ta nufi dakin Asabe, " inna na gama" tace da ita, "to kije ki daura girki ", “inna wallahi banci abinci ba ", “ka ji min shegiyar yarinya yo dan baki ci abinci ba sai me, ai aiki yanzu ma kika fara shi , sai kin gama aiki tsaf, sannan ki duba idan 'yar lele ta rage abincin ", to ta juya idanunta cike da hawaye , sai da ta kammala abincin nan tsaf sannan ta zuba musu ka'ida ne daman sai sun gama cin abinci sun rage kafin ta ci dan haka sai ta jira suka gama sannan ta dauki sauran taci a lokacin ta galabaita sosai, tana jan jiki ta shiga ɗaki, zaunawa tayi, sannan ta soma cin abincin cike da kewar mahaifiyarta, duk kuwa da bata santa ba ta ya ya zata iya cigaba da fuskantar wannan rayuwar mai cike da tsanani da dana sani "Allah ka kawomin dauki amin" taƙarasa haɗe da share hawayenta da suka gangaro mata kuncinta , tana wannan zaman har bacci ya kwasheta .
Tana cikin bacci nan taji an kwara mata , a razane ta farka, "au ke yanzu dan ubanki maimakon ki zo kiyi abin da za ki yi, kin san ki na da aiki shine kika zauna , shegiya mai mugun hali , tashi shegiya kawai" Asabe tayi furucin da bokitin ruwa a hannunta, "to inna zan fito ", “au jiran ki zan yi ki fito dan ubanki" ta tambayeta tana kokarin fincikota hade da kai mata duka, “inna dan Allah kiyi haƙuri wallahi na gaji" , “au ni ki ke cewa kin gaji, lallai wuyanki yayi kauri yau zaki gane kurenki a gidannan fito" , ta fada tana ƙoƙarin shiga daki , dukanta ta shiga yi ba ji ba gani, sai da ta tabbatar bazata iya moruwa ba, duk jikinta ta fasa mata shi "kuma ki tashi kije ki yayo itacen da zakiyi girkin dare tunda yau mallam IIlyan bai dawo ba" tana nufin mahaifinsu su Fatima , da Ƙyar ta tashi da rarrafe ta dauki yagaggen mayafimta ta fita domin yo itace a daji bata dawo daga itacen ba sai chan yamma a lokacin ta gaji sosai, amma haka ta daure ta daura girkin bayan ga Abu a zaune tana faman barar gyad'a tana zubawa a baki .
A haka rayuwar Fatima ta cigaba da tafiya, cike da tsanani, da tsauri, da azabtuwa, har suka kai shekaru goma sha biyar ita da Abu a lokacin ne maƙerin budurci ya fara ƙera su , Fatima ta fito a matsayin kyakykyawar budurwa son kowa, to a sannan ne fa samarin kauye suka ƙara yimata chaaaa a kanta ciki kuwa har da Ado wanda har yanzu yake kan bakansa na soyayya da ita , domin har ya sanar da mahaifiyarsa domin ta sanar da inna Asabe. Duk da wannan kyawun nata daya bayyana, amma hakan bai hana tsantsar wahalar da take ciki , ta bayyana akan kyakykyawar fatarta ba.
A wannan shekarun abubuwa sun faru na daɗi, da akasin haka, ciki kuwa har gama makarantar Fatima, ta firamare wadda da ƙyar hakan ta samu, bayan gwagwarmayar da aka sha da inna Asabe akan harkar makarantar , a yanxu cikin ikon Allah komai ya zama tarihi game da makarantarta ta primary, secondary ce dai bata amince ba, duk kuwa da cewar malaminsu na makaranta, malam Ahmad yayi gwagwarmayar ta cigaba, ganin irin hazakar da take da shi amma fafur ta k'iya , ganin haka ya hakura har ya koma garinsu Kaduna, dama bautar kasa yazo kuma ya gama ya koma ba tare da samun ya samu ya cika burinsa na ganin Fatima ta cigaba da makaranta ba .
