ya faru ba da matarka da daughter, son Fatima yarinya ce, bazata iya kishi da LAILA, kuma ko ba haka ba Fatima makaranta take zuwa , yanzu ta soma karatunta kana ganin in aka katse ta anyi mata adalci, tambaya tana jiran ya bata amsa"," Mummy ni dai kawai hakan nake so kuma bana San a d'auki lokaci mai tsawo nan da wani satin in Allah ya kaimu ya kama ranar juma'ah kenan", mummy ce ta dube shi , har cikin ransa da gaske yake ya sanya ta saukar da murya naji NA amince , amma da sharad'i za'ayi bikin amma nan da wata d'aya tunda ka matsu ayi a hakan", Fatima dake zaune jin abinda mummy ta fad'a sai da cikinta ya bada wata k'ara k'uuuuuuu , shikenan za'a kasheta da ranta ya zatayi kenan , kamata yayi ace tun kafin ayi auren nan ta samu ta fece, duk da son da mummy take mata ya kamata ace ta barta ko ba dan komai ba sai son tasan halin LAILA, a yanzu ma da ta gansu a tare ta fara sabauta mata rayuwa ballantana kuma ace ta auri mijinta ai shikenan kuma sai dai ta kai ta lafiya, tana cikin tunanin nan taji Mummy na kiran sunanta , cikin sanyin murya ta amsa. " ina fatan hukuncin da muka yanke yayi miki,mummy ta fad'a tana kallon Fatima da son jin me zata fad'a", Fatima tsintar kanta tayi da amincewa Mummy ba tare da ta San ta amince ba , murmushi mummy tayi , a gaskiya har cikin ranta ta aminta da Fatima , kuma tasan zata yiwa yaran d'anta tarbiyya, shi kuwa Ahmad da ke zaune sosai ya shagalta da kallon Fatima, sosai yarinyar take burgeshi, shi kad'ai sai kaga yana murmushi , mummy ce ta taimaka mata ta yi wanka ta gyara jikinta sosai a gurin cin abinci ne ta so tayi gardama , amma da Ahmad ya had'e fuska ya koma yallab'ai na asali, sai ta amsa ta fara ci sai da taji kamar zatayi amai sannan ta jijjiga kanta hakan ya sanya mummy ta k'yaleta, ganin da mummy tayi kamar Fatima na jin bacci ya sanya ta taimaka mata ta gyara kwanciyarta ba dad'ewa kuwa baccin ya kwasheta , su kuma suka ci gaba da tattaunawar bikin, nan Ahmad ya shaidawa hajiya ai LAILA tana gidansu , sosai ta nuna b'acin ranta akan haka , tace ya je ya taho da matarsa, ya fad'a mata bai ma San ta tafi ba jiya ne bai ganta a gida ba da ya koma , amma zai je ya dawo da ita, ya kuma sanarwa da hajiya Dan Allah ayi komai cikin sirri, wannan kenan.
A chan b'angaren LAILA kuwa , sun barbaje a falo ita da k'awayenta duniya ta koma mata sabuwa, ba abinda yake damunta, duk inda taga damar zuwa babu mai hana ta , hakan ya sanya take cin karenta babu babbaka, wata wadda suke kira da woman leader ce ta dubi LAILA a yatsine" wallah babbar hajiya kina bani mamaki , kamar ba LAILA ba, y'ar k'walisa, ki tsaya namiji yana b'ata miki rai, in nice ai wallahi sai na barshi , ko da shine autan maza"," ki kyaleta abinda nakeso ta gane kenan amma tak'i ta fuskanta , Aliya fire ta fad'a tana kallon LAILA", "yanzu toh me kuke son nayi , LAILA ta tambayi su Aliya fire, " ki rabu dashi kawai kizo a kwashi rabo da ke, Aliya ta kuma fad'a "," a'a inason mijina bazan rabu da shi ba gaskiya , amma nasan me zanyi ", Aliya naga ta tashi ta zagaya wajen LAILA ,suka gama maganganunsu ban dai san me ta fad'a mata ba , suka kwashe da dariya , su ka tafa harda woman leader, sannan su ka cigaba da hirarsu a haka mummyn LAILA ta sauko , aka cigaba da hirar da ita .
