, amma shiru , lokacin da iyayen ango su ka zo aka Sanar da su , sosai hankalin ango ya tashi na b'atan amarya Fatima , aka yi nema aka gaji hakan ya sanya aka hak'ura da d'aurin auren aka ba ri sai an ganta tukunna , zancen fa ya cika k'auyen Darki na cewa Fatima ta gudu, wad'ansu na cewar dama bariki ta ke yi shi ya sanya zaman k'auyen ba zai yi mata ba dole ta shiga duniya , haka dai aka hak'ura duk da cewar y'an uwan marigayi malam Iliya sun koka na rashin Fatima amma suka hak'ura, wannan kenan.
KADUNA STATE
Lokacin da Ahmad ya isa k'ofar falon , thumb print ya danna , aikuwa a take k'ofar ta bud'e , shiga yayi da sallama , masha Allahu wani tangamemen falo ya bayyana , ga sanyi Ac da ya gauraye wajen , a d'aya daga cikin kujerun d'akin , wayar shi ya d'aga ya k'ira daga chan aka d'aga "haba habibty gani fa na dawo ina falon k'asa , kuma wallahi na gaji ," daga chan b'angaren aka yi magana , ban san me a kace ba na ga ya b'ata fuska , ya kashe wayar , kai shi ya zai yi wajen ba dad'i cikin gida ma haka , "Allah ka duba lamari na, ya fad'a yana duba k'afar bene , wata mata ce take saukowa daga ganinta kasan hutu ya ratsa ta akalla ba za ta wuce Ashirin da bakwai ba a duniya , sosai tayi kyau ba k'arya , ba ta da tsayi sosai amma fara ce , anyi mata kitson attach ya zubo har kafad'a , daga ganinta kasan idanunta sun bud'e da duniya, ' LAILA ' kenan uwargida wajen Ahmad , " haba Laila kina sa ne da cewar jiya mu ka yi zan dawo ai kya kirani ki ji me ya tsayar da ni amma kika yi ignoring nawa, kamar ba mijinki ba haba Laila, ya fad'a yana dubanta ", tab'e bakinta tayi " haba my luv ka san dai nima banda time ko saboda ka ga nima na fita aiki , " kallonta kawai yayi ya girgiza kai ya rasa meyasa kwata kwata LAILA bata damu dashi ba yana matsayin mijinta , ganin ba za ta tambayeshi meya faru ba ya sanya ya fara fad'a mata abin da ya faru da shi , "uhmmm Allah ya kiyaye" kawai ta ce sannan ta juya ta fita a d'akin , girgiza kanshi yayi sannan ya tashi ya shiga band'aki , wanka yayi sannan ya shirya yana fitowa falo wayar shi tayi k'ara dubawa yayi ya ga Dr Sadeeq ne ya kira dan haka ya d'aga cikin hanzari , sallama yayi , aka amsa tachan d'aya b'angaren ," ok to gani nan zuwa , kawai ya fad'a ya nufi saman d'akin LAILA , ya na bud'a d'akin ya hango ta akan bed tana charting, sallama yayi mata bata amsa ba , kawai ta d'aga mishi kai , juya wa yayi ya fita had'e da girgiza kansa , harabar gidan ya nufa sanye da yadi d'an Abba kalar sky blue da hula zanna bak'a , da sauri direba ya taso, girgiza masa kansa yayi alamar ba tare zaku fita ba hakan ya sanya ya koma kan bencin baba mai gadi , shi kuma ya nufi motarsa , shiga yayi , ya kunna , baba me gadi ya wangale masa bakin gate ya cinna hancinta wajen gidan ya nufi titi .
