WACECE NI BY Fateema Muhammad Suleiman-1.pdf

Author :  Fatima Muhammad Suleiman Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   11 / 18

30K to 33K   out of 52.9K words

direct bayan na rufe kofata har hannuna Yana
karkarwa da nake dailing number yusuf bata shiga, is unavailable yake cewa
Haka nayi ta trying amma bata shiga zuciyata ta rayamun cewa kodai yusuf dama yaudarata
yake baya sona.wata zuciyar ta ce a'a w akwai dalili koma dai ya ya zandiga trying time after
time,ganin magriba ta gabato sai na dauro alwala na fito parlor,auntie Maryam tana zaune ta
manna waya a kunnenta hira sosai take amma duk tsawon zamana banajin abinda me take
fadi dagani hirar soyayya take.har na gaji na tashi yin sallah don lokaci ya yi banjirata munyi
jim'i ba.bayan na idar na gane tana fashin sallah.na juwo na ce inajin yunwa muci abinci batare
da ta dubani ba ta ce to ki fara ci I will join you later.
Har sai da na kusan gama cin abincin sannan ta fara cin nata.zan tashi sai ta kamo hannuna na
kuma zama sai ta ce zaratun.
Na amsa da na'am

Ta kamo hannuna dake ciwo tana kallo sai ta ce my Angel kinsan cewa ina sonki bazan so na
cutar da ba ko wani irin abu zai cutar da ke kuma zanyi iyakan kokarin ganin na kawar da shi,ke
yarinya ce bakisan komai ba zuwa gidan namiji ba muharraminki ba haramun ne koda kowa
saurayinkine ko mijin da zaki aure matukar ba'a daura maki aure da shi ba ballema na ki case is
different coz yaushe zaki iya da default person.kinga komai da komai ke zaki mashi sai kin fara
samun yara tukun za ki gane kuskurenki idan har kika biyewa zuciyarki Kika amince ya aureki
wanda nasan da wuya hakan ya kasance ma.ki nutsu ki koma hankalinki sannan ki tattara
wannan yusuf din ki cireshi daga ranki tun kafin sonshi ya kawo maki illa.
Idan ba abinki ba ga Khalid nan yana mutuwa akanki amma kinki tsayar da tunaninki waje daya
wai ke tausayi da soyayya ko.toh yanzu Ina kike ganin zaki samu inda yusuf din ya tafi?
Ki duba fa dan butulci bayan ya konaki sannan yabar gidan ba tare da ya sanar maki inda za shi
ba.
Tun da ta fara magana ban sanya mata baki ba ,sai da naga tayi shiru sannan na Fara magana
da cewa,auntiena nasan kina sona nima kuma ina sonki,maganar yusuf kuma babu yadda na
iya zuciyata ce tayimun laifi wajen sonshi kuma wallahi ya fadamun cewa he is not default,zaiyi
regain health dinshi aikine akeson za 'ayimashi to kudaden ne suka kasa biya amma yanzu
akwai wanda yadau nawin yin aikin,Ina ganinma can suka tafi wallahi ya yi ta kiran wayata dazu
bandaga saboda muna tare da khalid ko maganar tawa bata bari na karasa ba.
Ta ce kinjiki dai ana maganar lafiyayya wa yake kawo abin da babu tabbas ko da anyi aikin Ina
Kika taba ganin spinal cord injury ansamu waraka

Na ce kina musu da ikon Allaah ne kuma ai shi nashi mino injury ne in aha Allaah zai warke
nidai abu daya nake bukata awajenki give me courage ni kuma zanji da sauran wallahi ba na
nufin tozar taki ko kuma yi maki snatching naga nine tun farko kin nuna bakyayi da shi wallahi
kuma taimakonshi nake so nayi bayan ya nemi taimakon nawa kinsan halin zuciya daga baya
kuma muka koma soyayya Wanda bansan lokacin da tayimun dirar makiya ba.Ina wannan
magana ido kuma duk akanta Ina nazirin yanda take sauraron maganganuna.

