WACECE NI BY Fateema Muhammad Suleiman-1.pdf

Author :  Fatima Muhammad Suleiman Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   12 / 18

33K to 36K   out of 52.9K words

idarda sallar la'asar muka dawo faculty, lecture will not hold
today abin da class rep yarubuta a board kenan,saboda haka kowa yakama haryan fita daga
hall din.Latifa taso ta saukemu a gida amma na ce zan Kira khalid.
Ta tabe baki ta ce Allaah sarki khalid ina yimaka fatan alkhairi ya dauraka akan wannan cheeks
din girl din nan domin kana sonta diyawa.nayi murmushi nasan da biyu take wannan maganar.

Baifi minti goma da kiran khalid ba sai gashi,bakin wandon jens ne da long sleeve shirt sky blue
sanye a jikinshi. Masha Allaah kayan sun karbeshi sosai cikin murmurshinshi mai ban sha'awa
ya gaisa da Arrauda itama ta amsa,da kanshi ya budemun gaban motar duk muka shiga yaja
muka tafi... Yana fadamun abubuwan da yayi bayan rabuwarmu dazu,na waro ido na ce gaskiya Yau ka
aikatu sosai kuma dama naji ance wannan level coordinator bashi da sauki,duk Wanda aka
hadashi da shi to zaisha research a field but yana bada grade mai kyau.
Ya jinjina kai ya ce hakan yana da kyau.sai da muka tsaya a hajwan khalid ne ya shiga ciki,sai
gashi da ledoji niki niki.

Daidai kofar gidanmu mukayi parking sai na mikawa Arrauda keys din kofar,ta sauka da ledojin.
sai khalid ya juwo sosai yana fuskanta ta har inajiyo hucin numfashinshi nayi sauri na ja baya
sosai.

Yadanyi murmushin abin da na yi ya ce matsorociya kawai, ganin naja baya ya ce stop it karki
fadi sannan cikin dense voice dinshi yakira sunana zaratun please kibani dama asanda
maganata agidanku mana wallahi na kasa controlling Kai na akan sonki ki tausayamun duk
lokacin da muka hadu sai nayi mafarki da ke kuma kina sanyani yin wanka.na baki sati daya kiyi
shawara akaina so zan jira feedback.ki shiga gida sai munyi waya.

Cikin sanyin murya na ce toh.sai da na jira ya tafi sannan na shiga cikin gidan.lokacin dai dai
magriba ta gabato,na tarar har Arrauda ta dauro alwala nima ban zauna ba sai kawai na dauro
alwala na fito,sai da muka gabatar da sallah muka jawo ledojin kalolin abinci ne sauran kuma
fruits ne ga gashasshshun kaza guda biyu,munci sosai. Sai da muka jira lokacin sallar isha tayi mukayi sallah. sannan muka wuce bedroom domin
baiwa ido hakkinshi,saboda gajiya ko minti goma bamu kaiba bacci ya daukemu.

Can cikin bacci sama sama naji wayata na ringing cikin magagin bacci na Kara wayar ba tare
da na duba ko waye ba jin muryar yusuf ne yasa na watsake na nude idanuna sosai karfe biyu

da minti goma dai dai.

