WACECE NI BY Fateema Muhammad Suleiman-1.pdf

Author :  Fatima Muhammad Suleiman Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   7 / 18

18K to 21K   out of 52.9K words

a duke ta sadda da shi kasa sai
ya tallafo habartaya dago fuskar sai ta runtse idanunta nuna alamun jin kunya.


Ya ce aiko baki isa ba bude idanunki in kalli wannan fuskar ki mai yalwar haske da annuri
gaskiya yau Ina cikin farin ciki mara misaltuwa na mallaki wannan kyakkyawar model lady...
Ita sai ta yi shiru ta na sauraronshi kawai,kuma batasan me yasa ba zuciyarta na bugu kadan
kadan kamar da tsoro ne yakeson ziyartar zuciyarta.
A haka kuma har suka iso gida dai dai karfe goma kenan.

suna sauka babu kowa a harabar gidan sauran mutane har sun gama dawowa domin ga nan
motoci burjik a wurin cikin sauri ta sauko a motar tana saurin yin part dinsu mum sai ya yi saurin
riko hannunta,ya ce saurin me kikeyi ne haka ba za ki tsaya ki yi sallama mai kyau da mijinki
ba? baki ga yanzu duk sun mallakamun ke ba gaba daya tun awajen dinner kowa ya gudu ya
barmun ke ba yana wani Shu'umin murmushi ya ke wannan maganar.


Ta dan sako murmushi ta ce nasani kawai dai gajiya ce kuma kayan sunyimun nawi inason
ciresu ne.
Ya jinjina kai ya ce to na ji yanzu me Kika shiryamun ne kafin gobe
Ta yi shiru ta kasa bashi amsa.
Sai ya ce ya baki ce komai ba?
Ta ce to ai ni bansan meye zance ba.
Ya ce ya na da kyau kisan abin da da za ki ce.

Gaba daya ta kagu yabarta ta shiga amma sai da ya yi kicin kicin din da ya hada bakinsu wuri
daya tsawon lokaci ya na tsosan sai da ya gaji da karan kanshi ya sake ta kuma ta ci sa'a babu
wanda yafito sai da ta dan setu da yanayin da ta shiga sannan ta yi mashi good night shima ya
mayar mata da sallamar ta sannan,ya ce bear in your mind flight dinmu fa by nine ne so ki samu
shiri da wuri da wanda zaku tafi tare sannan ya kuma yi mata peak kiss a hannunta ya yi part
din da aka basu tun zuwansu.

Ta na shi duk yawanci mutane suna ta hayaniya wadansu kuma suna harkokin gabansu ba su
ma Lura da shigarta ba sai da ta shiga bedroom ta iske Fatima da Aisha wanda sune sa
'anninta yaran goggoninta ne cha sukayi mata da cewa kai wannan angon naki dan love ne tun
yaushe muke zaman jiranki amma sai yanzu zai barki Ku dawo mu fa har mun dauka fa a can

zaki kwana suka fada cikin zaulaya da dariya.

Ta harare su itama ma ta ce sai kuyi ai amma kuma rashin kunyar tawa ba ta yi yawan da zai sa
inbi miji makwancinshi kuma na gidanmu.
Su ka tabe baki suka ce ka ji mun mata yadai daga maki Kafa ne ai to hakkinshi ne dole kuma
zai kwata komai daren dadewa.
Ta ce kwaji da shi ni bara inyi wanka wannan kaya duk ya ta kurani Ku kuma parot kun cikani da
surutu.ba ta tsaya jin amsarsu ba ta shige bathroom ta sakarwa kanta shower......










