WACECE NI BY Fateema Muhammad Suleiman-1.pdf

Author :  Fatima Muhammad Suleiman Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   10 / 18

27K to 30K   out of 52.9K words



https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation



*page* 3⃣1⃣&3⃣2⃣




*Today's Beautiful Hadith is about Embracing Islam*

Narrated Abu Sa'id Al Khudri (RA): Allah's Messenger (peace be upon him) said, "If a person
embraces Islam sincerely, then Allah shall forgive all his past sins, and after that starts the
settlement of accounts, the reward of his good deeds will be ten times to seven hundred times
for each good deed and one evil deed will be recorded as it is unless Allah forgives it."
(Sahih al-Bukhari, Vol. 1, Book 2, Hadith 34)

_SubhanAllah! What a beautiful reminder! It's never too late to embrace Islam sincerely! Reflect,
read, learn and grow, come closer to Islam. If you're a revert then Alhamdulillah, if you're born

into the deen and have come closer to it, then Alhamdulillah!_


Tun kafin na karaso yabudemun kofar motar,yaja muka kama hanyar school Ina Allaah Allaah
kar Prof yafara holding lecture domin baya bari ashiga idan har ya shigo hall.cikin sa'a kuwa bai
shigo ba.amma ya sanar da class rep cewa ya samu emergency calling ne daga bursary.ya yi
fixing lecture zuwa 12-1. Duk mun zauna domin jiranshi kawata latifa ce ta dafa bayana da sauri najuyo da alamu yanzu
shigowarta nake tambayarta dama kinsan yayi shifting lec 12?
Ta ce muna nan class rep yayi mana informing sai naje gida,ko 20 minutes banyiba kinga har
na dawo saboda tsoron prof abu kadan ya hanaka attending lec.na ce ni Allah ya so ya daga
time coz nayi late sosai.

Ta ce to ke Ina kika tsaya ne?

Na ce gidan yusuf bashi da lafiya.
Ta tabe baki ta ce amma lallai zaratun bakijin magana duk kashedin da auntie ki ta yi baki
saduda ba,abin ya tashi a waya har biyoshi gida kike, anya ba son Yusuf dinnan kike ba kuwa?

Na harareta sannan na ce to 'yan sa idonawa masu bacci ido daya taimakona ya nema kuma
na taimaka mashi ko taimako laifina a wajenki?

Ta ce wallahi Ina dai duba maki auntie Maryam ne gaskiya she is strict person.
Bankuma cewa komai ba sai ga lecturer mu da sauri muka shiga hall din
Yana shiga abinda ya Fara fitowa daga bakinshi move in your seat type your ID number and
wait for the password.dukkanmu students kallon kallo muka tsaya yi wato shi kuma Mr Paul
tanan ya bullo test without informing.duka course lecturer's din haka suke mana.bayan ya fada
mana password kowa ya yi login Allaah yasa test din bai wani cire abubuwa masu wuya ba
base on previous lecture nashi ya cire.
Ni na fara fitowa sai ga Latifa ma ta fito.
Muka fara tafiya sai ga khalid shima ya fito daga faculty bansan gunwa yaje ba.na yi mamaki
da ganinshi.
Sai yadanyi murmushi ya ce kina mamakin ganina ko?
Na ce gaskiya dole na nayi mamaki mana kuma na ganka ka fito a faculty mu?

Ya ce eeh nazo wurin level coordinator Ku ne shine supervisor na project dina.so naga fitanku a
hall that's why i followed you back.

Na ce ya yi kyau,sannan na juya fa Latifa da tun farko Bata sanya bakinta a maganarmu na ce
dear meet my new friend Khalid.

Sai a sannan ta fuskanceshi tana murmushi ta ce good afternoon sir.

Shima ya sako murmushi ya ce afternoon dear my pleasure to meet you.

Itama ta ce my pleasure too.

A haka har muka iso car park direct gunda Latifa tayi parking motor ta muka nufa,shima Khalid
ya nufi wajen motarshi bayan munyi sallama....