Tun kafin ya ce wani abu na shiga yimashi kuka har da shishshika.sai rarrashina yakeyi ta cikin
wayar duk hankalinshi ya tashi,ya rasa inda zaisa kanshi saboda damuwa.shima cikin murya
kamar kuka ya ce sorry its OK,kiyi shiru ki saurareni,ya ce meye ne baby na kada kiyimun kuka
banaso meye ne yanzu toh. Cikin kuka kamar yaron goye na ce ba kai bane sai nayi shiru...sai ya ce toh am sorry wallahi
bansamu lokaci bane daga jiya har yau Muna kan abu daya sai dazu ne nasamu damar sayen
Sim card amma kina cikin zuciya ta.
You are the one, who holds the key to my heart.daga kisani kin riga kin mallakeni.yanzu na Kira
ne naji ya hannun naki? Ina fatan sakon da nabar maki ta sameki?bansan haka rabuwa da
nasoyi yake sai da na 72 hours ban sanyaki ko jin muryarki ba nasan cewa lallai wani bangare
na jikina babu.duk wannan maganar Yana yinsu ne cikin taushi murya duk yabi ya kashemun
jikina,naji duk duniya babu wanda ya kaini shiga farin ciki.what a miracles.haka na sauko da
fushin da nake da shi sannan na saki raina muka dinga hirarmu cikin nishadi nima nashiga
fadamashi irin damuwa da missing dinshi da nayi ,har kusan karfe hudu muna waya sai ga wani
Kira na shiga cikin wayanda muke babu tantama khalid ne dama ko yaushe idan karfe hudu tayi
Yana tashina daga bacci.ban damu da kiran ba har ta daina shiga shima bai kuma Kira ba dan
yasan cikin calling ne wayar ta shigo.sai da aka Kira asalatu sannan mukayi sallama ya katse
wayar.
Bayan mun idarda sallar asubah na shiga kiran number Khalid har sau biyu amma bai daga ba
abin da baitaba yimun ba kenan kodai yayi fushi ne da yaji number na is in another called....