*share and comment*

⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐


*WACECE NI*




✍by

*Fateema Muhammad Suleiman*
Email fmsuleiman743@gmail.com
Wattad teemacool2020



*KAINUWA WRITERS✍ ASSOCIATION*
```{United we stand and succeed;Our ambition is ton entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*page* 2⃣3⃣&2⃣4⃣

*wannan page naku ne masoya Aazeen amma wadanda suke comment kuyi yadda kuke so da
shi*



Sai da ta gama kimtsawa ta sanya kayan baccinta sannan ta fito falo duk yawanci mutane sunyi
bacci sai fatima ce da ke gaban TV tana kallon series film Hayati Azab.
Ta dago ta dube ta ta ce amarya agidan Dr Hameed yadai akwai wani abu ne?
Aazeen ta ce eh ki nemomun abinci felling hungry,
Da sauri ta mike ta dauko mata flask sai slace bread da kamoniya acikin plate ta ce ga wannan
ki yi manage.
Ta yi murmushi ta ce thanks wannan ma ya yi.
Ta na ci jefi jefi suke hira domin Aazeen din ba mai yawan magana ba ce.sai dai ita fatiman ce
ta ke dan jan ta da hira.suna cikin zancen yanda dinner din ya kayatar sai ga Akhayya,kanwar
mahaifiyarta ce,tare aka yi masu aure da Hajja fanna amma ita mutumin Ndjanmaina (chad) ta
aura ta haifi yara uku maza biyu da yarinya daya toh tunda mijinta ya rasu, ta dawo zama a
Nigeria.sai kuma bayan batan Aazeen da rasuwar Alhaji modu ta dawo gidan yayar ta ta wato
Hajja fanna domin ta taya ta zama.ita ce kuma duk wani gyara da za'ayiwa amare sai da tayiwa
Aazeen sirrika Kala kala wanda har ita Aazeen din sai da yafita akanta,yanzu ma zuwa ta yi da
wani irin hadinsu na shuwa ta umarci Aazeen din da ta sha, ta karba cikin langabe kai a
shagobe ta ce ni fa ammi abubuwanda kike duramun din nan,ya ishe ni.dubi jikina fa,duk sun
ciko nifa banason kiba shi ya sanya ko madara banason sha sosai amma sai da kuka sa nasha
peak da kwai har na tsowon wata daya ga sauran abubuwan da bansan Kansu ba da kike ta
bani gaskiya ni haka ya isa ta karasa zancenta kamar za ta yi kuka.

Akhayye ammi sunanda suke ki ranta da shi kenan,ta ce rakrak hanaki ,ke me ma kika gani
dan ma bakya chad ne da zan sanya har circumcision(kaciya) ammaki saboda yana cikin
al'adummu amma nan duk kunyi watsi da shi.wannan abubuwa da nake maki 'yancin kanki
nake nema maki kin manta kin haihu ne duk da cs ne duk service ya dan budu sannan mijinki
saurayi ne.yanzu abin da nake bukata ki ta shi muje ki kuma tsugunawa akan wancen kaskon ki
sanya lubban da gafgaf sai wannan ta mika mata wani kalan turaren wuta da bansan sunanshi
ba,sai da ta jira ta tabbatar ta yi abubuwan da ta sanyata ta yi sannan sukayi sallama ta koma
part din da take.

Aazeen ba ta samu ta sanya zaratun a idanunta ba kuma ta na son ganin 'yar ta ta amma sam
sunki kawo mata ita batasamma a gunwa take ba Kiri kiri suka sanya ta hana mata nono,ba ta
so hakan ba duk watan yarinyar shida amma anhana mata nono,duk dama exclusive breast
feeding ta yi mata yanzu sai dai SMA suke bata Masha Allah kuma ya karbeta ba za ka dauka
batashan nono ba,bulbul da ita tabarakallah.

Sai ga kiran angon na ta ya shigo sai da tayi ringing sau biyu sannan ta dauka a kasale domin

duk gabobin jikinta ciwo ke yi saboda gajiya duk kwanakin nan bata samun hutu.shidin ma
hakanne.