Wasa wasa shakuwa mai tsanani yashiga tsakanina da khalid domin shifa soyayya sosai yake
nunamun yayinda ni kuma gaba daya zuciya ta ta allaka akan yusuf wallahi abin kamar
asiri,tunda ya furta yana sona na amince mashi,amma ban fadawa kowa ba.ko Latifa da take
tight friend dina na boye Mata saboda ko kadan batason na kama mata sunan Yusuf,duk ranar
da na fada Mata cewa daga gidan Yusuf na tashi nayi mashi girki ne,cewa take yarinya ki ringa
yiwa kanki fada fa idan ma son Yusuf kike to iyayenki bazasu amince ba saboda banbanci
yanayi da kuke da shi Ina ke Ina gurgu.wannan statement dinta ya konamun rai sosai dan haka
na daina kawo maganar Yusuf ko da ko wane irin hira muke da ita.ita batasan cewa larurar da
yake da shi ne musabbabin sonshi da tausayinshi yadarsu cikin raina ba.
bana iya bacci sai naji muryarshi.da safe sai na biya gidansa na yi mashi dukkan abinda yake
bukata sannan na wuce school.duk wannan abin da ke faruwa auntie Maryam bata da
masaniya akai domin soyayyar Sirri muke amma mai tsafta.


Yau Khalid tunda muka fita daga lecture muna tare yana jaddadamun soyayyarshi,ya ce zaratun
Ina sonki so na hakika amma ke kuma bakya ko tausayamun ki amshi soyayya ta tun ranar da
na kyalla idanuna akan sonki yayimun mummunan kamu.please ki agaza ki amshi soyayya
ta.har da yin knell down nuna alamun optimum roko.sannan yaci gaba cewa Each time I look at your gorgeous face, I feel my heart melt in your love baby girl. I just cannot
stop thinking about you.please love me back...


Sai da na daidaita zamana sannan na ce wallahi Khalid ba haka bane ina sonka and I do love
you always amma yanzu kayimun uziri saboda yanayin karatuna yana bukatar lura da mayar da
hankali sosai idan na ce zan hada soyayya gaskiya zan takuru.amma believe me inasonka.

Sai yadan nisa ya ce hakane bawai inason shiga cikin rayuwarki ko na karatunki ba what I
wanted from you is your true love.ya tsuramun lumsassun idanuwanshi Khalid handsome guy
ne da duk wata mace zatayi mafarkin samunshi a matsayin mijinta ga kudi ga kyau.amma ni
kuma duk wannan baya gabana soyayyar Yusuf ne fal cikin raina,gudun kar yaga na
wulakantashi ya sanya na yarda muke soyayya da shi.yanzun ma da ya ritsani da idanuwanshi
bansan lokacin da na ce,
You complete my life and make it so worth living. you are nothing but an angel to me. I love
you.kar ka damu ina tare da Kai a koda yaushe...

Ya sako murmushi da nuna alamun ya gumsu da maganganuna sannan ya ce thanks so much

gaskiya yau zanyi bacci cikin farin ciki.

Har gida ya kawoni sannan mukayi sallama ya tafi.

na yi sallama auntie Maryam ta amsamun,Ina zama take tambayata Khalid ne yakawoki?
Na ce eeh ya ce na gaisheki.bayan munyi sallah mukaci abinci sai da muka kammala nadauko
assignment dina na farayi auntie Maryam dince take guiding dina saboda akwaita da ilmi daidai
gwargwado.itama wani lecturer su ne suke soyayya kuma da alama tana sonshi don har ta
gabatar da shi ga ya Anas through phone call. Yanzu ta cire maganar Yusuf ko sunanshi bata ambata ba.ni kuma bana nuna mata muna
alaka da shi balle har soyayyar da muke.


Tsawon dare muna waya da Yusuf.hirar soyayya muke Yana kuma kasheni da kalamenshi
masu rikitar da kwakalwata gaskiya Yusuf karshene wajen nuna soyayya da kalmomi masu
sace dukkan wanda ake yiwa sunana kawai idan ya ambata sai dukkan tsigar jikina ya amsa.

