Chapter 77 Reading Dare da Duhu Book Complete By Nimcyluv. Zeey Kumurya.txt Arewa Novels

Dare da Duhu Book Complete By Nimcyluv. Zeey Kumurya.txt

Author :  Nimcyluv Zeey Kumurya Category :  A Books

Chapter   77 / 78

228K to 231K   out of 231.7K words

mai daɗin gaske ta ce.
"Your welcome love of my life, rest of my life" kasa jurewa ya yi da ɗan sauri ya ƙarasu wajanta yana zame hular kansa.

"Uhm am speechless" ya faɗa yana jawota jikinsa tare da mannata da ƙirjinsa. Ta zagaye hannuwanta zuwa ƙugunsa tare manne gangar jikinsu waje guda ta ce. "Ina son ka Sp Adnan Aliyu Matawalle, i love You to the square of my...."
Ya manna bakinsa akan nata wani hot kisses yake sakar mata ta ko'ina, wanda ya kashe mata jiki baki ɗaya.
A hankali ya saketa ta manna fuskarta a ƙirjin shi tana shaƙar ƙamshin Pur oud wanda a kwanakin yanzu yake mata daɗin gaske.
Kama hannunta ya yi zuwa kan kujera bayan ya zauna ya ɗora ta akan cinyarsa ya ɗora kan shi a bayanta tare da zura hannunsa a cikin rigarta ya shafa cikin kaɗan daidai kunnanta ya ce.

"Ina tunanin nayi ajjiya fa" ta sauke numfashi idanunta lumshe idanun yanayin nayi mata daɗi sosai.
Kamar bata son magana ta ce "Ajjiya kuma?" Ya ƙara shafu cikin zuwa ƙirjin tayi zillo ta ce.

"Uhm Uhm"
Allah ya sani a lokacin a matse take da mijinta, shi take buƙata haka kurum Ubangiji ya ɗora mata kewar shi bata gajiya da shi kwata-kwata.

"Yes Madam, Aishatul-humaira ta kusa samun sister or brother, ko both ɗin ma" ta kwanta jikin shi tana mai jan gemun shi cikin shagwaɓa ta ce.
"Uhm ni a'a Please ba wata ajjiya?" Ya ɗan ɗagata sama kamar baby ya ce "haba yarinya ai tunda naga kina langwaɓewa kina shaƙar ƙamshin mijinki nasan Adnan ya yi ajjiya a ɗan ƙaramin cikin nan,
Wow Sp Adnan Aliyu Matawalle you're lucky ka cika namijin duniya a wannan karan ni zan amshi haihuwar matata da kai na"

"Ni ban so Allah" ta rungome shi sosai tana rufe idanunta gaba ɗaya gajiya ta saukar mata. Ya ɗagata sama yana tashi tsaye ya ce "Na san me kike so, muje nai wanka naci abinci sai samu ƙarfi da kuzari da kyau" ta maƙale jikinsa tare da kissing matar kunnan shi.

"Mijina" ya riƙeta tsam a jikinta ya ce "Matata ƴar Albarka, ƴar Aljannata"
Bata ya haɗa ruwan da kansa ba, duk da kasalar da take ji sai da ta haɗa masa ruwan wanka.
Tana ƙoƙarin fita ya fisgota suka faɗa cikin ruwan wankan.

Bayan cin abincin suna zaune a parlour suna hira irin ta masoya rabin hirar, I love you ne. Da matata ko mijina, ko kasan ina sonka ai.
Tana kwance jikin shi daga ita sai vest, da ƙaramin skert. Shi ma trousers ne jikinsa babu ko riga sai shafa kwantaccen gashin ƙirjinsa take.
"Uhm" ya shafa kanta ya ce "ya akai?" Ta maƙale shi sosai ta ce "Kai ne"

Ya gane me take buƙata dan haka ya share kawai ya ce "Wayyo me Adnan ya yi bawan Allah, zo nan zo naji" ta saki kukan shagwaɓa tana dukan ƙirjin shi ta ce.
"Allah ka gane fa"

"Ni ban gane ba" ta sauka jikin shi ta ce "To sai da safe" wani kalar murmushi ya saki yana jawo pillow ya ce.
"Ok good night sweetheart, my Queen"

Har taje bakin ƙofa ta kasa jurewa ita dai mijinta take buƙata ta juya da sauri tana kaɗa jiki ta nufi inda yake, yana ƙoƙarin magana ta faɗa jikin shi tare da kama fuskar shi, ta haɗe bakinsu waje guda ta kau da duk wata kunya ta ɗiya mace ta shiga bawa Adnan salon da shi kansa sai daya gigita masa lissafi bai taɓa tunanin zata iya haka ba, ɗaukanta ya yi da ƙyar ganin suna neman huce lissafi kai tsaye ya direta akan lafiyayyan royal bed ɗin shi.

