Author : Fatima Muhammad Suleiman Category : Romantic Hausa Novels
qur'an sai naga sabanin abinda iyayenmu su ke fada
mana sai gani ma nayi musulunci kiyaye rai yake ba kashewa ba.
wannan shi ne dalilina na son musulunta.
Mr suhaib ya ce Alhamdulillah da ma mu haka muke so mutum ya fahimci addini da kansa
sannan ya karbi kalmar shahada.yanzu ka shirya ne za ka karbi kalmar shahada ko kuma za
mu baka dama ka kuma fahimtar addinin sosai?
David ya ce na shirya ina bukatar a bani kalmar yanzu.
Mr suhaib ya sanar da jama'ar da ke wurin ga dan uwa yanason ya musulunta.
suka maso kusa da shi Mr suhaib ya na fada mashi kalmar shahada shi kuma ya na
maimaitawa har ya kammala sai duk 'yan wajen su ka sanya kabbara tare da rungumar David
su na cewa Alhamdulillah Barka da shiga addinin gaskiya Allaah ya kuma shirya da Kai ya
kuma fahimtar da Kai addini.
dai dai lokacin magariba ne to aka nuna masa yanda ake alwala sannan su ka nufi masallaci.
Su na idar da sallah sai ga hawaye daga idanuwan David.
Da sauri Mr suhaib ya matso kusa da shi ya na tambayar meye yasanya shi kuka?
David cikin jinjina Kai ya goge hawayen sannan ya ce ,
Wallahi yau zuciya ta, ta shiga wani irin yanayi da bazan iya kwatanta ma ka ba. Sai godiya da
zanyiwa Allaah da ya shiryayar da ni zuwa ga wannan tafarki madaidaici.
Sai ya kuma Kama hannunshi su ka rungumi juna har su ka bar masallacin da murmushin farin
ciki a fuskarshi da ganin shi za ka tabbatar ya na cikin matsanancin farin ciki.
**********
Yau kwana goma kenan da zuwansu mummy da misalin karfe tara na dare, sun hadu dukkansu
har da su Mr suhaib saboda su ma basu koma kasar su ba su na jiran *Aazeen* ta haihu
sannan duk su koma kasashen su toh gashi a wannan dare *Aazeen* ta fara jin matsanancin
ciwon mara da ma tun da yamma ta ke ji kadan kadan amma ba ta fadawa kowa ba sai yanzu
da abin ya ke so yafi karfinta haka aka kaita asibiti.cikin gaggawa aka karbeta,saboda tun a
gida *Hajja fanna* ta yi ma ta V.E ta na seven CM ne kuma su na zuwa ba su wani dauki lokaci
ba ta haife yarinya Mai kamanta Kamar antsaga Kare sai dai farin da ta dauko na turawa hakan
ya na nuna sperm donor din da aka yi ma ta inseminating din bature ne ana ba ta diyar ta ke
wani irin so ya ziyartar ci zuciyar ta sai yanzu kuma ta tabbatar da haka soyayyar uwa ta ke ga
danta take duk wani wahala da tasha ya kauce a jikin ta haka ta ringa kwararo addu'o'i ta na
yiwa 'yarta Allaah Kai ne ubangiji na ina kan wa'adinka da alkawarin ka ina kaskanda da Kai
kankantar da Kai na mai lafiya a gare ka ,ya Allaah na rokeka da sunayenka ka kyawawa da
suffofinka tsarkakku,ina rokonka roko irin na miskinai,kada ka kama ni da laifin da na yi cikin
rashin sani, ga wannan kyauta da ka yi mun ka shiryar da ita zuwa ga tafarkinka madaidaici da
bin sunnar annabinka Muhammad sallallahu alaihi wasallam,sannan ta yi ma ta huduba.
*Hajja fanna* ta karbi baby kowa da ya ke wurin sai da ya karbeta su ka dinga sanya ma ta
albarkacin bakinsu .
haka gari ya waye aka sallame su, su ka dawo gida kowa ya na farin cikin *Aazeen* ta sauka
lafiya. Sun bi sunnah a ranar Mr suhaib ya radawa yarinyar sunan sayyada Fatimatu zahra diyar
ma'aiki sallallahu alaihi wasallam.
*vaishal* ta daga ta sama ta ce Allaah ka raya ma na *zaratun*
flash back asalin yanda labarin ya faro kenan......
idan kun tuna,tube number 489 da *zaratun* ta ke neman bearer din wato asalin babanta kenan
muje zuwa dai, ga yusuf a gefe daya da auntie maryam......