Na amsa da na'am

Ya ce Allaah yayi maki albarka na gode da nunamun soyayyarki gareni,duk da halin da nake ciki
kina taimakona both financially da taimakon kuma karfinki duk da na kasance ni ba kowa
ba.amma dan Allaah meye dalilinki na kula da ni haka bayan nasan kedin mutane dayawa suna
rubibin sonki?
Ina iya jin sautin kukanshi kasa kasa.
Nima na karaya da jin muryarshi na shiga tsoro sosai kodai Yusuf mutuwa zaiyi yanayimun irin
wannan godiyar duk dadewar da mukayi bai taba yimun haka ba.sai da naji na dan daidaita da
yanayin da na shiga sannan na ce,Yusuf zuciyata ce ta amince da Kai kuma ta yardemun da
insoka kuma darurarka Allaah ne ya daura maka kuma kowa baifi karfin a jarabceshi ba.kuma in
aha Allaah za ka samu lafiya.

Ya ce na gode Allaah ya saka maki da mafi alkhairi,Ina sonki sosai kamar yadda na ce maki
wani bawan Allaah yadau nawi na zamu fita zuwa Germany ko za'a dace kinga mukam duk
karfinmu ya kare wajen magani saboda yanayin rayuwa iyayena,sun koma kauye dama ni ke
taimaka musu.
Na ce haka ne Allaah yasa aje a sa'a ya ce Amen.
Daren gaba daya mun karasashi cikin jimami sai kusan karfe biyu yayimun sallama bayan na
mashi alkawarin zuwa da safe.....

Saboda ina fashin sallah sai kusan karfe bakwai na tashi na shigo wanka bayan na fito na
shirya cikin dogon riga English wear ne pink color das kayan ya matukar karbata...

Na tarar da auntie Maryam har ta gaba hada kayan break ta jira bisa dining mug ne a hannunta
dagani coffee ne take sha domin tanason coffee...Good morning Ina shirin zama nake
gaisheta,ta amsa morning how was your night?
Na ce Alhamdulillah me fa?
Ta ce nima haka.

Cikin sauri na hada tea da bread kadan naci.tana korafin banacin abinci na damu kaina da
karatu.na ce zanci ne yanzu am almost late ne cikin shagoba nayi maganar,banjira me ta ce ba
nayi mata sallama na fito waje.banzame ko Ina ba sai gidan Yusuf.ko kofarshi bai budeba sai da
nayi knocking ya zo akan kekenshi na guragu ya budemun.
Yana ganina ya sakarmun murmushi nima na mayar mashi da martani sannan yaban hanya na
shiga dakin.
Komai a wargaje dan kwana biyun da banzo ba.sai da na share ko ina na kimtsa na daura
mashi abinci,sannan na zauna...Ina dan duba agogo lokacin lecture na ya kusa.na zuba abinci
cikin food flask,sannan na kawo kusa da shi na ajiye.na ce meye za ka Fara ci ko in zuba maka
tea first?
Duk abinda nake ya zubamun idanu ko kiftawa bayayi sai da na fura mashi iskan bakina sannan
ya dubeni ya ce ba laifi na bane yanuna zuciyarshi da hannu ya ce kinsan tanason mai kyautata
Mata.

Na danyi murmushi sannan na ce kaci abinci ga shayinma na zuba bansan ya akayi ba saboda
tsaban zafin da naji na kunar wuta gaba daya hannuna na hagu shayin ya zuba kuma yusuf
dinne ya zubamun garin zai dauki shayin bansan lokacin da hawaye masu zafi suka dinga
fitowa daga idanuna ba shima ya rikice sosai abinka da farin jiki duk sun tashi da rudo rudo,sai
sannu yakeyimun ya yinda ni kuma nake mashi kallon kamar da biyu yayimun hakan......
Sai tambayata yake ko zai kira abokinshi likitane ya dubamun na girgiza kaina sannan nadau
jakata nayi hanyar fita da sauri ya tare ni da cewa kiyi hakuri wallhai bangani ba subutar
hannune ki tsaya abokina ya dubaki kaina na girgiza na ce zanje clinic na makarantarmu zasu
dubanun.babu yanda ya iya haka yabarni na tafi school amma cikin zuciyata Ina ganin da
gangan yayimun hakan...

