amma Mami tayi duk mai yiwuwa ta toshe duk wata kafa, da zata sada shi da cinmma muradinsa, a hankali kuma sai ya koma tunanin ko Abra zata haɗu da iyayenta kan ta koma ga Allah? Ya zataji a lokacin da ta san cewar ba su Abbi ne suka haifeta ba? Tun da ya san gaskiyar wannan maganar, ya san komai daɗewa ita ma Abram zata sani.
Adnan bai dawo gida ba sai azahar, a gurin aiki Usman yana ta damunsa a kan cewar zai zo gidansa cin girkin amarya, amma Adnan yace bai isa ba, ba ze kuma kowa ya kallar masa mata ba.
Ko da ya koma gida, a gurin