Author : Nimcyluv Zeey Kumurya Category : A Books
mai dashi cikin Aljihu a nutse ya ɗaga kansa sama ya fara bin parlourn da kallo kamar daga sama taji ya ce.
"Kin rame, kamar ba Angel tawa mai son girman nan ba" kwaɓe fuska tayi tare da matsawa kusa dashi ta shiga dukan ƙirjinsa tana sakin kuka tare da faɗin.
"Why did you go and leave me? Kai ne wanda nake gani naji daɗi, kai ne walwalata, farin cikina, me ne yasa zaka barni a lokacin da nake buƙatar ka? Why Why Why Faris" ta faɗa tana sakin raunataccen kuka while tana ƙara dukan ƙirjinsa da dukkan ƙarfin ta. Jajayen idanunsa ya lumshe yana jin yadda take dukansa kamar wanda yayi mata babban laifin nan, baya ita ce wacce ta bashi lasisi da damar tafiya ya barta,ita ta zaɓi waninsa ta kasa fahimtar feelings ɗinsa a gareta, ta gagara gane cewa so da ƙaunar da yake mata ba iya na ƴan uwa bane, so ne irin na masoya wanda zai kai matakin Mata da Miji.
Jin kukanta yake har ƙasan zuciyarsa, zafin da zuciyarsa ke masa a yanzu ya tabbatar yafi wanda zuciyar take mata, ji yake kamar ana ɗiga masa ruwan dalma a zuciyarsa. Ganin yadda take kukan har numfashinta ya fara sama alamar zata sume masa, cikin rashin abin yi da mafita yabi umarni da kuma ragamar zuciyarsa ya jawota jikinsa tare da yi mata masauƙi a jikinsa ya rufe ta ruf da hannayensa. Kamar tana jira tai holding nasa back sai kuka take tana ƙankamesa tare da faɗin.
"Stay with me, don't leave me again. I am happy when you are near me. Idan zaka tafi ka tafi dani kaji"
Shiru Salman ya yi mata, har lokacin yana riƙe da ita a jikinsa zuciyarsa kamar zata fito waje haka nan ya keji.
"Faris.." ta faɗa tana ɗaga kanta tare da kallon fuskarsa wacce tayi jaa sosai. "Kayi magana mana ɗan ƙanina" ta ƙare maganar tana Murmushi while hawaye na zubu mata ta rasa yadda zatai she can't believe wai Faris ne tsaye a gabanta. Hannunta ta miƙa taja dogun hancinsa tana faɗin "Say sometimes yaushe ka zo? Waya faɗa maka gidana" zameta yayi daga jikinsa ya tsaya kamar an dasa shi ya ce.
"Banji daɗin ganinki haka ba, Abra." Kanta ta sunkuyar ƙasa a karo na farko taji kamar ta faɗawa wani halin da take ciki musamman yanzu da take ganin Salman a gabanta. Amma idan ta tuna gargaɗin Adnan a gareta, sai ta ji tsoro da fargaba ya kamata, kuma tayi tuni ga Sirrin Aure tsakanin ma'aurata, sai taji duk jikinta yayi sanyi. Shiru ta yiwa Salman ba tare da ta ce komai ba.
"Is something bad happened to you? Look Angel kasa jurewa da ganinki a cikin mafarkina da nayi ne ya sanya na biyo jirgi na tawo ba tare da sanin makarantar da nake ba,kina so zuciyar Faris ɗinki ta buga ne?"
Girgiza masa kai tayi muryarta na rawa tace "Ka zauna na kawo maka ruwa, me zaka ci?" "Banzo dan naci abincin gidan mijinki ba, I'm here sbd sanin halin da kike ciki, da kuma dalilin da yasa kike addabata a cikin barcina" shiru tayi masa hawaye wani yana bin wani wata tsawa ya buga ya ce "Talk Abra, Talk" dugun numfashi taja tana ɗaga kai da sauri ya ƙaraso inda take tsaye ya kama hannunta zuwa kan kujera ya zaunar da ita.
Juyawa yayi da sauri kuma ya nufi wajan deep freezer yaje ya buɗe, ruwa mai sanyi ya ɗauka ya dawo inda take zaune, a lokacin har idanunta ya fara lumshe a gefenta ya zauna ya kama Fuskarta tare da bata ruwan, tana sha yana ɗan bubbuga bayanta tare da shafa kanta. Ajjiyar zuciya mai ƙarfi ta saki kanta ta ɗora saman cinyarsa ta ce.