ASIBITI
Da sauri ya k'arasa asibitin , a bakin office ya had'u da Dr Sadeeq yana k'ok'arin fita domin komawa d'akin da Fatima ta ke , " ah mutumin ya haka tun d'azu na kiraka amma sai yanzu , ko dai madam ta rik'e ka ne , ya fad'a had'e mik'a masa hannu domin suyi musabaha" , shi dai Ahmad bai ce k'ala ba , suka juya suka nufi d'akin Fatima, a lokacin ta farka har nurses sun taimaka mata tayi wanka tayi sallah , da sallama suka shiga amsawa tayi had'e da kallon k'ofa , Dr Sadeeq ne ya fara k'arasawa cikin d'akin had'e da zolayar ta ah lallai kin warke irin wannan kwalliya haka , ya fad'a ya nunawa Ahmad wajen zama Wanda ya kafe a tsaye yana kallon yarinyar da ya kad'e , kyakykyawa ce ya fad'a a ransa , zama yayi , doctor ya gabatar da shi a wajen Fatima , gaisar dashi tayi cikin murya mai sanyi amsawa yayi, kuma bai d'auke idonsa daga kanta ba , shi dai yana yiwa yarinyar nan kallon sani , " ya sunanki ya fad'a yana dubanta ", Fatima " abin da tace kenan ta juya suka cigaba da hirarsu da doctor jefi jefi yake sanya musu baki , ya dad'e sosai daga bisani ya nufi gida bayan yayi mata sallama ya tafi ita kuma ta kwanta saboda har lokacin bata dawo daidai ba.
Sai da Fatima ta kwana kusan bakwai ta warke garau , amma ba ta tab'a fad'awa kowa maganar y'an uwanta ba , a nashi b'angaren Ahmad yayi tunanin ya tambaye ta ko dan ya mai da ta danginta amma ganin cewar ba ta da lafiya ya sanya sai a yau ya tare ta da zancen dangin na ta , bata b'oye masa komai ba dan tana ganin kamar wannan wata mafaka ta samu ko Allah zai sanya ya taimaka mata ta wani fannin ganin cewar yana da tausayi , jin labarinta ya sanya yayi alk'awarin cewar zai tafi da ita cikin danginshi kafin ya san me zai yi akai .
Satin Fatima biyu Dr Sadeeq ya ba ta sallama , har bakin mota Dr ya raka su , sannan ya koma su kuma suka fita daga cikin asibitin zuwa gida Alhaji Ahmad.........
Please
Share
&
Comments
To be continue...........
DAN ALLAH AYI HAK'URI DA WANNAN SABODA NA GAJI .
SAI ALLAH YA KAIMU WANI SATIN ZAN K'ARAYIN TYPING , LUV U FAN'S🥰🥰
🌿🌿🌿NUSSAD🌿🌿🌿
🌸🌹KISHIYAR UWA🌹🌸
(True life story)
🍁Daga Alk'alamin Nussad🌸
NA SADAUKAR DA LITTAFINA NA KISHIYAR UWA GA, PHAREEDA , INAJIN DAD'IN COMMENTS D'INKI SOSAI DA SOSAI, ALLAH YA BIYAKI.🥰
SHAFI NA 19_20
Ko da suka k'arasa cikin unguwar , tun daga bakin layin Fatima ke rarraba idanu , " oh ni Fatima na kawo kaina ga mahallaka , yanzu ace ni zanyi rayuwa anan , anya ma kuwa ba d'an mafiya na biyo ba , innalillahi wa'inna ilaihir raji'un , shikenan tawa ta k'are , duk abinda take fad'a tana fad'ar shi ne a cikin zuciyarta" , a take tayi dana sanin gudowarta daga k'auye , dama ta tsaya an d'aura mata auren da bilya da wannan yawon gashi bata ga tsuntsu bata ga tarko, shikenan a banza a wofi wasu mutanen zasu cinye ta , garin lalubar dangin mahaifiyarta ta b'ige da zuwa mahallakarta madadin ta ganta a zariya sai gata a Kaduna , ta shiga zurfin tunani da tashin hankali ta yadda har su ka iso k'ofar gidan mai gadin gidan ya bud'e suka shiga bata sani ba .