*share*
*comments*
⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐
*WACECE NI*
✍by
*Fateema Muhammad Suleiman*
Email fmsuleiman743@gmail.com
Wattad teemacool2020
*KAINUWA WRITERS✍ ASSOCIATION*
```{United we stand and succeed;Our ambition is ton entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*Fans kuyi hakuri da rashin ganin rubuta na akan lokaci hakan ya samo asali ne bisa zazzabi
da nasha fama cikin kwanakin nan nayi matukar farin cikin ganin add u'o'inku kuma nagode
sosai da sosai Allah yabar zumunci*
*page* 1⃣7⃣&1⃣8⃣
Hmmm su Aazeen da baby haka ta rungumi diyarta a kirji tsananin so ne fal cikin ranta
soyayyar 'ya da mahaifiya kenan satin su biyu da haihuwa jikin yanzu normal toh sun fara
shirye shiryen barin kasar...
Yau sunje follow up wajen Dr Hamid mutumin Nigeria ne amma haifeffen garin Birmingham aiki
ya kaishi san Francisco, kasancewarshi kwararren likitan mata gynecologist...shi ne kuma ya yi
conducting ceaserian sectioning...tun kuma a lokacin ya ji son Aazeen din ta sirgo cikin
zuciyarshi..ya yi ma zuciyar tashi alkawarin furta ma ta son ta idan ta zo next visit dinta kafin su
bar kasar.
Sai ga shi yau da baby ta zaratun yarinya bum bul kyakkyawa Mai shiga rai.
Haka yagama musu duk abubuwanda suke bukata sannan ya karbeta ya sanyata bisa
kafadarshi.Aazeen da tun farko ta sargo da kwallon kurilla da yake ma ta ,tadai sunkuyar da
kanta kasa ta na wasa da 'yan yatsunta na hannun dama ya yinda ya Kira sunanta cikin wata
siga da ba ta taba jin wani mahaluki ya kira sunanta ba.domin dukkan tsigan jikinta ya amsa da
kiran.
A hankali ta amsa ba tare da ta dago kanta ba. gaskiya tana ganin girmanshi saboda a takaice
zai kai shekaru arbain senior bachelor ne amma bai taba aure ba.
Ya ce,Aazeen so nake ki dago kai sosai ki dubani maganan da zan maki mai muhummanci a
garemu.kinga ke yarinya ce naso nafara tunkarar iyayenki kafin in maki magana but na danyi
tunanin hakan kamar tauyemaki hakkine,I just make my mind to express my feeling about you
duk da ke yarinya ce ina sonki kuma da aure.kinga idan ki ka aure ni zaratun ba za ta tashi da
bakin cikin rashin mahaifi ba...na baki lokaci daga yanzu zuwa gobe na ke son jin amsa don
bana so yadauki dogon lokaci,nima ina son ganin mace kusa da ni kuma nima ina son zama
baba tunda ga yaran cikina ma anzama mama yana referring ita kenan da kayataccen
murmushi yakarasa magananshi....
Ya mike da zaratun a hannunshi ya ce, muje in sauke ku ba sai kin kira driver ba.
Ta mike biye da bayanshi har suka isa car park din dai dai gunda an rubuta Dr Hamid
zaibaddeen shi da kanshi ya bude mata motor,kusan tare suka shiga ya yi wa motor key suka
bar harabar hospital din.ya na dan taba ta da hira jifi jifi take maido mashi amsa har suka iso
gida...
Ta yi mishi godeya sannan ta fito tallefe da zaratun,ya ce take care sai naji amsar ki..
Ta dan lumshe ido ta dubashi ido cikin ido bakinta dauke da murmushi har dimple dinta sun
lutsa ciki ta ce toh thanks safe journey.
Ta shiga gida tana ta jujjuya maganganunshi cikin ranta.babu (owa gidan duk sunje shopping
shiri suke sosai domin basu da isheshshen lokaci ta shimfida zaratun da har yanzu ke bacci
acikin baby bed dinta sannan ta sauya kayan jikinta zuwa na zaman gida,ta kwanta akan tree
sitter kiran vaishali ta shiga yi ringing na biyu sai ta daga sai ta ce habibty kina part dinku ne ko
kema kintafi shopping din?
Ta ce yes ina nan ba inda naje kin dawone?
Ta ce eh kisameni yanzu.
Da sauri ta sanya takalminta sai r&s gyale da ta yafa ajikinta cikin sallama ta shigo falon tare da
fadin barka da dawowa dear hope lafiya kira cikin gaggawa haka?
Ta ce ba lafiya ba habibty neman shawara ne kiji Dr Hamid fa he is madly in love with me kuma
serious relationship that lead to marriage ya Kika ce Anya zan iya aure at this situation da nake
ciki?
Tsawon lokaci vaishali tana juya zancen sannan ta yi dogon nazari vaishali yarinya ce amma
akwai dogon tunani wat a shawarar idan ta yanta ba za ka tabacewa ita tayishi ba akwai tunani
sosai shi yasanya Aazeen ba ta taba yanke hukunci ba tare da ta shawarce ta ba.