Washegari ya kama weekend ba tare da sanin Abra ba, Adnan ya zame jikinsa tun safe bai dawo ba sai azahar..
Ta bisa da kallon tuhuma ba tare da ta ce komai ba, ya langwaɓar da kai gefe guda yana riƙe kunnansa tare da faɗin "Double sorry Maa"
Ta juya masa baya murya sake ta ce.

"Ruwan wanka yana jiran ka Abou-Aisha"
Ya san duk lokacin da ta ce Abou-Aisha to fushi take da shi.
Ganin yadda ya tsaya yana kallonta ta taka sannu a hankali zuwa gare shi tana zuwa ta shiga ɓalle gaban rigar, ta zare ya rage sai singlet, ta sunkuya ta cire masa takalmi da safar ƙafar shi ta riƙe kayan a hannu.

Juya tai da nufin shigewa ya jawota tare da manna bayanta da ƙirjinsa ya zagaye ƙugunta, yana sunsunar wuyanta ya ce.
"Wannan sauyin fa? Akan me?"

"Magana nake Madam" tai masa banza tare da riƙe hannunsa kai tsaye bathroom ta shige da shi, sai ta fara zuba masa ruwan a jiki kana ta fito ta barshi.
Kayan shan iska ta fito masa dasu tana gamawa ta nufi dinning ta shirya lunch.
Adnan ya shirya cikin Arewa ɗin data fito masa da ita, da trousers sai baza ƙamshi yake jikinsa ya ƙara buɗewa sosai.
A dinning ya sameta tana ganinsa ta ɗauke kai bayan ta gama zuba masa abinci a plate zata juya ya riƙo hannunta yana zaunar da ita saman cinyarsa ya ce.

"Ki yafe mini matata, nayi laifi ban ƙarawa wani abu ne ya taso mini cikin gaggawa, am sorry bana son shirun nan"
Idanunta ya cika da hawaye tana kwanciya jikinsa ta ce.
"Ka bani tsoro, ai ko message kayi mini?"

"Nayi laifi ayi haƙuri a yafe wa mijin" tai murmushi ta ce "dole na"

"Ina son ka" ta faɗa tana shafa fuskar shi. Ya matseta a jikinsa ya ce.
"A duk sanda kika ce kina so na, ina jin kamar nafi ko wanne namiji sa a ne Abra, wallahi duk son da kike mini bai kai kwatankwacin wanda nake miki ba, Ubangiji shi ne shaida idanun zuciyata bai taɓa kallon wata ƴa mace ba da sunan soyayya sai a kanki, farin ciki, kwanciyar hankali, yarda da juna su ne abin da ake nema a zaman aure kuma mun samu a gidanmu, kece uwar yarana daga duniya har lahira Allah ya yi miki Albarka Matata"

Hawayen farin ya cina idanunta ta kasa cewa komai sai rungome shi kawai da tayi tana sakin murmushi.
Monday aka gabatar da Shari'ar su Bulama, bisa taimakon Allah da kuma jajir cewar Adnan. Dr Yusuf Garba Bulama ya kubuta, bayan binciken takardun makaranta da kuma na asibitin yabi komai bisa tsari, da kuma shaidar da aka samu na taimakon daya taɓa yiwa wasu daga cikin al'umma.
Farin ciki wajan Bulama ba a magana, yana fitowa ƴan jaridu sukai masa caa ya kasa cewa komai kawai sai ya jawo Abra da Adnan ya rungome, idanunsa cike da hawaye.
Gida na musamman Adnan ya bashi, bayan komai ya lafa ya faɗawa Abra rasuwar ƴar uwarsu.

"Allah sarki babu rabon ganawa, Ubangiji ya jiƙanta ya yi mata Rahama" a sanyaye Dr ya ce "Amin Ya Allah, ya kamata Ku tafi gida haka, Allah ya yi muku albarka ya baku zuri'a ta gari" a kunya ce Adnan ya amsa da Amin.