Cikin sexy voice nashi ya kira sunanta "Fatima" har sai da ya kira sau uku ana hud'un ne tayi firgigit ta farka daga mummunan tunanin da take yi , kallon gefen da ake magana tayi shine dai a tsaye yana kallon ta da tuhumar abinda take tunani , "sauko , yace da ita " a hankali ta sauko da k'afafunta kasa ta fito daga motar , kallon gidan da suka shigo ai da hanzarinta tayi hanyar bakin gate , gudu takeyi ba k'ak'k'autawa , shikenan ita kam k'arshenta a duniya ya zo , sai a sannan hawaye ya fara zubar mata a ido , da Sauri ya bi bayanta domin sanin meke faruwa, har ta kai bakin gate din gidan bata tsaya ba , ja tayi ta tsaya turus sakamakon tashin sanin ta ina zata fita , shima tsayawa yayi yana kallon ta , da mamaki fal a fuskarsa , to kodai hatsarin da ya faru da yarinyar nan ko dai ta samu matsalar k'wak'walwa ne, gabansa ne ya fad'i yayi saurin kawar da zancen daga cikin zuciyarshi , to ko kuma Aljanu gare ta , ah to ba mamaki ma aljanunne, ni kuwa nace to fa su malam Ahmad wata kam aljanu sune masu laifi ba kai ba🥴, k'arasawa yayi a hankali ya kamo hannunta ya jata zuwa har bakin falon gidan , thumb print yayi wa k'ofar aikuwa ta bud'e , shiga suka yi ciki , wani tsoro ne ya k'ara shiga zuciyarta, ita fa gaskiya mutumin nan tsoro yake bata , ga uban gida kamar ba'a duniya ba , inama ya kasance mafarki take yi ba gaskiya ita bazata zauna ba yana tafiya zata gudu, " to kuma idan kika gudu ina kika sani, zuciyarta ce ta bata wannan tambayar" , "babu , ta fad'a har sai da ya juyo " wajen zama ya nuna mata, sannan ya fad'a mata cewar bara ya haura sama ya yiwa matar gidan magana ta sauko su gaisa , sai ta bata wajen zama kafin komai ya tsagaita, " dama yana da aure , dama anayin aure idan mutum d'an mafiya ne kuma ya ajiye ta a gidan mafiya , anya ma ta sani kuwa, to kodai ita ma y'ar mafiyar ce , domin ita har yanzu bata yadda da cewar ba gidan mafiya ta ke ba , k'arar takalmi mai tsini taji na dukan tiles , hakan ya sanya ta kallon inda k'arar ta ke fitowa , wara idanunta tayi had'e da mutsitstsika su , "masha Allahu ta furta a hankali gaskiya matar gidan mai kyau ce ita ma ga gashinta har gadon baya , " ni kuwa nace lallai Fatima har yau kina da yarinta bakisan gashi natural ba bakisan na kanti ba , karasowa suka yi har falon hannunsu had'e da na juna , Ahmad ne ya kalli Laila wadda tayi kicin kicin da rai ganin an kawo mata budurwa gida ," Laila zauna mana yayi mata nuni da kusa da Fatima ," chab Allah ya kiyaye na zauna kusa da tsintacciyar mage " duk da Ahmad baiji dad'in yadda Laila tayi ba, amma yadda yaga Fatima tayi abin bai mata zafi ba ya sanya ya basar , magana ya soma yi takan Laila ya fara kasancewar ita ce babba " Laila ga y'ar uwa nan na kawo miki , ke kuma Fatima kinga wannan antinki ce banason tashin kunya duk da ba d'abi'ar ki bace ba, ki kula sosai , zaki dinga taya ta zama da hira kinga ko ba na nan , kinji ya tambaya ya na kallon fuskarta ," eh , kawai tace " ita kuwa Laila ranta in yayi dubu ya b'aci ta yaya za'ayi a kawo mata yarinya y'ar k'auye ace ta tayata zama amma Ahmad ma ya raina ta da ajinta da komai ya rasa wadda zata tayata hira sai bagidajiya , tsintacciyar mage, duban Ahmad tayi had'e da kallon ka raina min hankali ma wallahi , sarai ya gane me take , amma yayi banza da ita , gajiya tayi da zaman hakan ya sanya ta mik'e tsaye , tare da fad'in " in ka gama ina da abin yi , I can't stay and wasting my time about this rubbish, ta fad'a tana k'ok'arin tashi gyad'a kai kawai yayi saboda tsabar haushi domin bai ma san me zai ce mata ba, hayewa sama tayi ta barsu a wajen , Fatima batasan me Laila ta fad'a ba amma ta fuskanci bata maraba da zamanta a gidanta , ai taji dad'i ma da matar gidan bata so ta zauna , itama gwara haka, juyawa yayi ya kalleta " tashi muje na nuna miki masauki, abinda yace kenan ya yi gaba " ita kuma Fatima ta bishi a baya.