A yanzu gashi mahaifinsu girma ya kamashi dan haka baya iya tab'uka komai , duk da, ada ma ba iya yin komai ballantana yanzu da ƙarfinsa ya ƙare duk da yana gudu da ƙyamar abun a zuciyar shi, ganin yadda ake yiwa d'iyarsa , a lokaci da dama ya kan so ya baiwa yarinyarsa labarin mahaifiyarta amma idan ya tashi faɗa mata sai ya kasa , a haka yake barin abin a ransa badan yana so ba, wani lokacin ya kan ji kamar ya yi kuka, idan ya tuna da mahaifiyar Fatima da irin zaman da sukayi lallai ba shakka Fatima ta dauki halin hakuri irin na mahaifiyarta.
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
(Asalin labari)
Shin wai wanene mallam iliyasu mahaifinsu Fatima ?
Malam iliyasu hafaffen garin kano ne, a ƙaramar hukumar wudil yankin darki , yana zaune tare da iyayensa da yayyensa da ƙannensa, mahaifinsa malam Bello matan sa uku , laraba da hansai da kuma Rabi kowacce su tana da yara laraba itace ta fari, tana da yara biyar kuma itace mahaifiyar su mallam Iliya , bayan haka yana da ƙanne, biyu mata biyu, maza biyu, Khadija , Lami, da kuma Habibu da sulaiman , a dakin hansai wadda itace ta biyu yaranta huɗu , Adam, Muhammad, da kuma Salamatu, Rabi yaranta biyu , Hannatu da kuma Hadiza waɗannan sune zuri'ar malam bello .
Mallam bello da iyalansa suna rayuwa cikin nutsuwa da kwanciyar hankali da tarbiyarsu, abin birgewa da sha'awa , yana kulawa da iyalansa yadda kowa kanyi sha'awar waɗannan iyalan . Hakama matan gidan suna da haɗin kai sosai kowacce duk da zaman kauye ne takan taimakawa ƴar uwarta, kuma suna taimakawa mijinsu .
Malam iliya shine babba cikin yaran malam bello, gaba ɗaya ragowar yaran gidan kannensa ne , yakan sanya kannensa su tafi makarantar allo, kasancewar a lokacin babu makarantar boko, ya taimakawa ƙannenansa sosai wajen iliminsu na muhammadiyya.
Sana'ar malam Bello noma idan ya girbe abinda ya shuka ya kai birni ya sayar , aikinsa noma da fatauci ta haka yake rike da iyalansa , lokacin da malam iliya ya kai mizanin samartaka sai ya sanya iliya akan harkar suna tafiya duk Inda yake harkar fataucinsa , in sun tafi sauran yaran maza sukan kula da harkar noma ta yadda zasu taimakawa mahaifinsu, lokacin da suka dawo gida fatauci Allah ya hadashi da Asabe wadda ta kasance yarinyace ƴar mace mahaifinta ya rasu tun tasa ƙarama dan haka ta tashi hannun mahaifiyarta babu kwaɓa , anyi gwagwarmaya kafin auren dan mahaifinsa bai so auren ba, amma ganin d'an nasa ya na ce yana sonta yasa ya barshi a haka akayi auren ba tare duk da ba kowa yaso auren ba amma a haka akayi auren ...........
Please🙏🏻
Share
&comments
To be continue.........
🌿🌿🌿Nussad🌿🌿🌿
🌸🌹Kishiyar uwa🌹🌸
(True life story)
🍁Daga alk'alamin Nussad🌸
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*```We are the moonlight writers we shine all over the world.``🌍`* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
Fatan alkhairi ga duk makaranta littafina , godiya ta musamman ga masu gyara min kura kurai na .
Jinjina gareki aunty nersmah da aunty dije, kuna namijin kokari wajen kuga littafina yayi daidai ba tareda samun matsala ba ina godiya sosai Allah ya bar kauna a tsakanin yan moonlight writer's association amin.
Luv u all my dear fan's🥰 wannan page din sadaukarwa ne gareku.
