Author : Fatima Muhammad Suleiman Category : Romantic Hausa Novels
shuki da kyawarku
ta ce nayi missing dinku ko yaushe Allaah zai Sada mu da ku? *Vaishali* da ke gefenta itama
kukan takeyi ta ce ai gwara ke kina samun ganinsu koda a picture ne nifa tunda da muka rabu
da su sai dai inyi imagining nasu ko hoton mutum daya bani da shi wayyo Allaah ka kawo mana
mufita...
wunin yau haka suka yi shi cikin jimami...sunyi dai kudirin nemowa kansu mafita....
********
karfe daya da minti takwas na dare *Aazeen* ta tashi da mummunan ciwon Kai,nishin ta ne ya
tayar da *Vaishali* daga bacci cikin rudewa ta matso kusa da ita,tare da tambayar ta me ke
damunta ?kanta adafe ta ce sister ki taimakemu ni wallahi mutuwa zanyi, kaina kamar ana
bugamun da dutse nakeji
dukkansu kuka sukeyi gashi cikin dare, kyalle ta samu suka daure kan, amma babu sauki .
Allaah Allaah suke asubah tayi suje asibiti.....
*share*
*comments*
⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐
*WACECE NI*
✍ by
*fateema Muhammad Suleiman*
Email fmsuleiman743@gmail.com
Wattpad teemacool2020
*KAINUWA WRITERS✍ ASSOCIATION*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*Readers nayi matukar farin ciki da comments*
*Wannan shi yasanya ni* *kwarin gwiwar cigaba da rubutun Ana tare*
*page* 9⃣&
Daga *Aazeen* har *vaishali* babu Wanda Ya runtsa har Asubah.
A daddafe suka idar da sallah sai ga *David* ya na mu su knocking da sauri *vaishali* ta bude
kofar idanunta fal da hawaye sosai shi ma hankalin shi ya tashi da taimakonshi su ka sanya ta a
motor sannan su ka wuce asibiti....
Su na isa taimakon gaggawa ta samu saboda tun kafin su iso ya sanar da su da zuwansu.
An debi sample na jini da fitsara abin da Dr ya yi requesting urgent pcv, random blood sugar, sai
test na widal and mp.
Cikin sauri aka yi urgent pcv din kuma ya nuna normal sai random blood sugar shi ma normal
sannan suka sanya ma ta dextrose saline, bayan Kamar awa daya jikin ya danyi sauki.sai ga
sauran results din ma ankawo kuma komai normal....
Dr Thomas Ya Kore a fannin malignancy wato cancerous cells kasancewar cikin kwanakin nan
suna samun case din sosai duk patient da su ka kawo complain irin na *Aazeen* to idan aka yi
test results ya na nuna akwai cutar ba tare da bata lokaci ba ya ba ma David shawarar yin test
din Alpa protein. Hakan kuwa aka yi kuma ya nuna ta na dauke da cutar cancer na kokolwa (canccer of brain )
Ba karamin kidima su ka shiga ba da jin wannan labari an gwada, kuma ta na stage one cikin
gaggawa aka fara yin chemotherapy treatments kafin daura ta akan radiation treatment cikin
kwana uku duk ta fita haiyacinta saboda chemotherapy ya na matukar wuya gashin kanta duk
ya zube kan ya zama Kamar maku tal ba gashi gaskiya duk wani mai imani dole ne ya
tausayawa wannan baiwar Allaah.
Da taimakon Dr Thomas da David ne ake samun ta ke dan sausauta kukan ta da kuma cin
abinci ko da kadan ne vaishali ma duk ta fada saboda jinyar 'yar uwar ta da ta ke.
Ahaka suka share wata uku a asibiti amma yanzu kam Alhamdulillah jikin yana sauki sosai yana
responding treatment.
sai da ta yi wata uku da sati daya sannan aka sallomo ta.su ka koma gida sai dai sati biyu biyu
za ta dinga zuwa follow up.
Yauma su na zaune da vaishali ta na kwantar mata da hankali , *Aazeen* ta ce sister ina
tausayin Kai na sannan ina tausayin mu gaba daya yanzu idan na mutu shi kenan labari na ya
wuce ahlina baza su taba sanin gwagwarmayar da na sha ba har na koma ga mahalicci na.
Vaishali ma cikin tausaya ma ta ta ce in sha Allaah sis ba za ki mutu ba Za mu ga ahlinmu..
Haka kullum suke cikin juyayi har ya za na yanzu ta cire dukkan damuwa a ran ta shawarwarin
da Dr Thomas ke yi ma ta kuma duk ta na bi.