Sosai ya nuna mata yadda ake amfani da kayan band'akin kasancewar wasu ma ko ni bansan yadda ake amfani da su ba ballantana fatima🥴, bayan ya gama nuna mata komai sannan ya fita ya barta domin ta yi wanka, tunawa da yayi ba kaya a hannunta ya sanya da sauri ya fita ko d'an aike bai tsaya nema ba , ya hau mota ya tafi wani store na kusa domin samo mata kayan sawa domin a gurin hatsarin ta rasa kaya , dohayen riguna ya saya mata Arabian gown masu kyau , ko da ya dawo ta fita a wanka , ta sanya kayan ta da ta taho da shi , bata kayan ya yi ya mata umarni da cewar ta sanya ta fito ta ci abinci , bayan tayi sallah ta fita falo, a zaune ta tarar da shi a zaune a kujera ya dafe kansa , cikin sanyin muryarta ta masa sallama , d'agowa yayi masha Allahu kawai ya furta a cikin zuciyarshi " yarinya kamar balarabiya , " " me kace , ta fad'a, " a'a babu komai zauna kici abinci ga dinning chan ya nuna mata da hannu " cikin tafiyar k'asaita ta k'ara ta zauna a saman d'aya daga cikin kujerun , rasa yadda zatayi ta bud'e food flask din , juyowa tayi tana son yin magana ta kasa, ganin haka ya sanya ya gane me take nufi hakan ya sanya ya tashi yaje har kusa da ita ," matsa kawai yace " ta matsa ya bud'e mata yana k'ok'arin zuba mata a faratin , yayin da Laila tana k'ok'arin saukowa daga benen gidan , ihu da k'arfi ta sanya, ! Na shiga uku ni Laila me zan gani a gidana a kawomin karuwa , wallahi sai na kasheki yau , tab lallai ma," kanta tayo tana gurnani kamar zakanya tsabar rud'ewa Fatima batasan lokacin da ta k'ank'ame Ahmad ba wani yarrr yaji a cikin shi yana wannan yanayin bai san har Laila ta k'araso gurin k'ok'arin janyo ta Laila ta fara ita kuma tana k'ara k'ank'ame shi , hakan ya sanya Laila ta k'ara haukacewa , ta biyo Fatima ihun da ta saki ya fargar da Ahmad, hakan ya sanya yayi saurin maidata bayan shi Laila ta fad'o kanshi " wallahi bazan bazan yarda ba , haka kawai an kawomin yarinya tsintacciyar mace hakan ma bai isa ba sai anti karuwanci a gaba na kuma wallahi..... Ai bata k'arasa ba sakamakon gigitaccen Marin da Ahmad ya yi mata a fuska , abinda bai tab'ayi ba a iya zamansu na aure , ita kanta Laila sai da abin ya bata mamaki , tunda suke Ahmad ko da wasa bai tab'a sanya hannu a jikinta ba ko da ta sigar wasa ne , amma yanzu saboda wata bagidajiya , wawiya dabba ya sanya hannu har ya made ta , hakan ya k'ara mata tsabar Fatima a ranta ta yadda tana jin kamar ta kashe ta , lallai tunda daga zuwanta ta wargaza mata farin cikinta itama sai ta zauna cikin bakin ciki har iya rayuwarta a gidan dan da k'afarta zata gudu basai wani ya fitar da ita ba, da gudu ta haura sama fitar da batayi ba kenan ta shiga d'akinta ta hau rusar kuka.