BAYAN SATI 1
Alhmadulillah, bikin Fatima yayi sauk'i sosai sai abinda baza'a rasa ba, zaune su ke, likita ya shigo ya duba ta , sannan ya sanarwa da mummy dama yana son sallamarsu ne tunda mai jiki Alhamdulillah ta warke, nan ya basu sallama , mummy ta kira Ahmad yazo ya d'auke su ya mayar da su gida , ko da suka koma sosai Fatima ta gasa jikinta da ruwan d'umi , tayi wanka , abinci taci kad'an sannan ta kwanta bacci kasancewar tana fashin sallah .
A chan falo kuwa Ahmad yana zaune da hajiya so yalr ya ga Fatima ta fito , shi ya sanya ya zauna suka ci gaba da hira da mummy, ganin babu niyyar fito wa kuma yana da aiki a office ya sanya ya hak'ura ya koma office ya ban mummy ita kad'ai a falon.
BAYAN SATI 2
Ahmad zaune yake a cikin office, wayarsa tayi k'ara , d'agawa yayi , ganin mai kiran ya sanya da kamar bazai d'aga ba amma sai ya danne ya d'aga, sallama yayi sannan ya gaishe da mai kiran , magana suka yi wadda bansan me suka ce ba , naji ya amsa da toh, sannan ya d'auki mukullin motarsa ya fita, sai da yayi tafiyar minti arba'in sannan ya k'arasa a bakin gate d'in ya faka motarsa , ya k'arasa ya k'wank'wasa, Baba mai gadi da yake zaune yana jin radio ya k'araso yana tambayar waye, jin muryar Ahmad ya sanya ya bud'e, gaisawa suka yi sannan ya masa alkhairin da ya saba yi masa sannan ya nufi cikin gidan .
Ko da ya k'arasa a bakin k'ofar falon ya tsaya , sallama yayi sannan aka bashi izinin shiga , a zaune ya samesu , su ukun , daga mummyn har daddyn sai kuma LAILA , gaishesu ya fara yi , cikin yatsina su ka amsa,cikin b'acin rai daddyn LAILA ya fara magana" ashe kai Ahmad mutumin banza ne , ka dakar min yarinya kuma ka korota gida, sannan kak'i zuwa ka bada hak'uri, toh ko mu zamu zo mu baka hak'urin, mummyn LAILA ce ta chafke maganar" Alhaji ai rik'a yayi shiyasa ya yi mana haka , wallahi kawai mun kai zuciya nesa ne bamu kai kararku kotu ba ", nan dai suka gama yi masa rashin mutunci, ko da ya sanar musu zai tafi da matarsa hanawa suka yi wai sai ta gama hutawa, haka ya tashi ranshi a b'ace ya nufi bakin gate domin tafiya , kome ya tuna kuma sai ya saki murmushi mai k'ayatarwa , sallama yayi wa Baba mai gadi sannan ya tafi office.
Bayan kamar kwana biyar da faruwar haka, Ahmad ya nufi gidansu , domin sanar da Mummy abinda ya faru kasancewar yana busy, ko da ya sanar mata addu'ah ta masa akan Allah ya sanya hakan mafi alkhairi ne , yaso yayi magana da Fatima amma kuma tun ranar da ya bayyana abinda ke ransa , suke wasan b'uya da ita , wani sa'ilin tana jin yazo zata gudu d'aki, ita dai Mummy abin har dariya yake bata.