*share vote and comment*

⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐


*WACECE NI*




✍by

*Fateema Muhammad Suleiman*
Email fmsuleiman743@gmail.com

Wattad teemacool2020



*KAINUWA WRITERS✍ ASSOCIATION*
```{United we stand and succeed;Our ambition is ton entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*page* 3⃣7⃣3⃣8⃣



*Today's Inspirational Hadith is about Punishment*

Narrated Ibn Mas`ud (RA): A man said, "O Allah's Messenger (peace be upon him)! Shall we be
punished for what we did in the Pre-lslamic Period of ignorance?" The Prophet (peace be upon
him) said, "Whoever does good in Islam will not be punished for what he did in the Pre-lslamic
Period of ignorance and whoever does evil in Islam will be punished for his former and later
(bad deeds).

(Sahih al-Bukhari, Vol. 9, Book 88, Hadith 4)

_Hold yourselves accountable before you are held to account. Know that repentance wipes sins
and what you did when you didn't know the truth will insha'Allah be eradicated by what you do
once you come to realize it._





~wannan page naku ne wacece ni fans ina ganin comment dinku sosai da sosai~



Yau asabar bamu da lecture,fixed lecture ne kuma ya ce bazaiyi holding ba saboda haka daga
ni har Arrauda bamu runsa akan gadon ba itakam chat take yi abunta .

ni kuwa tunda na kira khalid bai daga ba sai na shiga kiran auntie maryam ringing na farko ta
daga wayar,ta shiga bani labarin yadda suka karasa da project supervisor ta har yanzu kuma
baigama da ita ba,nake tambayarta sai yaushe kenan zai barki baya ganin wahalar da kike sha
ne? Ta ce ki bari kawai my angel Allah ma ya taimakeni Ina da wajen yin bakuqnta da expanses

din sai ya yimun yawa.
kedai ki tayani add u'a nasamu mugama da shi cikin wannan week.
Na ce in sha Allaah,wish you best of luck.
Ta ce thank sai munyi waya,my regards to Arrauda.
Na ce toh za ta ji.

Laptop dina na kunna na shiga duba comment din da akayi akan sakon da na tura yawanci
sunayimun fatan alkhairi ne da addu'ar samun asalin mahaifina a duk inda yake,sai kuma
wadansu kuma kamar nidince suma suna neman real biological father su,gaskiya western part
of the world ana abu sosai wani abun haushi wani ko tsantsar kafircine ke damunsu.ina cikin
duba sakonnin naci karo da wani labari akan wata cleaner da me aiki a wani five star hatel sai
taji labarin wani prince da ya kwana a hotel din sai tayi tracing dakin da ya kwana da safe
tasamu condom da yayi using cikin wannan dare tayi inserting sperm dinshi zuwa jikinta,sai
gashi after one month da tayi test pregnancy test is positive.aiko dama abin da take bukata
kenan kawai tayi kararshi kotu akan cewa tana dauke da cikin wannan prince din.

aka nemeshi da yazo court ya yi musu akan cikin ba nashi bane domin shi baima taba ganinta
ba,ta fada musu gaskiyar lamarin cewa condom din da ya yi amfani ya jefar ta dauka ta zuba
maniyyinshi cikin al aurarta,toh da alkali yabada umarnin yin DNA test hakanne cikinshi ne,aka
yanke mashi kusan dollar dubu dari biyar yabita na renon cikinshi.yanzu haka tabar hotel ta
Kama business da kudaden.duk da shi ma prince din ya ce zai daukaka kararta akan shima
baiyarda da daukar maniyyinshi da tayi ba.toh ga dai iri iren abubuwan da sukeyi.
Gashi nima mahaifiyata ta fada tarkonsu ta aikata abin da yanzu daga ni har ita muke cikin
rudani.wannan zamani da kake da nasaba da komai ma idan bakaci sa'aba dangin miji sai su
wulakantaka balle kana da abin fada.

duk tunanin ni daya nake abuna Arrauda kam da ta gaji da chatting ta koma baccinta.da hankali
na taka matalan godon na sauko kasa da yake Ina kan up bed ne Arrauda kuma take kasa
saboda ta ce ita bata iya kwanciya a sama.da yake gadon dakin irin na 'yan makaranta ne.dama
unguwar da muke na students ne kuma ginin unguwar da komai anyishine bisa tsarin
student.kitchen na nufa lokacin dai dai karfe takwas 'yan mintoci,kwai kawai nasoya sai tea
sannan na hada fruit,sai da na gama jerawa a dinning na shiga,bayi nayi wanna na sanya riga
da wanda masu kauri lokacin winter ne akwai sanyi sosai,Ina gaban dress mirrow sai ga