Ta nisa! ta ce shawarar da Zan bayar kawai ki amince ko dan wannan cheeks din ta nuna
zaratun tana murmushi.
Kinga nima David oh! Na manta yanzu dai ya ce, na dinga kiranshi da Muhammad Al'ameen.
Ya dage shifa aure ya ke so kuma baya son daukan dogon lokaci kinga mu amince kawai mu
aure su hakan zai bamu daman sake zama cikin gari daya ko kuma country daya ba za mudai
yi nisa badai still we are together for good
Aazeen ta ja dogon numfashi ta ce to dear bari mummy ta dawo ko za ta amince kuma Ina fatan
hakan Allah ya zabar mana mafi alkhairi.
Vaishali ta ce Ameen.
Haka suka ci gaba da tattaunawa har lokacin sallar azahar ta yi.sai da vaishali ta idarda sallah
sannan ta jara musu abinci bisa dinning suna cikin ci sai ga su mummy sun dawo da niki Niki
sayayya ne masu matukar yawa.
Ita ma riskesu zuwa dinning din vaishali ta yi saving dinta sauran kuma duk suka wuce yin
harkokinsu bayan sun daga masu hannu su ma suka yi masu sannu da dawowa.
Mummy ta ce sannu diyata kindawo taya'yaruwarki ko? Kai Allah ya kuma Kara hada
kawunanku..a tare suka hada bakin fadin Aameen.
Shiru kowa Yana cin abincinshi sai vaishali ta katse shirun da cewa mummy Dr Hamid ne ya
maido Aazeen gida Ku ma ya bata assignment wai sonta ya ke yi da aure ya so ya tunkareku
tun farko anan ta tsakaita da magananta.ta na kuma jin shakkar abinda mummy za ta ce!
Murmushi ta yi Mai kayatarwa sannan ta ce Ku dai kuce kawai daga ke har 'yar uwar taki so ku
ke Ku sake samu yin kyawarku wanda har zaifi na da tunda wannan na zaman aure ne na din
din din.to sai dai anyi shawara da iyayenta idan har sun amince anyi bincike akanshi toh mace
dama ai ba ta da gari.
vaishali ta yi musu sallama ta ce sai dare za ta kuma dawowa.
Da daddare misalin karfe goma saiga Kira a wayarta bakon number ne tayi ringing har ta tsinke
taki dagawa saboda dama ita ba maison damuwa bane sai kira aka kuma yi kusan za ta tsinke
sannan ta daga amma sai tayi shiru a wancen bangaren.
Ya ce princess bakya daga layin da baki sani ba ko? To Hameed ne, how was your day?
Sai a sannan ne, ta gane muryarshi.cikin sanyin murya ta ce Alhamdulillah n urs?
Ya ce,boring duk cikin tunaninki na yini.na kasa jiran ki zuwa safe don Allah naji mai kyau can't
wait to see you at my side I love you and I also do love you with all my heart please ki ce mun
wani abu wanda Zan kwanta Ina jinshi cikin raina.
Ta yi shiru ita dai har ga Allah ta na sonshi amma kuma tana jin nawunshi sosai, saboda
gaskiya wannan shi ne first love dinta duk sauran samari da suka dinga yi mata caa ba ta taba
kula su ba,saboda bata yardada su ba,cewar ta duk bad boys ne.to ga Hameed kuma serious
and responsible man cos he is man enough.ta ce gobe in aha Allah zan baka amsa.
Ya ce,nasani ina neman sweet ward ne for now.
Batasan maye za ta ce ba ita kam,ta yi shiru.
Ya ce,kinyi shiru koh sarkin kunya kada ki damu zan cire maki wannan kunya nan bada dadewa
ba idan nayi sa'a ammallakamun ke.
Ya jita tana murmushi kasa kasa,sannan ta ce okay ahankali hakan ba karamin ji ya yi ajikinshi
ba, saboda ta fadane with her soft and husky voice dinta.
Ya ce seriously zaki gane hakan soon yanzu dai ina baby na take? hope kin bata abinci kafin ta
kwanta?
Cikin ranta ta ce jimun mutum sai da kagama shagalinka za ka tuno ta hmm! ta juyo ta duba
baby bed din lub zaratun tana ta barci ta ce eeh gashi tana bacci lafiyanta.
Ya ce,gud haka ya yi kyau good night take care.
Itama ta maida mashi da good night too have a nice dream.
Ya ce,okay dream of you koh?
Ta ce,yes ita dai kawai so take ya rabu da ita tayi bacci don bata saba kaiwa har warhaka ba
batayi bacci ba.
Sai ya ce, me too ina son ayi mafarkina gobe kuma zan tanbaya akai sai da safe sannan ya
kashe wayar.
Ta ja dogon numfashi ta lumshe ido tana imagining dinshi cikin ranta a haka har bacci barawo
ya yi awun gabada ita........
