ba me malam din ya ajiye a cikin zuciyar tasa shi take tunani fiye da rashin lafiyar tashi , haka suka gama komai da ake buk'ata kana suka zauna tare da shi.
Achan gida kuwa Fatima kasa tsinana komai tayi sai tunanin mahaifinta takeyi, bataso ta rasa shi a halin yanzu da take matuk'ar buk'atarsa a rayuwarta , ya Allah ka dubeta ka Sanya mata tawakkali a halin rashin lafiyar mahaifinta amin.
Har k' arfe uku na rana basu dawo ba, lokacin har ta gama abinci da komai da komai na gidan sai dai tallah ne yau kam bazata iya zuwa ba , gashi ta Sanya abinci a cikin kwano tana jiran ko za'a daukawa mahaifinta akai masa , haka tayita zaman jiran amma shiru.
Abu ce ta fito daga d'akinta da kaya a hannunta , watso mata tayi a fuska , " gashi nan ki wankemin saboda kayana sun taru babu masu wanki a cikin" dubanta Fatima tayi tare da cewa " amma ai kinga Baba bashi da lafiya ko ta yaya zan iyayin wanki a halin da nake ciki , " au bazakiyi ba kenan, to wai ma da kike cewa Baban bashida lafiya ina ruwana da rashin lafiyar tasa , kinga in zakiyi min wanki kiyi in kuma kika k'iyi kema kinsan sauran banza kawai, ta juya ta shige cikin d'akin na ta , tabar Fatima baki bud'e , babu yanda ya iya haka ta d'ebi kayan ta wuce ta wankesu, ba ita ta gama ba sai da akayi sallar magariba , kana ta gama wankin tsaf saboda akwai su da yawa.
A chan asibitin kuwa an bawa malam gado , dan ciwon nashi yayi tsanani dan haka kiri kiri da aka ce inna Asabe zata dinga kwana ta nuna itafa bazata iya ba , malam muhammadu ne ya tafi da kansa ya maidata gida kana ya dauko Fatima domin ya fuskanta da ita zanta iya juriyar kula da malam d'in , aikuwa koda akace ta shirya ba musu domin itama tana buk'atar ganin mahaifin nata , da Asabe ta so ta hana ganin in Fatima ta tafi to fa babu mai aiki a gidan haka zalika babu mai zuwa mata tallah ya ya kenan , amma da yake dama ba shiri sukeyi da muhammadun ba haka yayi Jan ido wa Asabe ya tafi da Fatima asibitin, ko da taga mahaifinta halin da yake ciki kuka ta kamayi da k'yar Baba Muhammadu ya lallasheta , da cewar ai dana samun sauk'i in taci gaba da kuka zai maidata gida , jin haka ya sanya tayi shiru ba shiri, a haka suka kwana bata samu damaryin bacci ba har asubah a sannan ne malam Iliya ya farka ruwa ya nema aikuwa da Saudi Fatima ta k'arasa tareda taimakon baba muhammadu su ka bashi ruwa" sannu Baba" abin da ta iya furtawa kenan sai hawaye , da Sauri ta goge da ta tuna da sharad'in da k'anin baban nata ya fad'a mata , murmushi malam Iliya yayi mata tareda shafa kanta da hannunsa wanda babu ruwa a jiki da muryarsa da bata fita yace " Allah ya miki albarka d'iyata " ," amin baba" tayi furucin a sanyaya , to bayan su taimaka masa yayi alwala suka jinginar da shi yayi sallah , kana suka soma hira har wayewar garin snnan ya koma bacci.
"Wallahi in baki fito daga d'akin nan ba ko ki kuka da kanki" , Asabe ce ke wannan hargagin wa Abu , karar bud'e k'ofar da k'arfi shiya sanya Asabe ja da baya " wallahi inna bazanje aike ba gwarama ki fita da kanki kije ki siyo, hana ayi ta damun mutane aikin banza aikin wofi" Abu ce tayi maganar ta karkad'a kafad'a, jawota Asabe tayi aikuwa itama ta kamata da kokawa sosai sukeyin dambe , ni kuwa abin nema ya samu jinayi kamar na kad'a musu ganga safiyi da kyau sosai" innalillahi kai kai kai menene haka" Baraka ce tafi wannan furucin tana tafa hannu ," ki barni in ji mata ciwo yarinyar nan kamar bani na haifeta ba wai har nace ta zo taje aike aike amma ta k'iya ", wallahi bazanje ba ehe ta shige d'aki had'e da Santa sakata , Baraka ce ta dubi Asabe ke ni ba wannan ba ma wai ya batun auren ne saboda yaron nan ya matsamin " ," eh na sanarwa da malam din ya amince yanzu saura saka ranar biki kawai " Asabe ta fad'a da yanayin alhini a fuskarta" ke malam din ma fa bashi da lafiya hana asibiti," " meya sameshi to Allah ya k'ara afuwa" bata saurari me Asabe zatace mata ba ta juya ta fita .
