hajiyarsa zama , hakan ya sanya ya amince da hakan , zancen gwaggonsa ta masa tace wallahi zanje gaidata aiki yamin yawa amma zan kirata, sallama yayi mata had'e da alk'awarin kawo mata fatiman.
Sai k'arfe takwas lokacin ya dawo daga fitar da yayi , yasan bazai samu abinci ba hakan ya sanya yayi take away yayiwa mutanen gidan ma , Fatima ya fara kaiwa sannan ya mata zancen zata koma wajen mahaifiyarsa dad'i sosai taji hakan ya mishi dad'i sosai dan haka ya haura zuwa sama, direct d'akinsa ya nufa ko takan Laila bai bi ba ya gama abubuwan daya saba yi ya kwanta bacci ranshi ba dad'i.
A b'angaren Laila ma hakan ce ta kasance tayi bacci marar dad'i ......
Please
Share
&
Comments
To be continue.....
🌿🌿🌿Nussad🌿🌿🌿
🌸🌹KISHIYAR UWA🌹🌸
(True life story)
🍁Daga Alk'akamin Nussad🌸
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/
*```We are the moonlight writers we shine all over the world.``🌍`* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~
BARKA DA SALLAH FAN'S, FATAN ANYI SALLAH LAFIYA, ALLAH YA MAIMAITA MANA AMIN.
KAMAR YADDA NA ALK'AWARTA MUKU CEWAR ZANCI GABA DA RUBUTU NA , INSHA ALLAHU GASHI NA CIKA ALK'AWARI NA.
SHAFI NA 21_22
A b'angaren Fatima kuwa , ta yi bacci ne mai dad'i cike da walwala kasancewar Allah ya yaye mata zaman gidan , matar gidan sam bata da hali mai kyau , a haka har bacci ya yi awon gaba da ita.
Washe gari karfe shida na safe har ta shiyar tana zaman jiranshi a falo, ganin zaman bazai yi mata ba ya sanya ta fita falon gidan , kicin ta lek'a ta tarar da kukun gidan tana dafa Karin kumallon safe , gaisawa suka yi da yake ita kukun na da sauk'in kai cikin k'ank'anin lokaci ta ya ta suka had'a abincin , kunun tsamiya suka yi da kosai sai farfesun kayan ciki sai shi mai gidan da ake dafawa shayi , komai suka jera shi a dinning table , komawa suka yi kicin suka cigaba da hira, sosai kukun mai suna Aisha taji dad'in hira da Fatima duk kuwa da k'ank'antar shekarunta.
Alhaji Ahmad ne ya fara tashi sakamakon k'arar wayarsa da ta tashe shi , mahaifiyarsa ce da sauri ya d'aga suka shiga gaisawa , bayan ta jaddada masa cewar lallai ya tabbatar ya kawo mata Fatima a yau , amsawa yayi da to , suka yi sallama , da sauri ya Shiga toilet yayi wanka , kasancewar yayi sallar asubah , k'asa ya nufa a tare ya ga Aisha da Fatima suna hira a tare suka had'a baki burin cewar " yallab'ai ina kwana " amsawa yayi sannan ya nufi dinning area sosai yaci abinci , sannan ya yiwa Fatima nuni da ta taso su tafi , Aisha bataji dad'in tafiyar Fatima ba , ita kuwa Fatima taso yiwa aunty LAILA sallama , amma da taga ba fuska sai ta hak'ura , haka suka fita daga gidan suka nufi gidansu Ahmad .
Fatima bata ga wani nisa tsakaninsu ba, a bakin gate su ka yi horn gate man ya zo ya bud'e musu alkhairi Ahmad ya mishi kamar yadda ya saba sannan suka shiga.
A falo suka tarar da hajiya zaune da fara'arta ta tarbesu , Ahmad ne ya fad'a kan k'afar hajiya ya soma yi mata shagwab'a wai ta tasheshi yana bacci sosai suka burge Fatima , yayin da hajiya sai lallashin shi takeyi ," ah daughter k'araso mana , kika tsaya anan " , duk da Fatima bata san abin da ake nufi da " daughter " amma tasan ita ake yiwa magana k'arasawa tayi ta gaida hajiya , bayan sun huta hajiya da kanta ta raka Fatima har d'akin da zata zauna , sosai d'akin ya burge Fatima a ranta, sai da hajiyan Ahmad ta gama nuna mata ko'ina na gidan sannan su ka koma falo suka cigaba da hira, tun Fatima bata magana har ta dawo tana sanya musu baki .
