Chapter 75 Reading Dare da Duhu Book Complete By Nimcyluv. Zeey Kumurya.txt Arewa Novels

Dare da Duhu Book Complete By Nimcyluv. Zeey Kumurya.txt

Author :  Nimcyluv Zeey Kumurya Category :  A Books

Chapter   75 / 78

222K to 225K   out of 231.7K words

ya yi nisa a kan aikin da take yi, taji ƙamshin turaren sa ya mamaye ilahirin kafofin hancita. A hankali ya tako har in da take ya tsaya yana ƙare mata kallo.
"Chef Yaya, girki in bana ki ba ƙanzo".
Abra tayi dariya ta ce "Allah yasa matarka ta jika" dariya yayi yace "Sarkin daru ba" ya cigaba da tsurawa Abra idanunsa, ta ɗago ta kalleshi ta ce "lafiya wannan kallon fa?".

"Angel, lokuta da dama zukatanmu suka mato a so da ƙaunar wani abu, har mu dinga jin tamkar rasa wannan abu na nufin tawaya ko samun naƙasu ga rayuwar mu, sai dai kash, tun gabanin mu zo duniya Alƙalamin ƙaddara ya kammala zana mana ƙaddarorinmu. Sai dai muyi ta lalube a duhu da sanyawa zukatanmu burika daban daban, wasu su cika wasu kuma saɓanin haka, wanda wannan hikima ce ta ubangiji da ba a masa dole.
Tabbas soyayya ba ƙarya bace ba, na rayu da soyayyar ki a lokacin da nake zaton, tsananin ƙauna ce ta 'yan uwantaka, sai bayan bayyanar wani sirri da ya zama makamin ruguza wancan tunani da nake a baya, ya sauya akalar wannan soyayyar da nake miki.
Abra ba kiyi Mamaki ba, yadda abubuwa suka dinga faruwa cikin hukuncin ubangiji ba, sama ta ka Adnan ya kutso ratuwarki, cikin ƙiftawa da bisimillah soyayya ta sanya kika rusa burin Abbi a kanki yayi miki aure. Sai dai duk da Auren da ki kai da zimmar Soyayya yayi silar rabuwar duniyarki zuwa abu biyu, idan ki ka tsaya da tunaniki kika duba hukuncin ubangiji da yadda abubuwa suka dinga wakana tamkar shirin film, sai ki gano ashe Adnan shi ne ƙaddarar ki. Duk da ya cuzguna miki a baya, sai ki duba a silarsa kuma kin haɗu da farincikin da kuɗi ba zai saya miki ba, ga iyayenki kin gano, ga kuma a silarsa 'yar uwakki ta bayyana, a silarsa Allah ya yi miki kyautar ɗan mutum sukutum guda.
Yayata, ke mace ce me yafiya, wadda muka rayu ta gini a kan raunin zuciya, haƙuri da kuma kawaici, Adnan be gaya mini meke tsakaninku ba, amma yanayinsa ya nuna yana cikin damuwa, kuma kin san bashi da cikakkiyar lafiya, kika iya yafewa Mami balle uban 'yar ki? Kiyi tunanin my Angel"
Tuni hawaye ya wanke fuskar Abra, saboda tasirin kalaman Salman a a zuciyarta, cikin kuka ta ce "Faris, Adnan ya cutar da ni san.....

"Shhh, a sanadiyar yafiyar da zaki masa, sai Allah ya yi miki abin da baki zata ba, ko kin manta shine masoyinki na farko? Am sorry to say Abra, mahaifinki ya cutar da zuciyar Adnan, duk da hakan ba hujja bane na ya huce a kanki, amma ke a kan kanki, ya faru a Asibitinsa, cikin duhun dare ba tare da ya san ke 'yar sa ba ce, idan aka ce uwa Yaya an gama magana, mahaifinki ya cancanci ya nemi yafiyar waɗanda ya cutar, ba wannan maganar muke ba, duk da shima ina son ki yafewa mahaifinki daga ke har Afra, dan kan mu wuce Dubai nake son, muje mu ganshi, dan Allah komai ya wuce yayata, musa a ranmu dukkaninmu Allah yayi mana zaɓi ne daidai da ƙaddarorinmu, da kuma abin da ya dace da mu"