Suna zuwa gida suka tarar da motar Hajiya Mama da Abba parke a parking lot.
Adnan ya yi parking tare da fitowa, hakama Abra suna zuwa Hajiya Mama ta fito hannunta ɗauke da Aishatul-humaira.
"Sannu da zuwa Mama,Abba" Hajiya Mama ta ce "yanzu muke shirin juyawa sai gaku,muma munzu taya murna"
Aishatul-humaira ta shiga tsalle a hannun Hajiya Mama tana miƙawa Adnan hannu. "Oh yaran zamani wai harta gane ubanta, shi ya sa na tattaro kayanta na dawo da ita" Adnan ya rungome Little wacce take gwaranci tana jan gemun shi.
Sun daɗe a gidan cikin ƙaramin lokaci Abra ta shirya musu girki lafiyayye. Suka ƙara tayata murnar fitowar Bulama kana suka tafi.

Adnan da Abra suka saka Little a tsakiya yau zasu kwana tare da ƴarsu wannan ya jawota wannan ya jawota. Haka suka kwana cikin farin ciki da ƙaunar juna, washegari ƙarfe 10 na safe jirginsu ya ɗaga zuwa Kano....
[12/10, 11:40 AM] Abk: Slowly Salman yake driving idanunsa akan titi daga airport zuwa gida, ya girgiza kai kaɗan yana sauraran maganar ƴar uwar tashi kuma yayar shi har abada..
Murmushi kawai ya yi speaking calmly ya ce.
"A'a yaya,My wife had a miscarriage in four months"

"Ya Salam yanzu Faris Afra tayi ɓari amma a rasa wanda zai faɗa mini?" Ta faɗa idanunta na cika da hawaye sbd tausayin Afrar tun kafin ta ganta. Ya numfasa kaɗan yana kallon Aishatul-humaira dake riƙe a hannun mahaifinta ya ce.
"Jiya ne fa, kuma na samu labarin za kuzo ba shikenan ba?" Abra na hawaye ta ce.
"Ba shikenan ba, daka faɗa mini ai ko a waya zan kira nai jaje ko?" Ya ƙara yin murmushi domin gani yake yafi kowa ciwon rasa gudan jininsa amma bai fidda rai ba zuwa wani lokaci, domin wannan ɗin ma bai san zai samu nan kusa ba.

"Am sorry yaya nayi laifi to" Adnan ya ce "Ba wani sorry kawai ka saka mini matata kuka, ka kiyaye ni fa" a wannan karan drya sosai Salman ya yi cikin farin cikin ganin Adnan da Abra suna zaune lafiya ya ce.
"To Yaya Adnan a yafe mini, amma kada a manta nima fa ba gwauro bane a to" a haka dai suka ƙarasa gidan.
Suna shiga Abra ta tafi da gudu ta rungome Mami tana hawayen farin ciki.

"Yau na shiga uku, wai ke kam komai na kuka ne, ɗaga ni to" Abra ta ƙanƙame Mami tana murmushi ta ce "Mami hawayen farin ciki ne fa"

"To nutsu kada ki samu asara yanzu" Abra ta ce "Asara kuma Mami tame?" Kai tsaye Mami ta ce "ina nufin kada kiyi ɓari irin na ƴar uwarki" Abra ta zauna kusa da Mami ta ce "Ayya Mami ai ni bani da ciki"

"Ɗan duma ne, zai bayyanar kan shi ai da zarar lokaci ya yi" murmushi kawai Abra tayi.
Adnan ya zauna ya ce "Ina yini Mami?" Ta ce "Allahamdulillah, ya hanya" kansa a ƙasa alamar martabawa ya ce.
"Allahamdulillah!. Allah kuma ya mai da na aike" murmushi kawai tayi tana kallon Aishatul-humaira wacce ta ƙara wayo sosai ga wani kyau da Allah ya zuba mata, ta luff a jikin mahaifinta sai barci take.

"Mamana an zama ƴan mata, ta fara tafiya ne?" Abra ta ce "Tab ƴar aiki muka samu Mami, wallahi komai ta samu fasa shi take, haka ta fasa wayar Abou-Aisha ta lalace ga surutu"

"Ah masha Allah, Allah ya raya mana ita" Salima ta fito tana musu Sannu da zuwa.
Bayan sun gaisheta, Mami taiwa Abra farin ciki kuɓutar Dr Bulama sosai tare da ƙara jajanta lamarin.
Daga nan ɓangaren su Salman suka nufa, dake bayan tafiyar Salman ɗin an sake gina sabon ɓangaren a gidan Abbi, kuma babu kowa ciki shi ne Salman da Afra na dawowa suka sauka a nan. Mami tabi bayansu da kallo gwanin sha'awa kana ta shiga kallon tilin kayan arziƙin da Adnan ɗin ya kawo musu.
A zaune suka samu Salman rungome da Afra sai kuka take taƙi haƙura tana ganin kamar gangancinta ya sanya ta rasa abin cikinta.
"Kai baka jin kunyarmu ko"?
"Ni kam Yaya zanji kunya ko kai? Ku rufe idanunku idan ba zaku iya ba" Adnan ya kwantar da Aishatul-humaira a cinyarsa yana ɗan jijjigata sai gani ya yi ta fara ɗaga kai da ƙafa kamar wacce akewa wasa.
"Babu abin da zamu gani wanda bamu san dashi ba, mun shige darasinku" Adnan ya faɗa yana zaunar da Little wacce take ƙoƙarin sakkowa zuwa wajan Salman domin tuni ta gane shi.
Abra ta koma kusa da ƴar uwarta tana dungure kan Salman.
Hira suka yi sosai kafin Abra ta janye Afra zuwa bedroom ta fara bata darasi mai zafin gaske.