Fatima ce zaune a d'akinta a lokacin saura kwana , goma d'aurin aure , sosai ta fad'a cikin kogon tunani , anya zata iya zaman gidan nan kuwa, me ya sanya ma ta amincewa Mummy akan maganar auren d'anta, saboda sunyi miki halacci a rayuwa, zuciyarta ta furta hakan, so da dama tana yin yunk'urin guduwa amma sai zuciyarta ta hana ta, ta so ta sanar da k'awarta amma tunawa da ta yi mummy ta gargad'eta da gayawa kowa ya sanya ta k'yale Halima, wayarta ce ta hau kuma sakamakon rurin da take yi , d'auka tayi ganin mai kiran sai da gabanta ya fad'i , cikin sanyin murya ta yi sallama, sai da ya ja ajiyar zuciya , har sai da taji , " Fatima me na miki ne irin haka, bakya so na ne kome, kinsan yadda kike a zuciya ta da har zakiyi min wannan horon, ya fad'a cike da sanyin murya ", ita ma kanta tasan zata kyautawa , amma ya zatayi ita gaskiya tana jin tsoro sosai, haka ya dinga janta da hira har ta saki jiki dashi , sukayi hira , sai da ya tabbatar da bata da damuwa sannan ya sanar mata da cewar za'a had'a mata kayan lefe zasu je ita da hajiya ta zab'i abinda takeso amsa masa tayi , sannan suka yi sallama.
Masha Allahu , a I gobe d'aurin aure mummy ta d'ibi akwatunan Fatima ta kai mata har cikin d'akinta , ta nuna mata ita dai Fatima duk kunya ta rife ta da k'yar ta gani sannan ta yi godiya , ko da dare yayi kasa bacci tayi har ladan yayi kiran sallah a kunnenta yayi , bata samu ko bacci d'aya ba saboda fargaba, a haka tayi wanka ta shirya cikin kayan da mummy ta d'inka ma ta , ta bi lafiyar gado ta kwanta saboda rashin baccin da ta samu ya sanya mata ciwon kai, aikuwa bacci ya kwasheta ba jimawa.
10:30am
Alhmadulillah, karfe goma da rabi amintattun hajiya mutum takwas wad'anda suka yi mata waliccin yaran na ta , su ka sheda d'aurin auren yaran na ta, Wanda wani amintaccen limami ya d'aura .
An daura auren Fatima Iliyasu da kuma Ahmad Muhammad Ahmad, akan sadaki naira dubu d'ari lakadan , sosai hajiya tayi musu alkhairi , bayan ta fad'a musu yadda angon ya tsara auren nashi , suka aminta da hakan sannan suka yi wa mummy sallama, su ka tafi.
Ahmad zaune a falon mummy , wanda farin cikin ya rufe wai yau shine ya auri d'alibarsa kuma masoyiyarsa tun lokaci k'uruciyarta, yana zaune Mummy ta fito daga cikin d'akin na ta , "yauwa son ina son magana da kai ", gyara zamansa yayi yana sauraronta" a gaskiya Fatima bazata tare a gidanka ba yanzu , saboda haka na maka yadda kakeso to nima kamin yadda nakeso ", wata kuwa yaji ta d'ebeshi jingina yayi da jikin kujerar da yake kai , ya lumshe idanunsa, me yasa mummy tace haka , me yasa zata masa haka..........
HMMMMMMM TO FA , KO MEYASA MUMMY TACE HAKA, FAN'S ANYA KUWA MUMMY? YA ZA'AYI KIYI MANA HAKA KUMA?😭😭😩
Please
Share
&
Comments
To be continue........
🌿🌿🌿NUSSAD🌿🌿🌿
🌸🌹KISHIYAR UWA🌹🌸
(True life story)
🍁Daga Alk'alamin Nussad🌸
SHAFI NA 35__36
" Mummy me yasa , ya tambaya kamar zaiyi kuka, idanunsa sunyi jazur da su alamar b'acin rai", duk da Mummy ta tsorata da yanayin da ta ganshi amma sai ta yi kamar bata ganshi ba " Ahmad ina da dalilai masu k'arfi wanda ya sanya bazan baka Fatima ba yanzu, dalilina na farko shine Fatima k'aramar yarinya ce bata san komai game da rayuwar aure ba sannan kanaso ka had'ata da LAILA a matsayin matanka, wanda hakan babbar illah ne ga rayuwarta , sauran dalilin sai lokaci yayi zan sanar da kai ko menene, yanzu lokacin da za'a bata dama ne tayi karatunta , mu barta , hakan yafi al'ala ", shi dai tunda ta fara magana ya kasa gane inda maganarta ta dosa , ita kuwa Mummy da gayya ta fad'a masa haka amma ita kad'ai tasan dalilin da ya sanya ta hana Fatima tarewa a gidan mijinta, ganin abun bana k'are bane ya sanya ya mik'e jiki a sanyaye ya nufi hanyar falo, hajiya na ganin shi , taji tausayin shi amma ta k'yale saboda tana da wani buri na daban akan Fatiman.