Waya ta,na ciro na Kira Khalid akan muhadu a makaranta na dan samu kunar wuta ne.
Reaction dinshi acikin wayar koda bangashi wallahi yafi shiga damuwa fiye da Yusuf din da
shine sanadin kunar nawa, ko minti goma bankai a school ba sai ga Khalid cikin shiganshi da
yake burgeni Yana duba hannun cikin tsananin kulawa sannan ya umarceni muje asibiti aduba.

Na ce to domin hannun har yafara yimun zugi...

*Please share vote and comment*
⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐


*WACECE NI*





✍by

*Fateema Muhammad Suleiman*
Email fmsuleiman743@gmail.com
Wattad teemacool2020



*KAINUWA WRITERS✍ ASSOCIATION*
```{United we stand and succeed;Our ambition is ton entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*page* 3⃣3⃣&3⃣4⃣



*wannan page naku ne masoya Aazeen amma wadanda suke comment*



*Today's Beautiful Hadith is about Charity*

It was narrated from 'Umar, meaning, from his father, his grandfather 'Umar, that: He gave a
horse in charity at the time of the Messenger of Allah (peace be upon him), then he saw its
owner selling it for a low price. He went to the Prophet (peace be upon him) and asked him
about that, and he said: “Do not buy what you gave in charity.”
(Sunan Ibn Majah, Vol. 3, Book 15, Hadith 2392)

_When you give in charity with that intention, let it go. Do not worry about the materialistic value
of things and know that the reward of your intentions lies with Allah alone. What a great Hadith
to remind us to reflect and work on ourselves to attain a higher status where everything is
fisabilillah!_





Ba mu zame ko ina ba sai wani asibiti A&E muka wuce suka dubamun hannun sai da suka
daye wajen sannan suka wanke da normal saline,iodine da gencial violet suka zubamun sai
magunguna da suka rubuta khalid ya sayamun su daga pharmacy sai sannu yake yimun duk
tambayar da yayimun ta ya ya hakan ta faru?na dai ce mashi mistake ne kawai.da yaga bani da
niyar fada mashi ya ja bakinshi ya yi shiru.sai da ya sauke ni a kofar gida ya yimun sai da safe
nima nayi mashi godiya na shiga gida.bansamu kowa a falo ba kawai sai na zauna na kunna TV
banfi minti biyar da zama ba sai ga auntie Maryam ta fito dagani wanka tayi bata lura da
hannuna ba sai ta zauna sannan cikin tsorata da hannun nawa duk ta tayar da hankalinta cikin
damuwa ta ce subhanallah zaratun meye ya samu hannunki yayimun tambayar tare da rike
hannun dake ciwo?

Kasa bata amsa nayi sai hawaye shar a idanuna,ta ce please kifadamun meye yasamu hannun
cikin rarrashi take tambayata? This time kam bazan boye mata ba dole na fada Mata gaskiya.

Na ce ruwan shayi ne ya zubomun shi ne na samu kuna yanzu Khalid ya sauke zuwanmu
kenan daga asibiti.
Cikin mamaki ta ce shayi kuma?
Waye kuma ya fara zuwa muku da shayi zuwa school?
Na ce ba'a school bane a gidan Yusuf ne ya kirani na taimaka mashi shi ne ya zubamun shayin
a hannuna.
Wani kallo da harara da ta sakarmun wallahi sai da hanjin cikina suka kada,na shiga da na
sanin fada mata gaskiya.
Cikin karaji har muryata baya fita dan masifa.
Ta ce banji meye Kika ce ba Yusuf ko meye naji kin ambata?