To har azahar sannan Asabe ta gama aikin gidan duk ta wahala ta jigata ta sauya kamanni, Rana gamawa Abu tazo da d'iba abincin ta kuma shigewa d'aki ta banko k'ofa .
To kwanan malam uku a asibiti a lokacin ya samu sauk'i ba laifi dan har ana tunanin za'a sallameshi , Fatima sosai tayi murna ga bisa samun sauk'in mahaifinta , domin shi ne a yanzu yake matsayin jigo a rayuwarta , a daren rana ta hud' u ciwon malam ya dawo sabo sosai hankalin fatima ya tashi kuka takeyi sosai , hankalinta ya tashi gashi baba Muhammad ya fita inna Asabe kuwa tunda ta tafi bata dawo ba tun ranar da aka kawo malam din, ta yunk'ura zata tashi ya rik'e ta "tsaya d'iyata mafi soyuwa a gareni" , wasu zantuttuka masu kama da wasiyya ya shiga yi mata wad'anda bata ganewa , nasan dai nayi mini laifi ban sanar da me ko asalin wacece ke ba hak'ik'a nasanki da hak'uri da juriya to kick gaba daga inda nasanki hak'ik'a akwai jarrabawoyi da yawa da ya kamata ki cinyesu ina fatan zaki cinyesu , kiyi hakuri da duk halin da kika tsinci kanki a rayuwa , kiyi taka tsantsan a gaskiya auren da akeson yimiki banasonshi amma saboda gudun wannan ranar da zan tafi in barki ya sanya na yanke hukuncin da kiyi aure amma d'iyata in kin samu miji ko bayan raina kiyi aure hak'ik'a inason kiji dad'in rayuwa ina mini wasiyya kiji tsoron Allah", a lokacin ya bata labarin mahaifiyarta sosai takeyin kuka sosai dana ashe yadda tayi hak'uri mahaifiyarta ta fita , lallai itakam batasan menene zai faru ba , muryarsa a lokacin ta farayin sanyi . Allahu Akbar a take a lokacin Allah ya amshi rayuwar malam Iliya Allahu Akbar said dai mice Allah ya jik'an musulmi jin shirun da Fatima tayi shi ya fargar da ita halin da ake ciki da gudu ta fita waje dan sanarwa da doctor halin da ake ciki , kafin ta k'arasa tayi kicib'us da k'annen malam din nuni ta Shiga yi musu bakinta ya Gaza furta komai , da sauri suka Shiga d'akinWRITER'S
dubawa baba muhammadu ya ja zanin gadon yarufewa malam fuska , ganin haka a take Fatima ta sulale k'asa sumammiya........
GODIYA A GAREKI
MAHAIFIYATA
HAJIYA FATIMA TURAKI ADAM, ALLAH YA JA DA RANKI YA K'ARA MIKI TSAWON RAI MAI AMFANI.
JINJINAR BAN GIRMA GAREKI AUNTYNA SHAFA'ATU SULAIMAN UMAR
JINJINA GAREKU Y'AN MOONLIGHT WRITER ASSOCIATION, ALLAH YA HAD'A KAWUNANMU AMIN.💔💔
🙏🏻please
Share
&
Comments
TO BE CONTINUE.....
🌿🌿🌿NUSSAD🌿🌿🌿
🌸🌹KISHIYAR UWA🌹🌸
(True life story)
🍁Daga Alk'alamin Nussad🌸
MASHA ALLAHU LAK'UWWATA ILLAH BILLAH.
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM, SALATI DA AMINCI SU TABBATA GA ANNABIN MU MUHAMMAD TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARESHI DA AHLAN GIDANSA DA SAHABBANSA MASU GIRMA.
