WACECE NI BY Fateema Muhammad Suleiman-1.pdf

Author :  Fatima Muhammad Suleiman Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   15 / 18

42K to 45K   out of 52.9K words

zabi acikin su Khalid ne ya
cancanta ya aureta,duk da shima zaid na yaba da halinshi to nayi la'akari da cewa Khalid ya
riga da ya furtamun shifa son zaratun yake kuma da aure,duk da bance mashi komai ba na ce
dai bari ta warke sannan muyi maganar toh kinga shi kuma zaid bai furta hakan ba.sai da na
dinga ambatar sunayen Allaah nadan samu relief wato ni fa akwai gagarumin tashin hankali
agaba saboda su basu ma san waye yusuf ba balle aje da zancen shi crippled,na dinga kullawa
da kuncewa ta yaya zan fara kawo musu maganar Yusuf kwamachala kenan ni zaratun naga ta
kaina ina zan tafi da son yusuf?

Har dare ina cikin jujjuya maganganunsu Mummy cikin raina.Allaah ya zarabceni da cuta gashi
na warke sumul kamar bantaba yin jinya ba,watana daya cib a hospital sallama kawai muke
jira,sai gashi yanzu nidin za'a iya kirgani a cikin young millionaire saboda kudaden da aka
taramun a account.

Wayar yusuf ne ya dawo da ni daga dogon tunanin da nalula,sam cikin kwanakin nan jikina so
weak idan muna waya da yusuf,cikin muryarshi da yake kashemun dukkan gabobin jikina ya
faramun magana da cewa ala nguro,your excellency barkanki da hutawa wannan irin
recognition haka yanzu na karanta labarinki a top of the insider news gaskiya your talented,ki
godewa Allaah, kina da baiwa sosai,nima ina tayaki murna da tona asirin makashinki da dubban
mutane da basu ji ba basu gani ba yayi sanadiyar turasu lahira,ki ji mutumin nan Ashe shi ne ya
kashe wani ambassador da dadewa na Nigeria lokacin America tashiga tashin hankali saboda
bilateral diplomacy dake tsakaninta da Nigeria.tun kafin ya gama zancenshi na ce dan Allaah ko
zaka iya sanin sunan ambassador da kake magana akanshi?
Ya ce eeh ai ga sunan a jikin jaridar Alhaji modu,ai bangama jinshi ba saboda kadewa na katse
wayar da sauri na sauko daga kan gadon na sanya takalmana na fito wajensu mummy da suke
hirarsu a common room na asibitin.

Saboda sauri har kafata na sarkewa na iso da Sauri wajen Mummy sannan na ce mummy kinga
wanda yayi attempting kasheni shi ya kashe daddy ki yanzu aka wallafa a jaridar the
insider,kafin na gama maganata sai ga daddy da jaridar a hannunshi yana nunawa Mummy
labarin sai ga hawaye daga idanuwanta shar gaskiya duk sai da mukayi ta kuka mutuwar
tadawo sabuwa awajenmu.muna cikin wannan jimanin sai ga kira daga danginmu na Nigeria,
sai ga kiran Vaishali itama dai jajen tayi ta yi.
Kiran kam munshashi daga duk Wanda yasan kabarin wancen al'amarin.

Kiran yusuf dinne ya kuma shiga cikin damuwa yake tambayata lafiya na kashe waya bamu
gama magana ba?

Sai da na nisa sannan na ce labarin da ka bani da sunan da na tambaya wato kana bani labarin
mutuwar kakane fa alhaji modu tsohon ambassador.sanadiyar mutuwarshi kuma ya jefa
mahaifiyata cikin mummunar al'amari mai rikitarwa.

Ya ce kai! Subhanallahi Ashe ki ce alhakin kakanki ne Allaah yasanya dubunshi ya cika gaskiya
wannan azzalumin ya cutar da ku sosai, ga kakanki da aminiyarki da ya zama sanadin aikasu
lahira,abin haushi kuma gashi kafiri.
Wane irin mummunar al'amari ne mahaifiyarki tashiga ya jefomun tambaya?
Na ce labari ne mai nisa in sha Allaah zan sanar da kai,yanzu gaba daya na gaji.