"Little Kinga mun rasa mijinki ko? Don't worry soon za a samaki wani" ya zauna yana mata wasa ina ita hankalinta na kan wayar shi.
"Yaushe kuka dawo daga ƙasar wajan ne?" Salman ya ce "Cikin satin nan, muna tunanin ma hawa jirgi ya kawo ɓarin Allah dai ya barwa kan shi sani"
"Ayyah Allah ya kawo ni soon" hira suka ɗan taɓa duk da Adnan hankalinsa yana kan Abra baya son tai nesa da shi baki ɗaya.
Bayan sun yi sallah Mami ta aiko da lafiyayyan lunch mai tsari kala-kala.

Fitowa tayi daga kitchen zata shige bedroom ɗin Afra ya yi saurin jawota jikinsa yana kissing wuyanta.
Ta marairaice fuska tana kallon shi, ya manna lips ɗin shi akan nata tare da yin kissing kaɗan ya ce "kin barni kamar maraya, Allah zan faɗawa Hajiya Mama"
Ta shafi gemun shi tare da wuyan shi ta ce "Please mana, yau ɗaya ka barni muci abinci da Afra kaji" ya langwaɓe tare da riƙe ƙugunta da kyau yana mannawa da nashi murya bata fita sosai ya ce.
"Ki gama yanzu,ina son mu gaisa da ƙanin Little" ta rungome shi sosai shi kuma ya fara ƙoƙarin kissing bakinta..
Ƙafar shi yaji an riƙe ana miƙewa tsaye tare da bubbuga ƙofar.
"Oh my God, jeki madam tunda little tazo ba za ai abin arziƙi ba, yarinyar nan kinawa babanki baƙin ciki yasin" ya faɗa yana miƙa hannu tare da ɗaukan ta, shi bai ma san yaya akai ta zo wajan ba.
Dry sosai Abra tayi tana shafa kan Little.

Da daddare Salman ya yi musu jagora zuwa gidan Ammi sosai taji daɗi, kamar ta ƙwace Little amma taƙi ta maƙale a jikin Salman sai ka rantse shi ne ya haifeta shi kam dry kawai yake, daga nan suka je gidan Uncle Shurem sun daɗe sosai, ko wanne gida sai Adnan ya ajjiye abin arziƙi.
Ganin Salman ya ɗauki hanya daban ya sanya Abra faɗin "Faris ina zamu?" Ya ce "Gidansu Mami angel"
Jin Salman ya ce angel ya sanya Adnan taɓe baki, yaci ace ya saba amma a kullum Salman ya faɗi haka sai yaji kishin Abra, yana dannewa ne kawai sbd yasan kawo yanzu babu komai a zuciyar Salman ɗin.
Salman kuma ba zai taɓa iya cewa Abra kai tsaye ba, bakinsa ya saba da angel babban dalili kuma Abra is his first love, yana ganin girma ƙimar sunanta ainun, ba zai taɓa iya manta abubuwa da suka faru ba, da yawan lokaci yana tuna first kiss ɗin shi da ƴar mace kuma Abra ce sai ya yi saurin yin Asstagafirullah. Shi ya sa a kullum ba a son namiji ya ɗinga zaƙewa yana aikata abu ga mace, sbd rashin samun tabbaci kasancewar ta mata wajanka, idan bata zana matarka ba a kullum ka ganta sai abin ya faɗo maka.