Shafi na 4️⃣
A haka akayi auren har amarya ta tare , kadahan kadaran ake zaune tsakanin Asabe da dangin malam iliya, babu wani jituwa a tsakaninsu , da yake ita kuma ba wani iya mu'amala tayi ba bata damu da su ba su ma basa zuwa inda take itama haka , a haka har akaci wata hud'u da aurensu a sannan ne ya ci gaba ta tafiye tafiyensa zuwa garuruwa , sai ya hutashshe da mahaifinsa akan ya zauna tunda shi ya kawo karfi sai ya dauki kaninsa su ka ci gaba da tafiya.
Abinda yake damun 'yan uwan malam iliya akan irin rashin mutuncin da matarsa Asabe keyi na bata ganin kowa da mutunci k'annensa basa zuwa gidan yayansu , duk kuwa da irin soyayyar da ta ke tsakaninsu dan shi Allah yayi shi mai so kyautatawa 'yan uwansa , amma kash sai Allah ya hada shi da mata marar sanin darajar mutane.
Har iya wannan tsawon lokacin Asabe ko batan wata bata tab'ayi ba hakan ne ya sanya ta kara bakin jini cikin dangin malam iliya , abinka ga k'auye sai surutai kala kala akan taki haihuwa , dan haka mahaifansa mata su ka fara mishi zancen ya kara aure , a sa'ilin da malam iliya yajewa da Asabe zancen nan kamar wadda zatayi hauka dan kishi , ta ci alwashin matukar dana raye babu shi babu kara aure , cin zarafi kuwa babu Wanda bai sha ba a wajen Asabe , ranar tayi yaji ta sanar da mahaifiyarta , abin ka ga gidan da babu tarbiyya haka mahaifiyar ta ta ta goya mata baya , kwananta d'aya a gidansu washe gari malam iliya yaje gidansu Asabe biko amma anan uwar ta ta ta sauke masa kwandon rashin mutunci da cin al washin ba za'a ayiwa yarinyarta kishiya ba indai tana raye kuwa , hakuri yayi ta bayarwa akan insha Allahu hakan bazata faru ba sannan ta yadda 'yar tata ta koma gidan amma sai da tayi ak'alla sati guda sannan ta koma.
Malam iliya zaune gaban mahaifinsa wanda ya sanya aka masa kiranshi , ya sunkuyar da kai kasa yana sauraron mahaifinsa cike da girmamawa , " kaji abinda na ce maka ba rigada na yanke hukunci na zab'a maka maryama 'yar gidan aminina malam kalla kuma umarni na baka ba shawara ba na yanke aurenka nan da saba'ar wata in Allah ya kaimu da rai da lafiya sai ka sanar da mai dakinka" , "to" ya amsa cike da girmamawa saboda baya tab'a jayayya da mahaifinsa akan komai ma , amma shi kadai ya san halin da ya ke ciki game da zancen da mahaifinsa ya fada masa , yayi masa sallama tareda shiga cikin gidan domin gaisar da iyayenshi mata , sosai inna hansai ta mishi fada tareda kwadaitar dashi romon da ake samu yayin da aka samu zuri'ah , ta gama yi masa nasiha sannan yayi musu sallama tare da innar sa ya tafi gida cike da fargabar ta ya ya zai fadawa matar sa Asabe a haka ya yini ya kwana babu sukuni da walwala , har sai da Asabe ta gane tambayarsa tayi yace mata ba komai wucewa tayi ba tare da kulawa ba .
Washe gari da safe ya tashi da nufin sanar da mai dakin nashi, amma ya kasa , haka yayi ta ajiye da maganar har biki ya kusa saura sati biyu bai sanar da iya ba.