Arrauda ta fitomun da wayata da na barta na fito daga bedroom,number yusuf ne da ya kirani
jiya,saurin dagawa nayi saboda ta kusan ta tsinke.muryarshi a dashe kamar wanda yayi kuka
yakemun magana cikin tsorata da jin muryarshi,nima kuma tawa muryar har taba m rawa na ce
my soul lafiya naji muryarka haka?

Cikin sanyin murya ya ce nashiga damuwa ne sosai, saboda banason na rasaki ne mu
soulmate,yanayin wannan aikin da za'ayimun between do or die ne kinga idan har ba'asamu
nasara ba banida hope akanki.yanzu aka gama yimun counseling akan aikin 10% ne chances
na warkewarshi.kinga ko dolene na shiga damuwa.

Tun kafin ya karasa maganarshi zuciyata ta karaya na fara yi mashi kuka tsawon lokaci yana jin
yadda nake shishshikar kuka, bai hanani ba daga ji shima yana cikin matsanancin tashin
hankali.da kaina ta tsayar da kukan da nake yi a take kuma na zama jaruma na danne damuwar
da nake ciki saboda na karfafa mushi gwiwa cikin confidence nake maganada cewa my soul
stop negative thoughts,in sha Allaah za 'ayi aikin nan cikin nasara ,kada ka cire tsammani daga
ni'imar Allaah domin shi mai yawan gafarane mai jinkan bayinshi kuma kullum muna cikin
rokonshi samun lafiyarka,sannan kasani cewa ni a haka naganka, kuma na soka ban taba
ganinka ka taka kasa ba.asalima wannan yanayin da na ganka acikine sanadin da yasanya na
soka,may be akwai wani abu da kayiwa Allaah na alkhairi ne ya kawoni cikin rayuwarka
bandamu da kana tafiya ko kishiyar hakan, ba ni Kai dinne nake. so fatana Allaah yabaka lafiya
but ka daina sanya kanka cikin damuwa sosai its can lead you to serious depression.sanya a
ranka zaratun taka ce itama yusuf nata ne.تنا ينم انا انم .sai da yaga nayi shiru ya nisa yaja gogon
numfashi,ya ce nagode sosai my wife and only soulmate,nagode sosai da karfafamun gwiwa da
kikeyi a koda yaushe what a beautiful soul, wallahi you too much.

yadanyi shiru sannan ya ci gaba da cewa let me show my affirmation in sha Allaah ,zan
warke,zamutyi aure zan nuna maki endless love dina. auren da zamuyi na zobe ne,for better for
worst.ki kularmun da kanki,I love you with all my heart. misalin karfe biyu dai dai za'a shiga da ni
aikin.
Na nisa sannan naji dadin kalamenshi sosai nima na ce I love you too wish you successful and
quick recovery over the work dai dai lokacin zan karanta suratul yaseen zanyi ta wassali da shi
akan Allaah ya sanya ayi aikin a sa'a.

Ya ce Aameen nagode sweetheart.

Na sako murmushi jin yadda ya koyikoyi muryata da zaiyimun sallama.tsawon lokaci ina rike da
wayar inaji a raina wannan aikin za'a dace idan anyi.har lokacin Arrauda ta gama wanka ta
shirya ta zo kusa da ni ta zauna tare da fadin toh laila majnun ko Romeo and Juliet zance ne irin
wannan kalmomin soyayya haka, na rausayar da idanuna sannan na lumshesu na kuma
budesu ido cikin ido nake kallon Arrauda sannan nace so kenan ashe shi baisan babbancin
yanayi ko kudi ko sarauta kyau ko muni ba a zuciyar masoyar wadannan abubuwa duk basa
tasiri,gaskiya ina son wannan guy madly...
Arrauda ta waro ido ta ce gaskiya zamu dage Yusuf dinki ya samu lafiya musha buki ko muma
mu samu kunnuwanmu su huta da wannan suna Yusuf Yusuf,Allaah dai yasa shima haka yake
sonki saboda maza yanzu basu da tabbas..

Yes but my Yusuf is different da sauran mazan.ta ce Allaah yasa haka,na ce Aameen sannan
muka je kan dinning domin yin breakfast......

Tsawon yinin ranar munyishi ne cikin nishadi da hirarrakinmu har group called muka hada da
kawayenmu muka sha hira Latifa ma taso tazo mana amma tana da abubuwan yi sosai shine
bata samu zuwa ba amma itama ta danyi hira cikin group call din.

Tun bayan trying number khalid da na yi bai dagaba bankuma dawo ta kanshi ba saboda tun
farko dama shine ya ce ya ji ya gani.sai ga kiranshi kamar na share amma sai nayi wani tunani
na daga muryarshi babu yabo babu fallasa ya ce baby yakike yaya kin mutane?
na dan yatsana fuskata kamar ina gabanshi sannan na ce bangane yaya kin mutane ba ka
kirani ina kan waya bansamu na dauka ba, sannan daga baya na yi calling you back kaki ka
daga kenan munyi one one to meye na korafi?
Baice komai ba na dan ji shi yana murmushi kasa kasa bai kuma nunamun damuwarshi ba