A chan b'angaren LAILA kuwa duk a zatonta Ahmad zai zo ya lallashe ta kamar yadda ya saba amma taji shiru toh me hakan yake nufi kasa jurewa tayi ta sauka k'asa , babu kowa a falon sai motsin da taji a kicin hakan ya sanya ta nufi kicin din , Aisha ta tarar tana goge gogen kan gas , da sauri ta tsugunna har k'asa ta gaida LAILA , bata amsa ba sai ma tambaya da ta hurga mata " Ahmad ya fita ne, ta fad'a tana kallonta da jiran ganin ta bata amsa " , eh sun fita, shi da k'anwarsa " wani zabura tayi " sun fita fa kika ce "? " eh , kawai ta fad'a ta juya taci gaba da aikinta " , zagaye LAILA ta shiga yi da taga bazaiyi mata ba sai ta haye sama ta fara rusa ihu , daga ta d'auki wayarta lalubar numbersa ta shiga yi bai d'aga ba , wayar mummynta ta shiga kira amma bata shiga ba , kawai sai ta fad'a kan gado ta rushe da kuka.
A chan b'angaren su Fatima kuwa , sosai suka yi hira anan ta fuskanci shak'uwa mai tsanani , a tsakanin hajiya ta d'an tilon d'an nata, Ahmad kuwa ganin da yayi Fatima ta saki jikinta da hajiyarsa hakan ya mishi dad'i sosai , bashi ya bar gidan ba sai bayan sallar la'asar kasancewar ranar Asabar ne , hakan ya sanya bai koma gida ba ya wuce asibitin DR Sadeeq , sosai sukayi hira sai bayan sallar isha'i sannan ya nufi gida , bai bi takan LAILA ba kawai yayi kwanciyarsa yayi bacci , shirun da LAILA taji yayi yawa ne ya sanya ta lek'a ta window, tabbas ya dawo , zaman jiranshi ta zauna yi , har 1 bai shiga d'akin ba , kawai sai ta sauka daga gadon ta nufi d'akinsa , handle din k'ofar ta murd'a amma a rufe gam, ita fa Ahmad ya sauya mata , bai tab'a yi mata irin wannan cin kashin ba sai yanzu da ya samo kilaki, ni kuwa nace au baki daddara ba ko LAILA, saura kad'an ta jiyoni ni kuwa na fece a miliyan😝.
A ranar ma bacci marar dad'i tayi.
Sosai rayuwar gidan yallab'ai Ahmad ta sauya babu walwala tsakanin ma'auratan kasancewar LAILA tayi fushin ta sauka amma Ahmad ya nuna baisan tana yi ba , kasancewar mai hak'uri bai iya fushi ba , yayin da a b'angaren Fatima kuwa sosai rayuwarta ta sauya tayi fresh tayi kyau , sai Sam barka , a yanzu ma hajiya shirye shiryen kai ta makaranta take yi abin gwanin burgewa .
Shin wai wanene yallab'ai Ahmad ,kuwa wacece LAILA, ya ya akayi suka had'u ?
OPPHHH DAN ALLAH AYI MANAGE DA WANNAN JIKI DA JINI SAI A HANKALI.
GAISUWAR BARKA DA SALLAH GAREKU DUK MASOYANA DA KUMA MASOYAN KISHIYAR UWA 🥰🥰
DAN ALLAH A DINGA YIMIN SHARE NA BOOK DIN NAN 👏🏻👏🏻👏🏻
Please
Share
&
Comments
To be continue..............
🌿🌿🌿NUSSAD🌿🌿🌿
🌸🌹KISHIYAR UWA🌹🌸
(True life story)
🍁Daga Alk'alamin Nussad🌸
" :; ' ". ; .