Tuni hawaye suka wanke fuskar Abra, Salman ya dinga share mata ya cigaba da rarrashinta, har ta ɗan samu nutsuwa ta cigaba da aikinta, har yana tayata.
Bayan ta kammala girkin, har suka yi bidirn cin abincin su, Adnan na ɗaki bai fito ba, bata son Salman ya kuma magana, dan haka ta bi Adnan ɗaki, ta tarar da shi a kwance a kan gado, yayi shiri ya zubawa wuri ɗaya ido.
Shigowarta ce ta sanya ya mayar da idonsa kanta, ta ƙaraso ta tsaya tana kallonsa "Ba zaka ci Abinci bane?".
"Angel bana jin yunwa sam, kewarki ce ke damuna" taɓe baki tayi ta ce "Dama zan gaya maka ne, gobe in Allah ya kaimu ƙarfe huɗu, Dubai zamu tafi, zan bi su Salman, zamuje wurin Ummi muyi mata sati ɗaya sannan mu dawo"

Cikin mamaki Adnan ya kalli Abra "Amma baki gaya mini ba sai yanzu?".

"Amma dai na gaya maka ko? Ba ɗaukar jaka nayi na tafi baka sani ba" tai maganar tana harrasa up and down.

Adnan ya jinjina kai ya ce "Haka ne, Allah Ya kiyaye hanya" ta amsa da Ameen ta fice ta bar masa ɗakin, yana cigaba da mamakin yadda gaba ɗaya Abra ta sauya, tamkar an canzo masa ita da wata.

A gidan su Salman suka kwana, sai dai basu fuskanci cewar ba ɗaki ɗaya su Abra suke ba.

Washegari tun azahar Abra ta gama kintsawa, saboda zasu je prison wurin mahaifinsu.

A ɗaki ta tarar da Adnan yana kwance, da alama jikinsa ya tashi.
"Zamu tafi, kuma na ga tun safe baka sake fitowa ba"
"Angel bana jin daɗin jikina ne, dan Allah kar ki tafi ki barni".
Idanunta ne suka cika da hawaye ta ce "Au kar in tafi in barka kace? Ai gara ni wurin iyayena zani, ka manta ni ranar da ka sa ƙafa ka tafi ka barni, kana ƙyanƙyamin jikina, saboda ƙazantar da ta fito a jikina?" Shiru Adnan yayi ya rintse idanuwa a hankali ya furta "Is ok Angel, Allah ya kiyaye hanya, ki gaishe mini da Ummina, ba zan iya driving ba da na raka ku, bari driver ya kai ku" Ya dafe ƙirjinsa a hankali ya miƙe, wani abu ne mai kama da tausayi ya fara fizgarta, amma ta maze.
Adnan ya fito falo, yana murmushi ya kalli Salman ya ce "Malam shine kawai zaka ɗauke mini mata, bayan kai kana tare da matarka"
Salman yayi murmushi ya ce "Ko zaka bimu ne? Kar mu gudu da ita?"

Adnan ya ce "Ai ina ganin likita ne, muje driver ya kai ku"
Suka ƙarasa har gaban mota, Abra na ƙoƙarin shiga motar, Adnan ya riƙo hannunta ta baya, ya saka bakinsa a daidai kunnenta ya ce "My Angel, ina sonki da yawa, Allah ya tsare mini ke ya dawo da ku lafiya, dan Allah Abrana ki yafe mini,. Ban sani ba ko kan ku dawo rai yayi halinsa, bana son in je wurin Ubangiji da hakkinki, dan Allah ki yafe mini" ya ƙarasa maganar hawayensa na zirarowa yana gangarowa daga wuyanta zuwa cikin rigarta. Da haka ya cikata, ya juya ya koma cikin gida.
Jikin Abra yayi sanyi ƙalau, amma ba ta ji zata fasa tafiyarta ba.
Prison suka fara zuwa, aka fito musu da Bulama, gaba ɗaya ya fita hayyacinsa, duk wannan gayun babu, jar fatar nan tasa duk tayi baƙi.
Abra na ganin halin da yake ciki ta fashe da kuka, ta rungume Bulama tana ta shesheƙar kuka, Bulama ma rungumeta ya yi shima yana kuka har da majina.
" 'ya ta dan Allah ki yafe mini, ke da 'yar uwakki dan Allah ku yafe mini" Afra ma dai kuka take yi, sai dai ta kasa zuwa in da yake.
Abra ta shiga share masa hawayen fuskarsa ta ce "Daddy ya ake ciki da zaman kotun naka? Insha Allah zan fara halarta kuma Insha Allah zan shawo kan Ummi ta yafe maka"
Kalmar Daddy da ta kira shi da shi, yafi komai faranta masa rai.
"Daughter, dan Allah ki yiwa mijinki godiya, duk da munin laifin da na aikata masa, tun ranar da aka fara zaman kotu, kullum shikaɗai ne wani nawa da yake zuwa, sai abokaina, kuma ya ɗaukar mini ƙwararrun lauyoyi har guda uku da zasu kareni, kuma koda Yaushe cikin yi mini aike yake na kayan Abinci, mahaifinsa ma ya zo, iyayenki ma Major da mai ɗakinsa sun zo. dan Allah ki nema mini gafarar mijinki akan abin da na aikata masa" Shiru Abra tayi, sam Adnan bai taɓa gaya mata wannan maganar ba.
Suna tsaka da magana ne, gandiroba ya ce lokaci ya yi, zasu mayar da Bulama, suka dinga kuka ƙarshe sai Salman ne yayi ta aikin rarrashi da basu haƙuri.