kawai ya basar da tambayar da na mishi ya ce idan zaki iya fitowa ina kofar gidanku maida
wukar ina sauri ne sako zan baki.

Na yi mamakin Khalid da sonda yake nunamun kamar bashi da zuciya, kodai akwai wata
manufa a wannan soyayyar da yakemun amma muje zuwa zanga iya gudun ruwarshi banso
fitowa ba amma sai kawai na ce da Arrauda zan fito wajen Khalid ya na bakin get.

Batayi magana ba kawai ta gyadamun kai saboda ta yi nisa wajen kallon wani film, the reef a
MBC 2.

Ina fitowa kufar gidan Khalid ya kuramun ido yana yimun kallon kurilla na je kusa da motor sai
ya yi saurin fitowa daga motar muka kuma gaisawa sannan ya danyimun kalmominshi na love
wanda nake jinsu kamar a dole ake fadamunsu bana kuma maida mashi duk wata kalma da ya
furta na so,saboda gaskiya na gaji da yaudarar kaina tunda ni gaskiya ba sonshi nake ba gwara
muyita ta kare tun abun yayi nisa.ya katsemun tunanin da nake kamar yasan zuciyata ya ce kiyi
hakuri nasan ba'ason ranki kike saurarata ba amma kuma nagode da kulawar da kike bani.ga
wannan ya mikamun vonch na dollars guda daya,naki karba kawai na waro idanu sosai sannan
na ce gaskiya bazan karba ba,ka daina yimun irin wannan kyauta gaskiya bansan gunda zan
kai wadannan kudaden ba, kaga wannan motor da ka bani bansan yadda zanyi na fada a gida
ba ina dai jiran auntie Maryam ne idan ta dawo duk abin da ta ce shi zanyi,idan ta ce na mayar
maka ma zan maido ta kasani am here to learn not to came and collect somebody
properties,tun kafin na karasa magana ta ya ce
thanks you, ni kike kira da someone ko?
Hakan yana da kyau kiyi duk abinda zakiyi amma bazan daina sonki ba ki daina ganin laifina
laifin zuciyata ce da ta fada tarkon wanda baya sonta,ya karasa maganarshi kamar zaiyi kuka.
Sannan ya yacusamun kudin cikin zumbulelen hijabin da na sanya ya ce wannan kuma naki
ne,idan kina so kiyi amfani da shi ko ki bayar sadaka amma ni na rigada na cirashi daga
dukiyata daga haka bai jira nayi magana ba ya shiga cikin motarshi yarufe niko nayi mutuwar
tsaye sai da zai ja ya kama hanya ya zuke glasshin gaban motar ya ce am sorry my habibty ki
shiga gida ni na barki lafiya sai da safe.
Bai jira yaji abin da zance ba ya yi saurin baiwa motarshi wuta yabar kofar gidan..

Sai da na kusan minti biyu sannan na shiga cikin gidan.....har kusan karfe tara sai ga kiran
auntie Maryam take tambayata lafiyata da gida sannan ta ce in sha Allaah,itama zata dawo
gobe idan Allaah ya kaimu.

Na ce Allah ya dawo da ke lafiya.
Ta ce Aameen.
Bayan munyi add u'o'inmu na bacci,muka kulle kofar dakin, nahau kan up bed dina na kwanta
Arrauda kuma ta kwanta a kansan bed din kowa yana ta danne dannen wayoyinmu
bamusanma lokacin da bacci yadaukemu ba.wutar dakin dim light ne,can cikin bacci naji kamar
ana sanya keys don bude dakin da muke saboda ni bani da nawin bacci sosai aiko bangama
tunanin hakan ba saiko aka bude kofar wallahi saboda tsorata kusan shudewa nayi,ina ganinshi
ya nufo daidai kan gadon da muke hankalinshi duka a kasan gadon ne ni kuwa na kankame
jikina sosai na kuma matsowa baya sosai amma na dan bude fuji kadan ta cikin bargon da na
rufu,ina ji ina gani ya ciro wani waka acikin duhun ma sai walkiya yake ina ta makyartata jikina
sai bari yake yi aiki sai ya caka wukar daidai kirjin Arrauda subhanallah readers a wannan
lokacin da naji Arrauda da take makarin fitan rai, na sadaukar da komai na riga na yi over
reacting,jikina da ruhina sun kasa resisting kawai sai wani irin kukan da yaci karfina ina kokarin
ganin na toshe bakina saboda kada ya farga da ni,saboda shi a zatonshi mutum dayane a dakin
duk kokarina na ganin na toshe bakin bai yiwu ba sai da nayi wani irin kuka duk da na toshe
bakina da hannuna sai da kukan ta fito haba dagajin wannan kukan ya ce da wa Allaah
yahadani,sai ya fincikoni daga kan gadon na fadi kasa cikin sauri ya sanya wukar a wuyana,
yafara yankani da ikon Allaah da taimakonshi bansan lokacin da nayi kiciniyar kwatar kaina ba
tureshin da nayi sai ya fadi kasa kafin ya mike ni kuma na samu hanyar barin dakin ban zame
ko ina ba ina bude kofar gidan da gudu na dinga buga

12 / 18