"Zuciyata babu daɗi Faris, komai ya lalace duniya ta juya min baya nasan da kana kusa dani da hakan bai faru ba, bana da mafita bana da mataimaki, bana da ikon faɗin abin da yake raina, Ubangiji ne zai min maganin komai ka tayani da addu'a...," Kukan da yaci ƙarfinta ne yasa ta kasa ƙarasa abin da tai niyya. Shiru yayi mata har lokacin yana shafa kanta ganin ta fara dawowa hayyacinta ya sa ya ce.
"Kinci Abinci?" Kai ta girgiza masa ya ce "to ɗagani, kin wani haye min cinya" murmushi tayi tana faɗin.
"Wallahi bacci ma nake shirin yi, naji cinyar ta ƙara laushi"
"Ko?" Ta miƙe tsaye tana faɗin "Sure" sai a lokacin ta shiga kallonsa maroon ɗin voyel ne jikinsa mai manyan zane amma shara shara haka Voyel ɗin yake, hatta farar singlet ɗinsa ana gani ya ƙara fari tas dashi, ga ƙirjinsa daya buɗe fuskarsa ta fara cika da gemu da saje, sai jajayen laɓɓansa da suke haske. Zaka iya tunanin yayi shekaru ashirin da biyar ko da bakwai haka.
Marairaice mata fuska ya yi ya ce "Yaya" dry tai tana watsa hannunta ta ce "You have changed totally wallahi mai kake ci acan China?"
"Tunanin ki ke ƙara min lafiya" idanunta a kansa ta kasa magana yana ɗago kai suka haɗa idanu ya zaro mata idanunsa ya ce "Ki je ki kawo Abinci Angel stop looking at me haka nan, kada ki fara ganin munina tun ina kyau a idanunki"
"Zoka ta yani" Waro idanu ya yi waje ya ce "Wa? Ni Salman Khamal Khamis? Jeki kawai Yaya ina jiran ki" "haba mana Faris yaushe rabon da muyi girki tare" girgiza kai kawai yayi ya ce. "Yaya gsky ba zan iya ba"
Turo baki tayi ta juya zuwa kitchen ɗin ajjiyar zuciya ya sauke sai a lokacin hawayen da suke maƙale a idanunsa suka silalo a hankali, da sauri ya sa hannunsa ya goge tare da Miƙewa yabi bayanta.
Duk abin da take da Idanu kawai yake binta, yana nan tsaye da ƙyar ta samu ya yanka mata albasa da carrot. Babu jimawa ta kammala haɗa fried rice with chicken kabab. A plate ɗaya ta zuba ta saka 2 spoons, ya rigata tafiya a zaune ta samesa kan kujera ta ce.
"Baka gaya min ya Mamina take ba da Abbi, Ammi, Granny i so much missing them wallahi" shi dai bai ce komai ba ta ce.
"Ga abinci" "kefa?" Girgiza kai tayi ta ce "bana ci" ƙuri yayi mata da ido kafin ya ɗauki spoon yana sakkowa ƙasa, A nutse yake bata abincin tana ci harta ƙoshi . Zamewa tayi ta ɗora kanta a cinyarsa idanunta a sama shi dai bai motsa sai girgiza ƙafarsa da yake, hakan yai wa Abra daɗi domin sai ya zamana kamar rarrashinta yake bai aune ba yaji saukar numfashinta bacci ya ɗauke ta.
Tunani Salman ya fara, game da sauyin Abra amma ya kasa gane gaskiyar al'amarin, sai ya alaƙanta hakan da sabuwar rayuwar data samu kanta ciki, da kuma tafiyar da ya yi barta wannan dalilin sune suka sauyata, ya san tana son mijinta tana kuma farin ciki da aurensa. Babu wanda ya san da batun zuwansa Nigeria, domin shi kansa bai yi tunanin cewa zai iya zuwa cikin gaggawa haka ba, Khairy ce ta bashi Information na gidan Abra, kuma yaci sa'a yana da aboki a Kaduna, yana zuwa kuma bai sha Wahala wajan maigadin gidan ba, har lokacin da ya nufi ƙofar parlourn bai yi tunanin zai sanya Abra acikin ƙwayar idanunsa ba, sai gashi yana buɗe ƙofar ta sadashi yayar tasa. Numfashi ya sauke yana kallon yadda take bacci ta ƙanƙame hannunsa a ƙirjinta, zuciyarta na ɗan bugawa a hankali. "Zaki dawo gareni, zaki zama mallakina Insha Allah yaya" kwanciya ya fara tunanin gyara mata.