Cikin sanyin murya ta amsa mashi sallamar da ya yi sannan ya ce,baby girl gaba daya yau
kinsa na kasa bacci yanzu kisan abin da za ki yi mun Wanda zai sanyani bacci.

Cikin lankwasawar murya mai taushi ta ce ni kuma na hanaka bacci sai dai ka ce gajiya ya
Hana ka bacci dai kamar yanda na ke ji yanzu haka duk jikina ciwo kamar anyimun duka ta na
maganan cikin shagoba kamar ta na gabanshi.

ya ce kada ki samu damuwa wannan gajiyar duk zan cire maki shi daga gobe ma.yanzu ki na
ina ne ya jeho ma ta tambaya?
ta ce Ina kan gado inason yin bacci amma yaki zuwa.
Ya ce ko dai za ki zo ne kimun ko da massaging ne (tausa)?
Cikin ware ido kamar ya na kallonta ta ce chab ta Ina zan fara dazu ma dakyar na kwace Kai na
a wurinka na lura sosai kana son sanyani jin kunya.
ya ce kunyar me? ai dama da suka mallakamun ke sun san abinda zai wakana kenan,dadin
abin duk abinda za mu yi lada za ki samu.ke din ce idan ki na kusa da mutum sai ya kasa
controlling kanshi dazun ma ba karamin hakuri na yi ba.
Ta yi shiru tsawon dakikai sai ya katse shirun da cewa.
Ya kinyi shiru ne?
Ta ce to ni meye zan ce?
Ya ce amaryata ki cire kunya ni fa ba na son mai kunya feel free I am ur husby kuma ina son ayi
treating dina like a baby,so kunya bashi da muhallin zama a gidanmu.

Ta nisa har sai da ya ji hucin numfashinta a cikin wayar ta ce don Allaah ka barni na yi bacci
yanzu kusan karfe daya fa nasan bazan yi bacci na two hours ba Ammi za ta ta sheni...
Kin gundura da ni kenan?
Ta ce ni bance ba kawai ina son na yi bacci ne before four o clock saboda gobe.
Ya nisa ya ce toh ya na iya gimbiya ta bani umarni am at your service always,to adan yimun
kiss ko zan dan samu relief.
Ta yi raurau da ido kamar ta na ganinshi ta ce nidai a'a kunya nake ji.
Ya ce no zanyi fushi fa
Cikin jin kunya ta tsumbaci wayar kuma ya ji ajikinshi sosai har idanunshi sun dan rikide,
Ya ce mayar mata da shi cikin kwarewa sannan ya ce I love you good night.
Itama ta ce good night too,sannan ya katse wayar.

Sai da ya shiga bathroom ya yi wanka sannan ya sanya boxes kawai domin garin akwai zafi sai
sanyin AC din da ke ratsa jikinshi.ya na ta tunanin Aazeen din cikin ranshi har bacci ya yi awon
gabada shi.
Itama Aazeen din haka batafi minti biyu ba baccin yadauketa saboda dama shi ke damunta.

Karfe hudu daidai wayar Dr Hameed ya tayar da ita daga bacci, sai da ta yi wanka sannan ta
dauro alwala ta gabatar da ra'atanil fajiri sannan ta gabatar da sallar asubah,ba ta tashi a

wurinba sai da ta yi sallar shuruk.
Ta bangaren Dr Hameed shiri sosai ya ke yi duk ya bi aminanshi ya yi musu sallama.sai ga
kayan karin kumollo abinci kala kala babban tare ne suka jera dukkan variety na abincin,haka
akeyi a chad wannan kuma shirin Ammi ne.itama Aazeen an yi mata shiga irin na al'ada wato
dan firirit din riga iya gwiwa sai farin laffaya da duwatsu sai walkiya suke Masha Allaah abin ba
magana sai Wanda ya gani.ga skin dinta sai sulbi da walkiya saboda gyara.zaratun ma an
shiryata cikin overall fari Sol,tana hannun Ammi ita ce kawai kuma za ta raka amarya dakinta
sai Fatima acikin kawaye.

Dai dai karfe takwas kowa ya shirya domin raka amarya airport ,uncles dinta da aunties dinta