Bayan sun gaisa Anuty Suwaiba ta ce
"Abra nayi miki abubuwa da yawa, don Allah ki yafe mini ina cikin jarrabar rayuwa, tun bayan aure na da rabuwar da mukai, har yanzu wani namiji bai taɓa cewa yana so na, don Allah ki haƙuri ki yafe ko zan samu sassauci da rahamar Ubangiji"
Abra ta ce "na yafe miki har abada" haka Uncle Faisal, wanda ya auri mace bai san halinta ba, sai gashi ashe maza take bi har sukai auren bata dai na ba.
Shima ta ce ta yafe masa babu komai, haka babar Mami. Daga nan shopping mall Salman ya shige ya dinga jidarwa Aishatul-humaira kaya kamar hauka, Adnan zai magana Abra ta ce ya rabu dashi ai yana da kuɗin kuma shima babanta ne, bisa dole Adnan ya yi shiru.

A ɓangaren Salman aka bawa Adnan da Abra wajan kwana Mami kuma ta ɗauke Little. Cikin dare Adnan ya ɗauke Abra zuwa bedroom ɗinsa, a ranar bata samu barci ba sai da sukai sallar asuba, sosai Adnan ya tara mata gajiya ga yanayin cikin dake jikinta wanda kawo yanzu ta san da zaman shi.
Washegari motocin Major Khamal Khamis suka sauka a gidan,yana shigowa yaci karo da Little da sauri ya ɗauke ta yana faɗin "Matar zuwan yaushe" ta dinga tsalle a jikinsa, Mami ta rungume shi ta baya tana cewa "Wlcm Man" ya jawota gaba yana riƙe hannunta.
Sosai Abbi yai farin ciki ya ƙara sakawa ko wanne albarka, a nan yake cewa ya kusa ritaya daga aiki ya dawo gida baki ɗaya hakan ya yi wa su Mami daɗi.
Adnan ya kwashi iyalan shi zuwa gidan abokinsa Fayyad sun jima suna hira..
Washegari gari jirgi ya ɗaga dasu zuwa Kaduna.

Rayuwa kenan, komai ya yi farko yana da ƙarshe a hankali Ubangiji yake tafiyar da komai cikin iko da buwayar shi, sauyi da ci-gaba yana ta zuwarwa Adnan da matsayinsa ya juye daga kan S.p ya dawo Inspector General of Police. Zaman gida ya yi masa wahala sosai. Da nacin su Abra da kuma addu'a haɗi da magiyar da Dr Bulama yake Ummi ta amince suka mai da hankalinsu, amma ta kwashe komai nata, Adnan ya buɗe sabon asibiti babba ya mallakawa Dr Bulama.

Da gudu manyan motoci ke shigowa cikin Bulama's twins privet hospital. Jijiya na tashi kota ina, wasu manyan jami'an tsaron suka buɗewa Adnan ƙofa ya sako da ƙafarsa zuwa ƙasa cikin sauri kuma ya fito sanye da blue ɗin uniform wanda suka amshi jikinsa. _Ag ISP Adnan Aliyu Matawalle Inspector General of Police_.
Ya juyawa da sauri zuwa cikin hospital ɗin yana ɗagawa sauran hannu alamar su tsaya, kai tsaye emergency ya nufa, yana zuwa ya samu Hajiya Mama tsaye da Ummi wacce bata jima da zuwa ƙasar ba, Abdullah na zaune shi da matar shi Soumayyerh a gigice Adnan ya ce.
"Mama where's my wife? Tana ina?" Da hannu ta nuna masa labour ya nufi shiga Mama ta hana shi bai tsaya ba yai shigarwar shi ciki, yana shiga idanunsa ya sauka akan Abra wacce take cikin halin ciwon naƙuda su duka sun tsorata domin cikin kusan watan shi goma sha ɗaya, da sauri ya rungume ta yana shafa kanta.
"Sorry Beb, sorry sweetheart sorry" shi ne kawai abin da yake faɗa, kuka sosai ta saka tana riƙe Adnan zufa na yanko mata, iya wahala tasha Adnan ya yi zaman dirshan a gadon lokacin da Abra ta fasa ihu daidai lokacin data haihuwa shima ya saki kuka yana riƙeta sosai a jikinsa ganin ko motsi ta kasa, tausayinta ya kama shi sosai.
Likitoci suka zare babyn wane yake ƙato dashi tubarkallah, aka shirya shi cikin wasu kayan sanyi masu laushi sbd weather garin. Itama Abra aka gyara ta tare da mayar da ita ɗakin hutawa. Adnan ya rungome Abra da baby boy ɗin, jaririn uban shi ya yo baƙi ne sosai sai jajayen laɓɓa da yake dasu sai motsi yake yana kai hannu baki, a hankali Adnan ya lumshe idanun tare da faɗin.
"Allah ya raya mana Abdullah bin Adnan Aliyu Matawalle" Abra tai farin ciki sosai soyayyar Abdullah ta wanzu a zuciyarta musamman ganin kamar shi

77 / 78