Yana ƙoƙarin ɗaukanta zuwa saman kejera yaji ance "Well-done Salman Khamal Khamis Well-done masoyi na ƙwarai" ko ba a faɗawa Salman ba ya san Sp Adnan Aliyu Matawalle ne. Murmushi ya yi a hankali ya ɗauki Abra ya kwantar saman Kujera yana duba yadda baccin nata ya yi nisa, hannunsa ya zuba cikin Aljihu idanunsa akan Adnan ba tare da ya ce komai ba.
Adnan daman ba barin gidan ya yi ba, domin tun safe yana nan, kuma a lokacin daya fita yabar ƙofar a buɗe ne, sbd bai tunanin zai jima, sai gashi yana zuwa cikin Garden ɗin gidan nasa har bacci ya ɗaukesa a can, wannan dalilin ne ya bawa Salman damar ganin Abra cikin sauƙin.
Adnan ya ce "Daka fahimci ka zama loser a Soyayyar Abra sai ka tattara kayanka zuwa China, saboda kada ayi aurenta akan idanunka right?"
Salman ya juya ya kalli Abra ba tare daya kalli Adnan ba ya ce. "I love her, duk wani bugun numfashina da Soyayyarta yake fita, ban san adadin son da nake mata, idan da ace nine mijin Angel a yanzu ina da tabbaci da tafi haka, fari, ƙiba, kwanciyar hankali" janye idanunsa ya yi daga kanta ya kalli Adnan ya ce.
"Loser? Haka kace ko baka da labarin sbd ina gab da rabaku aka tura ni China karatu? Baka da labarin Soyayyar da Angel ke min kwatankwacin ta bata yi maka? Ban san ina tunanin Sp Adnan Aliyu Matawalle ya tafi ba, daya kasa gane cewa ba soyayyya ƴan uwa Abra ke min soyayya ce irin ta Miji da mata"
Tafa hannu Adnan ya shiga yi kafin ya ce "Kace duk a sbd farin cikin Abra aka haɗa baki dakai wajan muna furtarta, kuka kasa faɗa mata cewa Major Khamal Khamis ba shi ne ya haifeta ba?" Dry Faris ya yi irinta Abbi sak kafin ya riƙe ƙirjinsa sosai ya ce.
"Masoyi na Gaskiya shi ne zai gujewa ɓacin ran wacce yake so, Abra matsalar ta shafa amma naji inama nine wanda aka tsinta ba ita ba, a kuma ranar dana san ba a ciki ɗaya muka fito ba, na gane cewa ina tsanin so da ƙaunar Abra, ina mata son da ko rabinsa baka yi mata, ban taɓa zama loser akan abu ba, haka ba zan fara akan soyayyar Abra ba, ka sanya a ranka tamkar ajjiya haka take a wajanka Tabbas zan dawo na amsheta a hannunka a lokacin da babu abin da ka isa ka aikata".
"The you love me Faris?"
Suka ji saukar Muryar Abra a kunnuwansu. Runste idanunsa ya yi ya kasa juyawa ya kalleta. "Mene ya sa Faris? Ashe kasan gaskiya wacece ni ka kasa faɗa min? Kana tunanin rashin faɗa min zai sanya nai farin ciki? Ina yarda da junan da mukai? Ina kariyar da kace zaka bani tana ina?" Shiru kawai ya yi mata da sauri ta ƙarasa gabansa ta ce.
"Magana nake Faris" idanunsa da sukai jajur ya buɗe tare da zuba mata su. Ya ce "kibar wannan maganar yaya"
"Me ya sa zan bari Faris? Ka faɗa min gsky Say something Salman Khamal Khamis say it" ta faɗa tana jijjiga shi idanunsa a kanta ya riƙe hannayenta ya ce.