Ya ce toh ina expecting
Na bugo ne dama na sanar da ke cewa munyi landing yau,kuma na sauka a kauyenmu aiki
Alhamdulillah ya yi kyau saura na uku da za'a gabatar wanda shine final daga shi idan Allaah ya
taimakeni zan iya fara takawa da kafata.
Cikin murna na ce,well come on board my hubby gaskiya na tayaka murna abin sona Allaah
yasa Wanda za'a kuma yi,ayi a sa'a.

Ya ce Ameen my wify bara na barki ki huta Good bye take care.na ce toh bye bye sannan muka

katse wayar.......








_ignore any typing errors_





*vote comment and share*


⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐


*WACECE NI*




✍by

*Fateema Muhammad Suleiman*
Email fmsuleiman743@gmail.com
Wattad teemacool2020



*KAINUWA WRITERS✍ ASSOCIATION*
```{United we stand and succeed;Our ambition is ton entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*page* 4⃣4⃣&4⃣5⃣

*wannan page nakune masoyan wacece ni musamman masu yimun comment _zaratun_ tana
godiya da kulawarku*



Best Line

“Keep in company of people of virtue; you will become one of them. Keep aloof from people of
vice; you will remain safe from them.”
Remove your gaze from the splendor of the World. Do not let the love of this World enter your
heart. Beware! The love of this World does not perhaps destroy you, just as it had destroyed
previous nations.

(H) *Umar Bin Khatab* ( r.a )




Ina zaune a bakin gadon gaba daya asibitin gundireni, yau wata daya da sati daya kenan.
tsananin mamaki da al'ajabi nake rayuwar duniyar kenan,Allaah kuma mai iko ne sannan shi
mai yawan hikimane da jujjuya lamuransa yadda yaso waye zai kawo a ka cewa ni ce sanadin
tona asirin wanda ya kashe kakana, tun kafin asan da zuwana duniyar? sai da na tiriyo dukkan
abubuwan da suka wuce masu ban mamaki sannan na nisa na fada a fili cewa lallai Allaah
mabuwayine gagara misali.sallamar da akayi ne ya dawo da ni daga tunanin da nake Dr zayd
ne yashigo fuskarshi dauke da Fara'a.na amsa mashi sallamar cikin sakin fuska,ya shigo sai da
ya zauna a kujerar da ke dab da gadon sannan ya ce your Excellency,ya dai duk tafiyar ce kike
zaune a daburce haka?

Na rausayar da idanuna sannan na lumshesu na bude dama idanun nawa yanayinsu kamar mai
jin baccine,na ce wallahi kuwa, duk na kagu ingani a gida gaba daya zaman asubitin ya
gundireni,

Sai da ya gama karemun kallo sosai sannan ya yi murmushi ya ce mu kuma gashi bamu gaji da
ke ba,saboda ke yanzu fitila ce ga wannan asibitin kin zama sarauniyarmu,saura kiris ki dane
kujerar mulkinki ya karasa yana dariyarshi mai ban sha'awa Masha Allaah shima bashi da
makusa kib kib da shi.
Na waro ido cikin mamaki, na ce nidince sarauniya? lallai ko da anga mulki.

Ya ce aiko kin tara kin samu domin mulki kam sanya a ranki kamar kinyi ne sai dai kiyi ta shan
kamshinki,mu kuma muna tayaki.

Na ce toh Allaah ya bamu dukkaninmu
Ya ce Aameen.

kusan minti uku babu Wanda yakuma cewa komai sai can ya nisa sannan ya kira sunana da
wata siga da bantaba jin ya yi irin ta ba.

Na dago idona sai kuma nayi saurin sadda kaina kasa ganin yanda ya kuramun manyan
idanunshi masu matukar shiga rai gaskiya na kasa juriyar ganin idanun nashi.

Sai yayi saurin cewa ki dago idanunki ki kalleni maganar da zan maki mai mahimmanci ne
inason ki fahimce sosai
Da hankali na juyo da fuska ina kuma fuskantarshi ido cikin ido.