Yau Sun fito bakin kogin dake gefen unguwar su su na dan hutawa sai *Aazeen* ta dago Kai ta
na furkan ta vaishali da ke wanka a cikin ruwan ita ma ta ba ta full attention na ta sosai.
ta ce sis ina da shawara akan wannan abin da ya sa me ni jiya ina karanta wata jaridar insider
na ga abin da ya ja ra 'ayina sosai, kuma mafita ne ga abin da na ke ciki kin ga Doctors sun
tabbatar mun da cewa chances na rayuwa ta ba zai wuce shekara daya watanni ba kin ga bani
da tabbacin za mu hadu da family mu may be ma a lokacin na bar duniya shi kenan tarihi na ya
za ma babu duk wannan abubuwan da nayi encountering ba za su taba sani ba tun da har yau
babu mu babu labarinmu duk iya kokarin da muke har yanzu shiru tabbacin ba su farga da
sakonnin da mu ke ta turowa net ba duk da power dake kan net Allaah baisa sun gano mu ba
kawai ina ganin akwai abin da Allah ke so da mu ta kasashe zancen ta cikin share hawayen da
ta kasa controlling dinsu.
ita ma vaishali da tun ta Fara magana ta zo kusa da ita ta zauna ta rike duka hannayenta biyu
to ita ma hawayen ta ke duk da ba ta ji shawarar da ta son yankewar ba. ta dai barta taci gaba
da yin hawayen don tasan wannan kadai zai sanyaya zukatan su.
sai da ta dan samu relieve sannan ta ce I have an idea of doing artificial insemination.
Vaishali cikin tashin hankali marar misaltuwa ta ce sis kinsan abin da kike fada kuwa?
Cikin jinjina Kai ta ce na sani sosai kuma ina cikin hayyaci na nake maki wannan maganan.
sannan ta ci gaba da cewa kinsan da angano gunda da muke komai daren dadewa toh lokacin
ni fa na bar duniyar ma saboda ba ni da tabbacin cikakkun shekaru biyu masu kyau toh kin ga
samunki zai sanya mahaifiya ta cikin tsananin damuwa karshe ma ta rasa ranta saboda dalilin
rashin samuna na kin san ni daya Allaah ya arzurta su da samu sai maza biyu na san kuma
iyayenmu baza su taba cire tsammani da mu ba.
Saboda haka na yanke shawarar yin shi, kin ga bamu taba yin zina ba Allaah ya kiyaye mu toh
jiya sai na yi Karo da lab din da su sayar da sperm donor duk Wanda ya ke da sha'awar samun
yaro zai biyu kudade sai ahada da Kwan mace sannan za ta Haifi cikekken yaro ko yarinya. Kin
ga idan har na samu na yi haka koda bani nan a duniya,ina da Kwan da uwa ta za ta gani ran ta
ya dan kwanta.
Daga wannan ba ta kuma cewa komai ba,ta na son jin abin da vaishali za ta mayar ma ta ...
lallai sis baki kawo shawarar da zan iya dauka babu. ince Ki yi wannan gurbatacciyar shawarar
da zuciyar ki gindaya maki ina kika ga gun da iyaye za su yi farin cikin samun yaro ba tare da
uba ba duk da na ki shawarar za sayi sperm ne a ki kenkeshe da kwanki wannan ma ba mafita
ba ne gwara ki ce aure to da dan dama.
waye ki ke ga zai aure ni a wadannan kwanakin da suka ragemun mutanen da basu ma da
addini balle sanin kaddara ko tausayi.
Allah ya sani bazan yi zina ba amma insemination kam dole zan yi before then zan nemi
shawarar Dr Thomas idan har ya ce zan iya rainon cikin a wannan yanayin to ni kuma na shirya.
ke abin da nake so daga gareki zaki rike mun abin da zan Haifa duk lokacin da aka samu
labarin mu sai ki hada dukkan takarduna da yaron ki kaina mahaifiya ta.
Vaishali ta sake rike hannayen na ta da karfi ta ce sis toh gobe za mu ga Dr Thomas idan ya ce
babu matsala shikenan kuma in sha Allaah zaki samu sauki har ki warke gaba daya har agano
inda muke, ta sanya hannu ta na goge ma ta hawayen ta.
*Aazeen* ta jinjina Kai ta ce nagode sis I love you.
ita ma ta mayar mata da I love you too abar kaunata.
hakan kuwa aka yi yau tun da su ka yi sallar asubah ba su kuma kwanciya ba,su na lazimi har
gari ya yi haske suka shirya dukkansu jacket su ka sanya ,su ka Kama cab ya kai su asibiti.