Har suka isa Dubai, Abra na Mamakin a yadda Adnan ya tsani mahaifinta, amma ya iya taimaka masa, take taji kaso mafi rinjaye na haushinsa da take ji ya ragu a zuciyarta, dama can ƙasan zuciyarta tana jin tausayinsa dannewa kawai take yi.

Ummi ta rasa in da zata saka kanta dan daɗi, ganin yaranta a tare da ita, ta dinga farinciki tana nan nan da su, shi kansa Salman tana matuƙar son yaron nan, saboda kulawarsa ga yaran nata, kamar yadda yayi mata alƙawari ya cika, ya kawo mata yaranta wurinta.
Sai dai tayi ta mita, saboda rashin kawo mata Little.
"Abra ina wannan mijin naki masifaffe, naji babanki wai shi suka kuma aurawa, koda yake mahaifinki ne ya janyo miki koma menene"

"Ummi ni mijina ba masifaffe bane, wato ba kya son mijina sai wannan ɗan naki ko?" Tayi maganar tana tura baki.
Ummi ta ce "Abra raina ya ɓaci da jin abinda ya yi miki ne, ban san me su Major suka gani suka kuma bashi ke ba, ni so nayi su bani ke in aura miki balarabe"
Abra ta ce "Ni bana son farin namiji, Caramel nake so kamar baban little" Hira me cike da soyayya da ƙaunar juna ce ta shiga tsakaninsu, a haka Abra ta shigo da batun Ummi ta yafe wa Daddyn su, nan da nan Rumaisa ta haɗe rai ta ce "Ko dukiyarta zata ƙare, sai ta tabbatar an kai shi prison, kuma sai an nemo Matarsa an musu Shari'a a kan abin da ta aikata mata" Babarsu Abra na da sanyin hali, amma a wannan karon ta ɗau zafi da yawa, duk irin kukan da Abra tayi mata, fafur ta ƙi amincewa da yafewa Bulama.

Duk da tattali da kulawar da Ummi ke basu, hankalin Abra na Nigeria wurin mijinta, saboda yadda yake haki lokacin da zasu rabu, ta san yana jin jiki matuƙa, ga kuma wannan abun alkhairi da ya yiwa mahaifinsu.

Salman ya cigaba da yiwa Abra nasiha, a kan ta yafewa Adnan, mussaman duba da irin abin alkhairi da ya yiwa mahaifinta. Ita kanta ta san Adnan ya yi laushi na gaske.
Sai da Abra ta kwan goma a daddafe, gashi ta nemi lambar Adnan da ya dinga kiranta kwanakin baya, amma ba ta gano lambar a wayarta ba balle ta kira shi a waya, ta ji ya yake?.

Ranar kwana na goma sha ɗaya, suka rako Abra airport, Abra da Afra sun sha kukan rabuwa, haka Abra ta hawo jirgi zuwa Nigeria.

Ƙarfe biyar na yamma ta sauka. Shatar taxi tayi zuwa gida, saboda bata da lambar Adnan balle ta ce ya turo a ɗauketa.
Ba laifi gidan bai yi datti ba, amma Abra ta zage ta sake gyara ko ina.
Ba ta ji motsin Adnan ba, dan haka tayi zaton ko baya nan.
Haka nan taji tana matuƙar son ganinsa.
Har zuwa magariba bayan ta kammala girki, ba tsammani ta ga Adnan ya fito daga ɗakinsa, ba tsammani kawai yaga Abra, duk wannan motsin da take a gidan bai ji ba, ita kuwa tsorata tayi, ramar da Adnan ya yi ya wuce misali.
"Ya a kai kika dawo baki kirani a waya ba na zo na ɗauko ki? Ai da ko girki na miki" yayi Maganar yana kallonta.
Kallon kansa ya yi ya kalleta ya ce "Ya naga kina kallona? Wani laifin na kuma yi?"
Tausayinsa ne ya cika zuciyarta, ta girgiza kai ta ce "Bakomai, masallaci zaka ne?".
"Eh, ya hanya ya su Ummi?".
"Suna lafiya tana gaisheka"
"Bari inje in salla in dawo"
"A dawo lafiya"
"Allah ya sa my Angel".