"Sbd ina Sonki, Ina Sonki Angel, na buɗe idanu dake, na rayuwa dake, mun tashi tare da Soyayyar juna, ina jinki a Zuciyata ina kishin ki tun ban san wacece ke ba, na ɓoye miki gskyar Al'amarin sbd farin cikinki ki, ina son ki dauwama cikin farin ciki. A duk sanda kika gane cewa Abbi ba shine wanda ya haifeki ba kina iya zama wata Abrar ba wacce na sani ba, a lokacin kuma na fahimci tsanar da Mami ke maki haka ne sanadi, daga nan kuma soyayyar da nake maki ta fara juyewa zuwa so na aure. Na kasa fahimtar dake how much I loves you, how much I care for you... Kullum cikin tunanin ni ƙaninki kike, kallon yaro kike min Angel so I have no choice wanda ya sa dole naja bakina nai shiru ina kishin mutumin da kika aura".
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" shi ne abin da Abra ta faɗa, is that the reason da ya sa Faris yayi kissing nata a lokacin da zai bar ƙasar? Ta kasa fahimta. Kuka ne ya kwace mata ta ce "Me yasa ka tafi ka barni?"
"Bani da laifi, Mami ta shirya komai sbd na faɗa mata sonki nake ƙaunarki nake, gaba ɗaya plan ɗinta ne, babu wanda ya san da zuwana ƙasar nan a family Khairy ce ta bani Information inda kike zaune da komai. Bani da farin ciki Yaya ban ga alamar kina farin ciki da wanda kike aure ba?"
Abra ta kasa cewa komai domin bata san da wacce kalma zatai amfani da ita wajan faɗawa Salman cewa bata jin daɗin auren ba, kuma bata da ikon faɗa masa komai, ajjiyar zuciya ta sauke "tayaya zan farin ciki Faris? Baka tare dani rashin ka shine sanadin shigata cikin wannan halin"
Adnan dake tsaye ya dakawa Salman tsayawa ya ce "out of my house loser!" Girgiza kai Abra tai ta ce "No Salman kada ka tafi akwai abin da nake son faɗa maka"
Kauuuu!! Adnan ya ɗauke ta da mari, haushi, baƙin ciki, kishi suka taso masa lokaci guda kafin ya ce "Kina matsayin matata kike magana da wani banza ɗan iska under age? You're mad Abra!" A zafafa Abra ta ce "Salman ɗin shi ne ɗan Iska?"
"In a capital letter YES ɗan iska akwai abin da zaki ne?" Abin ka da mai haƙuri gaba ɗaya tai kansa tana ɗaga murya ta ce "Sai dai idan kai ne...."
"Nooo!!! Abra don't try he's your husband karki ƙarasa" Salman ya faɗi haka cikin tsawa kuka ta sanya ta ce "ba kaji ya ce maka ɗan iska ba? Bayan shi...," "Shut up, nace kiyi shiru and so what dan ya ce min ɗan iska? No matter what Kada ki kuskura ki aibata mijinki"
Numfashinta ne ya fara sama tana ƙoƙarin kiran sunan Salman Amma ta kasa luuu tayi zata kifa Salman ya yi kanta kafin ya ƙarasa Adnan ya kai masa duka a ciki, tare da ɗauke sa da wasu maruka ya ce.
"Useless, Wanda ba shi da rabo. Wallahi wallahi zan illataka anan wajan kai da Abra kuma har Abada, ba zaka sake ganinta ba kuma ba zata sake ganin ka ba, This is my promise ka saka ranka sai dai ku haɗu a darun Salam.."
"Zan nuna maka cewa, a rayuwa Salman baya taɓa zama loser baya neman abu ya rasa, Salman a kullum cikin samun nasara yake, ko yara nawa zaku tara,duk tsofan da zaka sanya tayi duk lalacewa da tayi ka ɗauka ita ɗin ajjiya ce a gareka, zan dawo na ɗauke ta... Abra is my life just wait for me" yana faɗin haka yai waje kai tsaye kuma airport ɗin kaduna ya nufa yaci Sa'a akwai jirgi babu jimawa jirgin ya keta hazo a karo na biyu zuciyoyi biyun suka sake rabuwa.