daga bangaren uwa da uba sun sanyata a tsakiya nasiha sosai suka yi mata sai Alhaji Ahmad
ne na karshe ya fara da cewa,
To diyata ina mai yi maki nasiha da kiji tsoron Allaah a gidan auren ki,ki rike amanarku ki
kyautatawa iyayenshi da 'yan uwanshi da dukkan danginshi,shi aure 'Yar hakuri ce,ki kauda
idanunki da kunnuwanki da jin ko ganin aibin da za a kawo maki na mijinki,ki sani cewa mun
aurar da ke ne ba dan mungaji da ke ba sai dan bin umarin annabinmu da yake cewa, Idan wani bawa da ya zo Neman auran'ya 'yanku mata idan kun gamsu da addininsu to Ku aura
musu wannan shi ne yafi alkhairi.sannan kuma mutumcin'ya mace dakin mijinta to iyakancin
gatan da za mu yi maki kenan saboda haka ki bi mijinki sau da kafa ,Allaah ya yi maki Albarka
ya Albarkaci aurenku.duk suka amsa da Aameen. Aazeen dai sai kuka ta ke kasa kasa sai Hakka fanna ma ta yi na ta nasiha a matsayinta na
uwa ita ma kuma hawyen take sosai.
Ya Anas ne ya shigo ya bada umarnin a fito da amarya jin wannan faruci Aazeen da sauri ta
Dada jikin mummy ta sai kuka wiwi da kyat dai aka banbare ta aka fito da ita har wurin motor..
Motor da aka ta nada mussamman dan amarya da ango aka sanya ta ,motoci kusan bakwai ne
kuma suka yi musu rakiya zuwa airport duk tsowon tafiyar kuma sai fesa turare su ke yiwa
jama'a duk cikin motor kamshin turaruka Kala Kala ke ta shi.a haka har aka iso airport manya
mata sai guda sukeyi.angonma ba laifi ya yi shiga na al'ada babbar riga dau ngashau da fula
yaudi mai matukar kyau duk cikan wajen ya fito daban acikinsu.bayan angama yin screening din
kayayyakinsu sannan duk suka shiga musabahar hannu da juna na bankwana.
Sai da suka jira jirgin ya daga sannan suka koma gida.

Ango da amarya kujeransu a jere da juna sai Ammi da Fatima suma suna can gefe kusa da
juna.sai dad dinshi da kaninshi suma suna kusa da juna.tun da suka shigo jirgin Aazeen kuka
take babu sausautawa sosai yashiga cikin damuwa ganin kukan da take,ya kwantar da kanta
bisa kafadarshi yana lallashinta da hankali yake mata magana cikin taushin murya,shhhhhi kiyi
hakuri I am there for you,nasan kinyi missing gida amma kuma ni bazan ji dadi ba wannan
kukan zai iya sanyaki ciwon kai so take heart na yi maki alkawari,ba za mu dau lokaci mai tsayi
ba za mu koma ziyara.

Awa goma sha biyu suka yi a wannan jirgi sannan suka sauka a France,sai suka kwana da safe
suka kuma daukan hanyar USA.sai kusan karfe goma sha biyu suka landing a babban birninsu
wato Florida,anan suka yada Zango gidan da suka sauka babban gida ne mai part uku ginin ya

tsaru dai kamar ko wane gini dake America akwai tsari.daidaikun mutane ne suka tarbesu
saboda yanayin rayuwarsu basa shiga rayuwar kowa,mind the own business.part na farko su
dad ne suka zauna,sai na biyu su Amma na uku kuma ango da amarya.

Sai da su dan nutsu sannan aka kawo order abinci da abinsha Kala
Kala,sai da ya lallashata ta danci abincin kadan.
sai kusan karfe biyar ammi ta hafa wuta a irin gawayin China da ake kunnawa sai ya Kama da
wuta acikin karamin kasko ta hurashi,kabbasa n da suka so da shi mai naduwa ta warware ta
kifa kayan Aazeen akai,sannan ta umarceta da ta yi wanka,bayan ta fito jikinta danye haka ta