Ba ta kuma cewa komai ba kawai ta ce toh Allaah ya bada sa'a,amma nikam kada ki sanyani
cikin shafgar yusuf dinnan.
Banyi magana ba naja bakina nayi shiru.da misalin karfe tara, na yi mata sallama na shiga
bedroom shirin bacci nayi sannan na kira Humaira Muna Dan yo hirar school tana bani labarin
yanayin makarantarsu,nima na dan bata namu makarantar sannan na kira dad naci sa'a suna
kusa da mummy sai da suka Dan yimun nasiha irin na iyaye da in kula da kaina da karatu na ce
yaushe zaku zo mana visiting dad ya ce very soon idan mun sanya lokaci za mu sanar da ke na
ce I love you so much miss u.shima ya ce we love you too dear.
sannan na katse kiran.number Yusuf na kuma kira still is unavailable gaskiya nashiga damuwa
sosai wannan wane irin abu ne haka amma koma meye ke fararuwa he should at least let me
know,kamar in kuma komawa gidanshi nake ji amma babu hali.inacikin zancen zuci sai ga kiran
Khalid din ta shigo kamar kar na dauka saboda Sam bani da mood din yin magana da kowa at
this moments.
Muryata can kasa na amsa sallamarshi

Cikin damuwa ya ce ya hannun hope yayi sauki?
Na ce eeh Alhamdulillah
Sai ya ce ya muryarki somehow kodai hannun ne har yanzu na lumshe idanuna na ce a'a kawai
na gajine kuma inajin bacci ya ce bari na barki ki samu Hutu ya ce I love take care .
Na ce loves you too thanks.
Daren ranar haka na kwana da mafarke mafarke barkatai babu Wanda na rike ko daya tun
asubah na kuma kira number har yanzu dai bata shiga,komai cikin sauri na gabatar saboda
kaguwan zuwa gidan yusuf .....ko tea na kasa sha auntie Maryam tana tambayata irin wannan
sammako haka kamar wanda zaibar garin?
Na ce ehh ina da seven ne.
Ta daga Kai ta dubeni daga sama har kasa cikin kallon tuhuma amma Bata ce komai ba kawai
ta ce yau zan je wurin supervisor na,na waro ido na ce kai! Auntie rancen ma da Kika je baki
sameshi ba ance sai yamma lis yake zuwa?
Ta ce eeh to ya zanyi kinga samples din tun yaushe aka kawo kinsan idan har sun dade
baigani ba karshenta yayi rejecting so ni kuma ban shirya yin asarar nakudan kudade ba.
Ki dauka wancen kawarki na hostel meemah Ku kwana tare da ita nikam idan ta kama kwanane
ma zan kwana muhadu ya samun hannu.

Na ce to safe journey.

Ta ce thanks take care.

Na tare taxi nahau unguwarsu yusuf din na ce ya kaini tun daga kofar gidan na gane yadda
muka barshi jiya haka yake ina cusa kaina sai wani mutum zai fito daga dakin yusuf shirin kulle
kofar dakin yake nayi sauri na iske tare da tambayar mai dakin wato yusuf?

Sai da ya gama nazarina sosai sannan ya ce,ayyah yusuf an mayar da shi kauyensu tun jiya da
yamma naji yana maganar ko sun samu mai maganine,ni makocinshi ne ya barmun gidan nan a
hannuna ya ce akwai sako da yabarmun ya ce akwai wata da za ta zo gidan na taba sakon duk
lokacin da ta zo please ya ya sunanki ya tambaya?
Na ce zaratun.

Eeh haka ya ce bara na dauko maki sakon,na tsaya jiranshi sai gashi da dan takarda ya
mikamun sannan ya Kama hanya ya fita nima nabi bayanshi muka fita tare.