SADAUKARWA GA DUK MAKARANTA LITTAFIN KISHIYAR UWA DAMA FANS DIN GROUP NA NUSSAD HOUSA NOVELS.
Shafi na9️⃣-1️⃣0️⃣
Ganin haka ya sanya sukayo kanta da sauri cikin gaggawa baba Muhammadu ya nufi ofishin likita , domin sanarda shi abin da yake faruwa.
Tare da likitan suka shigo d'akin cikin tare da nurses guda biyu , direct wajen malam iliya ya nufa su kuma nurses din suka nufi wajen Fatima dake kwance a sume, suka d'aga ta suka d'aurata akan gado domin bata agajin gaggawa domin ganin ta dawo hayyacinta.
A chan d'aya b'angaren sosai likitan ya shiga duba malam Iliya amma ina hak'ik'a rai yayi halinsa k'ara rufeshi yayi , ya juya ya fuskance su tare da fad'in "sai dai hak'uri , Allah ya yi masa cikawa ", sosai d'akin ya rud'e da kawar jama'ah da kuka, da k'yar aka lallab'esu suka sanya gawar malam Iliya a mota aka nufi gida domin sada shi da gidansa na gaskiya.
Ko da suka isa gidan Asabe kamar tayi hauka , sosai takeyin kuka tuburan , ita kuwa Abu ko a jikinta , sai dai ta kai ta kawo , tana taunar cingam da wak'a, Allah wadai kam tasha shi ba kad'an ba a gurin mutanen garin.
Karfe takwas na safiya aka kai malam Iliya gidansa na gaskiya da yake rasuwar dare yayi , ko da akazo kaishi da k'yar Asabe ta bari aka fitarda shi daga gidan kuka sosai kamar mhaukaciya ta koma haka dai aka rik'eta aka zaunar da ita sannan aka kai shi gidansa na gaskiya Allahu Akbar sai dai muce Allah ya jik'an malam Iliya da rahama amin.
Har aka kwana uku da rasuwar Fatima bata farfad'o ba sai a rana na hud'un ne ta farka , zabura tayi ta mik'e zaune kamar a mafarki abubuwan da suka faru suka dinga dawo mata , k'ara ta sanya ta k'ok'arin cizge ruwan da aka sanya mata , d'aya daga cikin k'annen malam Iliya ce ta rik'eta , " sannu y'ar nan " ta fad'a tana k'ok'arin rik'eta , "inna ina baba na yake" ta fad'a tana kallonta da zak'uwa da son jin amsar da zata bata ," karkice min Baba na ya tafi ya barni " , ta k'ara fashewa da kuka , sosai suka tausaya mata , da k'yar baba Muhammadu ya k'araso cike da tausayin yarinyar dan yasan tana cikin halin maraici a yanzu " dakata yarinyata malam yana nan yana gida kina warkewa zamu tafi ki ganshi " jin haka ya sanya taji sanyi a ranta, bata kuma tada zancen ba saboda baba Muhammadu ya mata alk'awarin zai kaita gurin babanta in ta warke , hakan ya sanya ta kwantar da hankalinta.
Kwananta takwas a asibiti , aka sallameta suka koma gida , sauri ta dingayi domin tayi kewar mahaifinta ," baba ina Baba na yake "ta tambaya ta shirin lek'a d'akinsa , "dakata d'iyata " anan take ya gama yi mata nasiha daga bisani ya sanar da ita halin da ake ciki , kuka sosai tayi sannan ta tsagaita , ta rok'i baba Muhammadu tanaso ta bishi gidansa ta kwana biyu , ya yarda suka tafi , sai da tayi wata d'aya sannan ta koma cikin gidan ko da yaushe sai tayi kuka , idan ta tuna da mahaifinta , sai da akayi arba'in sannan al'amura suka koma gidan jiya.
Bayan wata biyar da rasuwar malam al'amura suka k'ara runchab'ewa komai ya koma gidan jiya , da kamar inna Asabe tayi sanyi amma I zuwa wannan lokacin azabtarwa take yi mata ba kama hannun yaro safe da rana da dare tallah gashi bata samun abinci sosai tunda ganin yanzu ba mahaifinta sai abin da aka bata na abinci in ta samu ta ci in bata samu ba ta hak'ura , duk da wannan halin da take ciki bata tab'a fad'awa kowa ba duk da cewar y'an uwan malam din sukan zo dubata amma bata tab'a fad'awa kowa ba .