A b'angaren Ahmad kuwa , dawo da Fatima yayi gabanshi , hawaye sosai ya gani akan idonta , cikin sanyin murya take magana" dan Allah yallab'ai ka taimaka ka barni na tafi , nasan dama zan kawo muku fitina a tsakaninku, shiru tayi sannan taci gaba , kaga kuna zaman zamanku zan wargaza muku farin ciki , daga zuwa na gwara ka barni na koma k'auye tunda yanzu rayuwa bata da amfani a gareni kuma.... Kuka ne yaci k'arfinta ta yadda ta kasa ko da motsa bakinta , shi kuwa shiru yayi yana kallonta kuma ya k'urawa d'an karamin bakinta ido ya gaza cewa komai , jiyayi kamar ya kamata ya rungume saboda rad'ad'in da yakeji na kukan da takeyi , yana yiwa Fatima kallon sani kuma yanayi mata kallon kanwarsa , amma to a ina yasan fuskar Fatima , tunani ya shiga yi gaskiya yasan fuskar amma ya manta , lallashinta yayi had'e da kwantar mata da hankali kuma ya shaida mata a hankali zai sanya a bincika mata dangin mahaifiyarta , haka da ya furta shi ya sanya ta yardarwa kanta da cewar zata ci gaba da zama a gidan har tsawon lokacin da za'a ga dangin mahaifiyarta , sai da ya tabbatar hankalinta ya kwanta sannan ya barta ta shiga d'akin shi kuma ya fita saboda b'acin rai , gaskiya dole ya san abinyi Laila ta sauya ba haka ya santa ba to me ya chanza ta ko dama haka take kawai dai dan tana sonshi ne ya sanya take bin umarninsa a baya , a haka ya k'arasa cikin mota ya kunna ya fice a gidan , Laila da ke bakin window tana kallon lokacin da Ahmad ya fita k'ara rushewa tayi da kuka, ta fad'a kan gadon d'akin tana k'udurtar yadda zatayi da rayuwar Fatima , tunani ta fara to tayaya zata yi mata illah , ta tambayi kanta , ni kuwa nace oho ke za'a tambaya😏.
Ko da Ahmad ya bar gida tafiya yayi ta ak'alla minti biyar kafin ya k'arasa inda zaije , a bakin wani tangamemen gida ya tsaya , da sauri aka bud'e gate din kasancewar gate man din yasan ko waye , gaisawa sukayi yayi masa alkhairin da ya saba sannan ya shiga ciki , gaskiya gidan ya had'u har yqfi nashi had'uwa , tun daga bakin k'ofar falon ya fara k'wala mata kira kamar k'aramin yaro " mummy , mummy , mummy! Da k'arfi yake fad'a wata mata dattijuwa ta fito daga cikin d'akin da yake hannun dama , "kai Ahmad wallahi baka girma , ta fad'a tana k'ok'arin zama a kan d'aya daga cikin kujerun d'akin ", gaisawa sukayi sosai ya kwashe komai da ya faru ya fad'a mata , " wai amma wannan yarinya bata kyauta ba , kaima kuma ka daina Marin mace hakan ba daidai bane ba , kaci gaba da hakuri , yauwa ita ina fatiman take tana cahn to in ba matsala ni ka kawomin ita zatafi jin dad'in zamanta anan ", ba'a son ranshi ba ya amsa da to ganin hajiyarsa ta nuna sah'awar zaman Fatima a gidan kuna batun haka shi kad'ai iyayensa suka haifa babu abokin taya