Ina shirin bude takardar sai kiran Khalid,ya na tambayata Ina nake?
Nayi mashi kwatancen gunda nake ko minti biyar ba'ayiba sai gashi nayi mamaki sosai da
ganinshi Ina murmushi na ce sai kace dama kana wajen sometimes Ina ganinka kamar
monitoring spirit kake na fada ina tabe baki sai ya ce ai dole nayi tattalin abata kafarki
kafata,yanzu ma na zo ne muje ki zabi motor saboda gaskiya na gaji da ganinki kina hawa
motar haya.

Na dafe kirji na ce nidin gaskiya I can't believe it,
Cikin farin ciki na shiga motar,bai zame ko Ina ba sai gunda ake sayar da motor,motocine Kala
Kala new model burjik awajen ya ce ki zabi duk Wanda ranki ke so...

Kasa zaban motar na yi ina ta ruwan ido sai cen wata red color na zaba kawai mukullin Motar
aka mikomun Wanda yake mikamun mukullin ya na murmushi ya ce favorite color na oga kenan
kika zaba,bansan wani oga yake nufi ba saboda ga khalid din har ya nunamun naby blue na ce
banason color shine nadau red colorn...bakina bai gajiya da yi mashi godiya ba shiko sai
murmushi yake. auto ne motar, kuma a take na fara driving a hankali muka jira da khalid muka
Kama hanyar gida.......duk da ina farin cikin samun motar to dayan bangaren zuciyata tana
ayyana sakon yusuf da na boye acikin Jakata.......