*please share and comment*
⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐
*WACECE NI*
✍by
*Fateema Muhammad Suleiman*
Email fmsuleiman743@gmail.com
Wattad teemacool2020
*KAINUWA WRITERS✍ ASSOCIATION*
```{United we stand and succeed;Our ambition is ton entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*page* 1⃣9⃣&2⃣0⃣
Komai ya yi farko dole ya yi karshe yau rana ce da su Aazeen za su yi bankwana da san
Francisco zuwa kasar su na gado.Aazeen da vaishali kan kuka ba'a magana.sunyi kuka har
sun gode Allaah,saboda rabuwa aminiya abokiyar shawara da tsananin shakuwa, har iyayen
na su sai da suka sanya a kuka.rabuwa ne da basu da tabbacin sake haduwa idan ba ikon
Allaah ba.dukkansu suna airport ko wannensu kuma yana jiran tashin jirgin kasarshi ne, David
(Mohd Ameen) da Dr Hameed ma suna tare da su,shi dai muhd Ameen ya samu karbuwa Dari
bisa dari daga wurin Mr suhaib kuma anyi alkawarin Sanya ranar aure da zarar sun je
Pakistan.duk da shima Hameed din sunyi zai je Nigeria domin neman auren Aazeen din.haka
suka yi kusan awa daya, kafin jirginsu ya daga bankwana da masoyi ba Abu ne mai sauki ba sai
dai hakuri tunda ya za ma dole hakan za ta faru.Dr Hameed ne ya matso kusa Aazeen sannan
ya sanya zobe a hannun ta.ya ce,
All my life I have searched but never found someone like you,who is so perfect for me. With
you I do not need to worry about the future.I love you with all my heart I promise to give you my
endless love,in sha Allaah ina nan tafe zuwa gare ki,ki rikemun soyayyata da zarar na je kasar
ku,zan yi duk iyakan kokarina dan ganin na mallakeki in sha Allaah sai da igiyar aure zamu
dawo zuwa wannan kasa.kada kusamu damuwa keda vaishali kam mutu karaba ne.....hawaye
shar daga idanunta ta ce in sha Allaah na yi maka alkawarin duk rintsi duk wuya ina tare da
kai,wannan alkawarine,take note.
Ya ce nagode meye za kiyimun Wanda zan dinga tunawa da ke kafin nazo Nigeria?
Ta ce bear in your mind I am yours and promise to be yours forever I love you so much..sannan
ta Mika mashi zoben da ke hannunta na azurfa.
Ya ce nagode da wannan kyauta bazan ta ba manta shi ba. da yake yatsunta sirarane,sai ya
sanya a dan karamin yatsanshi.ya yi kissing zoben sannan ya yi blowing iska zuwa gare ta
nuna alamun ya gamsu da kyautar da ta mishi.
ita ma ta yi murmushi sannan ta jinjina kai ta furta ahankali I am gonna miss you for a while.....
Ya ce, its just for few days ne da zarar na kammala abubuwanda nakeyi za ki ganni....haka har
ta hau matalar jirgin su na dagawa juna hannu har suka daina kallon junansu.
Ta bangaren vaishali ma hakanne ya kasance.
Sun yi landing a Nigeria misalin karfe biyu na yamma saboda sai da suka kwana a France
sannan da safe suka kama hanyar Nigeria....daga abuja international airport sai Maiduguri
international airport mutanen da suka zo tarbarsu ba abin magana bane daga familin mommy
har daddy babu Wanda aka bari a baya..kowa kuma turuniyar son ganin Aazeen yake ya Anus
da ta Almustapha su ne kan gaba.sai washe baki suke suna kuma mayar da gaisuwar da family
friends dinsu suke musu.Aazeen kam sauran fuskokin ma ta kasa ganesu.har suka je gida
zance dayan nan ne suke ta maimaitawa da ganinsu duk suna cikin farin cikin ganin gudar
jininsu.kam dangi sun hallaru a wannan makeken gidan Alhaji modu,basu barsu sun huta ba
sai kusan magriba kowa ya watse sai kannen Hajja Bintu da Alhaji modu da suka rage domin
su kam zasu kwana a gidan domin za a gabatar da family meeting.
Gaba daya Aazeen ta zama kamar wata bakuwa a gidan nasu tun da ta shiga bedroom da
zaratun bata fitoba duk kuma wadanda su ka zo yi mata maraba da zuwa sai dai su shiga su ga
is he ta sannan su fito anyi anyi ta fito cikin dangi taki,sai su ka ce a bar ta yanzu tana
bakuntane idan ankwan biyu za ta washe ta Saba da mutane...ya Anas ne iske ta tana ta danna
wayarta,
Ya ce, sis ya dai you have to be feel free and be at home fa dan na lura baki son zama cikin
mutane wanda duk wannan Jama'a