Ɗakinsa ta nufa, ta gyara masa, ta kukkuna turaren wuta.

Adnan da uban ledoji ya dawo gidan, ya sissiyo kayan ciye-ciye duk dan ya farantawa Abra rai.
Ta karɓi kayan ta ajiye, ta ce "muje dininga ka ci Abinci, dan banga alamar kana cin abinci ba da bana nan" Wani irin farinciki ya kama Adnan ganin Abra na kula shi.

Ba musu ya wuce dining, ta zuba masa Abinci, yana ci yana mata hira cike da farinciki.

"Wannan jikin naka, ko dai ƙasar waje zaka a duba ka, ka rame da yawa kalli yadda ka ke numfashi fa"

"Kar ki damu, ni dai ko ban warke ba, fatana ki yafe mini kan in mutu Abra" ya yi maganar idonsa fal hawaye.
Bata amsa ba masa ba, ta janyo plate ɗin gabansa, ta ɗebo Abinci ta kai bakinsa "Maza ka ƙara Abincin nan, i want my well biuld body Adnan back, maza ka cinye" tana bashi Abincin tana zubar da hawaye.
Fuskar Adnan ɗauke da hawayen shima ya ce "Please Abra, yafiyarki ita ce babban abin da nake fata kan bar duniya, ko na mutu na san Little ba zata yi maraici ba, na barta a hannun nagartacciyar uwa, dan Allah talk My Angel" Ajiye plate ɗin ta yi, ta tafi ɗakinta.
Bayanta Adnan ya bi zuwa ɗakinta, amma ta rufe ƙofar ɗakin.
Haka Adnan ya haƙura ya sake alwala zuwa Masallaci, dan gabatar da sallar isha'i.
Bayan ya dawo yayi wanka ya kwanta a ɗakinsa, yana jin yadda zuciyarsa ke bugawa fiye da kima. Ya lumshe idanunsa hawaye na zuba ya ce "I deserve it, kome kika mini, ba zai kai wanda nayi miki ba".

Ƙofar ɗakin yaga an turo, Abra ce hannunta ɗauke da robar ruwa da kofi, ta kalli Adnan ta ce "Mun yi waya da Mama, ta ce mini kana da magunguna da kake sha, suna ina?"

Ya nuna mata side bed, ta janyo ta ɗauko magungunan, ta dinga miƙa masa ɗaya bayan ɗaya yana sha, idonsa a kanta ko ƙiftawa ba ya yi.

Miƙa hannu tayi, ta ɗan ja gemunsa kawai ta yi murmushi.

"Please Abra forgive me, a Wannan karon kalamaina daga cikin zuciyata suke, ina sonki abra ko a wancan lokacin ma, ina cikin ɗacin ran abin da mahaifinki yayi mini ne, amma nayi nadama Please my wife forgive me, ina ji a jikina kamar ba zan rayu ba, saboda yanayin ciwona, kar in mutu....

Abra ta toshewa Adnan baki, tare da kwantar da kansa a kafaɗarta, tana shafa bayansa.

"Angel kin yafe mini?".

"Mu bar waccan maganar, lafiyarka nake fata, bana son Little tayi maraici, ka daina kuka dan Allah"
"Hawayena ba zasu tsaya ba, muddin ban ji daga gareki ba My wife"

"Kaga kwanta, ka samu numfashinka ya daidaita".

Ba musu Adnan ya kwanta, tare da ita a jikinsa.

"Baby, kayi mini wani abu da ya cancanci in maka godiya, abin alkhairi da ka yiwa mahaifina duk da laifinsa a wurinka".

"Angel ban yiwa mahaifinki haka dan ya zama makamin da zan amfani da shi ki yafe mini ba, sai dai daga ni har shi masu laifi ne, kuma yanzu ya zama uba gareni tun da na haɗa zuriya da shi, ni dai yafiyarki nake nema".