' :
"
DAN ALLAH NAJI K'ORAFINKU KUYI HAK'URI WALLAHI BANDA TIME , A YANZU INA BUSY AMMA INSHA ALLAHU ZANYI K'OK'ARIN GANIN NAYI MUKU YADDA KUKESO.
INA GODIYA BISA GA NUNA KULAWARKU DA KUKE A GARENI , INA JIN DADI SOSAI , ALLAH YA BIYAKU , AMIN.🥰
SHAFI NA 23-24
Ahmad Muhammad Ahmad , haifaffen garin kaduna ne , a unguwar kawo , mahaifinsa Alhaji Muhammad shahararren d'an kasuwa ne, mahaifiyarsa hajiya Amina ita kuma haifaffiyar garin Zaria ,mahaifiyar Ahmad sun had'u ne ata dalilin bikin abokinsa da akayi anan ne suka had'u sosai ya yaba da halinta , aka sasanta har Allah ya sanya akayi aure , hajiya amina su biyu ne kachal Allah ya basu daga hajiya amina sai k'anwarta Maimunatu , a lokacin da hajiya Amina tayi aure taso tafiya da k'anwarta maimunatu , saboda halin rashi da iyayensu su ke fama amma mahaifan nasu suka k'ek'asa k'asa , suka hana ta tafiya da ita .
Shekararta d'aya Allah ya azurta ta da samun haihuwa ta haifi jaririn d'anta namiji Wanda yaci sunan Ahmad, sosai ake nunawa jariri gata da soyayya , musamman Maimunatu k'anwar hajiyan, Ahmad ya tashi cikin gata , shekarar goma a lokacin ya gama primary zai tafi secondary akayi auren k'anwar hajiya wato Maimunatu , aka kaita garin kano, sosai basu ji dad'in rabuwa da juna ba amma ba yadda suka iya, haka suka hak'ura.
Ajin Ahmad biyu a secondary , Allah ya azurta Maimunatu k'anwar mahaifiyarsa da samun k'aruwar yarinya mace hakan yayi masa dad'i sosai ganin cewar dama bai tab'a zuwa gidan gwaggon ta sa ba, amma kash lokacin yazo musu ana dab da fara jarabawa , haka ya hak'ura , ya gama makarantar secondary da kwali mai kyau , a lokacin business din mahaifinsa ya bunk'asa dan har k'asar waje yake fita , a haka Ahmad ya fara makaranta , toh a wannan lokacin Allah ya had'a shi da LAILA, y'ar gidan Alhaji Abbas mai dollar , tunda LAILA ta d'ora idanunta akan na Ahmad , taji ta kamu da sonsa, tun baya lura da ita har sai da tasan yadda akayi ta cusa masa soyayyarta a zuciyarsa , sunyi soyayya sosai , a lokacin da iyayensu suka sani abin ya musu dad'i sosai ganin ko wanne a cikin yaran nasu daga babban gida ya fito , a wannan lokacin kuma Ahmad ya tafi bautar k'asa a wani k'auye a kano cikin k'aramar hukumar takai , bayan ya gama bautar k'asarsa ne aka d'aura musu aure kuma ya tafi da LAILA k'asar wajen domin k'aro karatun na sa, a farkon aurensu sosai LAILA takeyi mishi biyayya , sun zuba soyayya amma daga baya kuma sai abin ya chanza salo rashin mutunci sosai ta farayi masa , ya rasa gane kanta , a iya saninsa LAILANSA bata da mugun hali amma ya akayi ta fara nuna masa wani hali na daban, babbar matsalarsa guda d'aya itace ta rashin haihuwa , da farko ya zaci yana da matsala amma da akayi masa bincike aka gano ai lafiyarsa k'alau , yayi nacin duniya LAILA taje a duba ta amma tace ita ba inda zataje ai haihuwa ta Allah ce, baisan da gangan LAILA take shan magungunan hana d'aukar ciki ba , bayan tabi shawarar k'awayenta , su Aliya fire, lokacin da ta sanar dasu tana da ciki suka ingizata ta zubar da shi a cewar su wai zata tsofe da wuri , tun daga nan take amfani da maganin hana d'aukar ciki , Allah sarki ko shi Ahmad d'in baima San tayi cikin ba kuma an b'arar masa da abinda yake nema ido rufe, a haka suka yi shekarun da zasu yi su ka dawo Nigeria , ko da suka dawo yaso su zauna a gidansu amma tace ita za'a takura mata , haka bada yaso ba ya gina musu gida , a wannan shekarar da su ka dawo , Allah ya yiwa mahaifin Ahmad rasuwa sunji rasuwar ba kad'an ba amma daga baya su ka hak'ura suka dangana , su ka ci gaba da rayuwa ,Ahmad kuma ya ci gaba da kula da kamfanin nikan da mahaifinsa ya rasu ya bar masa.