Duk da sammako da su ka yi sun iske Dr Thomas a office, cikin fara'a da sakin fuska ya
tarbesu.
Bayan ya dudduba ta kuma yaji dadin yanayin da ya ganta gaskiya jikinki ya na responding
treatment na ji dadin hakan ki cire damuwa a ranki a hankali komai zai zama normal.
ta ce nagode Dr. Cikin sanyin murya ta ke maganan sannan ta gaya mashi shawarar da ta
yanke.
ya tsura ma ta ido na seconni sannan ya ce shawarar ki ma abin dubawa ne, amma sai mun
tabbatar bazai kawo bara zana da lafiyar ki ba.
Da yake su wannan abin is normal thing ne bai dauke shi da wata matsala ba toh su mace
lafiyayya ma sai ta ce bazatayi aure ba kawai zata je lab ta sayi sperm din kuma ta haihu yaro
ta girmar balle wannan da yazo ma ta da darura ai shikenan nan fadawa ce ta zo daidai da
zama.
Bayan gwaje gwaje da suka yi ma ta da taimakon Dr Thomas aka nuna mu su tube kusan
number dubu daya.
aciki Dr Simon ya ce su zabi tube number 489, suka biya kudaden da ake bukata sannan aka yi
komai,sannan su ka ba ta sati biyu ta komo su duba ta.....
magunguna ya Kara rubuta ma ta Wanda za ta sha na sati biyu din.
sannan su ka dawo gida.
*share*
*comments*
⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐
*WACECE NI*
✍ by
*fateema Muhammad Suleiman*
Email fmsuleiman743@gmail.com
Wattpad teemacool2020
*KAINUWA WRITERS✍ ASSOCIATION*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*page* 1⃣1⃣&1⃣2⃣
Su na dawowa gida *Aazeen* bathroom ta wuce ta sake shower akan ta sai da ta ji sanyin
ruwan ya ratsa ko ina na jikinta sannan ta fito,ta iske *vaishali* bisa dinning table gaban ta duk
kayan ciyeciye ne da ta girka tun kafin su je asibiti.
Ta na zama ta ce nifa coffee kadai zan sha coz ba na son cin komai a yanzu.
Vaishali dai ta dan ci kadan sannan dukkan su su ka mike da cup dauke a hannunsu falo suka
zauna,ta kunna musu Deen TV taji dadi program din ta kuwa ake yi Wanda sheikh Asim
Alhakim ke gabatarwa yau topic din su akan Al'ayn (kambin baka)evil eyes da turance.
sheikh ya yi dogon bayani akai inda ya ce
Hakika Annabi saw acikin hadisi ya na cewa Al'ayn hakk kambin baka gaske ce, hakika
Al'ummata bayan kaddarar ubangiji to toh kambin baka ce ke kashe su.saboda haka duk
lokacin da ku ka ga Abu ya burgeku toh ku sanya albarka a wannan abin domin sanya albarka
zai kawar da cutar da 'yan uwanku ka ce, tabarakallah Masha Allah.
sannan ya yi bayani yawancin cutuka yanzu ya na faruwa ne bisa dalilin kambin baka.
Musamman wannan cuta ta cancer.
Ga addu'a da sheikh ya bada vaishali ta na rubutawa Kamar haka,
Bismillahi, A'uzubillahi min kudratihi min sharri ma ajidu wa uhazir .
Marar lafiya zai rike wajen ciwon,sai ya karanta wannan addu'ar sau bakwai
Sannan cutar cancer marar lafiyar ya kasance ya na shan nonon rakumi da fitsarinsa tsawon
watanni shida. Yadda zai sha kuma gorar robar ruwa na nonon sai fitsari kuma daidai murfin
robar sai ya hada ya sha in Allaah za'a samu waraka.
Gaskiya sun ji dadin shirin kuma sun karu musamman *Aazeen* da ta tattara dukkanin hankalin
ta bisa ga shirin ta kudurce a ran ta duk za ta bi abin da sheikh ya yi bayani akai.
David su ka sanarwa cewa su na neman nonon rakumi da kyar ya samu irin Wanda ake shigo
da shi daga yankin saudia saboda su ba su da rakumi a yankinsu.