Toh ko da mummy ta sanarwa da Fatima shawarar da ta yanke taji dad'i duk da cewar itama bata fad'a mata asalin b'oyayyen sirrin na ta ba , wanda daga ita sai mahaliccinta suka sani.
A haka satittika suka dinga wuce wa, tun Ahmad baya nuna damuwarsa akan hanashi matarsa da hajiya tayi har ya fara nunawa , akwai wata rana da yazo takanas ya cire kunya , ya fad'awa hajiya amma fir ta kafe ta nuna batasan zancen ba, gashi LAILA ma har a lokacin iyayenta sun hana ta dawo wa, wai sai ta k'ara hutawa sosai ita kuwa duniya tayi mata kyau yawo kam ba inda bata zuwa duk kuwa da aure akanta , dan bayan barinta gidan Ahmad , ta je kasashe kusan guda uku, ba tare da ya sani ba a cewar iyayenta wai yawon bud'e idanu, kuma wanne mutum ya tsayar da ita zata tsaya ta yi magana da shi har ma ta bada phone number d'inta ga mutum, dan tana bin maganar k'awayenta na cewar itama ta shiga duniya a dama da ita ta mori abun arzik'i, lokacin da ta fara wannan rayuwar ji tayi ai a da duk kuwa da mai kud'i ta aura amma a cikin kurkuku take, saboda had'uwar ta da wani guy d'an gidan wani tsohon minister, Alhaji Badamasi Ali , suna soyayya a yanzu sosai ,duk da cewar ta fad'a masa tana da aure ,amma ta yi masa k'aryar cewar mijin na ta ya saketa, rayuwa kam sosai ta sauyawa LAILA tana cin karenta babu babbaka , k'awayenta kuwa su Aliya fire abun nema ya samu suka dinga ingi zata , a cewar su ita ma kamata yayi tunda basu yi aure ba itama bazata zauna ba.
A b'angaren Fatima kuwa, sosai ta maida hankalinta akan karatun ta, kasancewar sun shiga ajin Senior ne , sannan a b'angaren science take , Halima ma sosai take karatu kasancewar ta samu k'awa mai kaifin basira, zuwan Halima kusan biyar gidansu Fatima bayan da aka d'aura aurenta da Ahmad, amma tun zuwan Fatima na farko , tayi tambayar duniya mummy tace ta tambayi mijinta, kuma ta tambaye shi ya hana ta, shi ma tunda suka masa haka , sai ya ja zarensa, ita dai mummy wani sa'lin abun har dariya yake bata, shi kuwa Ahmad a nashi ganin da had'in bakin Fatima aka hana shi ita, in ba haka ba ai sai ta fad'awa Mummy cewar ita gidan mijinta take so, chab kaji fa wata rashin kunya wajen Ahmad🤪.
Mummy ce ta masa magana akan dawo war LAILA , ya fad'a mata yayi magana da mahaifinta amma yace har yau bata gama hutawa ba, Allah ya kyauta abinda tace kenan ta juya ta shige d'aki ta bar shi a tsaye, shi yayi tsammanin ma zata dawo ma sa da matarsa ne kawai tunda ita LAILA iyayenta sun hana ta dawo wa, a gaskiya fa yana buk'atar matarsa , toh ko kuma kawai zuwa zai yi Mummy bata nan ya d'auke ta ai bazata dubi tsabar idonsa tace ya dawo da ita ba, kai akwai rashin kunya kuma, haka dai ya gama tsayuwarsa ya juya ya fita, ya nufi gidansa.