mika mata kaskon wutar da ta zuba turarukan wuta Kala daban daban, Sai da ta tabbatar turaren ya ratsa dukkan jikinta sannan ta mika mata kulaccam da jannaniye
da musuk ta shafa dukkan jikinta,duk wannan shiri kuma a part din su Ammin sukeyi domin sai
dare za su kawo ta shashinta.
Shima uban gayyar shiri sosai ya yi duk yabi ya yi decorating dakin sai wani creative da ya yi a
kasan dakin ya rubuta I love you forever.duk suna tsaye ba za ka gane meye a rubuce ba sai ya
yi sign da tap me.
Sai akan gado ma duk ya zuba jajayen flowers masu shape na heart abin gonin ban sha'awa.

Sai kusan karfe takwas suka kawota lokacin Dr Hameed ya tafi masallaci sallah,yana zuwa
kuwa abin da yayi tozali da shi kenan Aazeen laulube da laffaya baya ganin komai nata sai
gyalen cikin zuciyarshi ya ce what a surprise,nadauka ba za Ku kawomun ita ba ai, ya ayyana a
zuciyarshi.cikin girmamawa ya gaishe da ammi,sannan ya juyo ga Fatima,ya ce sannu da kokari
Fatima ya gajiya ?
Ta amsa da alhamdulillah.gaba daya sai nan nan yake ya kasa sukuni har Ammi ta gane
yanayinshi sai ta ce da Fatima tashi mu koma sai da safenku sannan su ka bar part din.
Su na fita ya yi sauri ya matso kusa da ita sosai har ya na jin hucin numfashin ta.
Kanta a kasa kuma a rufe sai ya ja luffayan ya bude kan nata ya ce,ki dago fuskarki ki duba
angonki please.
Ta dan dago ta dubeshi ido cikin ido ya yi mata kyau sosai sai ya ce ki ta shi ki dauro alwala mu
gabatar da sallah.
Ta,ce ina da alwala sai da na idarda sallar isha'I muka zo.
Ya ce fine bismilaah za mu gabatar da sallah raka'a biyu domin Mika godiya ga mahaliccinmu.
Sai da suka idarda da sallah sannan ya Kama kanta ya yi addu'o'I,sannan ya yi mata tambayoyi
akan addininita.
Duk a takure take da yanayin da yake shige mata sai yadan ja luffayar ya ce wannan lullubi
haka ki bude kisha iska mana,ya na warwarewa sai,gashi riga rub fitil da shi da babu duk
dayane aiko baisan sanda ya ce Tabarakallahu Ahsalkhalikin ba, ganin yanayin surarta.a take
kuma ya dimauce ba shiri ya shiga sarrafata tun tana jan jikinta ta na kuma bashi hakuri saboda
gaskiya ta tsorata da shi sosai. a cikin wannan dare dai ya mallake ta ta zama nashi na har
abada sai Albarka yake samboda mata 100% ta yi sai sumbatu ya ke sirrika ne tsananin miji da
matarshi gaba daya ta galabaita domin ya murza ta son ranshi.yanayin da take ciki batada
bambamci da budurwa saboda gaskiya sirrikan Ammi ya yi dari bisa dari.

*comment and share*

⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐


*WACECE NI*




✍by

*Fateema Muhammad Suleiman*
Email fmsuleiman743@gmail.com
Wattad teemacool2020



*KAINUWA WRITERS✍ ASSOCIATION*
```{United we stand and succeed;Our ambition is ton entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*page* 2⃣5⃣&2⃣6⃣


*wannan page naku ne masoya Aazeen amma wadanda suke comment*


Sai kusan asubah ya saurara mata, bakinta baigajiya da rokonshi da magiya amma duk da
haka sai da ya yi ta ribatanta kusan sau hudu sai da ya dawo haiyacinshi sannan ya gane aika
aikan da ya yi.
Idanuwanta luhu luhu duk sun kumbura saboda kukan da tasha,ya shiga lallashinta da bata
baki.

Cikin tattausan murya kasa kasa a hankali kamar rada ya ce Allaah ya yi maki albarka hakika
yau kin shayar da ni zuman da

7 / 18