Ya gyara zamanshi ya jingina bayanshi jikin kujerar sosai,fusjarshi kuma ba yabo babu fallasa
cikin dakewa ya ce your excellent,

Tun kafin ya cigaba da maganarshi na katseshi da cewa haba Dr,wani irin nadi ne kukeson
dangantani da shi?
ina fahimtarku tun jiya kuke dangantani da wani excellency,ina murmushin yadda yayi kasake
yana kallon lebuna na,kamar yau ya fara ganinsu.
sai na ce zanfi jin dadi da kirana zaratun

Sai da ya sauke numfashi sannan ya ce haba wannan sarauta fa Allaah ne ya baki ba mu ba
saboda haka dole kin amshi abin ki kawai,yanzu ma na zo da kokon barata ne bazan boye maki
da gaskiya zuciya ta takamu da sonki wanda ina ganin idan bata sameki ba zata iya fadawa
cikin wata matsalar duk da nasan akwai masu sonki ba sai kin fadamun ba amma nima inaso ki
sanyani cikin masoyan naki tunda ance allura cikin ruwa mai rabo kan dauka.

Duk wannan magana yanayin sune cikin kuramun idanuwanshi.

sai da na nisa kamar bazanyi magana ba saboda na fada wata tunani wato su maza dama haka
suke basu da kunyar furtawa mace so?dama nasan arina tunda na farfado daga gigin alluran
anesthesia naga yadda yake zumudi da saurin at the end of day, abin da yake harin kenan.

zuciya ta kuma sai dukan uku uku take tunda ya furtamun yana so na toh ni meyema zance
mashi gaba daya rasa amsar da zan bashi nayi.

Ganin da yayi bani niyar bashi amsa sai ya sauko har kasa yayi kneel down da gwiwowinshi
cikin roko ya ce please answer me

Sai da nagama karemashi kallo, yana da qualities din da ko wacce mace za ta so ta mallakeshi
a matsayin miji,amma ni nawa case dabanne,take jarumtakar yin magana tafadomun na runtse
idanuna sannan na ce gaskiya Dr kafi karfin neman abu awajena Wanda zan iya hana makashi,

sannan kai kana da duk wata qualities da namiji zaiyi gadara da shi,idan na ce zan tsaya yi
maka godiyane bisa taimakona wallahi I don't have anything similar to upper you, compare to
what you did to me....sannan bani da kalma da zanyi amfani da ita wajen gode maka.
Kai ne ka ceci rayuwa a lokacin da nake dab da stage na za ta kubucemun.,amma kamar yadda
ka ce allura cikin ruwa mai rabo kan dauka yanzu ni bani da zabi sai wanda Allaah yayi coz you
guy really throw me into something,with your beautiful heart and amazing care and loving...

Sai da yaga nayi shiru da maganar ya mike tsaye fuskarshi dauke da murmushin farin cikin
magangaguna.

Sai ya ce toh nagode my sweetheart, Ku zauna cikin shirin yanzu Dr on duty zai bada
sallamarku.
Haba tun kafin yakarasa maganarshi nashiga yin murna har da dan mikewata na fara hada
kayan abincin da ke kan table.
Kasake ya ja ya tsaya, ya ce lallai kam wannan duk murnar tafiya gidane? toh can dinma zamu
dinga binki ne yarinya,nayi murmushi da jin maganarshi.bayan ya fita na dauko wayata number
Humaira na kira na sanar da ita shirin sallamarmu.
Sannan na rubuta sako na turawa yusuf da Khalid kalmomin da sakon yakunsa duk iri daya.
Ga abin da na ce

My hubby mun samu sallama yanzu Uncle Mustapha zai wuce da mu gida.idan na koma gida
zamuyi waya.....

Kusan lokaci daya amsar sakonnin suka shigo.Tayani murna yusuf yayi sannan ya ce nayi
kyawarki my wify ki kulamun da kanki sai kinji ni a waya....
Shina Khalid abin da ya ce kenan sai dai ya kara sa cewa shima zai zo har gidan gobe in sha
Allaah.

Alhamdulillah na warke sumul Dr on duties ne ya yi discharge dinmu, bayan ya tabbatar da