CIGABAN LABARI.
Ranar litinin da wurwuri Fatima ta shirya , domin tun dare hajiya ta sanar da ita cewar da safe , yayanta zaizo ya kaita makaranta , dan haka kafin k'arfe bakwai ta gama shirinta tsaf , tana jiransa , a bakin k'ofar falo su ka yi kicib'us lokacin ya shigo ita kuma zata fita , da sauri ta dafe k'irjinta tsabar tsoro dan bata zata shi bane ba, " yallab'ai ina kwana , ta fad'a tana dubansa ", shi kuwa lulawa yayi chan duniyar tunani , ya'akayi yarinyar nan ta girma , to kwata2 kwana nawa rabona da ita , ko da yake dama wahala ce kuma tana sanya haka, " yallab'ai fa ina gaisheka ," sai a sannan ya farga sannan ya amsa , tambayarta yayi ina hajiya ta fad'a masa tana cikin d'aki , juyawa yayi yana tunanin girman da Fatima tayi a k'ank'anin lokaci, gashi kayan makarantar sun amsheta gaba ki d'aya kayan maroon colour ne amma rigar tasu mai gida gidan bak'i a jikinta , kuma hijjabin d'an karamine dan da kad'a ya haura k'asa k'irjinta,da sallama a bakinsa , sun gaisa da hajiya , ya fad'a mata zasu wuce makaranta zai kai Fatima, sosai ta musu addu'ah sannan su ka fita daga cikin gidan bayan sunyi sallama da Fatima, toh a hanya sosai su ka yi hira , har ya dinga mata tambayoyi tana bashi amsa daidai ," am ni kuwa Fatima har yau bansan labarinki cikakke ba , ko za'a taimaka a bani nasha", ya tambaya yana murmushi , sosai ta shagala da kallonsa, har sai da ya juyo ya kalleta sannan ta sunkuyar da kai tana murmushi, shima murmushin yayi , dab da sun k'ara bakin gate d'in makarantar , anyi mata cike cike da komai na sabon d'alibi , sannan aka bata aji , shi kuma Ahmad ya tafi wajen aiki.
Koda aka kai ta a desk din da aka ajiye ta su biyu ne," sannu ta cikin bencin ta fad'a", " yauwa sannu" ," suna na Halima Nasir, nice too meet you", ni kuma suna na Fatima Iliyas ", murmushi ta mata sosai suka yi hira , a rana ta farko su ka shak'u ko da aka tashi , Halima taso su kai Fatima gida kasancewar yallab'ai Ahmad bai zo ba amma Fatima ta sanar mata yayanta zaizo d'aukarta, ilai kuwa suna tsaye ya k'araso sallama sukayi kowa ya nufi wajen Wanda yazo d'aukarsa , a hanya sosai Fatima ta saki jikinta da Ahmad ta dinga bashi labarin makarantar da sabuwar k'awarta da tayi, shi kuwa ba abinda yakeyi sai murmushi, " to kince zaki bani labarinki ko ba yanzu ba", " zan baka amma abinda zan iya cewa , akwai sark'ak'iya cikin labarina, ka bari in mun samu lokaci ba school, kazo ni kuma zan baka labarina ", murmushi ya sake yi , a daidai nan su ka k'arasa bakin gate d'in gidan , sun shiga cikin ko gama parkinga bai yi ba ta fita da gudu ta nufi falo da sallama ta k'arasa a lokacin shi kuma ya kunno kai , a cinyar hajiya ta zauna , "wash sai kin karyani , cewar hajiya da take k'ok'arin d'aga ta daga kan cinyarta ", shagwab'e fuska tayi ta turo d'an k'aramin bakinta waje , Ahmad dake tsaye zuba mata idanu yayi abin kawai ya burgeshi , lallai wannan yarinyar shagwab'ab'b'iya ce , hajiya ta mishi magana , firgigit ya dawo daga tunanin da ya tafi , gaisawa su ka k'arayi , a yayin da Fatima tace" mummy wallahi makarantar akwai dad'i sosai bari nayi wanka nazo na baki labari "," to kiyi Sauri ina jiranki, shi kuwa Ahmad rakata yayi da idanu har ta shige d'akinta.