Paid book.... Contact to subscribe if you need 08119237616
[10/21, 1:06 PM] Abk: "Faris! Faris! Faris!" Shi ne kawai abin da take maimaitawa cikin fitar hayyaci. Adnan dake tsaye yana huci cikin Masifa ya ce. "Ki daina kira mini sunan wani gardi a cikin gidan aurena." Duk da halin da take ciki na tashin hankali bai hana ta duban shi a fusace ba tare da faɗin. "Ba zan daina ba ɗin, na faɗa na maimaita Salmanul Farisi, Namijin duniya, yaro mai halin manya, and lastly I love him with all my hear....." Ba ta ƙarasa ba saboda wata damƙa da Adnan ya yi mata, cikin zaro ido ya ce. "Ko me za ki faɗa ki faɗa, amma ki sani ke da shi har abada, na riga na gina katangar ƙarfe a tsakaninku, wadda ba za ta taɓa rushewa ba." Ya ƙarashe maganar tare da wancakalar da ita. Kafe shi ta yi da idanunta da suka ƙirmushe babu alamar hawaye a cikinsu ba ta ce komai ba, sai haki kawai take da rawar jiki. Tsaki ya ja tare da yin ƙwafa ya juya ya bar parlour'n. Sai a lokacin wasu hawaye masu ɗumi suka samu damar zubowa daga cikin idanunta, slowly ta lumshe idonta tana shaƙar ƙamshin Salman da har lokacin bai bar parlour'n ba, zuciyarta cike da tsananin shauƙinsa.
"Me ya sa ka sake tafiya ka bar ni a karo na biyu? A lokacin da nake tsananin buƙatar ka a kusa da ni, why my Faris? Yaushe za ka ƙara dawowa gare ni?" Ta faɗi haka a fili cikin tsananin damuwa da ƙunar zuci.
Hajiya Ni'ima ce kwance a kan dogowar kujera a parlour'n gidansu, idanunta a lumshe tana tunanin abin da ya dame ta. Siririn tsaki ta ja saboda yadda hayaniyar da Aunty Suwaiba da Uncle Faisal ke yi ta cika mata kunne, ga yunwa dake damun ta, sakamakon kasa cin abinci da ta yi. Cikin takaici ta buɗe idonta tare da miƙewa ta tashi ta shiga ɗakin Mahaifiyarsu.
"Wai don Allah Mama har yanzu su Aunty ba su girma da wannan faɗace-faɗacen ba? Ni fa shi ya sa ban fiya son in zo gidan nan in zauna ba."
Taɓe baki Mama ta yi ta ce. "Ina za su girma, ai ita Suwaiban ce ba ta jan girmanta, shi ya sa shi kuma ya raina ta." Cike da takaici Na'ima ta ce. "Allah ya sawwaƙe, ni yunwa ma nake ji, kuma gaskiya ba zan iya cin wannan tuwon da Aunty ta jaɓa ba."
"Sai ki fitar da kuɗinki ki sayi abin da za ki iya ci."
"Dole na ma." Na'ima ta faɗi haka tare da ficewa daga ɗakin.
Tunda Major ya dawo gida ya rasa me yake masa daɗi, idan ya tuno halin damuwar da ya baro Abra a ciki sai ya ji damuwarsa ta ninku, babban problem ɗin kuma bai san ta inda zai fara neman asalinta ba, don tun farko da ya kalle ta ba ta yi masa kala da ƴan ƙasar nan ba, ta fi kala da half case. Haka ya shirya yau da safe ya koma gurin aiki, cike da ƙudirin fara bincike a kan Abra, don gano asalinta kamar yadda ya yi mata alƙawari.
Zaune yake shi kaɗai a cikin ƙawataccen office ɗinsa, yanayinsa kaɗai za ka kalla ka san yana cikin damuwa, duba da yadda yake yawan yamutsa kwantacciyar sumar kansa, gami da sauke numfashi akai-akai. Runtse idonsa ya yi a lokacin da kalaman tsohuwar da ko fuskarta bai gani ba suke yi masa amsa kuwwa a cikin kunnensa, a karo na babu adaɗi.
_"Malam ya mutu, ya tafi ya bar mu a lokacin da muke tsananin buƙatar shi a cikin rayuwarmu, Ubangiji ba ya barin wani don wani ya ji daɗi, kuma duk wanda ya mutu kwanansa ne ya ƙare. Amma