*please comment share and vote*


⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐


*WACECE NI*




✍by

*Fateema Muhammad Suleiman*
Email fmsuleiman743@gmail.com
Wattad teemacool2020

*KAINUWA WRITERS✍ ASSOCIATION*
```{United we stand and succeed;Our ambition is ton entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*page* 3⃣5⃣&3⃣6⃣




*Tambaya* shin mace mai jinin biki zata zauna har kwana arba'in ne baza tayi sallah da azumi
ba?ko kuma Abin Lura daga gareta zatayi tsarki ,tayi sallah kuma nawa ne mafi karancin
kwanakin da zata tayi kafin tayi tsarki?

*Amsa*
Mace mai jinin biki bata da kaiyadadden lokaci sai dai duk lokacin da jinin ya zo Mata zata
zauna baza tayi sallah ko azumi ba sannan mijinta bazai iya saduwa da ita ba.amma idan taga
jinin ya dauke,wato ta tsarkaka ko da kafin ta cika kwana arba'in ne ko da jinin iyakacin kwana
goma kawai yayi ko kwana biyar sai kawai ya dauke,to sai tayi wanka tayi sallah da azumi kuma
mijinta zai iya saduwa da ita babu laifi cikin hakan.
Sai dai abin da yafi muhimmanci shi ne jinin biki al'amarine kebantacce kuma hukuncinsa Yana
ratayuwa ne da shi ,wato idan jinin yazo hukuncinsa Yana nan baza tayi sallah da azumi ba
kuma mijinta bazai iya saduwa da ita ba.duk lokacin da tayi tsarki to ta wofanta daga
hukuncinsa.



Duk da na dade da koyar motar sai yau najita kamar sabon koyo koda yake hakan yadanganta
da dadewa da nayi banyi tuki ba kowane abu idan dai practical aspects ne idan ka dade baka yi
ba za ka manta,khalid har zolayata yake yi wai kawai na sanya L wato laner.na dan harareshi
cikin wasa na ce anki din har da dan zunguro bakina duk wannan hirar munayine shima yana
cikin motarshi amma muna kusa sosai.daidai kofar gidanmu mukayi parking tun kafin na shigo
sai ga auntie Maryam ta fito da shirin tafiya turus taja ta tsaya ganin Ina nuna mata car keys din
hannuna tare da pointing din motar nuna alamun na wane,shi kuma khalid ya fito a motarshi ya
harde hannayenshi duka biyu a kirjinshi,Yana ta kallonmu cikin nuna sha'awar hadin kanmu
sosai ta nuna farin cikinta sannan ta gaishe da khalid tayi mashi godiya ta ce my angel zan tafi
sai na dawo zamuyi celebration da lunching na motar Muna rungumi juna tayimun kiss a goshi
na ce miss you ta ce miss you too,har ta fara nisa sai khalid ya ce na dakatar da ita mukaita
park....sai da na shigar da motar cikin gida na kulle kofa sannan dukkanmu muka kama hanyar

park domin train zatabi.sai da muka jira tahau train din sannan muka kama hanyar komowa gida
kawai na ce mashi ya saukeni a school saboda Ina da 2-4 human physiology lecture.Muna
tafiya Yana ta jaddadamun soyayyar da yakeyimun ya ce please zatatun inason ki tsayar da
hankalinki waje daya ki fadamun gaskiya akwai wanda kuke soyayya ne bayan ni?
Nayi shiru kuma na sadda kaina kasa saboda bani da amsar da zan bashi.
Ganin banida niyar magana ya kuma kiran sunana da wani irin husky voice dinshi mai tayar da
hankalin wanda akayiwa,ya ce look at me what do you encounter in my eyes?
Da sauri na dauke idona daga lumsassun idanuwanshi da suka rine suka zama ja daganinsu
tsansar sona ne aciki.

Gaskiya ni ba irin 'yan matan nanne masu yaudara ko ruwan ido da son abin hannun samari ba,
once nace ina sonka I really mean it,saboda wannan dalilin ne ma na kasa sakin jiki da khalid
ba,wanda shi kuma khalid ya kasa fahimta ta ..cikin sanyin murya sannan a hankali dama tun
asali bani murya sosai na ce khalid gaskiya bazan boye maka ba akwai wani da muke soyayya
kusan waya shida kafin haduwarmu da kai,amma kayi hakuri ban sanar da Kai ba tun farko
please forgive me na nuna alamun roko da hannayena.

Tsawon lokaci ya kuramun idanuwa Yana naziri da maganganuna sai ya ce naji dadi da
fadamun gaskiya,dama nasan bazai yiwu ace ni kadaine na kyalla ido akan wannan
kyakkyawar fuskarki mai annuri da wannan ass da boob din da suke jawo hankalin mai
kallonsu. Duk kunya ta kamani da wannan maganarshi ta karshen.
Ashe shi ya sanya duk wucewar da zanyi agaban maza sai naga suna kananan maganganu Kai
har lectures din suna kawomun hari amma duk babu wanda na bashi fuska,bana manta ranar
da Muna practical a lab to ni Ina kusa da wani supervisor da yake duba ayyukan da muke na
sargu da kallon kurilla da yake yiwa kirjina muna hada ido yayi saurin kawar da kanshi yabar
wajen bayan kamar minti biyar sai gashi ya dawo da wata karamar takarda ya ajiye ya tafi Ina