Ana cikin wannan yanayi Baraka tazo mawa da inna Asabe zancen saka ranar aure tunda yanzu sun shirya shima ya fara zuwa kudu kai kaya a babbar mota jin wannan zancen ya sanya Asabe kwadaitawa yarinyarta auren Ado ba Fatima ba , sosai sukeyin shirin biki kud'i aka kawo da komai da komai aka sanya biki wata d'aya, Asabe fa hankalinta ya tashi ganin cewar Ado na samun kud'i sosai ganin har dubu ashirin aka kawo kudi'n auren ya sanya hankalin ya tashi saboda a rayuwarta bata son cigaban Fatima ta ci son tayi aure cikin k'ask'anci wannan dalilin ne ya sanya take Neman hanyar da zata hana auren Fatima ya koma kan na zainabu , haka tayi ta fafutukar ganin bayan auren sunje wajen boka ita da Abu ya basu tabbacin cewar zaa fasa auren kuma da d'iyarta zaayi , amma me har ana I sauran kwana biyu biki ba abin da ya sauya .
A daren d'aurin auren ne Ado ya samu mahaifiyarsa da zancen shi fa ya fasa auren Fatima Abu yakeso , sosai tayi mamaki da jin haka , kuma tabbas tasan Asabe ce tayi aiki dama ance abokin mugu , mugu ne .
Ranar d'aurin aure da safe lokacin kowa ya hallara a inda za'a d'aura auren komai ya gaba daidaituwa aka sanar da cewar an sauya ango yace Abu yakeso ba Fatima ba , sosai mutane sukayi mamaki aka d'aura auren Abu da Ado cikin sadakin kud'i naira dubu goma.
A lokacin da aka d'aura aure Fatima tana gida tana sharb'ar kuka saboda batasan auren dan kawai anfi k'arfinta ne ba yadda ta iya , mata kuwa aikinsu suke tayi kowa na murna inna Asabe kuwa da suka san me yake faruwa Murna sukayi ta yi .
Marok'i ne ya fara sanarwar d'aurin aure! An d'aura auren Adamu da zainabu akan sadaki naira dubu ashirin! Yana ta sanarwar har ya shiga cikin gidan yana sanarwar, matan da ke tsakar gidan mamaki ne ya cika su jin abin da marok'in ke fad'a .
Fatima da take zaune a cikin d'akin abin da kunnuwata suka jiyo mata ne ya sanya ta fito da gudu domin ganin abin da ke faruwa.......
Please
Share
&
Comments
To be continue.......
🌿🌿🌿Nussad🌿🌿🌿
🌸🌹KISHIYAR UWA🌹🌸
(True life story)
🍁Daga Alk'alamin Nussad🌸
GODIYA GA ALLAH DAYA BANI DAMAR CIGABA DA RUBUTUN LITTAFINA , BAYAN DAN HUTUN DANA DAUKA BISA GA UZURIRRIKA .
A YAU INSHA ALLAHU ZAN CIGABA DA RUBUTUN LITTAFIN KISHIYAR UWA FATANA ALLAH YA YI MANA JAGORA
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌹🌹🌹🌹🌹
🌸🌸🌸🌸
🌹🌹🌹
🌸🌸
🌹
SHAFI NA 1️⃣1️⃣-1️⃣2️⃣
Koda Fatima ta fito ganin abin da ke faruwa , ji tayi wasu mata daga k'ofar d'akin girki suna magana ,d'ayar matar ta dubu y'ar uwarta " ke ni kuwa hansai bakyaji min abin da kunnuwa na ke ji ta fad'a tana k'ara kasa kunne", matar da aka kira da hansai ta ce" ashe dai bani kad'ai ke ji ba , yau naga lalata da idona, mu da aka kira mu bikin wannan yarinya Fatima ta ya ya auren ya sauya kan wannan fitsararriyar yarinyar, ta fada tana sallallami had'i da tafa hannayenta".