Asabe na zaune a tsakar gida aminiyarta ta shigo da gudu cike da alamar firgici a fuskarta , dubanta Asabe tayi cike da haushi ta ce " wai baraka yaushe zakiyi hankali ne wai ke ba kiga cikin da ke jikinki ba kika shigomin irin haka salon ki zo haihuwa ki mutu " dakatar da ita Baraka tayi ta hanyar cewa " yo ba gwarama mutuwa ba an san lokacin ka ne yayi akan wannan bala'in da ya ke shirin tunkararmu" " wanne bala'i kuma Allah ya tsaremu da shi "ta fada tana tura d'an kwalinta gaba har zuwa girarta , " ke Asabe da labari na zo miki naga alamar ke baki sa ni ba ko " ? Ta tambayeta ta jiran amsarta "dan Allah ki fadamin mana kina wani jan zancen" ta sake tura dan kwalinta gaba, "to wallahi mijinki yqna nan yana shirin k'ara aure" , "kan uban chan ba Ankara da garin da ta b'arar ba , ta zunduma wani uban ashariya ," haba biri yayi kama da mutum , shiyasa ya kasa sukuni a cikin gidan nan har ya tafi fataucin nan ashe ya san abin da su ke shiryawa shi da matsiyatan iyayan na shi ", lallai ya taro wa kansa bala'i wallahi ," a'a tsaya mana ai ba hargagi zakiyi ba " cewar baraka da ta ke sake neman wajen zama, " tsayawa zamuyi mu fitar da maganin matsalar da ta ke tunkaro mu", zaman 'yan bori tayi ta zuba uban tagumi hannuwa biyu biyu , " inajinki baraka" ta fada dana kallonta " me ki ke so ayi yanxu "? Ta tambayeta tana kallonta , " kinsqn babu yadda za'ayi nabar wata mata ta auri malam wallahi kina ganin bana haihuwa ta yaya zaayi na bar wata ta shigo ta haifawa malam iliya d'a musamman ma na miji ta yadda zata cinye dukiyarsa " " kinyi gaskiya kuwa aminiyata" yanzu kinaso a tsayar da maganar aurenko"? Ta tambayeta ," eh " ta bata amsa " to yanzu tashi zakiyi mu tafi chan kauyen lajawa akwai wani hatsabibin boka , sunanshi boka sha yanzu magani yanzu , amma ina fatan kinada kudi a hannunki "? Ta tambayeta tana kallonta ," eh da akwai wanda malam ya barmin da zai tafi ban tab'a komai ba ", " to tashi zakiyi mu tafi dan kinsan da zafi zafi akan daki karfe", " eh to bara na Shiga na dauko mayafina" ta shige daki a birkice domin dauko mayafi ,sannan su ka yi waje cikin hanzari.
Mata mu kula! Mu kula ,a kula! , kawaye sukan kawo cikas sosai a zaman aure , kar ki bari kawarki ta rudeki takaiki ta baroki akan tudun dana sani , sirrinki ki boyeshi karki sake ki bayyanawa kawarki halin da kike ciki da mijinki , zata sanyaki kiyi danasani a rayuwarki da rayuwar aurenki baki d'aya, daga k'arshe mijinki ya sakeki , in batada aure ta aure miki shi , Allah ka shiga tsakanin na gari da mugu amin .
Basu k'arasa cikin dajin ba sai da sukayi tafiya sosai har rana ta fad'i kana suka karasa , dan har Asabe ta sare amma Baraka ta k'arfafa mata guiwa da kyar su ka karasa bayan bakar wahalar da su ka sha k'afafunsu sun kumbura sosai sun jigata , kana su ka karasa wajen , tunda su ka nufi wajen Asabe takejin iface iface namun daji kukan tsuntsaye da sauransu , a haka su ka karasa ," Ku shigo da baya" cewar boka sha yanzu , cikin wata gabjejiyar murya, da sauri suka juya har suna kokarin bige junansu , Baraka ta zunduma ashar ta yiwa Asabe da nunin itama tayi wannan itace sallamar Shiva wajen bokan , aikuwa itama tayi , sannan ya basu izinin zama , su ka zauna ,Asabe ta bud'e baki zatayi magana yayi mata nuni da tayi shiru , zuwa kamar Minti biyar sannan ya bushe da wata mahaukaciyar dariya sai da yayi mai isarsa sannan ya dakata, yayi nuni da wata kwarya sai ta taho da kanta ta zauna a mazauninta kan wata tararriyar kasa , yayi nuni da ruwan cikin kwaryar aikuwa yayi bakikkirin daga baya kuma ya koma fari, aikuwa ya shek'e da dariya" angama bukatarki ta biya za'a fasa auren nagama komai , yanzu maganar aure babu ita na Sanya kiyayya mai karfi tsakaninsu " Myrna sosai Asabe tayi najin an fasa auren malam iliya ,su ka yiwa boka sallama da zasu tafi ya bata maganin da zata zuba masa a abinci da Wanda zata zuba tayi wanka sai turaren da zata sanya Wanda idan har ya shak'a to zai manta da kowacce mace a duniya sai ita, sannan suka nufi hanyar gida a lokacin anyi sallar magariba sannan su ka karasa gida , sai da suka huts sannan Baraka ta nufi gidanta itama, da kudirin aikata abinda boka ya sanyata ta kwana , dan tana tsammanin dawowar malam a tsakankanin wannan lokacin , a haka tayi bacci tattare da mummunan k'udiri a ranta.