komai normal,munyi murna sosai Humaira ce ta tattara mana dukkan kayayyakinmu,uncle
Mustapha ya yi dropping namu zuwa gida. bayan mun sanar da su daddy zuwanmu.sai gashi
munzo gidan kamar yau ne naje makaranta,saboda lectures da muke having on and off, ya
sanya bana samun zuwa gidan.
to gashi yau sanadiyar kaddarar da ta sameni, da badan ikon Allaah ba yanzu sai dai wani
labarin.
na yi kuka har na gode Allaah da rasa Arrauda kawata ce na kut da kut bana boye mata komai
saboda tamu tazo daya Allaah ya jikanki azizati.
na goge hawayen da suka fara zubomun,daga lumsassun idanuna.

Kanina yusuf ne ya shigo dakin,hannunshi dauke da flask na shayi da kofuna.sai da ya zauna,
sannan ya ce, haba sister kidaina sanya damuwa cikin ranki mana komai yawuce ai, su mummy
bazasu so ganinki cikin damuwa ba. please kiyi hakuri ga shayin kisha sannan ki fito parlor cikin
mutane zaman kadai ke sanya mutum cikin tunani.

Gyada mashi kai nayi sannan na tsiyaya shayin cikin mug kamshin shayin ne yabugi
hancina,nasha shi sosai kuwa don ni shayi yana daga cikin favorite dina.



***************





Yau juma'a kwana na shida kenan da sallama daga asibiti,shirin komawa makaranta nake
saboda dab muke da mufara jarrabawa.Allaah ya taimakeni duk Assignment da ake badawa
sauran colleague dina ke yimun shi,sai karatun ma suna turomun duk lecture da aka gabatar
ina karantawa through waya. Gidan yau full House ne,saboda dukkanmu muna gida Auntie Maryam ce ke bamu labarin
wahalan da project supervisor ta ya bata,da yadda ta lallabashi har yagama tama duk abinda
take bukata daga gareshi,sai ga su Latifa da tawagar friends dina sun kawomun ziyara haka
muka yini cikin farin ciki da walwala duk dauniyar girki kuwa Humaira ce ke yi.saboda gaskiya
daga ni har Humaira yin girki baya bamu wahala don mun saba tun muna yara tarbiyar mummy
kenan.mun taso dashi ajikinmu girki kam babu irin wanda bamu iya ba.mun zama professional
coolers..
Sai kusan magriba suka kama hanyar gidajensu saboda train sukabi sai da muka ga tashinsu
sannan muka koma gida..

Cikin wadannan kwanakin kuma Khalid zuwanshi sau uku kenan kuma har cikin parlor yake
shigowa ayi hira da shi kamar dan gida,sai zayd da yazo sau daya saboda shi bashi da
ishashshan lokacin kansa kullum suna asibiti...soyayya santsa suke nunamun wadannan
zaratan samarin Wanda har na kasa sanin waye acikinsu yafi kaunata? Ga yusuf kuma a gefe da yake rikitamun zuciya da tsantsar sonshi da rurutashi I don't know
why this love duk da bajintarsu da kulawarsu sun kasa cire yusuf a cikin zuciyata kullum gani
nake kamar son yusuf din Kara karuwa take a zuciyata...idan na dubu kudaden da suke cikin
account dina sai na ce meye amfaninsu kawai na dauka na bayar asake yiwa yusuf aiki cikin
gaggawa,na fison ya warke sannan na gabatar da shi ga iyayena saboda yanzu su suna kallon
cikin Khalid da zayd dole zan zabi dayansu.toh bani da kwarin gwiwar nuna yusuf a halin yanzu
duk da zuciyata shi take so amma nasan su mummy ba za taba yarda da shi a halin yanzu
ba.duk wata shawarar da na kulla sai ta warware na kasa yadda zan bullowa lamarin.kullum
dare kuma sai munsha hirarmu na soyayya da Yusuf.duk wata hira da mutum zaiyimun idan ko
ba Yusuf ba,
lami nake jinshi....

A daddafe na koma school badan ina so ba sai dai babu yadda na iya.Daddy da kanshi ne

yakawo har gidansu latifa saboda fafur sukaki yarda na kuma zama a wancen gidan ,yahadu da