"Ka daina kukan nan Please, baka da lafiya yi bacci kaji Baby" Murmushi Adnan ya yi ya ce "Ni ba wannan nake so ba, ki amsa mini".
"Zan tashi in tafi idan ba zaka yi baccin ba".
"Ba bacci zan yi ba, let me show you how much I missed you"

Cikin shagwaɓa ta ce "Mhmm Daddyn Little, baka da lafiya fa, dan Allah ka bari"

Adnan bai saurareta ba, sai da ya ƙara tabattar mata da yadda ya yi kewarta, da kuma irin tsananin ƙaunar da yake mata.
"Allah ya sa mun samu rabo, wannan karon ki haifo mana twins" "Ba Ameen ba" Abra ta faɗa tana tureshi daga jikinta.
Dariya yayi yana sake ƙanƙameta a jikinsa yana sake neman yafiyarta.

"Hmm Daddyn Little kenan, daga abin da ba zan manta ba, irin ina amarya ka kawo mini karuwa gida"

"Wallahi Wallahi Abra ba halina bane, nayi ne kawai dan in ɓata miki rai, hayota nayi. Amma kiyi haƙuri please" A nan ya sake bata labarin yadda aka yi mahaifiyarsa ta rasa ranta a sakamakon abin da Bulama ya yi.

"Amma ai ka yafewa Daddyna ko?".

"Wallahi na yafe masa Abra".

"Hmm mutum ya ci sa'a he is my first love, kuma ina ɗan son shi kaɗan, duk da laifukan mutum akwai kuma alkhairansa ds ba zan manta ba"

"Kin yafe mini Abra?"

"Na yafe maka Baby, Allah ya ƙara mana zaman lafiya da ƙaunar juna"



LITTAFINMU NA KUƊI NE, A BAMU HAKKINMU KAN A KARANTA ₦300 NE KACAL.
08081012143[12/4, 12:01 PM] Abk: Farinciki mara misaltuwa ya ji ya mamaye dukkan zuciyarsa, ajiyar zuciya ya sauke mai ƙarfi tare da ƙara ƙanƙame ta a ƙirjinsa, yana jin tamkar an sauke masa wani abu mai nauyi da ya danne zuciyarsa tsawon lokaci. Lumshe idonsa ya yi yana jin sa tamkar wanda ya shekara a sahara da dakon ƙishirwa ya samu ruwan sanyi yake sha.

"Thank you, thank you so much matata, Allah ya yi miki albarka."
Ya faɗa cikin hawaye.
Hannu ta kai ta fara share masa hawayen tare da faɗin. "Ba na son ganin hawaye ko ɗigo yana zuba daga cikin idanunka, ka daina ka ji, kai fa jarumi ne, wanda ko kallon ka aka yi sai zuciya ta girgiza." Murmushi ya yi cikin jin daɗin kalamanta ya ce. "Ni rago ne mai rauni akan soyayyar ki Angel, walwalata, farincikina da kuzarina duk sai zuciyata ta samu nutsuwa daga gare ki za su ɗore." Hannayenta ta saka ta saƙalo wuyasansa da su ta ce. "Zuciyarka ta samu nutsuwa, in dai Abra Khamal Khamis ce ta zama tata har abada." Ƙara ƙanƙameta ya yi tamkar zai mayar da ita ciki ya shiga jera mata kalaman soyayya masu tsayawa a zuciya, tare da zagaye dukkan jikinta da hannunsa, cikin wani irin salo mai cike da shauƙi. Daɗin yanayin ya sa ba ta san lokacin da ta ɗora hannunta a kan lallusar sumar kansa ta shiga yamutsa masa ba tana sakin ajiyar zuciya, hakan ya ƙara jefa Adnan a cikin buƙatuwa da ita. A hankali cikin nutsuwa ya ɗora soft lips ɗinsa a kan nata, numfashi ta ja ta fesar tana ƙara shigewa jikinsa, wani baƙon yanayi na ziyartar ta. Salon Adnan na yau ba ƙaramin birkita ta ya yi ba, ba ta son lokacin da ta fara mayar masa da martani ba. Bayan komai ya lafa tana kwance a jikinsa tana mayar da numfashi, shi kuma yana shafa gashin kanta da ya birkice. Cikin murya mai kama da raɗa ya ce. "I love You! I love You! I love You with all my heart!" Murya ƙasa-ƙasa ta ce. "Love You too my Baby." Kissing forehead ɗinta ya yi cikin tsananin nishaɗi, yana jin tamkar bai taɓa kasancewa a cikin damuwa ba a rayuwarsa. Tashi ya yi ya ɗauke ta cak ya kai ta toilet, tana rurrufe

75 / 78