Kuma ta dage shi ta ke ta sha kuma ta na jin dadin yanda jikinta ke samun sauki.
yau sati biyu kenan kwanakin da likitocin ta su ka bata,tun da safe ta shirya ta je asibiti sai da ta
fara zuwa wajen Dr Thomas ya duddubata ya kuma rubuta ma ta magunguna.sannan su wuce
wajen Dr Simon test su ka rubuta serum and urine pt, bayan sun dau sample na jini suka ba ta
Universal container ta kawo fitsari.sannan suka koma office din Dr Thomas.
bayan Kamar minti ashirin da biyar sai aka aiko da results pt positive
Haka ya yi ma ta bayani da cewa ciki ya zauna ajikinki zaki reneshi har zuwa wata tara sannan
ki haihoshi normal delivery ko cs Allaah kuma yaraba lafiya.
zuciyar ta ta dan tsinke da bayanan Dr cikin tsoro ta ce Dr yanzu kana ganin zan iya Haihuwa
ba wata matsala?
cikin murmushi ya ce babu matsala *Aazeen* sarkin tsoro idan da akwai matsala tun farko ba
za mu fara ba kedai ki kula da duk bayanan da muka yi maki kuma kici gaba da amfani da
magungunanki sannan bayan wata daya zaki zo follow up.
ta mike ta mishi godiya da sallama ta fito daga office din.
Ta na fitowa daga office din ta ciro wayar ta ta kira number Vaishali,baifi ringing daya ba ta dauki
wayar ta kara a kunnen ta cikin fadin abar so na ya dai daga wannan bangaren *Aazeen* ma ta
ce masoyiya ina kan hanya na bugo ne kawai na ce everything going on successfully and I will
became a mother in next 9 months and daughter to you.
Amma kinsan wani Abu wallahi kawai sai naji na tsorata tun da Dr ya ce mun cikin ya zauna
Zuciyata ta fara bugawa kuma har yanzu ban koma normal ba.
daga wancen bangaren vaishali ta ke bata baki da cewa haba abar so na meye na tada
hankalin ki bayan sanin da kikayi damuwa ba naki ba ne saboda darurar ki,kuma amfada maki
ba'aso ki daga hankalin ki ko kadan
Please Kiyi sauri ki taho gida in sha Allaah za ki haihu normal kuma ki reni babin ki Allah dai ya
baki lafiya ita ma ta ce Aameen ga ni na kusa isowa ma sannan ta katse wayar.
Haka suka ringa renon cikin vaishali ba ta barin ta ta yi komai.
David ma ya na iyakan kokarin shi wajen kyautata masu.
Yauma ya zo su na hira da vaishali a falo.kasancewar *Aazeen* cikin kwanakin nan sai
barci....ya kamo hannayenta duka biyu yayinda ya ke murza zuben da ke tsakiyar hannunta.ya
Kira sunan ta da whisky voice din shi.
Ta amsa cikin sanyi murya ba tare da ta dago Kai ta dubeshi ba ta na kokarin kwace hannunta
da ya yi ma ta rukon bazan Sake ki ba,cikin kashe ma ta ido ya ce ki yi hakuri bazan wuce gona
da iri ba na san addininku ya haramta maku yin musabaha da namiji amma ni sonki ne ke
azabtar da ni kuma ki San cewa bani da nufin cutar da ku tun ranar da na sanya idanuna akanki
naji ajikina na samu matar aure sai da na bincika aka ce ku ba 'yan kungiyancen ba ba ta kukayi
sai kuma ku ka fada hannunsu toh tun daga ranar nayi alkawarin cire ku daga cikin su.
kuma yanzu haka muna iyakan kokarin ganin mun Sada ku ga kasar ku, ku yi ta addu'a in sha
Allaah komai zai daidai ta may be embassy Australia da muka aika matsalar ku su nemeku..ba
karamin dadi ta ji ba da bayanashi ya tallabo habanta.ita ma tana murmushi har dimples din ta
sun lotsa ta rausayar da ido cikin dubara ta cire hannayenta daga nashi.
ya kura ma ta idanunshi masu matukar daukan idon Wanda ke kallonsu sannan ya ce I love
you, and I will die for your love will you love me back as I did to you?
ta sadda kanta kasa nuna alamun Jin kunya, ya ce yes ki dube ni sosai kuma ki bani amsa ta.
ta ce zan fada amma ba yanzu ba.
ya ce no yanzu nake so idan ba haka ba zanyi fushi ya yi kicin kicin da ido nuna alamun kuka.
haka suka yi ta hirar su Kamar kar su rabu amma ana ta kiranshi awaya babu yanda ya
iya,haka yakasance yi ma ta sallama ya ta fi bayan ya manna mata kiss a bayan hannunta.
Cikin *Aazeen* har ya shiga wata na takwas, kuma jikinta yana ci gaba da samun sauki har
likitocin sunyi mamakin ganin yanda cancerous cells din ke komawa baya.dama sun daina yin
radiation