budewa naga ya rubuta number wayanshi sannan wai give me call and meet me at my office.
Dogon tsaki na ja,na yaga takaradar nayar. tunda daga ranar ya kullamun har yau kuma Ina
carrying course din da yake daukarmu.sai yanzu da khalid ya kawo zancen ass da boob na
gane Ashe abin da yasa duk wani namiji ya kalleni sai yayi attempting yimun magana hakan ya
sanya bana kula kowa saboda na kasa gane manufarsu a kaina yusuf kam daban yake a
cikinsu....

Kinyi shiru meye kike tunani haka?

Maganarshi ce ta dawo dani daga dogon tunanin da na fada firgigit na ce wallahi na tuna gida
ne
Yadan sako murmushi sannan ya ce cikin masoyan naki ina neman alfarma da ki sanyani star
saboda ba yadda zanyi na hanaki soyayya but sooner or later zan koyar da ke soyayyar da zaki
manta sauran samarinki cox am always lucky musamman kan abinda nake so I will do what
ever I can to have it..so wish me luck Yana duba cikin idona,gaskiya idanuwan khalid akwai

wani abu kamar magnet da yake fizgar mutum sometimes yanayin kallonshi da maganganunshi
suna yimun shige da na yusuf...sai dai yafi Yusuf tsaurin ido.
Nayi murmushi na ce wish you all the best of luck...

Ya ce thanks zan tafi idan kingama lecture give me a beep I will drop you back home.na girgiza
kaina na ce haba gaskiya wahalar tayi yawa man sunan da nake kiranshi kenan,zan kira
cab,amma karka wahalar da kanka nasan kaima kana da naka hidimomin nagode sosai da
kulawarka gareni.
Stop it,nafada maki cewa zanyi iyakan kokarina wajen cinye gasar da nake ciki daga yau ne ma
assignment dina zai fara aiki bear in your mine I am always at your service.kuma banason
yawan godiya a duk lokacin da nayi maki abu bakisan yanda kike a zuciyata bane.

Na ce to nagode sosai idan kunyi waya da neelah my regards to her.

Ya ce to,sannan yayimun sallama tare da jaddadamun na kirashi idan mungama lecture.
Na ce toh....

Sai naje hall ba mutane sosai, saboda har yanzu da sauran lokaci,sai a wannan lokaci na samu
daman dauko takardar da yusuf ya barmun ga abin da nagani...

*my soul mate*
Things were said in haste, things happened against fate, but if you do accept my apology,
everything will be better again.wallahi I didn't mean to hot you.ya ciwon hope kinje asibiti sun
dubaki? Tun ni anki a saurareni na kira likita,
Bada niya hakan ta faru ba kuskure ne,koda yake nasan ki sarai kina da sanyi hali da tausayi
wadannan halayyarki su suke karamun kwarin gwiwar cewa nima fa cikkekken mutum ne, I
reflected on the things I don't have in life but I remember I have you thats made me completed.
so ki ci gaba da rikeni da amana da soyayyar da kikeyimun ni kuma na maki alkawari zan rikeki
amana duk rintsi duk gaskiya.Na kira wayarki sau ba adadi amma baki daga ba.kamar yanda na
fada maki wani bawan Allaah ya taimaka zuwa Germany akan aikinda za'ayimun.ranar Monday
zamu tafi amma kafin nan Ina Michigan,zan kira ki idan nayi landing,ki kularmun da kanki sosai
I love you take care.....

Sai da na gama karantawa na kuma nadewa na jefa a jaka sai yanzu kuma hankalina ya
kwanta,amma toh meye yasa bai kirani ba har zuwa wannan lokacin?
nabarwa zuciyata,a haka har hall din ya fara cika dama kuma bamu wuce mu talatin ba a
wannan course din elective ne...Muna gama lecture, ina hada littafaina sai ga latifa,ta tayani
hada takardun ina tambayarta ina Arraudah? wata course mate dinmu ce kuma Muna zumunci
sosai da ita. tana hostel bata daukan wannan course,amma yanzu ki tabota a waya idan tana nan sai muje,wallahi ni
gaba daya lecture4-6 din nan ya Fara fita akaina tana magana tana yatsuna fuska.
Na danyi dariya na ce ki rabu da prof paul lafiya dai kawai amma ba kina korafin time na lecture

ba.
Na kara wayar a kunnena ringing na biyu sai ta daga da cewa yes ina nan ku tafomun da burger
a web 10,na ce toh na kuma juya ganin web din Muna kusa da wurin sai da muka saye burger
sannan najira Latifa ta dauko motar ta a parking lot muka wuce hostel.hira sosai mukeyi irin na
kawaye kowa kuma yana kawo maganar samarinshi kunsan dai taron 'yan mata,munyi ciye ciye
sosai saboda dukkan kawayenmu na hostel kowa abin da take dashi muka taba gonin ban
sha'awa.sun tayani murnar sabuwar motar da nayi.na roki Arrauda da ta tayani kwana a gida
saboda auntie maryam taje michigan wajen supervisor ta idan bata bata samu sun gama da
wuri ba za ta jira shi.sai da muka

11 / 18