kuma auntie Maryam ta kusan gama karatunta itama ta koma gidanmu da zama lokaci lokaci
suke zuwa wajen supervisor su contact dinsu da makaranta ya ragu.Faruwar wannan lamarin
ne muka gane mahaifin Latifa abokin daddy ne school mate nashi.yanzu kuma yake lecturing a
makarantarmu.gidan dai dai ginin turawa komai yaji,dakin Latifan nayi parking kayana.bansamu
wata matsala da gidan ba,saboda zamane da ake gudanar da shi cikin tsari.



Da misalin karfe goma duk muna parlor kowa ya baza takardunshi muna karatu nikam
assignment dina nake sai kanin latifa guda biyu Abyan da Abyad twins ne shekarunsu kusan
goma sha daya identical da su, kyakyawa masu ban sha'awa.sai latifa da ke kallonta.sai da na
gama duk abin da zanyi sannan na mike na ce dear felling sleepy,ta dago kai ta dubeni sannan
ta ce OK nikam sai nagama kallon wannan show before nayi joining naki,ga wannan ki
shigomun da shi daki.bayan na karbi takardar da take mikamun.bacci ne yake so yaci karfina
adaddafe nashigo dakin himar din dake saman rigar baccina na cire sannan na gabatar da
addu'o'in bacci na kwanta.

Can cikin bacci na farajin karar wayata na dauko ta ko duba sunan wanda yakira banyi ba kawai
na kara a kunnena.muryar Yusuf dinne kamar yadda nake zato,cikin muryar bacci nake amsa
mashi maganganunda yakeyi.da kanshi yagane ina cikin magagin bacci ya danyi dariya har
inajin muryarshi ya ce my wify wane irin baccine ke damunki yau?ki tashi ki wanke fuskarki ina
son jin cikekken labarin da Kika ce zaki bani....
Na dan zunguro bakina kamar yana kallona na ce uhm uhm ni ka kyaleni bacci nake ji sai
gobe.

Yusuf mutum ne Wanda yasan yadda zai tafiyantar mace har ya mantar da ita dukkanin
tunaninta.

Shima sai yayi irin muryata cikin shagwaba ya ce naki wayon yanzu nakeson ji.

Da kaina na watstsake na shiga bashi labari tiryan tiryan kamar yadda mummy ta sanarda ni
banboye mashi komai ba tsawon lokaci yana saurara na,sai dai naji yana jan numfashi.

sai da na zo dai dai yadda aka sameni har zuwa haihuwata sai kuka yaci karfina har da
shishshika,shiga lallai shina yake,kamar karamar yarinya. shish shish,shikenan kiyi shiru ya isa
haka.sorry my wify,gaskiya I felled your story is so touching.

Sai da yaga na yi shiru da kukan da nake yafara magana cikin tattausar muryarshi daga ji
labarin da na bashi ya girgiza shi,ya ce,hakika my wify naji labarinki,amma wannan ba wani
abin da zaisa ki tayar da hankalinki ba kada ki samu damuwa nidinnan zan zame maki garkuwa
bazan taba guje maki ba duk rintsi duk wahala zan kasance tare da ke, amma kiyimun alkawari
duk halin da Kika gani tattare da ni zaki dau hakuri domin akwai abubuwa masu matukar

sarkakiyan da zaki fuskanta gareni, toh idan lokacin yayi, ki kasance mai juriya da kau da kai.
toh na tabbatar maki cewa gaba kadan zaki samu farin cikin hakurinki.,saura kiris ya rage na
baki cikekken tarihina,wannan labarin da zan baki shi sai naga nafara takawa da kafata ina
tafiya,amma wani hanzari ba gudu ba idan aka kuma yin aikin ba'asamu nasara ba shikenan fa
bani ba taka kasa toh idan hakan ta kasance zaki yarda ki aureni?

Gaskiya tambayar ta girgiza ni, idan ni na yarda to su mummy fa ga matsalar Khalid da zayd a
gefe...wadannan abubuwan duk suna bukatar amsa.kuma bani da amsarsu .
Kinyi shiru fa ya jefomun tambaya?

kawai na tsinci kaina da

15 / 18