Ita dai Fatima ji tayi kamar tayi sujjadar godiya saboda dad'i , surutai ne ya fara tashi a tsakanin mata , wannan ta fad'i nata wannan ta fad'i nata, Baba Muhammadu k'anin marigayi malam Iliya mahaifinsu Fatima ne ya shigo gidan ransa a matuk'ar b'ace , d'akin inna Asabe ya shiga da sallama , mutanen ciki suka amsa , tambayar Asaben ya yi sai gata ta fito, sadaki kawai ya mik'a mata na d'iyarta sannan ya sanya kai ya fita cike da takaici, yana fita ta wani rangad'a gud'a sannan ta kama habaice habaicenta , niko na ce kyayi kya gama .
Achan b'angaren Fatima kuwa d'akinta ta koma cike da jin dad'i, tana cikin wannan farin cikin Baban nata malam muhammadu ya Shigo d'akin tsammaninsa ya same ta tana aikin kuka saboda yasan ya zuwa yanzu tasan koma da yake faruwa , amma me sab'anin haka ya tarar domin kuwa fuskarta ba abinda take fitarwa sai annurin haske da murmushi, tashi tayi , tayi masa sannu da zuwa yana amsa, nasiha mai ratsa zuciya ya mata, daga bisani ya shaida mata abubuwan da suka faru , yadda yaga bata damu ba hakan yayi masa dad'i sosai , ya yi mata sallama ya fita ya koma wajen y'an d'aurin auren.
Toh a haka aka daura aure su inna Asabe baki har kunne yarinyarta ta samu mai kud'i , Wanda yake fita birni dama hakan tafi so ace yau d'iyarta tafi ta kowa sa'a a k'auyen , haka dai aka k'araci bikin anci an kuma sha biki kam sam barka amma fa Fatima tasha habaici wajen inna Asabe da k'awayenta har ma da zainabu da k'awayenta dare nayi aka kai amarya gidan mijinta da zummar sati d'aya zasu yi su tafi Lagos sai mu ce Allah ya bada zaman lafiya ya kad'e fitina amin .
Lokaci nata tafiya bayan anyi biki amarya su ka tf da mijinta Lagos , a haka lokaci ke ta tafiya , cike da k'alubalen rayuwa a yanzu shekara d'aya kenan da bikin zainabu da Ado , a yayin da Fatima take cikin tsaka mai wuya , cin zarafi ,kyara , habaici, duka , zagin cin mutunci, ba Wanda bata fuskanta ba daga mahaifiyar ta ta inna Asabe, ga wani cin zarafi da y'an k'auyen keyi mata , duk inda suka ganta zancensu d'aya tak'i aure , wasu ma har cewa sukeyi tana zaman karuwanci ne kawai ganin mahaifinta baya duniya , dama dai sauran maganganu barkatai , haka take d'auke kanta daga wad'annan habaice habaicen wani zubin inna Asabe da k'awayenta ne zasu taru a gidan su ci mata mutunci son ranta, ga aikatau iri iri bata hutawa , ita kuwa inna Asabe taci mai kyau tasha mai kyau ba abinda ya dame ta saboda y'arta tana aiko mata da abin duniya , Fatima kuwa sai tayi sa'a sannan ta samu abinci taci say d'aya a rana , kuma duk wannan halin tsananin da take ciki bata tab'a tarar kowa ta fad'a mishi ba , gashi samari yanzun basa zuwa wajenta mutane suka dinga tunanin ko shafar aljanu ce , ko kuma dan ta huce mizanin y'an matantaka a k'auyen , abinda basu sani ba inna Asabe ce tayi asirin da ba Wanda zaiji yana Sonta kaf garin , tun abin baya damun Fatima har ya dawo yana damunta , in ta zauna ba abinda take tunawa sai rayuwarta da mahaifinta da kuma labarin mahaifiyarta Wanda mahaifinta ya bata , sai dai taci kukanta babu mai rarrashinta, abin d'aya ta k'udurta a zuciyarta Wanda idan tana tunawa takan samu sa'ida a zuciyarta , shine yake sanyawa ta k'ara nutsuwa , na cewar bashakka ko ba dad'e ko ba jima zata nemo asalin dangin mahaifiyarta ,wannan yakan sanya taji dad'i sosai a ranta.
🌹🌹🌸🌸🌹🌹🌸🌸
A yau Asabar tun safe ta tashi ta kama kiciniyar aiki sosai takeyin aiki sakamakon