Dago Kai nayi na kare Mata kallo sosai gaskiya na gaji da kunbiya kunbiya da boye boye yau
dolene na zama jaruma na fito fili na fada Mata gaskiyar abin da ke raina koma dai meye zai
faru ya faru,cikin sarkiwar murya kasa kasa na ce Yusuf dai daya shi nake nufi tun daga ranar
da mukaje gidanshi bayan dawowarmu na Kira number sa don bashi hakuri akan abin da ya
faru na so na dai dai taku amma da Kika ki ni na tausaya masa nake dan taimakonsa toh zuciya
ta ta kamu sa sonshi kuma shima Yana so na.
Tunda nake magana tayi sakeke tana kallona maganganu na ma mamaki suka bata she is
totally confused.

Sai da taga nayi shiru ta ce lallai zaratun kinyi babban kuskure ina hankalinki da tunaninki duk
sukaje da har zakiyi garajen fadawa tarkon soyayyar musaki,a musakinma kuma talaka ta sake
tabe baki ta ce wallahi am speechless amma zanyi maganinku daga shi har ke.
ke kam naki maisauki ne,yarinta ke dibarki.
Tunda ta ce haka zuciyata ke ta faman dukan uku uku,kuma Ina tsoron kartayiwa Yusuf rashin
mutunci ni fushin da nayi da shima duk na zafin ciwone,amma ko kadan banrike abin da wani
serious ba.tun muna asibiti yayi ta faman kirana amma bandauka ba saboda Khalid Yana
wajen.toh yanzu idan auntie Maryam ta kirashi ta balbala mashi ruwan masifa ya zanyi zai
dauka ma ni na sanyata,aiko bangama tunani ba ta fito sanye da hijabi.
Ta ce tashi muje gidan Yusuf din ashe shi Munafiki ban yarda kwallar mangoro ba kenan shinan
yasamu karamar yarinya Yana fure mata kunne.
Na ce ni wallahi ba inda zani,kuma baya furemun kunne ni kawai tausayinshi nake yi,kuma
gaskiya ba yadda za'ayi domin zuciyaya na sonshi,saurin fincikoni tayi ta mikar da ni tsaye sai
da ta ingiza keyata waje sannan sa sanya kuka amma dole ta sanya muka kama tafiya da ma ta
yi magana da cab bamufi minti biyu ba sai ga motar sai da Muna daidai layinsu Yusuf ta umarci
driver da ya yi parking tun kafin motar ta daidaita parking ta kamo hannuna muka fito Muna m
shiga cikin gidan,wayam dakin ba kowa ita ce ke duk duba ko ina na dakin amma ba kowa ,nayi
mamaki shi kuma Yusuf ina ya shiga ne kodai tayi fushine da ni ya chanja apartment saboda
kar bazo inda yake,amma kuma bazaiyimun haka ba ina cikin wannan tunanin auntie Maryam
ta dakamun tsawa da cewa wato kin sanar mashi cewa zamu zo Kika sanya ya gudu to wai shi
wannan gurgu ta ina ma ya samu ya fita ne tayi maganar cikin tabe baki nasan da biyu take
kushe Yusuf don na ce ina son shi.
Bandamu da maganganunshi ni hankalinane ma ya tashi sosai kodai dama ba so na yake ba
yaudara ce wata zuciya ta ce mun a'a akwai dai wata dalili munfi minti ishirin a gidan amma
babu Yusuf babu dalilinshi abin mamakin ma kofar gidan da na dakin duk a bude.haka muka
koma gida ta na ta yimun balbalin masifa sannan ta ce yanzu kam kin samu kanki idan kuma
mutuwace zakiyi akan sonshi sai ki mutu, tunda ya gudu ya barki wallahi ya ci sa'a, da Yau yaga
rashin mutunci ai.
Nidai bance komai ba Ina son kawai mu komo gida na Kira wayarshi inji Ina yajene munje
gidanshi bayanan.
Bansanma mun iso gida ba sai jin motar ta tsayane ya ankarar da ni banjita ba nayi saurin
sauka a motar na shiga cikin gida.daki na wuce

10 / 18