8 MONTHS LATER.
Fatima ce ta shigo cikin falo sai nishi take yi alamar hajiya da yunwa da take addabarta, kasancewr sun fara exam , hakan ya sanya bata samu wani bacci na kirki ba, tana shiga bata ma lura da mutum ba , kawai ta shige d'akinta, tana shirin kulle k'ofa dan tana so ta shiga wanka, tasan Mummy ba ta nan amma tasan ta kusa dawo wa, dan haka take ta sauri tayi wanka, ji tayi an tura k'ofar d'akin baya tayi tai taga taga zata fad'i yayi sauri rik'eta team a jikinshi , k'ok'arin kurma ishu take yi , ganin zata tara musu jama'a ya sanya ya rufe mata bakinta da tafin hannunsa , cikin kunnenta ya fad'a ma " its me", gauron numfashi ta sauke , sanin ko waye,rungume ta tsam yayi a jikin shi , ita kuwa ba abinda takeyi sai k'walalo idanu waje, bayanta ya shiga shafa mata a hankali, yana magana" daughter d'in mummy har da ke aka had'a baki aka hanani ke ko, me yasa kika biyewa mummy, da takeson raba mu , ya fad'a yana k'ok'arin kai bakinsa ya zuwa na ta, k'ok'arin kaucewa ta shiga yi ya sanya ya rik'e ta tsam yadda baza ta iya k'wacewa ba , jin lallausan bakinsa cikin na ta ,karamar sumewa tayi , sai da ya gama jagulata iya son ransa, ganin da yayi tsayuwa na k'ok'arin gagararsu ya sanya ya jata har kan gadonta, still bakinshi na cikin na ta, ita kuwa, ido yayi wuri wuri anji sabon hannu , wata masifaffiyar kunyarsa take ji , shi kuwa sai da ya gama bidirinsa sannan ya d'aga ta ya rungume ta ajikinsa , sosai Fatima yayi enjoying na wannan al'amari da ya kasance tsakaninsu amma kuma tana bala'in jin kunyar yallab'an, k'ok'arin tashi ta shiga yi , hakan ya sanya ya k'ara matse ta , sannan ya fara magana cikin muryarsa kamar ta masu jin bacci , yana sanya mata albarka, ta dole ya sanya ta tayi alk'awarin in dai ya zo gidan Mummy zata dinga barin shi yana yin abinda ya mata yanzu, sai da ya gama , sannan ya fito har lokacin Mummy ba ta dawo ba , ya nufi motarsa ya shiga ya kunna ya bar gidan cike da nishad'i.
ONE YEAR LATER.
Alhamdulillah , Ahmad na zaune a falon gidansa , wayarsa tayi k'ara , a wannan lokacin iyayen LAILA sun dawo da ita , amma sun gindaya zarud'a da dama, ya kuma aminta da su kasancewar yasan shi ma abinda ya k'ulla , dan rashin mutuncin da su ka masa bazai k'yale ya tafi a banza ba, ita kuwa LAILA duk wasu al'amura da take yi a baya bata sauya ba sai ma k'aruwa da tayi , kuma tayi sababbun samari duk da tana tare da d'an gidan minister, shi kuwa Ahmad kusan kullum in dai yaje gidan Mummy ya tarar bata nan, kuma Fatima tana nan sai ya kwashi romonsa , duk da ba wani abu da yake shiga tsakaninsu amma romancing kuwa tana shansa, tun bata saba ba har ta zama gwana.
D'aukar wayar yayi , sabuwar lamba ya gani, da kamar bazai d'aga ba kuma sai ya d'aga, cikin mutunci su ka gaisa da mutumin , a nan yake sanar ma sa da cewar shine wanda yasan inda kakan nin Fatima suke, ya dawo daga fataucin da ya tafi , cikin farin ciki , ya amsa masa suka gama maganar akan sati mai kamawa zasu zo ya kaisu sosai ya masa godiya , ya ajiye wayar , cikin hanzari ya d'auki mukullin mota ya nufi gidan Mummy.
Ko da ya k'arasa a lokacin suna falo a zaune, yayin da Fatima take tsefewa mummy kitson da