A chan gidan su malam iliya kuwa anata shirye shiryen biki saboda wannan bikin na so ne , ana wannan yanayin malam iliya ya dawo saga fatauci , lokacin da ya je gidansa da yaga Asabe bata nuna masa wata alama ta nuni da cewa tasan zancen hakan ya saka ya ji dadi kuma yayi mamaki bisa ga yadda yasan qauye da gutsuru tsoma , amma yaga sab'anin haka, hakan ya sanyashi ya tafi gidansu domin gaida mahaifins. Tana fita Asabe ta yi shirinta tsaf da magungunan da bokq sha yanzu ya bata ta zauna zaman jiran malam ya dawo daga gidansu ..............
Please🙏🏻
Share
&comments.
To be continue........
Luv u all my fan's🥰🥰😍
🌿🌿🌿Nussad🌿🌿🌿
🌸🌹Kishiyar Uwa🌹🌸
(True life story).
🍁Daga alk'alamin Nussad🌸
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*```We are the moonlight writers we shine all over the world.``🌍`* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
Ina matuk'ar godiya gare ku masoyana , saboda nuna kulawarku ga littafina mai suna Kishiyar uwa , a gaskiya na rubuta shi ne badan komai ba sai don tunanin da nayi wannan shi ne abin da yake damun al'umma , idan mata taga an bar mata 'ya'yan abokiyar zamanta idan har basa shiri da ita to fa su ma yaran nata sun Shiga uku , dan Allah mata mu kiyaye wannan hakkin lallai sai Allah ya tambayemu a kanshi , ki sanya a cikin ranki idan da yaranki ake yiwa haka ya ya zakiji a cikin ranki , Allah yasa mu gyara amin.
Ina ganin comments naku gaskiya ina jin dadi , kuma ku ma burgeni , insha Allahu bazan baku kunya ba
Comments🥰
Maman Ammar
Kishiyar uwa🌹💞nicely sis Allah ykara basira ina matukar jin dadinsa wlh 🥰🥰
~phareeeda
Allah sarki Fatima zakisani kuka 😭😭😭😭😭😭😭😭
Duk naga comments ina godiya.
Shafi na5️⃣
Ko da malam Iliya ya k'arasa gidansu ya tarar ana ta shirye-shiryen biki , wajen mahaifinsa ya fara zuwa ya gaida shi amsawa yayi kana ya mishi maganar "angama komai da ake buƙata yanzu abinda ake jira shi ne saboda su na so su kai kayan aure da sadaki, saboda auren ya kusa, amsawa yayi da to , kana yayi godiya, ya yi masa sallama ya shiga cikin gidan wajen iyayen sa mata , nan ma ya tarar suna ta shiri sosai , ya gaida su ya mu su alkhairi, ya tsaya sai da su ka ga ma komai na harkar kai kayan auren, da sadaki sannan ya nufi hanyar gidansa.
A can gida kuwa Asabe ta gama har had'a komai da tasan boka sha yanzu ya ba ta, dan haka a halin da ake ciki malam Iliya kawai ta ke jira ya dawo gida, tayi wanka da magani ta shafa turaren da sauran kayan amfanin da ya bata za ta sanya masa a abinci.
Da sallama ya shiga a bakin sa , amsawa tayi cike da kwarkwasa , ƙamshin turaren da boka ya bata shi ya shak'a ai kuwa