Bayan tayi wanka tayi sallah ta fito ciki Riga doguwa sai siririn hannu , kalar ruwan hoda , rigar ba ta da nauyi , tayi parkinga gashinta da ribom shi ma pink , a kusa da mummy ta zauna ta shagwab'e fuska , ni kuwa nace su Fatima an samu abinda akeso ko da da kike hannu Inna Asabe anayi oho, " mummy yunwa nake ji wallahi", tashi maza kije kici abinci kinsan bana San kina zama da yunwa ", tashi tayi ta nufi dinning area , yayin da Ahmad ya rakata da idanu , ya rasa abinda ke faruwa dashi komai yarinyar tayi abun birgewa ne, " tana da kyau abinda yace kenan ya kautar da kansa gefe guda", da sauri ta nufi wajen zama ta zauna abinci taci sosai sannan ta koma su ka ci gaba da hira , Ahmad bashi ya bar gidan ba sai bayan sallar isha'i.
A b'angaren LAILA kuwa, sosai duniya ta dawo mata sabuwa, saboda sun shirya da Ahmad yadda ya kamata, kuma a nata tunanin ai Ahmad ya mayar da Fatima garinsu , batasan su na tare da mahaifiyarsa ba kasancewar ita d'in ba mai son zuwa gidan sirikarta ta bace ba, sosai hankalinta ya kwanta , takecin Karen ta babu babbaka , hmmmmm hajiya LAILA muje zuwa , mata a gidan Alhaji Ahmad.
A b'angaren Fatima kuwa, sosai ta ke karatun ta cikin hazak'a , kuma halinsu yazo d'aya da Halima, dan a waje d'aya suka bambanta da juna shine , ita Fatima miskilace , while Halima kuma na da surutu da yawa, jarabawar farko , Fatima ta d'auki first class , Halima kuma second class, sosai yallab'ai Ahmad ya ji dad'in haka , yasan kuma ba asarar kud'insa yakeyi a banza ba, kyauta ta musammam yayi mata , kuma had'a mata da waya k'irar IPhone 11 pro, murna sosai tayi , da wannan kyauta bayan sun samu hutu Fatima ta tambayi hajiya kan tanasan taje gidansu Halima , hajiya a barta , ta kuma fad'awa driver ya kaita , sosai su ka yi murna da ganin juna, har k'arfe bakwai , sannan ta koma gida bayan mahaifiyar Halima ta bata kyauta da kyar su ka rasu, ko da ta isa gidan , a falo ta tarar da hajiya da yallab'ai , sannu da gida ta musu sannan ta nunawa hajiya kyautar da mamansu Halima ta mata, ran Ahmad ne ya b'aci au dama fita take yi any how any time , sai da ya bari bari hajiya ta tafi d'akinta sallah , sannan ya kutsa kansa d'akin Fatima a lokacin ta idar da sallar isha'i kenan , fuskarsa babu walwala, " ke dama yawo like zuwa, ya tsare ta da idanu yana jiran amsarta ", sosai ta tsorata , dan haka cikin rawar murya tace" am...am..ba.. ba haka bane ba , wallahi..... ba ta k'arasa ba ya katse ta " kar na k'ara ganin k'afarki a waje kin tafi yawo kinji na fad'a miki ", sannan ya juya ya fita, saboda ranshi ya b'aci ko sallama bai yiwa hajiya ba fice daga gidan ya nufi gidansa, ita kuwa Fatima zama tayi ta fashe da kuka sai da ta yi mai isarta sannan ta yi shirin kwanciya bacci , shi kuwa ko